Showing 48001 words to 50006 words out of 50006 words
Chapter 17 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
ce?"
Taɓe baki Ardiya tayi tace "Kowa dai na gidan nan ya san gaskiya na faɗa, na tabbata soyayya
ke hana Saleema karatu har sha'awarta ke ƙara tunzura, idan ba'a aurar da ita yanzu ba wata
rana abun kunya za ta ɗauko..."
Cokalin da take zuba miyar da shi dake hannunta ta buga a kan teburin da ƙarfi tana rintse ido
tace" Ya isheki haka."
Duk kallon Safiya sukayi da tayi kwaratsin, nuna Ardiya tayi da cokalin za ta yi magana, da sauri
Alhaji Yusuf ya miƙe tare da jawo Safiya jikinshi ya ɗan rumgumata, ba ya so ta ɗaga murya
sosai, ba ya so ta yi faɗa da Ardiya, ba ya so ta ɗaga hankalinta kamar yadda likita ya faɗa
masa a kiyaye duk wani tashin hankali da ɓaci ranta saboda cikin dake jikin na wata uku.
Yunƙurawa ta yi za ta tashi tana sake faɗin "Wallah..."
Hannu ya kai kan bakinta ya toshe cikin raɗa yace "Ya isa haka Sofeena, rabu da ita kinji
uwargidana."
A hankali ta dinga sauke numfashi tana ƙara tusa kanta a ƙirjinshi, shafa bayanta ya dinga yi
yana kallon fuskar Ardiya dake kumbura tana musu wani mugun kallo. Saleema kunya ce ta
sake kamata a ranta ta ayyana" Tofa! Mun dawo kenan, wai Abbanmu ba ya girma ne shi?"
Ɗago kai Safiya tayi ta kalleshi idanunta taf da hawaye tace" Dama ina son magana da kai."
Cike da kulawa da guje duk abin da zai ɓata mata rai ya tallabo haɓarta yace" Ina jinki, ko sai
mun shiga ciki?"
Turo baki tayi cike da shagwaɓa ta ɗan saci kallon Ardiya da har yanzu ke kallonsu tana
mamakin mijin na su, mamakinta bai wuce yadda in suna tare yake nuna ba wata sai ita ba, ko
aikace wasu lokuta ya na nuna mata ta fi Safiya mahimmanci, amma duba yanzu yanda yake ta
naniƙeta a gabansu wai dan tana da ciki, hmmmm! Ta faɗa tana ayyana "A haifeshi mu gani."
Safiya da ta fahimci haka cikin shagwaɓa tace "Dama kuɗi na ke so, kuma ka ga watan da ya
wuce ba ka bani komai ba."
Ajiyar zuciya ya sauke jin matsalar ta ta ba wata babba bace, dama dan bata aiki ya ɗauki
alƙawarin bata jaka saba'in kowane wata, duba da Ardiya tana aiki kuma tana ɗaukar albashi,
dan kar abun ya mata yawa ya shi ɗaukar wannan matakin, duk da wasu lokuta idan ya bata
ma sai ta ce ba ta buƙata ko kuma ta ɗauki rabi, wani lokaci kuma shi yake mantawa kamar dai
yanda ya yi watan da ya wuce.
Cikin sassauta murya yace "Shikenan, zan ganki anjima, yanzu je ki huta ɗakinki ina zuwa,
bana son hayaniyarki."
Jinjina kai tayi alamar to tare da nufa hanyar ɗakin na ta, da kallo duk suka bita har Hadeeya ta
taɓe baki, dan ita ba ta taɓa ganin haka ba sai yau, Saleema kuma zaman ne ta ji zai isheta
tunda babu mai tsaya mata a wurin, miƙewa tayi za ta bi bayanta ba kunya ba komai Alhaji
Yusuf yace "Kar ki sake ki takura min mata da matsalolinki, ciki ne da ita kuma bana son abin
da zai ɗaga mata hankali."
Rufe idanu Saleema tayi sai kuma ta girgiza kai tace "Ba wajenta zan je ba, falo zan zauna."
Tana wucewa Hadeeya ta kalleshi cike da wauta da gaɓanci tace "Abba, ka ga ni dai irin wayar
da na ke so ka siya min, ta ya ma Saleema za ta riƙe wannan wayar ni ina fama da wannan
Samsung."
Ko kallonta bai yi ba yace "Um um! Ban da arziƙin da zan siya miki wayar nan."
Turo baki tayi ta kalli Ardiya tace "Momma..."
Da yatsabta nunata tace "Kar ma ki fara, ubanki bai iya sai ni ce zan iya?"
