Showing 12001 words to 15000 words out of 50006 words
Chapter 5 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
Ita kam tsakaninta da shi ido ne shi ma a akasi idan sun sark'e, kamar
yanda ba ta damu da shiga abinda bai shafeta ba, haka ta kula shi ma ba ya shiga sabgar da
ba'a saka da shi ba, dalilin da yasa kenan ko sannu ba ta tab'a had'asu ba, kuma ta ji ma an ce
shi ne shugaban matasa na makarantar.
Sum sum sum! Ta nufo hanyar wucewa wacce dole ta gefenshi za ta ratsa ta wuce, hakan yasa
ta k'ara sadda kanta k'asa dan ba ta so su had'a ido, sai da ta zo daf da shi har ta d'an wuce
kad'an *Huzeifa* da ya shiga halin d'imuwa da tashin hankalin da bai tab'a riskar kanshi ba ya yi
k'arfin halin d'an matsawa kad'an da tunanin kar ta k'arasa warware masa alwalarsa ya na
ambaton "A'uzubillah!"
Duk da ba ta tsaya ba amma sai da ta saci kallonshi ta gefen ido da son gano me ya ke wa
a'uziyya? Ido suka sake had'awa dan shi mamakinshi bai wuce "Wai dama haka ta ke a cikin
dogon hijabin nan?" Ba, shi ya na ganinta ba ruwanta ashe bama-bamai ne a cikin hijabi,
tsakani da Allah da Annabi ya d'auro alwalawarsa ya zo da niyyar d'an tab'a karatu kafin 12:30
ta yi ya yi sallah, sai kawai ya wani sameta zigidir haka daga ita sai siket da k'aramar riga, anya
kuwa ta san halin da ta sakashi a ciki? Shi fa idan ka cire matan banza da ya ke gani a tv
wanda ya ke iya k'ok'arinshi wajen ganin ya kare kanshi daga kallonsu, da kuma ko da ya
kallesu ba abinda yake ji, shi bai tab'a ganin irin haka ba, k'annan shi ma mummunan kashedi
ya kirta musu kan zama haka a cikin gida. Yanzu ga shi yarinyar da ko sunanta bai sani ba ta
gayyato masa da wata larurar da bai san ya na da ita ba.
Wannan kallon mamakin da Saleema ta hango a k'wayar idon shi ya sa ta tunanin ko dai ji yake
shi ma malaminsu ne ? Nufinshi kuma ta gaisheshi? Sai kawai zuciyarta ta raya mata ai ba
komai ba ne, gaishe shi ya ci albarkacin malaman. D'an tsayawa ta yi ta sake kallon inda ya ke
amma ba ta kalli fuskarshi ba tace "Ina wuni."
Tsura masa ido ta sake yi ganin mak'walaton wuyanshi ya yi sama da k'arfi alamar ya had'iyi
yawu sannan ya yi k'asa kamar wanda ya had'iyi kunama, da sauri ta d'aga k'afafunta za ta bar
wurin ta ji rikitacciyar muryarshi mai bala'in sanyi da taushi wacce ta dace da yanayinshi na
sahihin namiji mai sassauk'ar k'ira yace " *Ya sunanki*?"
Cak ta tsaya tare da juyowa a hankali ta sauke ido a kan shi, kamar ba za ta amsa mi shi ba sai
kuma a sanyaye ita ma sosai cike da ladabi da kamun kai tace "Sunana kuma?"
Ido kawai ya iya lumshewa alamar e, d'an kawar da kanta tayi gefe sannan tace " *Haleematu
Yusuf Saddi*."
A kan labb'anshi ba tare da ya san maganar za ta fito fili ba ya sake furta "Haleematu."
Kallonshi ta yi da kyau sai kuma ta juya ta ci gaba da tafiyarta, bai daina kallonta ba har said ya
ji zuciyarshi na tambayarshi "Haba Huzeifa, wannan kallo ai ya wuce k'ai'da."
