Showing 36001 words to 39000 words out of 50006 words

Chapter 13 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf

30 Mar 2025

6145


ko dai ban miki ba ne?"

Lumshe idonta tayi tana tantance ƙamshin me ye bakinshi ke fitarwa? Inibi ko tuffa? Take
sheɗan ya saka mata wani tunani cewa "To ai dan ya taɓani ba wani abu ba ne, wayewa ce
kawai, kuma da babu kyau ai da Mamanmu ba ta yi a gabanmu ba ita da Abbanmu, dan haka
ba komai ba ne, kuma ma ai so na yake shine zai aureni, dan haka ba komai a ciki."
Ta na gama wannan tunanin ta buɗe manya kuma fararen idonta ta sauke a cikin na shi, ba tare
da tunanin komai ba ta zubar da ajinta ta kai laɓɓanta a kan kumcinshi ta sumbata, sai bayan ta
yi ne kuma sheɗan ya bijiro mata da wata kunyar ƙara durmiyata halaka sai ta rufe ido da sauri
ta jaye jikinta ta ruga a guje. Da kallo ya bita bayan ya ɗora hannunshi inda ta sumbata ya saki
wani shaƙiyin murmushi, a zuciyarshi ya furta "Tukuna ma, sai ranar da kika fara tatso min
madarar da ke addabata da bakinki."

A hankali ya shiga takawa har ya isa inda bai tsammanin samun mutane, amma sai ya samu su
Saleema zaune suna aiki, Nafissa ce tace "Ina wuni Alhaji."

Ɗaga ido tayi ta kalli Nafissa cikin raɗa tace "Wai Alhaji, sun je makka ne?"

Ita ma Nafissa cikin raɗa tace "Ai har autan gidan nan ya je."

Taɓe baki tayi tace "Amm..." Zabura ta yi saboda sunkuyo kanshi da ya yi daf da wuyanta kamar
zai taɓata, ƙurawa juna ido sukayi Saleema na kallonshi cike da jin haushin wannan ɗabi'a ta

shi, murmushi ya sakar mata ya ƙyabta mata ido ɗaya yace "Ina sonki."

Raɓata ya yi ya wuce ta bishi da harara, tsaki ta ja sannan ta koma ta zauna, Nafissa kuma
dariya ta yi ganin yanda Saleema ke ta kumbura kan wannan abu da ba komai ba ne a wajen
samarin wannan gida.

Daga cikin falon Alhaji Auwal ya ƙwala ma Saleema kira, da sauri ta amsa da "Na'am."

Aje farantin dake kan cinyarta tayi ta miƙe ta shiga, tsaye duk ta same su shi da matan sun
sakashi tsakiya, tana zuwa ƙasa ta durƙusa tace "Abba gani."

Kuɗin da ke hannunshi ya miƙo mata yace "Yawxa yar albarka, karɓi wannan kin ji, ku je ƴan
kasuwa yanzu ku siyo labulen ɗaki mai kyau da carpet, sannan ki siyo sababin kwanuka guda
biyu da ƙaramin tebur na tsakar ɗaki."

Ba ta tambayi komai ba ta jinjina kai tace "To Abba."

Saida ta miƙe sannan ta rusuna tace "Abba zan iya tafiya tare da Nafissa? Saboda dreba baya
nan."

Jim ya yi kamar mai tunani sai kuma ya kalli ɗakin Mu'az sannan yace "A'a, ku je ke da Yayanki
Mu'az, bana son hawa abun hawa na waje."

Tsammm! Ta kalli fuskarshi, ta ya za ta nuna masa ba ta son kusanci da *tantirin nan*? Bare har
ta fita da shi waje, kamar ya san a kan me take tunani sai yace "Karki damu kin ji, ku je tare da
shi kuma kar ku jima."

A sanyaye kawai ta jinjina kai ta nufi ɗakinta dan shiryawa ta fito, tana ji Alhaji Auwal na faɗawa
Hajia babba ta sanarwa Mu'az za su fita yanzu.




