Showing 3001 words to 6000 words out of 50006 words
Chapter 2 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
yana sumbatarsu, cike da
kissa da karairaya Ardayi a ta k'arasa gareshi, ba tare da jin nauyin komai ba suka rumgume
junansu tare da sumbatar kumatunsu.
Safiya dake jera abinci akan tebur bata kallesu ba dan dama abinda ta san zai faru ne, inda
Saleema dake zaune k'asan carpet ta bisu da kallo a ranta take ayyana "Ko me yasa Abba bai
da kunya?"
Manyan ledojin hannunshi ya ciro kwalayan dake ciki na wasu mahaukatan dogayen riguna da
k'ananan wayoyi masu kyau ya ba wa Hameeda da Haddeya, inda Hamdeeya ya bata riga da
wani k'aton abun wasa da sunan kyautarsu, da sauri Saleema ta mik'e abun ka ga yaro jikinta
har b'ari yake ta ajiye k'aramin almakashin hannunta ta tunkareshi tace "Abba ni ina nawa?
Baka ban ba fa."
Wani kallon raini ya mata yace "Ni d'in zan kashe miki kud'i? Wace tsiyar kika tsinana? Wannan
shirmen da kike?"
Ya fad'a yana nuna tsummokaran data tara gabanta kala kala na atamfa, leshi, shadda da
saurensu ita a dole d'inki take, juyawa tayi ta kalli kayan sannan ta kalleshi tace "Abba d'inki ne
fa nake yi."
Kallon Safiya yayi da ke ci gaba da aikinta duk da tana jin me ke faruwa amma ta dake kamar
ba ta ji ba. Yace "Kina ganin irin shirmen da take tara min a gida ? Madadin wannan me zai
hana ta d'auko littafinta tayi karatu?"
Shiru ta masa dan tun jiya yake nemanta da rigima ido bud'e, dan haka ba ta kulashi ba, Ardayi
dake d'an gyara matsatsan rigarta mai k'ananan hannaye ce ta d'an tab'e baki tace" To ita kanta
karatun ya sha mata kai ne bare kuma ta koya ma 'yarta?"
Sai lokacin kad'ai Safiya ta kalleta tace" Kinga, idan muna magana tsakaninmu ki daina saka
min bakinki, bana so."
Kallonshi tayi fuskarta a d'aure tace" Me ya sa ka hanata kyautar ita ma?"
K' ank'ance ido yayi da mamakin tambayarta yana d'an gyara rigarshi ta shadda da aka ma
k'aramin d'inki kasancewarshi d'an zamani bai cika son manyan kaya ba yace" Ban gane ba?
Ke baki ji abinda na ce ba ce?"
D'auke kanta tayi daga gareshi sannan tace" Gaskiya ba ka adalci ko kad'an, ita ma fa
haihuwarta kayi kamar sauran, me yasa za ka dinga fifitasu a kan ta?"
" Saboda sun fita. " Ya fad'a cikin d'aga murya, ido cikin ido ta kalleshi kafin ta kalli Saleema
tace" Zo nan."
Da sauri Saleema ta k'arasa gareta tana matso k'walar da suka taru a idonta, kama hannunta
tayi suka juya a wurin suka barsu nan, tab'e baki yayi irin ko a jikinshi kafin ya shiga wata
sabgar.
*Kwana uku* kenan da faruwar wannan abu ya ga sauyi sosai daga Safiyar, dan ta daina
walwala haka ma Saleema ba ya ganinta a falon tana wasarta, wanda dama ko can ita kad'ai
takr wasar suma su Hadeeya suna ta su, k'arara duk mai ido ya ke gane da bambaci a tsakanin
matan, wanda ba komai ya jawo haka ba sai fifikon da amarya ta samu fiye da uwar gida, ita ma
kumata same shi ne dalilin dogon karatun da tayi wanda a yanzun take cin gajiyarshi ta hanyar
aiki a banki.