Da sauri ya d'auke kan shi yana jan d'an gemunshi da ya tara dan koyi da sunna tare da fad'in
"Astagfirullah! Allah na tuba ka yafe min, a'uzubillah, shaid'an me ka yi haka? Ya aka yi ka samu
nasara a kai na yau?"
Dab'as ya zauna a dakali ya na ci gaba da furta neman tuba ga mahaliccinshi kan ya gafarta
masa, dan ya tabbata da shi ta ke fuskata da ta ji kallon ya fara cutar da ita, wanda kuma aka
hana a shari'a cewa _" Bai halata ka dinga kallon musulmi ba kallo wanda zai cutar da shi, sai
dai in ya kasance fasik'i ne, to k'aurace masa ya zama wajibi."_
In da a farkon karatun littafin Akhdari kuma aka lissafi a jerin abubuwan da baligi kuma ak'ili ya
kama ya kiyaye shi ne _" Kallon ajnabiya (manisanciya-wacce ta ke ba muharramar ka ba),
sannan ka kiyaye jin dad'in zancenta._
*Yau* kam suna cikin farin ciki na gama jarabawarsu, ko ba komai sun samu hutu su ma daga
ranar da ake k'wlawa, musamman ma Saleema da take ganin wahalar banza take, sai dai farin
cikin na ta ya koma ciki sanda mahaifin na su ya umarcesu da su shirya zai sa dreba ya kaisu
gidan *Alhaji Auwal* wanda zai iya cewa mai gidanshi ne a fannin siyasa, dan shi ya kama
hannunshi ya durmiya a cikin tafiyar, duk da a girme ya girmeshi nesa ba kusa ba, dan ko
Yayan Alhaji Yusuf d'in ya girma amma suna mutumci da mutumta junansu.
A tsanake mamanta ta kalleta tace "Saleema, lafiya ki ke ta had'e fuska?"
K'ara turo baki ta yi gaba ta na k'ok'arin saka rigarta duk da sanye take da hijab saboda kunyar
Maman da ta ke ji ba za ta iya tub'ewa a gabanta ba tace "Ni wallahi Mama ba na son zuwa
gidan nan, dan kar Abba ya ce na rainashi zan tafi kawai."
Murmushi Safiya ta yi da mamakin wai Saleema ba za ta iya saka riga a gabanta ba dan kar ta
lafiyayyen k'irjin da ya cika mata gaba tace "To wai me ya sa ba kya so? Can ma gidan hutu ne
fiye ma da na mahaifinku."
Juyowa Saleema ta yi ta kalleta tace "Mama, ba wannan ne matsalar ba, kin san ko k'auye zan
iya rayuwa, kawai dai yaran nan na sa ne ni wallahi ba su kwanta min a rai ba."
Da mamaki Maman tace "Su wa kenan?"
Cike da yatsina fuska tace "Yan mazan mana, duk ba su da tarbiya wallahi."
Rik'e hab'a Maman ta yi da mad'aukakin mamaki tace "Ikon Allah! Saleema yaushe ma ki ka
musu sanin da ki ka gane haka? Shin *Mu'az* d'in da ko shekara bai yi da dawowa daga karatu
ba? Ko kuma *Mu'awwaz* d'in da ke da tsantseni da share mutane?"
Ta na gama saka rigar ta cire hijabin ta na saka zip tace "Dukansu Mama, wallahi kura ce da
fatar akuya, dukansu rainawa mutane hankali suke, ba ma kamar tuzurun nan."
Dariya Maman ta sake har da k'yalk'yalawa tace "Wa ye tuzuru kuma?"
Ba alamar wasa tare da ita tace "Shi Mu'az d'in mana, shekara talatin ba aure amma ya na
nuna bai damu da komai da kowa ba, hmmm ! D'an rainin hankali kawai."