*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BAIWATA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍



*NA*

_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ��
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️


_Bismillahir rahamanir rahim_


_15_




A sauƙaƙe ta shirya kamar dai kullum cikin shigarta ta mutumci ta fito, Hajia babba ce ta mata
nuni da ƙofa tace "Mu'az ɗin na zuwa, ki jirashi a waje."

Hanyar ƙofar ta nufa inda amarya dake zaune kan kujera ta bita da uwar harara cike da takaicin
wannan yarinya, ita gaba-ɗaya ma ta ga komai na gidan ya sauya tunda yaran suka zo, kuma
Saleema ita ce silar komai, yanzu ma gashi Alhaji na wata banzar magana wai za'a gyarawa
Baba ɗakinshi, ga wasu uwayen dokoki da ya lafta musu cewa dole yanzu wacce ta yi girki ita
za ta kai masa har ɗakin da rana ko kuma a ba cikin yaran da ya haifa, na safe da dare kuma
shi kanshi zai kai mishi, sannan wai kowace safiya sai sun je gaisheshi, abun da bai taɓa
faruwa ba! To idan ba Saleema ba wa ye ua zigashi? Ƙiri-ƙiri ya ɗauko maƙodan kuɗi ya bata ta
siyo kayan ɗakin bayan sai da ta roƙi ya bata dan ta san sauran canji za su zama na ta amma
ya ƙi. Dan haka ita gwara ma su gama kwanakinsu su bar gidan, idan ba haka ba za ta kasa
ɓoye ɓacin ranta har ta fatattaki yarinyar nan ta koma gidansu, dan dama uwarta ma ba wani
shiri suke ba, saboda ita ma dai kamar ƴar take, amma abun mamaki uwar ma ta fi Saleema
wayewa da ɗan cakarewa, dan ita tana saka mayafi musamman bikin ƙawaye, sannan ta na
kwalliya ga uya ɗaukar wanka sannan ga ta kyakyawa ta fi ƴar, amma ita sai fama da hijaban da
suka fi ƙarfinta, da haka ta jinjina kai da tunanin za su haɗe idan ta sake kutse a rayuwarsu.

*Saleema* kam ta ɗan jima a tsaye kafin ta hangeshi ya na tahowa, juya baya ta yi har ya
ƙaraso ta bayanta yana faɗin "Matata ki gafarceni na saka ki jirana."

Buɗe mata ƙofa ya yi da kanshi yace "Shiga mu je."

Shiga ta yi ba tare da ta kula shi ba, dan niyya ce ta yi ba za ta biye mishi sosai ba bare har ya
ga damarta ya kawo mata wargi, suna ɗaukar titi ya kai hannu ga redio ya kunna pm3, take
sautin tattausan kiɗa ya karaɗe cikin motar, sanyayyar waƙa ce ta hausa ta soyayya ka rantse
babu komai a duniya sai zallar soyayya saboda yanda baitukan suka fita. Hannu tasa ta na
wasa da kuncinta saboda jin Mu'az na bin waƙar yana kaɗa kai alamar dai da a tsaye yake zai
uya taka rawa ma, dan yanayinshi ya nuna hakan ba kaɗan ba, girgiza kai tayi a hankali yanda
ba zai ji ba tace "Allah ya shirya."

"Ameen matata." Ya faɗa yana kallonta sannan ya ɗora da "Abinda na ke son ji daga bakinki
kenan, ina ji a jikina addu'arki gareni karɓaɓɓiya ce."

Numfashi ta sauke ta kawar da kai ba ta tanka masa ba, leƙa fuskarta yayi yace "Matata, hushi
kikayi ne?"

Kallonshi tayi sai kuma ta sake maida dubanta ga titi, cike da tsokana yace "Gaskiya ki saki
fuskarki, yanzu idan na haɗu da abokina ta ya zan nuna masa ke da wannan haɗaɗɗiyar fuska?
Ya ɗauka satoki na yi?"

A hankali ta furta "Ya Allah." Waro ido yayi yace "Lahhh! Wai har na dameki hakane?"