Tsakanin mata da miji dama aka ce sai Allah, damuwa da hakanyasa shi dawowa gidan bayan
ya tabbatar yaran na makaranta kuma Ardayi na wajen aikinta, a d'aki ya sameta kwance da
alamar bata jin dad'in jikinta, k'arasawa yayi ya zauna kusa da ita yana kallon kyakyawar
fuskarta wacce tana d'aya daga cikin abinda yasa har yau yake tare da ita da kyautatawa.
Hannu ya kai ya tab'a wuyanta yace "Me yake damunki ne?"
A hankali ta yunk'ura ta gyara zamanta kafin tace "Ba komai."
Da sauri ya fuskanceta sosai ya rik'o hannunta yace "Safiya hushi kike da ni akan abinda ya
faru? Kiyi hak'uri kinji, b'acin rai ne ya sa da kula son da nake ma Saleema, ina so na ga ita ma
ta zama kamar 'yan uwanta, shiyasa kika ga ina haka."
A tausashe ya d'an fara lumshe ido ya kwanto da ita jikinshi cikin muryar da ta fahimci kan
zancen yace" Kiyi hak'uri kinji *Sofee*."
D'an murmushi tayi ta d'ago daga jikinshi za ta yi magana, sai kuma ta yi saurin rufe bakinta
saboda aman da ya tuk'ota, da sauri ta sake toshe bakin tana had'eshi gudun kwafsawa, cike
da kulawa ya kalleta yace" Oh! Baki da lafiya ne? Me yake damunki ne?"
Sunkuyar da kai tayi cike da kunya ta girgiza kai, d'an kawar da kai yayi a ranshi yana mamakin
kunya irin ta Safiya, shekara goma sha d'aya da aure amma har yau kunyarshi take, shi ba zai
iya tuna ranar da ta nuna mishi buk'atarta ba sai dai ya karanta a tsakiyar idonta ko daga jin
sautin muryarta, hakan na birgeshi matuk'a a game da ita, sai dai kuma a matsayinsu na
ma'aurata yana so ya ga tana komai b'aro b'aro, duk da dai hakan ba wata matsala ba ce dan
kunyar tana taimakonshi sosai. Sake kallonta ya sake yi yace "Safiyyyyya."
Yanda ya ja sunan na ta ya sa ta d'agowa ta kalleshi, da murmushi a fuskarshi yace "Ko dai ciki
gareki?"
Da sauri ta rufe fuskarta ta sake duk'ar da kanta tana ji kamar ta nutse k'asa, cike da farin ciki
ya jawota jikinshi yana fad'in "Masha Allah Sofee na, dama kullum addu'ata Allah yasa ke ce za
ki haifa min auta a gidan nan, kin san na fad'a muku yara shida na ke da buk'ata a rayuwata,
idan ma zan samu k'ari to kar su wuce bakwai."
Ita dai rufe fuskarta tayi da da rigarshi tana mamakin tsari irin na shi, in banda abun shi ko wa
ya fad'a masaana wa Ubangiji iyaka? Wato shi ne ma zai k'ayyade yaran da yake so ya haifa a
duniya.
D'agota yayi yana lek'a fuskarta yace" Amma dai ki shirya mu je asibiti dan a duba lafiyarku,
bana so na rasa wannan Safiya kamar yanda na rasa sauran."
Narai narai tayi da manyan idonta tace" Bana tunanin wannan ma zai tsaya, kamar sauran
shima na san zai tafi ne."
Girgiza kai yayi yace" A'a ki daina fad'in haka, in sha Allah za ki haifeshi. "
Kamar za ta fashe da kuka ta kalleshi tace" Abban Hajia shida fa, shida na samu duka suna
zubewa, har hutu aka bani ko hakan zai sa a dace amma har yanzu shiru."