Maman ta dai abun dariya da mamakin yanda ta hak'ik'ance ta na ta sababi take, to ita ba ta ma
san yaushe ta musu wannan sanin ba haka? Tabbas sun tab'a zuwa gidan amma fa tun ba ta
kai shekara goma ba a duniya, duk da ta san ta bata da mantuwa kan abin da ya shafi rayuwar
duniya da karatunta na islamiyya, amma dai ba ta tunanin har yanzu ta na tune da abinda ya
faru shekara *tara* da ta wuce.
Haka ta gama shiryawa amma sam ba ta so haka ba saboda ita ta gama fahimtar duk wani da
Abbansu ke alak'a da shi ta kusa sosai to d'an boko ne da ke da wayewa, sai dai na wani ya fi
na wani kawai. Ta na gama shiryawa ta fito farfajiyar, a nan ta samu su Hadeeya har da
mahaifin na su a tsaye da alama so ya ke ya ga tafiyarsu da kuma Mamansu gefe ta na amsa
waya.
Sanye take da doguwar riga wacce gaba d'aya gabanta yake a bud'e, ma'ana aka masa
doguwar tsaga har zuwa cibiyarta, sai siket d'in atamfar da ya rufe mata cibayar inda a baya
kuma yake yage da tsaga shima har idan tana tafiya kamar za ka hango gwiwoyinta, k'aramar
jakarta ta rataya ta tsakiyar wuyanta da hannu, sai takalmin kalar jakar masu d'amara da
rufaffiyar sama, kwalliya ce ta ban mamaki ta d'auka sai dai ko d'an kwali babu a kan ta,
hasalima d'an kwalin rik'e yake a hannunta, a hakan wai shi ma wani kalan tsarin ne.
Kayan sun matseta sosai yanda suka fito da kyakyawar surarta da kuma kyawun fuskarta,
masha Allah kuma abun ka ga farar fata sannan mai kaurin jiki, hakan yasa Hadeeyar ta zama
basu da maraba ita da Saleema da ta bata shekara uku da haihuwa saboda su na da kumari.
Cike da rashin jin dad'in yanda ta ga yan uwanta sun shiryo ta kalli Hadeeya a tausashe tace
"Haba Hadeeya, wannan wace irin shiga ce? Kina 'yar musulmai amma ki fita haka kanki babu
rufi? Idan ma ba zaki saka hijab ba ko gyale ne ki saka mana."
Cikin tsiwa da raini da kaud'i Hadeeya ta kalleta tace "Ke kuma malama ina ruwanki da shigata?
Kina da matsala da hakane? Ka ji min mata kai, so kike na yi irin shigarki kamar wata matar
aure?"
Kafin kowa ya yi magana Ardayi da aka mata kiran gaggawa a wajen aiki ta k'araso da sauri kai
tsaye mahaifinsu ta tunkara cikin shagwab'a tace" Bébé, kira ne da wajen aiki ana buk'atata
yanzu, zan tafi sai na dawo..."
Ta yi maganar ta na fad'awa jikinshi ta sumbaci labb'anshi tare da d'agowa tace" Ba zan jima ba
Bebe, sai na dawo."
Saleema da tun da ta ga ta nufeshi ta d'auke kanta saboda kunya, shi kan shi yanzu da shekaru
su ka k'ara ja ya kan ji nauyi idan irin haka ta faru, sai dai Ardayi ta saba kuma ba ta ganin
hakan a matsayin wata matsala.
Hannu kawai ya d'aga mata bai iya furta komai ba har ta k'arasa kusan su Hadeeya da ba ta
san akan me suke magana ba ta rumgume su su ma musamman Hamdeeya har tana fad'a
mata "Shoyerta (autata) ki kula da kan ki."
"To Momma." Ta fad'a cike da farin cikin za ta tafi unguwa na wasu kwanaki, suna kallo ta shiga
motarta ta bar gidan.
Sai lokacin Hameeda da ita ma dai wata arniyar shigar riga da siket na shadda ne jikinta tace"
Kama da matar auren ma wacce ta haihu, dan wannan hijabi da ta saka sai matan aure masu
'ya'ya, dubi fa daga nan baya har k'asa yake ja mata."
Kallon hijabin na ta sukayi kam mai hannaye wanda ya mata kyau sai kawai suka bushe da
dariya suka tafa hannu Hadeeya na fad'in" Wa ya ga ta Allah."
Murgud'a baki Hameeda tayi ta harari Saleema tace" Wai a haka za ta bi mu, ki ga fuskarta ko
hoda ba ta murza ba sai k'yallin mai take, mtssss! Ni wallahi da Abba da ma ka hanata zuwa."
Wani kallo Saleema ta ma Hameeda sai kuma ta kalli mahaifin na su da duk da yana jin me ke
faruwa amma hankalinshi na ga waya yana latsawa tace" Abba ka a yaran nan magana mana,
dubi fa shigarsu?"
Wayar da ya d'ora a kunne ya sa shi nuna mata su wuce su tafi kawai dreba na jiransu, cike da
takaicin halin ko in kula ta fara yin gaba ta shige motar.
Tsaki Hameeda ta sake ja har suka k'arasa kusa da mota inda dreba ke jiransu suka shiga ya
jasu zuwa gidan.
*______________*
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_7_
Tabbas sun yarda Alhaji Auwal ya fi mahaifinsu kud'i nesa ba kusa ba, dan daga irin ginin da ya
tarwatsa za ka fahimci haka, da kuma irin kayan alatun da suka k'awata gidan, ba su daina kalle
kalle ba har mai aikin da ta musu jagora zuwa cikin gidan suka shigo k'aton falon.
Saleema da ke baya cikin sharb'eb'en hijabinta kallo d'aya ta ma uwar gidan ta saki murmushi
saboda tuna shekarun baya da su ka sameta tana cikin ganiyar k'uruciyarta mace yar gayu da
wayewa, amma yanzu shekaru sun lak'ume duk wannan ji da kan da k'uruciyar, ba abinda ya
rage mata face dattijuwar fuskarta mai d'auke da gilashi.
Kusanta suka fara zuwa inda take zaune, Hadeeya da Hameeda daga tsaye suka gaisheta da
"Ina yini?"
Hamdeeya kuma kusanta ta zauna dan ta san matar ita ma tana wangale mata baki sai dai ba
ta ce mata komai ba, yayin da Saleema dake gefe ta durk'usa kamar za ta yi zaune tace "Ina
wuninku Mama."
Da fara'a da kuma jin dad'in gaisuwar ta Saleema ta kalleta cike da kulawa tace "Lafiya
lauSaleema, kina lafiya?"
"Lafiya lau." Ta fad'a cike da kunya, maida hankalinsu sukayi kan wata dattijuwar da ke shigowa
falon hannunta rik'e da waya, kallo d'aya suka mata ita ma suka gaisheta kasancewarta
amaryar gidan. Cike da yauk'i da jan aji ta wani yatsina fuska tace "Lafiya lau, har kun iso ?"
Kafin kowa ya ce wni abu Hameeda ta kalleta tace "Aunty ina *Ummeeta*?"
Cike da yatsina fuska tace "Ta na ciki." Ta fad'a tana nuna mata k'ofar da ta fito, mik'ewa
Hameeda ta yi ta nufi d'akin suka bi bayanta da kallo, wani d'an murmushi amaryar ta saki
saboda sak ta hango Hameeda da d'anta Mu'awwaz a matsayin ma'aurata, a ganinta ba
k'aramin kyau za su yi ba. Dan haka ma ta wuce inda za ta je ta na ayyana abubuwa da dama a
game da ganin Hameeda, dan sam shigarta ba ta d'auketa bakin komai ba sai kawai wayewa
da zamananci, sannan ta na da labarin ilimin yaran daga wajen mahaifiyarsu.
Hajia *Rabi* ce ta kalli su Hadeeya tace "Ku wuce ciki kuma, kun san ana rana duka yaran su
na bacci."