Yatsa biyu ya sa ya damƙe laɓɓanshi yace "Shikenan na yi shiru, idan na sake magana ki mari
fuskata irin na jiya."

Da sauri ta kalleshi dan ita kam ta ma manta da ta mari fuskar nan ta shi da alamu suka nuna
yana kula da ita, sunkuyar da kai tayi cike da jin kunya, dubanta yayi da kyau yace "Hajia kin
san da marin nan ko kaɗan ba zafi? Shin tausayina ne ya hanaki marina da kyau? Ko kuma dai
iya ƙarfinki ne?"
Ƙala dai ba ta ce masa ba, dogon numfashi ya ja yana kallon titi yace "To! Mu'az ka yi haƙuri, ita
dama soyayya haka take, fatana bai wuce wanna. Babyn ta so ni kamar yanda na ke sonta,
idan kuma ba haka ba..."

Da sauri ta kalleshi da ɗan jin haushin takura mata da surutu tace "Idan ba haka ba fa?"

Da hannunshi ya yi alama a wuyanshi kamar wanda zai yanka maƙogoronshi ya ɗan zuro
harshe waje kamar wata dabbar da ta yi mummunar mutuwa yace "Ƙitttt! Sheƙawa zan yi."

Me Saleema za ta yi? Sai kuwa ta bushe da dariyar da za ta rantse tun da suka zo gidan nan ba

ta yi ba, dariya sosai take shi kuma yana kallonta cike da birgewa yanda haƙoranta ke jere reras
farare tas, cikin dariya ta dafe ciki tace" Wallahi ka na da abun dariya."

Cike da ƙwarin gwiwa yace" Na sani Matata, dan ma baki sakin jikinki da ni, da ba ke ba zama
gum."

Wani kallo ta masa tare da ɗan tsagaita dariyar tace" Ka taɓa ganin inda aka ba kura ajiyar
nama?"

Tsammm! Ya yi yana kallonta, tabbas magana ta faɗa mai kyau, sai dai bai ji haushi ba tunda
gaskiya ta faɗa, sai kawai ya bushe da dariya ya nuna kanshi yace" Ni ne kura?"

Wata yar harara ta galla masa tace" Ni dai ban ce ba."

Hannunshi ya kai da niyyar tallaɓo haɓarta dan ta kalleshi, wanda sabo ya jawo masa hakan ya
manta da wacece ya ke tare, yana daf da zai kai hannun sai kuma ya tsaya cak yace" Oh! Yi
haƙuri, na tuba Allah."

Sai kuma ya ɗora da" Kin san wani abu, alƙawari na ma kaina zan daina duk wani abu marar
kyau, saboda ke."

Haɗe fuska tayi idonta har sun ɗan rarako tace" Saboda ni? Me yasa sai ni?"

Saida ya cire duk wasa ya mayar gefe cike da kamala sannan yace" Saboda ke kika tunasar da
ni mahimmancin sallah, hakan yasa na fara bibiyar wa'azizzikan malamai, hakan kuma ba
ƙaramin tasiri ya yi gareni ba, dan na ƙara jin tsoron ubangijina."

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi tace" A taƙaice dai tsoron haɗuwarka da Allah
yasa za ka daina?"

Jinjina kai yayi yace" Ƙwarai."

Sanyayyan kallo ta masa mai ban sha'awa tace" Allah ya ɗoraka a hanya madaidaiciya, Allah
ya baka ikon gyara duk wani kure da ka san kana yi a rayuwarka, Allah kuma ya baka lada a
kan yaƙi da zakayi da tsohuwar ɗabi'arka wajen ƙirƙiro sabuwar ɗabi'a."

"Ameen, nagode matata." Ya faɗa yana kallonta da ƙauna kamar a ce an ɗaura musu aure ne.

Da mamaki ta sake kallonshi tace "Me yasa ka ke kirana da matarka? Bayan kuma ka san ba
haka ba ne."

Ɗaga gira yayi yace "To ai ina sonki, kuma na faɗawa su Abba sun san da maganar, har ma ya
min alƙawarin zai je ya ga Abbanki, kin ga kuwa kin zama matata."