Cike da jimami da tausaya mata ya k'ara rumgumeta a jikinshi yana rarrashinta, kasancewar
d'akin a bud'e take yasa Saleema da ta taso daga islamiyya shigowa kan ta tsaye ba tare da
tunanin za ta samu mahaifinta a d'akin ba duba da kwana uku kenan ma ko magana ba ta ga
sunayi da mahaifin na ta ba, sai dai tana ganinshi ta zabura ta juya za ta koma waje, inda
Safiya ma ta firgita da sauri ta mik'e daga jikinshi tana son matsawa nesa da shi, da mamaki ya
kalli uwar ya kuma kalli 'yar, sai ya rasa duk me ye haka d'in? Kamar wani wanda aka kamada
wata matar? Da fa Ardayi ce ba ruwanta, hasalima ita har kayan baccin take sakawa kuma a
gaban yaran, idan ta kama ma har rumgumeshi za ta fara yi a hakan kuma a gabansu, a
ganinsu dai ai iyalinsu ne ba komai.
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_3_
Cikin ladabi Safiya ta kalleshi tace "Abban Hajia."
"Na'am." Ya amsa yana kallonta, ci gaba ta yi da cewa "Dama Saleema ce take fad'a min wai
tana son shiga koyon d'inki, ka san nan kusa da mu akwai wata dake koyawa mata d'inki."
Murmushi ta saki a fuskarta ta ci gaba da fad'in "Na fad'a mata ta yi yarinta dayawa, amma
kuma na ga tana da k'ok'ari wajen yin d'inki, dan kullum da abubuwan take fama a gidan nan."
Aje cokalin da yake cin abinci ya yi ya kalleta sosai yace "Safiya, gaba d'aya alamu nuna min
suke ke kike hana yarinyar nan maida hankali kan karatunta, 'yata ta cikina ta yi d'inki? D'inki fa
?"
Girgiza kai yayi dake nuna abun ya ma bashi dariya yace "A tarihin gidanmu ko mai siyar da
sutura babu, ta ya zan bar yata ta fara koyon d'inki?"
Kallonta yayi da kyau yace "Kina ji na? Saleema idan har ba ta fito min a matsayin babbar likitar
mata ba to ta zo min a matsayin wata engineer ko babbar 'yar jarida, idan fa hakan ya gagara
ne zan so ta zama hazik'ar mace a cikin siyasa."
Kallon Hadeeya yayi dake cin abinci yace "Me kike so ki zama a rayuwa?"
Cike da iyayi ta waina idonta kafin tace "Abba, ni dai gaskiya irin aikin Momy nake so, irin yanda
take shigarta idan za ta tafi, da jajircewarta a kan aiki yana birgeni sosai."
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa ya kalli Hameeda yace "Ke kuma fa yar Abba?"
Cike da yarinta tace "Abba, ni dai so nake na yi dogon karatu akan harkar tattalin arziki."
Cike da jin dad'i ya jinjina kai har da murmusawa yace "Da kyau 'yata, wannan shi ne abinda ya
kamata."
Hamdeeya ya kalla da fara' a yace "Autata dai na san bata da matsala ko?"
Cike da k'uruciya Hamdeeya tace "Abba ni dai malama zan zama."
Dariya yayi yace "Hakan ma burine mai kyau."
Kallon Ardayi yayi wacce duk abun nan da ake hankalinta na kan wayarta yace "Masoyiyata kin
ji fa, dan haka sai ki k'ara zage damtse."
D'an murmushin yak'e tayi dan hankalinta ba nan yake ba tace "Dole mana, kar ka damu
masoyi."
Sai lokacin ya sake kallon Safiya dake ta kallonshi da mamaki yace "Kin dai ji, dan haka ke ma
idan za ki d'ora ta a turbar da ta dace ki fara tun yanzu, amma bana son maganar shirmen
banza da wofi."
*Bayan kwana biyu*
Hannunta ya kamo suna shigowa d'akin ya kalli Safiya dake gyara gadonta yace "Yanzu
wannan shirin da shi za mu tafi da ita? Baki ga yanda yan uwanta suka shirya ba?"