Tab'e baki Saleema ta yi a ranta ta ayyana "Tunda an saba musu ba."
Mik'ewa sukayi Hajia Rabi ta kalli mai aikin tana fad'in "Ki nuna musu inda aka gyara musu, idan
su ka yi wanka sai ki kai musu abinci."
Kallonta Saleema ta yi sanda suka kama hanyar d'akin tana mamakin to wankan me za su yi?
Ba fa daga wani garin suke ba, tafiya ce da ba ta wuce minti ashirin ba, amma dai ba ta ce k'ala
ba suka wuce cikin.
*_____________*
K'aramin littafin dake d'auke da kala-kalan abincin da aka mik'o masa ya girgiza kai tare d'an
murmushi yace "Um-um! Nagode da wannan ma."
Kyab'e fuska *Sharhasila* ta yi kamar za ta yi kuka tce "Haba dai Yallab'ai, ka zab'a mana, ni fa
zan biya."
D'an sunkuyar da kai ya yi kamar mai tunani sai kuma ya d'ago ya sake girgiza kai yace "Ya isa
haka Baby, kin san bana son zuwa irin wuraren nan cin abinci, hasalima ni na fi jin dad'in cin
abincin gida."
Had'e fuska tayi tare da kawar da kai sam abinda ya fad'a bai mata ba, to ita ina za ta iya wani
girki? Tabb'! Kallonshi tayi tace "Yallab'ai, amma dai ka san ba ni zan dinga girki ba idan mun yi
aure ko?"
Da mamaki Huzeifa ya kalleta yace "Ban gane ba? To wa zai yi? Ni?"
D'an murmushi ta yi cike da shashanci tace "A'a haba, ina nufin sai mu samu yar aiki."
Iska ya feso a bakinshi yana jin wani b'acin rai na hauhawa masa, to shi bai san wane irin aure
ne za su yi da Sharhasila ba, dan tana tak'amar ita yar mai kud'i ce, kuma ita ta nunashi ta ce
tana so, sai ya zama zai zaunata mulkeshi ne? Abubuwa na hauka da kidahumanci ta ke kawo
masa fa, wannan wane irin abu ne?
Kallon kyakyawar fuskarta ya yi wacce ta fad'a masa wuni ta yi wajen gyaran jiki da kwalliya wai
dan za su had'u wurin cin abincin nan kawai wanda shi a wajenshi bai da wani anfani, cikin
tausasa murya yace "To me yasa ke ba za ki dafa ba?"
Turo baki ta yi irin shagwab'ar nan cikin harshen faransanci tace "Amma Bebe ai kasan ni aiki
nake zuwa ko? Yaushe zan maka girki sannan na yi aikina? Ba zan iya ba gaskiya."
Shi ma a harshen faransancin yace "To ai macece ke, kuma ba'a yi auren ba, zaunawa za ki yi
kafin lokacin ki tsarawa kan ki rayuwarki, kar ki maida hankali kan abinda ba zai anfani lahirarki
ba, Sharhasila wannan aiki da kike moriyarki da shi iya duniya ne kawai, idan ki ka fi k'arfin
shed'an ne za ki nemi lahirarki da aikin, dan haka a ganina tun ba'a d'aura aurenmu ba ki
tsarawa kanki komai ta yanda za ki ba wa komai lokacinshi yanda ya kamata."
K'ank'ance ido yayi sosai ya na ci gaba da kallonta yace" Kin san wani abu? Mutum ne ni mai
matuk'ar son kulawa, hakan yasa mahaifiyata ke fad'a min wai wasu lokuta kishi nake da
k'annaina..."
Yar dariya ya yi ya d'ora da" Gaskiya ne, sai na ji idan ina magana da ita bana so kowa ya mana
kutse bare a tilasta mata raba hankalinta gida biyu, sannan ina da matuk'ar son abincin gida,
ma'ana ina son abinci irin su tuwo, d'an wake, faten doya, biski, dambu...da sauransu."
Tsareta ya yi da ido yace" Da fatan