Showing 18001 words to 21000 words out of 50006 words

Chapter 7 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf

30 Mar 2025

6154

da inda
yarinyar ta kalla a matuƙar tsorace, a hankali ta ɗan ƙyallara idonta ta kalli inda idon yarinyar ke
kallo. Karaf! Idonta suka sauka kan Mu'awwaz da ke ta ma yarinyar signa da ido, da sauri
Saleema ta sake kallon yarinyar ta ga ta juya ta fita, taɓe baki kawai ta yi da tunanin wannan shi
ne abinda Mamanta ta faɗa cewa Mu'awwaz ya cika tsantseni, wato shigar da ke jikin yarinyar
ya ke ƙyamata? A karo na biyu sake taɓe baki ta yi ta ɗauki cokalinta za ta ci gaba da cin
abinci, Mu'awwaz ta ga ya miƙe ya na faɗin "Na ƙoshi."

Kallonshi amarya tayi tace "Bebe, ba ki ci sosai ba fa?"

Ba tare da ya ko kalleta ba ya kama hanyar fita ya na ɗaukar tuffa ɗaya yace "Ya isheni."

Da kallo Saleema ta bishi mamaki ya lulluɓe na tunanin wai su mutanen nan ba sa jin kunyar
kiran kowa Bebe ne? Haka matar Babansu ma take kiran ubansu Bebe, sai ka ce wani ɗan
goye.

Su Hadeeya ma miƙewa sukayi suka ce "Mu je mu shirya kar mu tsayar da Yaya."

Su uku ne suka nufi ɗakin su dan shiryawa, Saleema kuma da ta kalli Alhaji Auwal ne tace
"Abba, ya na ga yanzu gidan babu yara?"

Murmushi ya yi ya saki kallon amarya yace "To ai yaran da kika sani su ne suka girma yanzu,
ga Mu'awwaz nan kin gani ya zama saurayi, ga Ummee, Safwan ne kawai kuma ya na ƙasar
waje karatu."

Jinjina kai tayi kawai ta ɗan tsakurar abincin ta na jin duk ba daɗi sai ita kaɗai yanzu a cikin
iyayen, fitowar su Hameeda yasa ta juya dan ganin da wace shigar aka fito?

" A'uzubillah!" Ta fara ambata a ranta, dan kuwa a cikin shigar ta Hameeda ce kaɗai ta ga da
ɗan dama-dama, saboda ita ce ta sa doguwar riga irin na material ɗin da ake ɗingawa da
ɗan-kwalinta, ɗinkin ya bi jikinta yanda ya fito mata da surarta, kallabin kuma ta ɗorashi a kan
ne kawai amma ba ta ɗaure ba. Amma shigar Ummee abun ya munana sosai, dan riga da
wando ne da suka kamata, wandon ma irin wanda ya ɗan ɗage mata bai sauka ba sosai, sai
takalma dake ƙafarta ƙafa ciki, kanta kuma wata ƴar yaloluwar hula ce ta ɗora sai gashinta na
doki da ya bayyana.

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli fuskokin iyayen, dukansu fara'a ce a fuskarsu har da tagomashin
faɗa musu "Sai kun dawo."

Da gudu Hamdeeya ta tashi ta bi bayansu tana faɗin "Ni ma zan je."

Dariya Alhaji Auwal ya ƙyalƙyale da ita yace "Tafi a hankali to kar ki faɗi."

Suna fita ya ɗauki wayarshi ya turawa Mu'az saƙo cewa ya karɓi makullin morarshi hannun
dreba akwai kuɗi ciki sai su tafi.

Saleema da har yanzu ta kasa daina kallonsu da mamaki ne yasa ta ɗan numfasa, a ladabce
sosai cikin nutsuwa bayan ta aje cokalin hannunta tace "...



*Ku yi haƙuri da wannan.*



*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BAIWATA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ��
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️


_Bismillahir rahamanir rahim_


_9_

A ladabce sosai cikin nutsuwa bayan ta aje cokalin hannunta tace "Abba, ku yi haƙuri dan Allah
idan abinda zan faɗa zai ɓata muku rai..."