Juyowa tayi tana kallonshi sai kuma ta kalli shirin jikin Saleema, doguwar riga ce ta shadda
jikinta mai kwalliya sai hijab da ya dace da kayan tare da takalminta masu kyau da tsada, sake
kallonshi tayi tace" Me ye aibun shirinta?"
D'an gajeran tsaki yayi yace" Kin wani saka mata manyan kaya, baki ga na yan uwanta bane?"
D'an kawar da kai tayi tace" Ka yi hak'uri, amma gaskiya bana sha'awar koyawa yarinyata fitar
da tsiraici tun tana k'arama, gwara ta san hijab shine rufin sirrinta."
Cikin jin haushi yace" Ke da anyi magana sai ki nuna kin fi kowa tsoron Allah, to wannan 'yar
abar wani ne zai yi sha'awarta ? Ina ma abun yake a nan?"
Wani tsaki ya sake yi yace" Kinga dan Allah d'auko min wasu kayan na canza mata idan ke ba
zaki iya ba."
Jinjina kai tayi ba yanda za ta yi ta d'auko mishi riga ta kanti ta kawo, da kanshi ya fara k'ok'arin
taimakawa Saleema, hakan yasa ta fara kakkare jikinta cike da kunya saboda rashin sabo, yana
gama taimaka mata ta saka kayan ya kama hannunta za su fita, da sauri ta kalleshi tace "Abba
hijabina?"
Harara ya wurga mata yace "Dallah muje malama."
Haka ya ja hannunta suka fice a gidan tana ta jin ta wata iri ba yanda ta saba fita ba. Wajen
taron ma da suka isa kasa sakewa ta yi har matar abokin na shi wacce take murnar shagalin
k'arin shekarar d'aya daga cikin yaranta ta masa magana ko me yake damunta, cike da takaicin
halin k'auyenci da dabbanci a ganinshi na Saleema yace "Ba komai, iskanci ne kawai."
Dan a ganinshi k'auyenci ne duba da yan uwanta da sauran yaran yanda suka sake cikin yara
yan uwansu suna ta tik'ar rawa dalilin k'aton redion da aka saka musu, sai ita da ba ta waye ba
za ta wani had'e wuri d'aya kamar mai jin mugun sanyi.
Dawowarsu ke da wuya ya samu kiran waya daga malamin Saleema, dan ba ya kirashi da
malaminsu duka ba saboda su Hadeeya sai sun ga dama suke zuwa makarantar islamiyya,
Saleema ce dai babu abinda ke hanata zuwa dan ba ciwo ba, bayan sun gaisa a tsanake da
mutumtawa malamin ke fad'a masa "Alhaji dama akan Saleema ne, shiyasa na ce bari na kira
muyi magana."
Gabanshi ne ya fad'i dan abu d'aya tunaninshi ya bashi, wato a islamiyar ma bata gane komai?
A nutse malamin ya d'ora da "Dama Saleema na d'aya daga cikin hazik'an yara a islamiyar nan,
kuma abun birgewa yanda take da matuk'ar fahimta akan ilimin hadith, to dama akwai lokacin
da aka ware ga maye da suke d'aukar karatun hadith, shine nake neman alfarma ko za'a
lamunce mata sai ta dinga zuwa lokacin da za'a yi darasin? Zai zama idan an tashi k'arfe sha
biyu na rana ita ba za ta koma gida ba za su wuce ajin d'aukar hadith, k'arfe d'aya da rabi sai a
sallamesu."
Shiru Alhaji Yusuf ya yi yana tunanin abinda malamin ya fad'a, sai shed'an ke raya masa to
dama tana gane karatun islamiya na boko ne ba ta ganewa? Sai kawai zuciyarshi ta raya mishi
ai da gangan ne ta ke k'in aje hankalin a boko, tunda gashi tana gane hadith. Jinjina kai kawai
ya yi yace "Shikenan."