Hankali tashe ta marairaice tace "Dan Allah Yaya Mu'az ka rufa min asiri, aure da soyayya, ni
sam ban ma san su ba, dama-dama ma auren tunda ta hanyarshi aka haifeni, dan Allah kar ka
ruguza min burina, sannan ka ga ina karatu kuma Abba ma ya ce ba yanzu zai aurar da mu ba
sai mun cimma wata ƙwaƙwarrar matsaya a rayuwa."
Yana tuƙi yana kallonta da mamakin dama tana dogon surutu haka wanda bai shafi nasiha ko
karatu ba? Sai kuma ya ɗauke kai ya taɓe baki yace" Matata kar ki damu, idan mukayi auren za
ki ci gaba da karatunki, burinki kuma ki zayyane min shi yanzu, ni zan cika mi shi da yardar
Allah."
Girgiza kai tayi tana kallonshi tace" Ni dai dan Allah ka dakatar da almarar nan da ka ke rerawa,
sam bana son aure a yanzu saboda wasu dalilai na."

Ba alamar wasa ya kalleta yace" Faɗi biyu na ji."

Rumgume hannaye tayi tace" Ba na sonka, sannan ina da burika."

Da hannu ya mata alama ya ƙanƙance ido yace" Faɗa min buri ɗaya na ji."

Wani murmushi tayi mai kama da kuka amma ba tace komai ba, cikin kulawa ya kalleta sosai
yace" Uhum! Ina jinki?"

Iska ta feso daga bakinta ta haɗe kukan da ya taho mata tace" Babban burina shine nima
mahaifina ya yi alfahari da ni, ko sau ɗaya ne ina so ya furta min cewa *ina alfahari da ke*, zan
so ya dafa kaina ya saka min albarka, sai dai ban sani ba ko zan cimma haka, dan na yi iya
ƙoƙarina wajen koyawa kaina fahimtar karatu amma abun ya gagara, ban san me yake damun
kaina ba, gashi yanzu za..."

Shiru tayi ta kalli Mu'az kamar a tsorace, dan gani take ta yi suɓul da baka sosai wajen faɗin
abinda ke ranta ga wanda ba wata shaƙuwa ba ce tsakaninsu, goge hawayenta tayi ta ɗaure
fuska a dole ita ba komai kawai, lura da haka yasa Mu'az bai ce mata komai ba saboda a
karatunshi ya karanci l'homme et le monde (mutum da duniyarsa) yasa ya bata damar hucewa
kafin ya ce mata komai.

Ba wanda ya sake magana har suka isa kasuwa shagon Alhaji Ibrahim, wanda Saleema ce ta
san shi a nan suke siyan duk wank abu da ya shafi atamfa, leshi, shadda da sauransu, zaune
take kan benci daga baki-bakin shagon, shi kuma ya na tsaye ya rumgume hannaye yana
kallon duk wani motsinta, ita kam hankali na kan kayan da ake ta fito mata da su tana dubawa
dan zaɓen wanda ya mata. Mu'az da ya kula da wani matashin da ke yawan kallon Saleema
gyara tsayuwa ya yi yace "Ƙanena, sassauta mata kallon nan haka ka j, ka yi haƙuri ka bar min
ita ta wa ce, ka ga ni ma ba kulani take ba bare kai."

Tunda ya fara maganar ta ɗaga kai tana kallonshi tana kallon matashin, sai da ya gama ta
girgiza kai ta kalli yaron shagon da kunya ta kamshi yana ta sosa ƙeya tace" Yawwa wannan na
ke so."

Nuna masa duk wanda ta zaɓa ta yi sannan ya jinjina kai yace" Bari na faɗawa Alhaji."

Shigewa ya yi ciki ita kuma ta kalli Mu'az tana sauke numfashi, shi ma kallonta yake da fara'a a
fuskarshi yace" Ban san me yasa ba, amma dai haushi na ke ji idan wani na kallonki."

Fuskarta a haɗe tace" Ka daina wasar nan mana, na faɗa maka komai fa yanzun nan, sam ni
da kai ba mu dace ba."