Da hannunta ta ɗanyi alama tace "Sai na ga kamar ba ku damu da yanda su ka fita ba kamar
dai yanda yanke faruwa a gidanmu, Abba a ganinku haka dai-dai garesu a matsayinsu na ƴaƴa
mata? Ina ganin kamar rufin asirinku da na su shine ku tayasu kare mutumcinsu..."

Ganin duk sun ƙura mata kamar mamakinta suke ko kuma dai wani abun sai ta tsagaita, ɗan
sake kallonsu tayi cike da kunya musamman ma amarya da ta ga kamar ta na mata kallon jin
haushi, sunkuyar da kanta tayi ƙasa tace" Ina ƙara baku haƙuri, na yi aiki da faɗar Manzon Allah
(S. A. W) ne, ya koya mana hani ga mummunan aiki idan ka na da iko, sannan ya faɗa mana
idan za ka iya ka hana da hannayenka, idan ba zaka iya ba da harshenka, idan ba zaka iya ba
ya ce to da zuciyarka, ma'ana ka ƙyamaci abun a zuciyarka, shiyasa na mu ku magana amma
ban yi da raini ko ɓata muku ba."

Mamar Ummee da take ganin kamar da ƴarta Ummee ne take, dan ita bata ga aibun shigar su
Hadeeya ba ma sam, cikin fushin da ta kasa ɓoyewa ta kalli Saleema tace" Kinga ƴan mata ki yi
abinda ya shafeki, bana son mutum mai shiga sabgar da babu ruwansa, ina aibun shigarsu a
nan? Yaranki ne mu da za ki zaunar da mu kina mana wannan maganganun? Oho! Idan na
fahimceki so ki ke ki ce mu ɗin ba mu san abinda ya dace ba sai ke."

Dogon tsaki ta ja ta miƙe tsaye tana ɗaukar wayarta ta juya ta bar wurin, da kallo Alhaji Auwal
ya bita kafin ya maido kallonshi kan Saleema da ba ta ji daɗi ba tace" Abba dan Allah ka bata
haƙuri, ita dama gaskiya ɗaci ne da ita, mafi alkairin mutane kuma shi ne wanda za'a faɗa ma
gaskiya ya ɗauka har ya yi anfani da ita."
Ajiyar zuciya ta sauke jiki a sanyaye ta miƙe tsaye ta kallesu tace" A ci lafiya."

Juyawa ta yi za ta fita a falon Hajia Rabi tace" Ina kuma za ki je?"

Juyowa tayi da fara'a tace" Zan fita waje ne."

Jinjina kai Alhaji Auwal ya yi yace" To, amma ki kula da kanki."

Ƴar dariya tayi tace" Ba ƙofar gida zan fita ba, iya farfajiya ne kawai."

A tare suka jinjina kai cike da jin ƙaunar yarinyar, in har suka ƙi abinda ta faɗa to ba su da wata
hujja ta ƙin ta, sannan ba ita su ka ƙi ba sai gaskiyar da ta faɗa, dan haka ma suka ji ta birgesu
duk da su ma ba su ga aibun shigar ta su ba sai yanzu ne da ta faɗa hotunan shigarsu ke dawo

musu a kai, musamman ma ta Ummee da ta fi munana.


*Ta na* fita a hankali ta shiga ɗan zagayawa ta na jin ina ma tana da waya da ta kira Mamanta,
amma sai ta yanke shawarar idan Hadeeya ta dawo za ta karɓi ta ta sai ta kira dan su gaisa,
saida ta kai ƙarshen katangar da a saninta nan ɗin bayan gida ne sai ta dakata saboda akwai
duhu wurin, juyawa ta yi da nufin ƙarasawa wajen motoci da ta ga akwai haske ta ko ina. Sai dai
kamar gizo kunnuwanta su ke jiyo mata abun da ya kayar mata da gaba duk da ba ta san me ye
ba? Amma dai ta shiga zulumi da ɗumbin mamakin wa ye haka? Me kuma ya same shi da yake
irin haka? Alhalin daga ji muryar ƙosasshen namiji ne.

Cikin sanɗa ta ɗan fara leƙa kanta, ba ta ga komai ba sai dai ta ɗan ƙara jin sautin kusa da ita,
tako ta yi da bai wuce uku zuwa huɗu ba ta sake leƙawa dan a tsorace take. Da bala'in sauri ta
rufe bakinta da tafin hannunta na hagu ta saki siririn numfashin da ya fitar da sauti kamar wacce
ta sha yaji, gaba ɗaya ta ƙwalalo idonta tsabar kaɗuwar da ta yi na ganin wannan lamari, take
jikinta ya ɗauki rawa tamkar mazari, da mugun gudu zuciyarta ta shiga bugawa, dan a
rayuwarta ba ta taɓa mummunan gani irin wannan ba na yau.

Tabbas ba ta tsiraicinsu ba saboda duhun da ke mamaye a wurin, sai dai hasken wata wanda
dama ɗaya ne a cikin dalilin da ya sa ubangiji ya saka mana shi dan ya haska mana abunda ya
shigarana duhu a yanar idonmu, ta hakane ta gane su waye a wurin da kuma abinda suke
aikatawa. Riskar yanayin da bai taɓa samu ba yasa su kansu suka tsorata sosai, yarinyar
durƙushewa ta yi ita kanta jikinta ya ɗauki ɓari, inda shi ma ya shiga kiciniyar saka wandonshi,
jikinta na makyarkyata ta juya da sauri sosai ta tunkari komawa inda ta fito, tana jin ya biyota
yana kiran "Sssaleema, Saleema dan Allah... Saleema dan Allah tsaya ki saurare ni, na roƙeki
S..."

Shigewar da ta yi falon da sauri ya sa dole ya ja birki ya tsaya ya na hangenta, ganin ta nufi
sama alamar masaukinsu za ta shiga ya sa ya daki iska yana buga ƙafarshi da mugun haushi
ya furta" Shiiiit!"

Dafe kanshi ya yi ɗaya hannun kuma ya riƙe ƙugu ya na safa da marwa a ƙofar ɗakin ya rasa
me zai yi, juyowar da zaiyi yarinyar ta taho har yanzu jikinta ɓari yake duk ta rufe fuskarta da
tsohon hijabinta alamar kuka take, saida ta zo kusa da shi ta durƙusa cikin kuka tace "Dan Allah
na roƙeka ka ƴantani hakanan, na gaji da wannan rayuwar, yanzu haka ni da mhaifiyata da ƴan
uwana muna samun abun da za mu ci dai-dai gwargwado."

A rikice Mu'awwaz ya zuba hannayenshi biyu cikin aljihu ya lalaba ya ciro kuɗi, miƙo mata yayi
cikin tashin hankali yace" Karɓi, daga yau kar na sake ganinki gidan nan, ki tafi kar ki sake
zuwa."

A razane ta ɗago ta kalleshi sannan ta kalli kuɗin, a ƙalla za ta iya jan jari da su, da haka za ta
tsira daga sharrinshi, karɓa ta yi ta miƙe tana faɗin" Nagode."

Juyawa ta yi za ta fice sai kuma ya canza shawara, da gudu ya tari gabanta yana faɗin" Kin ga!
Gobe ma ki dawo, saboda nasan halin Abba da sa ido a kan komai, idan ya ji ba ki zo ba zai sa
a bincika masa, ni kuma ina tsoron kar yarinyar can ta faɗa masa abinda ta gani."

Ƙasa ta yi da kanta alamar hukuncin nan bai mata ba, ita kam da ya barta ta tafiyarta shikenan,
amma ita kanta kunya ba za ta barta ta zo gobe ba, cikin taushin murya ya sake faɗin" Dan
Allah ki zo gobe kin ji, bana so Abba ya yi zargin wani abu aka miki."

Kallonshi ta sake yi irin kallon nan na da ke nuni ko dai wani abun za ka sake min? Kamar ya
fahimci kallon kuwa sai yace" Na rantse miki da Allah ba abinda zan miki, wallahi haka ba za ta
sake faruwa ba."

Fuska a gintse ta ɗaga kai alamar to, sannan ta raɓashi ta wuce ta bar gidan tana kuka na
takaicin yanda ta rasa mutumcinta dan kawai ta ciyar da ahalinta, yanzu gashi dalilin haka ba ta
san me zai faru ba a gaba.


*10:46* su Hadeeya suka dawo gidan, har sun fito daga motar Mu'az ya bi Hadeeya da wani
kallo yace "Ƙanwata zo ki ji."

Juyowa tayi ta na sakar masa fari da ido ta dawo ta zauna, ganin bata rufe ƙofar ba yasa shi
zura hannu ta gabanta kamar wanda zai taɓa mata ƙirji ya rufe ƙofar yana kallonta yace "Sirri za
mu yi."

Murmushi tayi ta sassauta murya tace "To Yayana ina jin ka."

Daf da ita ya matso sosai ya na wani kashe mata ido yace "Ki na da saurayi?"

Ɗan jim ta yi kafin ta kalleshi ta na ɗan lumshe idonta saboda kusancin ya yi yawa sosai tace
"Ina da, amma..."

"Amma me? Kina nufin ki ce Yayan na ki ba zai samu shiga ba?" Yanda ya yi maganar ya na
kamo hannunta yana matsawa ya sa ta kasa cewa komai sai rarraba ido take, sake matsowa ya
yi har numfashinsu ya fara gyauraya sannan yace "Uhumm! Ina jin ki."

Dake hakan bai taɓa faruwa da ita ba, duk yanda take samun kusanci da namiji ba ya wuce ƴar
gaisuwa da hannu ko dafa kafaɗar juna da dai irin haka, kaa cew komai ta yi, hakan yasa shi
sake faɗin " *Deeya*."

A hankali ta ɗan ɗago kanta da niyyar saka idonta cikin na shi ta faɗa masa wacece za ta ƙi
namiji kamar shi? Sai dai kafin ta gama ɗagowar ya yi wuf da bakinta ya sumbata.

Ɗuf! Hadeeya ta yi dan yau ta gamu da gamonta, zazzaro ido ta yi a tsorace sai dai ba ta yi
yunƙurin dakatar da shi ba, a hankali ya raba bakinshi da na ta yana kallon yanayin da ya jefata
alamar dai sabon shiga ce, sake kashe mata jiki yayi da faɗin "Ki na sona Deeya?"

Yanda ta yi kiskirim ta kasa motsawa ya sa shi sakin murmushi yace "Haba dai babbar yarinya,
ya ki ke abu kamar ba ki waye ba, kar ki badani mana."

Ƴar dariya yayi mai sauti ya jawo kanta gaba-ɗaya ya manna a ƙirjinshi yana shafa kanta yace
"Shikenan to ƙanwata, yanzu ki shiga ciki gobe da safe sai ki faɗa min shawarar da ki ka
yanke."

Ɗagata ya yi daga jikinshi ya buɗe mata ƙofar, jiki a mace ta fita kamar wacce aka ma dukan
tsiya, saida ya ga shigewarta ya jawo ƙofar ya rufe yana wani munafikin murmushi ta gefen
laɓɓa yana ayyana" Na san ma za ki amince, wannan tarkon ya fi ƙarfin tsallakewarki, da sannu
zan samu sabuwar babyn da za ta dinga ɗebe min kewa."
Dantse leɓɓenshi yayi yana jinjina kai sannan ya ja motar ya bar gidan, dan yau kam ba ya jin a
zai kwana a gidan, duk da ba mata yake nema ba, shi dai barshi da ƴan wasannin nan da
mace, dan a zaman da ya yi ƙasar waje ya koyi hakan, dan mutum ne mai ƙyamar hakan
kasancewarshi likitan da ya karanci mecece mace? Yana matuƙar jin ƙyamar shiga hurumin da
ba na shi ba, amma Hadeeya ya ga yarinya ce ɗanya shakaf, dan haka zai yi ƙoƙarin yi mata
wayo ya fara buɗe hanyar da kan shi kafin ya gama tantancewa ya samo matar da ta dace da
tsari da zubin yanayinshi da kuma tunaninshi. Duk da ya ga Ƴaƴar su Hadeeya ta ɗazu
(Saleema) ta na da irin ƙirar da yake so, wato kakkauran jiki da kuma manyan mazaunai har ma
da ƙirji, ama zai fara tabbatarwa kanshi wani bai fara kai ko da hannunshi a kan kayan ba kafin
ya sallama mata.

*Saida* tatabbatar su Hadeeya sun yi bacci sannan ta miƙe daga kwancin da ta yi tana ta
hango abunda idonta suka gane mata, ita a zahiri dai ba ta taɓa ganin kusancin mace da namiji
fiye da haka ba bayan na matar Babansu da shi Baban na su sai yau, ƙiri-ƙiri Allah ya nuna
mata Mu'awwaz da yarinyar da ba ta gama sanin me ye aikinta ba a gidan yana saduwa da ita a
tsaye, a tsayen ma a jikin bango bayan ba matarsa ba ce. Alwala ta ɗauro ta zo ta kabarta
sallah kamar yanda ta wa mamanta alƙawarin za ta ci gaba da addu'a dan Allah ya bata nasara
a kan jarabawar da sukayi, sau biyu kenan ta na rasa wannan jarabawar, idan ta sake faɗuwa
yanzu Hadeeya kuma ta yi nasara ba ta san me Abbanta zai mata ba.

Ƙarfe 02:30 na dare ta samu ta canza kayanta ta saka riga da wando na bacci sakakki sannan
ta nufi inda Hameeda take dan gadon ɗaya Hadeeya ce da Ummee, ta kwanta kenan za ta ɗan
ja bargo saboda sanyin acn ɗakin kawai ta ji an murɗa ƙofar alamar za'a shigo.

Zazzaro ido tayi mugun tsoro ya kamata da tunanin wa ye a wannan daren? Me ya zo ɗakin ƴan
matan a wannan lokacin? Ƙurawa ƙofar ido ta yi saida ta ga an buɗo da gaske dai ana shigowa
ta matsa da sauri ta haɗe a jikin bayan gadon ta kai hannu ta ɗan zungurar Hameeda dan ta

tashi. Dake da kanta ta kashe wutar ɗakin sai mai ƙaramin haske, hakan yasa ya na shigowa
suka haɗa ido, ai zabura ta yi tana neman durkowa a gadon tana faɗin "Kkk... Kai kuma?
Malam..."

"Shiiiiiiii!" Ya ɗora yatsarshi a laɓɓanshi alamar tayi shiru, ta kan Hameeda ta wuntsila ta sauka
a gadon tana sake nunoshi da yatsa tace "Ka ga malam ka fita a nan, ni ban ga komai ba kuma
ba wanda zan faɗa ma, idan ma kasheni ka zo yi to ka yi haƙuri."

Takawa ya ƙara yi har ya kai daf da gadon cikin raɗa yace "Saleema ki zo dan Allah za mu yi
magana, ba cutar da ke zan yi ba."

Da mamaki tace "Magana..." Da yatsa ya sake mata alamar "Shiiiii! Yi magana a hankali."

Sassauta murya tayi tace "Maganar me za mu yi a wannan lokacin? Ka ga ni ba zan saurareka
ba, kawai ka fita a nan wallahi ko na maka ihu."

Da sauri ya durƙusa ƙasa yace "Dan Allah Saleema kar kiyi, ki zo muje mu yi magana, iya nan
ƙofar ɗakina saboda bana so mu tashesu."

Ƙura masa ido tayi kamar mai nazari, amma sai yayi saurin katseta ta hanyar haɗe
hannayenshi alamar roƙo yace "Dan girman Allah Saleema?"

Da sauri ta ɗaga masa hannu tace "Shikenan to na ji, ka daina haɗani da ubangijina kan
ƙaramin abu."

Zagayowa tayi tace "Mu je to."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login