Ya kashe wayar da tunanin matakin da zai d'auka, har ya yanke hukunci bai sanar da kowa
abinda zuciyarsa ta yanke masa ba, yana jiran lokaci yayi ya zartar kawai kowa ya gani ya
kuma sani.
*Washe gari*
Ganin ta dawo da kuka yasa ta tarbeta cike da kulawa tana tambayarta "Saleema, me ya faru ?
Wa ya dakeki?"
D'aga kanta tayi tace "Abba ne a waje yace wai na dawo, kuma wai daga yau ba zan sake zuwa
makarantar ba."
Da mamaki sosai a fuskarta tace "Ban gane ba za ki sake zuwa ba? Me kika masa?"
Cikin kuka tace "Nima ban sani ba, kawai koroni yayi."
Numfashi ta sauke tana ji akwai dai wani abun, amma haka kawai ba zai hanata zuwa
makaranta ba, nuna mata gado tayi tace "Zauna nan, bari na je na ji me ki ka yi."
Za ta fice a d'akin Saleema tace "Mama idan ya ce wani abu na masa ki bashi hak'uri dan
Allah."
Murmushi ta sakar mata sannan ta fice a d'akin, a farfajiyar ta sameshi zaune da na'urarsa yana
dannawa, kujerar gefenshi ta ja ta zauna a nutse tace "Abban Hajia, ta sameni yanzu take fad'a
min wai ka hanata zuwa islamiya, shine na ce na san dai wani laifin ta yi ko?"
Ba tare da ya kalleta ba fuska a d'aure yace "Ba ta yi laifi ba, kawai dai na soke zuwa
makarantar ne, ba kuma ita kad'ai ba har da yan uwanta."
Hankali tashe zuciyarta a kid'ime ta furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"
Da sauri ya juyo yana kallon da tunanin me ye na salatin? A razane tace "Alhaji, islamiyar fa ka
ce ka dakatar da zuwa?"
A k'ufule yace "Haka na fad'a Safiya, ko kina da ja ne?"
Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tace "Me ya yi zafi haka? Islamiya?"
Mik'ewa yayi a hassale ya d'auki wayarshi da na'urar sannan ya kalleta yace "Na riga da na
gama yanke hukunci, na kula wannan karatun ne ya ke d'auke mata hankali tana kasa fahimtar
wanda nake so ta fahimta, shiyasa na ciresu gaba d'ayansu dan hankalinsu ya tsaya wuri
d'aya."
Mik'ewa tayi tsaye tace "U'uzubillah! Alhaji ka san me kake shirin aikatawa kuwa? Kai tsaye fa
kamar kana k'ok'arin ingiza yaranka ne ga mummunar hanyar da ba zata b'illar da su ko ina ba
sai halaka."
Cike da shashantar da zancen ya kalleta sama da k'asa yace "Allah ko?"
Sai kuma ya ja tsaki ya wuce ya barta tsaye yana fad'in "A ganinki kenan."
Da kallo ta bishi tana jin yanda hankalinta ke sake tashi dan gaskiya wannan babban bala'i neke
tunkarosu, islamiya ? Inda za'a koya wa yaran sanin ubangijinsu? Shi ne zai tsigesu saboda
karatun da anfaninsa iya duniya ne kawai, shi ma a haka ba kowa da yayi shi ke morarshi ba.
Kamar wasa sai kuwa maganar nan ta zama babba, Safiya da abun ya dameta ta yi iya
k'ok'arinta wajen sake tuntub'arshi, amma a k'arshe mummunan kashedi ya kirta mata cewa zai
d'auki tsatsauran matakin da ya dace a kan ta idan ta sake mishi maganar nan, hakn yasa ta
tuntub'i wanda take ganin sun isa su fad'a masa su ji.
Duk shekarun da suka d'auka haka ba ta tab'a faruwa ba, amma sai dayawa suke ganin laifinta
dan su ma bokon suka sha suka k'oshi, dan haka suke ganin me ye a ciki to? Abinda yake
ganin ya fi mishi ne ya