Sam babu alamar ya ji zafin maganarta ko makamancin haka, sai ma murmushi da ya sakar
mata yace" A gaba za ki so ni, lokaci kawai ki ke buƙata na baki, kuma na baki daga nan har a
ɗaura mana aure."

Ɗauke kai tayi ta kalli mai shagon dake fitowa yana mata murmushi suka gaisa, nuna masa
kayan ta yi ya lissafa ya faɗa mata tare da mata ragi sosai saboda sanayya, godiya ta masa
bayan ta biya kuɗin yaronshi ya ɗauki kayan ya na saka mata a mota. Ba su yi nisa ba aka fara
kiraye-kirayen sallah magriba, faka motar ya yi gefe ya kalleta yace "Matata, za ki iya jirana na
yi sallah?"

Buɗa baki ta yi za ta yi magana sai kuma ya langaɓe kai yace "Dan Allah madame, kar ki
hanani, ke ce fa ki ka nuna min mahimmancin sallah kan lokacinta, shiyasa na ke ƙoƙarin
kamantawa yanzu."

Sakin fuskarta tayi daga ɗaurewar da ta mata ta saki murmushi tace "To shikenan, a sakamu a
addu'a."

Buɗa motar ya yi zai fita yana faɗin "Tunda na ganki na ke addu'ar samunki, kar ki damu
matata, addu'ata ta ki ce."

Saida ya rufo mata ƙofar kawai ta saki wani sanyayyan murmushi tana girgiza kanta, gyara
zamanta tayi sosai tana hangenshi bakin ƙofar masallacin yana alwala, irin yanda yake sauri
saboda an kusa tayar da sallah, amma kuma a nutse yake kamar ba jikinshi ke kazar-kazar ɗin
ba, ba ta gushe tana kallonshi ba har suka kabbara sallah.

______________



Da sallama dattijuwar ta shigo ɗakin, a sanyaye ya amsa yana tashi zaune, cike da ladabi ya

karɓi kwanon hannunta yace "Mama da kan ki? Ina su Fareeda?"

Saida ta zauna tana fuskantarshi kafin tace "Suna can suna aikin da aka saba, ka san asabar
ɗin nan uta ce ta farkon hutun makaranta da aka shiga, dan haka akwai bukukuwa da dama."

Jinjina kai ya yi yace "Hakane, amma Mama ai da ba ki kawo min da kanki ba."

Irin kallon nan na manya ta aika masa tace "Na kawo maka da kaina ne saboda a gabana na ke
so ka ci ka bani kwanon."

Cike da kunya ya sosa ƙeya yace "Mama, Allah za..."

Dakatar da shi tayi da hannu tace "Ka ga Huzeifa, ka ci abincin nan yanzu ko ranka ya ɓace."

Sunkuyar da kanshi ƙasa ya yi tare da tallaɓe haɓarshi, bai san ta ya zai kwatanta ma
mahaifiyarshi ba ya sha'awar cin komai ba? *Allah sarki, Allah jiƙan Babanmu*! Wannan
zazzaƙar murya ita ke masa amsa-kuwa a kunnuwa, sahihiyar fuskarta mai cike da kamala da
haiba, tsintar kanshi ya yi da murmushi shi kaɗai a zaune.
Mahaifiyarshi da ta ƙura masa idanuwa ta na jiran ya ci abincin ta ga shiru, a ƙarshe sai ganin ta
yi ya ɓige da murmushi shi kaɗai, cike da kulawa tace "Huzeifa."

Zunbur ya kalleta dan ya manta a gabanta ya ke, da sauri ya kalleta ya ɗan rarraba idanu yace
"Ah...ahhh, na'am Mama."

A tausashe tace "Me ya ke damunka?"

Girgiza kai yayi kanshi ƙasa yace "Ba komai Mama."

Ƙara gyara zama ta yi sosai tace "Huzeifa, kada wannan jarabawar ta sa ka illata kanka, ka
daina cin abinci gabaɗaya, kullum karatu ba ka da lokacin hutu, ɗan lokacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login