Ɗan kallon Ardiya ya yi sai kuma ya girgiza kai ya ci gaba da cin abincinshi, Ardiya dake
kallonshi tana ta hassala ne tace "Shi ne ma ba zaka kulani ba."
Ɗagowa yayi yace "Me ya faru?"
Cike da masifa da harshenta na hausa da baya fita da kyau tace "Shi ne zaka wulaƙantani a
gabanta? Ka yi ta wani rumgumeta dan na gane ita ma mowa ce a wurinka."
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ki yi haƙuri to, ba dan ranki ya ɓace na yi ba, na faɗa miki yanda
likita yace game da lafiyarta, dole mu kiyaye ɓata mata sannan mu lallaɓata."
Jinjina kai tayi tace "Shikenan to ya yi, sai ka yi ta lallaɓatan ai."
Miƙewa tayi a hassale ta nufi ɗakinta, da sauri ya tashi ya bi bayanta dan ba zai so ita ma ta yi
hushi ba, dan wallahi alƙawari ya la kanshi cewa ba zai kuma kusantar Safiya ba sai ya ga
cikinta ya girma, dan yanzu gani yake motsi kaɗan zai sa ta yi ɓari.
*09:00* Safiya ta sameta ɗakinta har ta yi shirin bacci tana zaune kan gado tana karatu, da
fara'a ta ƙaraso ta zauna kusanta ta miƙo mata kuɗi, da sauri ta amsa tana murna ita ma,
ƙidaya kuɗin tayi ta kalleta tace "Mama duka wannan ne suka bayar?"
Da murmushi ta jinjina mata kai alamar e, ita ma jinjina kan tayi ta faɗa jikinta tace "Nagode
Mamana, gaskiya Abbanmu yana sonki."
Murmushi kawai ta sake yi amma ba ta musa mata ba, dan gaskiya ne ya na sonta kuma yana
yawan faɗa mata haka, sannan a aikace ma yana nuna mata, duk irin yanda take da sani kan
ya auro Ardiya ne saboda iliminta da wayewa, sannan ya na sonta da kuma ƴaƴanta kyawawa,
amma tana da tabbacin soyayya ta gaskiya yake mata, dan kuwa ba ta nemi komai ta rasa a
wajenshi ba, duk abin da zai ma Ardiya shi zai mata, idan zai kashe ma Ardiya million ɗaya to
ita ma haka, matsalar Saleema ce ma kawai ta sa wasu lokuta yake faɗa mata magana mai
ɗaci ko a gaban yaran, wanda hakan take ɗaukarsa a matsayin saɓani na ma'aurata. Amma ko
daren jiya da suka je asibiti aka faɗa masa tana da ciki, kai tsaye wajen cin abinci suka wuce ya
kashe mata kuɗi sosai a kan abinci kafin su zo gida, jimawar da sukayi yasa Ardiya rufeshi da
masifa har saida ya faɗa mata dalilin kaɗai.
Ɗagata tayi daga jikinta ta kalli fuskarta tace "Kin san me? Baƙi mukayi a gidanmu."
Da mamaki tace "Baƙi kuma? Su wa ye?"
Irin kallon tuhuma da tsokana ta mata tace "Alhaji Auwal ne da mahaifinshi, sai kuma... Yaya
Mu'az ɗinki."
Ta ƙarashe tana mata dariya, waro idanu tayi tace "Mu'az kuma?"
Da sauri ta nemi saukowa daga kan gadon tace "Mama mama, na roƙeki Mama kar ki bari Abba
ya biyewa haukan Mu'az, shi fa sam ba ya da hanakali."
Dariya ta ƙyalƙyale da ita tace "Zamu gani dai waye mahaukacin, yanzu tashi ki je Abbanki na
nemanki."
Kyaɓe fuska tayi kamar za ta yi kuka tace "Maaamaaa."
Ita ma kyaɓe fuska tayi tace "Na'aaaam.." Ɗaure fuska tayi tace "Tashi ki je."
Jiki a sanyaye ta miƙe ta ɗauki hijabinta iya gwiwa ta saka sannan ta fice cike da fatan ba abin
da take tunani ba ne zai faru. Dan in kuwa hakane to tabbas Mu'az bai da sanya a lamura kuma
ya mata shigar sauri, amma fa hakan ba ya na nufin za ta amsa buƙatarshi ba ne, duk da kuwa
bayan dawowarsu ta yi tunaninshi sau ɗaya, dan sosai kalaman nan na shi a haɗuwarsu ta
ƙarshe suka tsaya mata a zuciya da ma ƙwaƙwalwarta.
Tashin muryar Alhaji Auwal yasa ta nutsuwa sosai ta sadda kanta sosai duk da faɗuwar da
gabanta ke yi ta ƙwanƙwasa ƙofar tare da sallama a sanyaye sosai, ba tare da ya amsa ba
Alhaji Yusuf ya bata umarni da "Shigo."
Tura ƙofar tayi a hankali ta shiga takawa a nutse ba tare da ta ɗaga ta kalli kowa ba, ita dai
kawai ta ji idanun mutane a jikinta suna yawo, sannan daga ƙamshin turaren one million ta gane
kusurwar da Mu'az yake zaune dan shi ke anfani da turaren, daga kallon ƙafafu ta gane inda
mahaifinta yake, a kusa da shi ta zauna a ladabce tana faɗin "Ina wuninku."
"Lafiya lau Saleema." Alhaji Auwal da Papi suka faɗa a tare sai Alhaji Auwal da ya ɗora da
"Baby kin ga har na fara kewarku tun yanzu, ina ma za ki koma gidana da zama?"
Sai kuma ya yi dariya yace "Ko da yake abinda ya kawomu kenan, amsarki ita za ta bayyana
mana shin za ki rayu da mu ko akasin haka, dan babu wanda ya isa ya miki dole in dai ina
raye."
Wani kallo Mu'az ya watsa mishi ta ƙasan idanu da tunanin "Za ko kaga abin da zan yi, a cikin
gidan nan zan ɗirka mata ciki in ya so kwa shafa mana fatiha bayan raɗawa ɗanmu suna."
Maida dubanshi ya yi ga surukin na shi dake kallon Saleema yana faɗin "Mu'az ne dama ya ce
yana sonki, kuma ya ce kin san da maganar, yanzu haka sun zo neman aurenki, kin amince a
bashi aurenki?"
Alhaji Auwal ne ya katseshi da cewa "Ba ta amince a ba da aurenta ba, ta amince ta na
sonshi?"
Ɗaure fuska Alhaji Yusuf yayi dan shi wannan sa'a ta Saleema a ganinshi ba sai an tuntuɓeta
ba, dan kawai Papi da Alhaji Auwal ɗin sun matsa ne, wanda ya tasa dalilin da ya sa suke wani
ririta yarinyar, alamu ma nuna masa yake Alhaji Auwal zai iya yin komai dan Saleemar, kamar
dai wacce ta aikata masa wani babban abu da ba wanda ya taɓa kwatanta yi masa. Maida
dubanshi yaui ga Saleema yace "Muna jinki, kin amince?"
Daga cikin hijabi ta zuro hannunta ta share gumin da ya jiƙa mata goshi har zuwa dogon
hancinta, rawa jikinta ya kwasa da tunanin mafita, duk ƙoƙarinta na satar kallon Mu'az ta kasa
ganin fuskarshi saboda tsayinshi sannan ya shige cikin kujerar da yake zaune sosai, tana so ko
ya ne su haɗa idanu ta aika masa kallon "Ya za ka min haka? Haka kwatsam?"
Saidai rashin nasarar ganin fuskarshi yasa ta ɗauki sama da minti ɗaya ba ta amsa ba har ma
ta manta a ina take saboda tashin hankalin da take ciki, ba ta san me ye so ɗin ba kanshi, ba ta
san wane irin zama za ta yi da shi ba, hasalima ba ta jin komai a game da shi, sannan
abubuwan da ya dinga mata farkon haduwarsu ya saka mata shakku a kanshi, idan fa bai da
ɗabi'ar ƙwarai? Za ta rayu da baƙin ciki kenan har abada?
A kausashe Alhaji Yusuf yace "Malama ke fa muke jira, ya zaki wani yi mana shiru kamar
yaranki."
A gigice ta ɗago kanta, hakan ya ba hawayen da suka taru a idanunta damar zirarowa suka
sauko kan kutatunta, a kiɗile ta girgiza kai sai kuma ta kalli inda Mu'az yake, suna haɗa idanu
ya jefo mata kallon" Ki min rai Saleema."
Inda ita ma ta bishi da kallon" Ba zan iya ba Mu'az." Alhaji Auwal ne yace "Ƴata."
Kallonshi tayi saidai suna haɗa idanu ta fashe da kuka, cikin kulawa ya taso daga inda yake ya
zo kusanta ya tsuguna, cikin tausasawa yace" Baby, kina ji na? Idan ba ki shirya ba ki faɗa
mana, kamar yadda na faɗa miki da farko babu wanda zai miki dole, faɗi ina jinki?"
Sadda kanta tayi ƙasa cikin muryar kuka tace"...
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef:
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef:
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef:
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef:
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef:
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef:
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: