Showing 24001 words to 27000 words out of 50006 words
Chapter 9 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
ya lumshe ido a kafaɗarta kamar bacck zai
ɗauke shi. Tureshi tayi tace" Kai ɗagani, har yanzu ban shiga madafa ba."
Takwaf-takwaf ya yi da fuska yace" Mama yunwa fa na ke ji, shiyasa na shigo da wuri."
Nuna mishi ƙofar madafa ta yi tace" Ka shiga madafa ba za ka rasa abun da za ka ci ba."
Turo baki ya yi gaba ya nufi hanyar madafar ita ma ta ƙarasa in da za ta je sam ta ma manta da
Saleema na madafar.
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_11_
Yana shiga madafar ya tsaya cak! Ya na ƙare mata kallo daga baya, rumgume hannaye ya yi da
tunanin to ita haka take shigarta kullum? Ko kuma dai baƙunta ce ta sa haka? Sai kuma wata
zuciyar ta raya masa "Idan baƙunta ce ai ƴan uwanta ma baƙuntar suke, me ya hanasu kama
jikinsu kamar ita?"
"Tarbiyya ce kawai." Wata zuciyar ta bashi amsa, abaya ce jikinta da kallabinta wanda sam
jikinta bai bayyana ba, a hankali ya sauke hannayenshi daga ƙirjin ya shiga takawa gareta,
bayanta ya tsaya ya ɗan dubi tukunyar da ke kan wuta wacce take soya naman da ta samu a
fridge, tsilalar da yake na jajjagen da ke jikin naman kuma aka saka cikin mai me zafi, wannan
tsuwar ce ta hanata jin tako daga bayanta saboda tana ta ƙoƙarin kare kanta kar mai ya ki
ƙonata.
Ba ta ankara ba, ba ta san da faruwar abun ba, hannaye bibbiyu kawai ta ji sun zagaya
kumkuminta an kwantar da kai a bayanta cikin wata tattausar murya yace " *Leema* sann..."
Tunda ta ji irin ruƙunƙumewar da aka mata ta sa ma ranta mace ba za ta mata haka ba, ko da ta
ji muryar Mu'az tun bai gama maganar ba ta juyo a mugun tsorace kuma a fusace ta ɗauke
fuskarshi da mari ta bayan hannunta. Kallon kallo su ka tsaya kowa da irin fitinannen kallon da
yake aika wa ɗan uwanshi, ita kam mamaki da ɓacin rai ne suka lulluɓeta cike da dana-sanin
zuwa gidan nan da ta yi wanda sam babu alkairi a ciki sai jafa'i da ta ke gani kala-kala.
Shi kuma mamakin ƙarfin halin ta da kuma tsoron da ya ke hangowa a idonta mai ɗauke da
ɓacin rai na aljabi yasa shi sakin murmushi, a hnkali ya jaye hannunshi daga kumcinshi ya ɗa ja
baya kaɗan, cikin raha alamar dai abun bai wani ɓata ransa ba yace "Na samu abinda na ke so,
wannan shi ne abinda ya kamata na gani a tare da wacce na ke so sa'ilin da wani wanda bai da
hurumi a kan ta ya kai hannunsa jikinta, hakan alamu na cewa za ki iya yankar duk wanda ya yi
ƙoƙarin taɓa min *halaliyata*."
Wasu mugayen hawaye ma su zafin gaske ne suka kwaranyo mata daga kurmin ido na takacin
wannan rana da ta risketa, tunda ta balaga ko Mamanta kunya take ji ta rumgumeta bare kuma
Abbanta, amma yau ƙato da ba ta da haɗin komai da shi ne ya kwanta a bayanta tamkar wata
matarsa. Hannu tasa ta share hawayen ta furta "دمحلا لله يذلا هتمعنب متت تاحلاصلا (Godiya ta tabbata ga
Allah wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika)."
Da sauri ta yi azamar raɓashi za ta bar wurin duk da kuwa ta na jin naman da take suya ya na
neman ƙonewa, da sauri ya tare gabanta har tana neman faɗawa kan shi ya yi saurin faɗin
"Dakata."
Da sauri ta kalleshi cikin muryar kuka da kuma ƙunar da ke cin zuciyarta tace "Ka matsa min a
hanya, idan ba haka ba wallahi zan maka ihu."
Cike da isa ya rumgume hannaye a ƙirji yana murmushi yace "Bismillah, yi, ko ba ihu ba? Yi ihu
ki ce kwarto ne ni."
Da mugun sauri ta liƙe kunnuwanta tana fashewa da kuka ta durƙushe ƙasa tana faɗin "Dan
Allah ka rabu da ni, ka tafi ka bani wuri, wai me yasa ba ku da ɗa'a ne? Ku wasj irin karnuka
ne?"
Da wani mugun sauri ya finciko hannunta da alamar ya ji zafin kalmar ta ƙarshe, ba tare da ya
saki hannunta ba ya haɗata da bango ya matse mata wuri sosai, tsabar tsoron da ya kamata
yasa ta duƙar da kanta ta gandarawa hannunshi cizo. Amma da ke ranshi ya ɓace da ta
haɗashi da kare sai ya yi kamar bai ji ba, matse hannunta ya sake yi sosai har ta saki ƙara tana
matse fuskarta, Mu'az kam mutum ne mai son raha da barkwwanci, sai dai akwai abun da sam
ba ya ɗauka kuma a take ranshi ke ɓacewa. Cikin jin zafi ya kalli fuskarta yace "Wa ye kare? Ni
ki ke haɗawa da dabbar da ake ajiyewa dan tsaro kawai?"
Wani kukan ta sake sakawa mai ban tausayi tana neman sulalewa ƙasa a ƙasan maƙoshi ta
furta "Hannuna."
Da sauri ya kalli hannunta da ya matse, a hankali ya sassauta mata riƙo yana jin tausayinta na
mamaye zuciyarshi, saida ya saki hannunta gaba-ɗaya sannan ya sunkuyar da kai yace "Ki yi
haƙuri, kuma nagode da marina da ki ka yi."
Juyawa ya yi har zai fita sai kuma ya tsaya, a hankali ya tako ya dawo gabanta ya tsaya duk da
ta rufe fuska tana kuka, cikin tattausan murya mai kashe jiki yace " *Ina son ki*."
Da sauri ya juya ya fita a madafar ya ma manta me ya shigo da shi da fari, tana jin ya fita da
sauri ta ƙarasa gaban gas ɗin ta kashe wutar, tana kwashe naman ta na sako da hawaye har ta
kammala abinda ta fara sannan ta barsu a nan ta fita a madafar, tana haurawa sama tana
tunanin tafiyarta gida ne, ba zata iya zama a gidan nan ba ko kaɗan, ba ta sani ba ko
mahaifinsu ya san haka gidan yake ya turosu? Amma dai ba ta zauna ba ita kam, dan in suka
zauna daga ita har ƙannenta cikunna ne za su bayyana garesu nan da kwana kaɗan, dan ita
tsoronta kar shi ma uban haka ya ke ya fara ƙare musu kallo.
Tana shiga ɗakinsu da kuka ta share hawayenta ta nufi inda jakarta take da kayanta da basu
wuce guda uku ba bayan na bacci, Hadeeya na kwance da waya a hannunta, Hameeda ma
kwance take suna kallon hotuna a waya ita da Ummee, da kallo duk suka bita sanda ta ɗauki
jakar tana tattara kaya tana zubawa ciki, saida ta gama tsaf ta ɗauki zunbulelen hijabinta ta
saka, ta ɗauki jakar kenan za ta fita Hameeda da ta fi damuwa da abinda ta ga Saleema na yi
tace "Ina za ki je?"
Juyowa ta yi ta kalleta tace "Gida, sai kun zo."
Da mamaki Saleema tace "Gida kuma? Abba fa cewa ya yi..."
Cike da raini Hadeeya tace "Ki barta ta tafi mana, ai ta san Abba ya faɗa mana zai turo a
ɗaukemu bayan kwana biyu, shi ne dan ta rainashi za ta ce za ta tafi yanzu."
Dogon tsaki ta ja ta maida hankalinta ga abinda take, Hameeda kuma ci gaba da kallonta tayi
har saida ta fita a falon, tana sauka ƙasa Hajia Rabi na fitowa daga madafa, dama kuma ta
shiga ne dan ɗorawa Alhaji abinda ya buƙata, ta samu abun kari an gama shiryawa amma ba ta
ga Saleema ba, fitowarta dan ta duba ɗakinsu ne sai kuma suka haɗe.
Cike da kulawa da kuma fara'a a fuska tace "Yawwa Saleema, na duba ciki ai ban ganki ba,
ashe har kin gama girkin? Kai gaskiya Saleema kin yi ƙoƙari, dama haka kika iya girki?"
Hijabin da ta jawo tana ƙara goge fuskarta yasa Hajia Rabi ganin jakar dake hannunta, da
mamaki ta matso kusanta tana faɗin" A'a! Saleema ina za ki je da jaka kuma?"
Sunkuyar da kanta tayi cike da kunya da shaƙaƙƙiyar murya tace" Mama gida nake so na tafi,
ina kewar Mamana ne... "
Da sauri ta riƙo hannun Hajia tana ci gaba da faɗin" Dan Allah Mama kar ki hanani tafiya, ina so
na ga Mamana ne."
Sosai Hajia ta shiga mamaki da kuma zuba mata ido tana nazarinta da kuma son gano gaskiyar
kalamanta, cike da kokonto tace" Saleema, wani abu aka miki ne a gidan da ba ki ji daɗi ba?"
Da sauri ta girgiza kai tace" A'a Mama, ba abinda aka min, nk dai kawai ki barni na tafi."
Sakin hannunta tayi ta ƙara riƙe jakarta ta ɗan raɓata tace" Nagode Mama, sai anj..."
Riƙota Hajia tayi tace" A'a Saleema, ba zan barki ki tafi ba, ko dai ki faɗa min abinda aka miki?
Ko kuma na kira Alhaji na faɗa masa."
Kamar za ta durƙusa ƙasa ta shiga gurfanawa tana faɗin" Mama, Mama kar ki faɗa mana dan
Allah, Mamata na ke ji kamar tana cikin wani hali, ki barni na je na duba idan na sameta lafiya
sai na dawo."
"Ina za ki je?" Alhaji Auwal ya faɗa daga bayansu yana fitowa, tare suka kalleshi sai da
Saleema ta sauke ƙaƙƙarfan numfashi, saida ya ƙaraso gabansu ya tsaya yana kallon Saleema
yace "Ina na ke jin kina cewa za ki tafi?"
Tsareshi tayi da ido ta girgiza kai alamar ba komai, kallon Hajia ya yi yace "Me yake faruwa?"
Kallon Saleema tayi sannan ta kalleshi tace "Wai gida za ta tafi, na tambayeta me aka mata ta
ce ba komai."
Kallon Saleema ya yi da ke ta fiƙi-fiƙi da ido yace "Me aka miki?"
A raunane tace "Ba komai Abba, dama kewar Mama na yi."
Wani kallo ya watsa mata kafin yace "Je ki aaje jakar, ba haka mukayi da Abbanki ba, idan
kuma kin dage za ki tafi sai na kira na faɗa masa."
Da sauri tace "A'a Dan Allah, kaa yi haƙuri Abba na fasa tafiyar."
Hanyar ɗakin ta kama sai kuma ta juyo tace "Amma Abba Mu'a..."
Sai kuma ta ga kamar bai kyautu ta faɗa musu ba, dan haka ta juya da sauri kawai ta barsu nan
tsaye suna binta da kallo har ta shige sannan su ka bar wurin.
*Bayan minti 20*
Hamdeeya ce ta shigo da sauri ɗakin tace "Saleema wai in ji Abba ki zo."
Kallonta tayi kamar ta ce ba za ta zo ba, dan ta fi jin nutsuwa a zaman ɗakin, amma sai ta jinjina
kai tace "Ina zuwa."
Da gudu Hamdeeya ta fita kafin ta miƙe jiki a sanyaye ta ɗauki hijabinta akan riga da siket ɗin
da ta saka yanzu bayan ta yi wanka, cikin nutsuwa da dattako ta shiga taka matakalar, ba ta
ɗaga kai ta kalli inda ta ji mutanen suke ba, sai dai daga yanda take ji akwai ido sosai dake
yawo a jikinta, bata kuma tantance su waye a wurin ba.
Saida ta gama sauka sannan ta ɗan ɗaga kanta dan ta san inda za ta dosa, fahimtar Alhaji
Auwal ya na kan teburin cin abinci ya sa ta nufa can ɗin, tun kafin ta ƙarasa yace "Yawwa
zauna."
Kanta a sunkuye kamar wacce ta aikata abun kunya ta ja kujerar da ta kula ba kowa a kai ta
zauna, hannayenta da suka fito waje sanadiyar hijab ɗin ta mai hannu ta ɗora akan teburin ta
na wasa da yatsunta cike da kunya da ladabi. Hajia Rabi da ke kallonta cike da birgewa da
ƙaunar yarinyar tace "Saleema, ki saki jikinki kin ji, ki ci abinci."
Sai lokacin ta ɗaga kanta dan kallon Hajiar, sai dai a lokacin ta kula da waɗanda ke wurin, Alhaji
Auwal ne da amaryarshi, sai Hamdeeya da ita Hajiar da kuma wannan *kuren*, ba ta yarda ta
haɗa ido da shi ba dan jikinta ya bata kallonta yake, a hankali ta ja farantin gabanta ta ɗauki
cokalin ta fara tsakurar abincin. A sace ta kalli Hamdeeya cikin raɗa tace "Ina su Hadeeya?"
Nuna mata wani ɗakin ta yi dake nan ƙasa tace "Suna ɗakin Yaya Mu'awwaz."
Wani irin faɗuwar gaba ta ji ya ziyarceta, da sauri ta ƙwalalo ido tace "Me suke yi?"
Taɓe baki ta yi tace "Ni ma ban sani ba."
Ɗaga idonta tayi da niyyar kallon Alhaji Auwal, sai kuma idonta suka sauka cikin na Mu'az da ya
rumgume hannaye ya na kallon duk wani motsinta, shi da ma saboda ita ya tsaya wurin ba dan
ya ci abinci ba, wani irin kallo ne ya ke mata ya na jin shi dai kawai birgeshi ta yi lokaci ɗaya ba
dan kyanta ko nasabarta ba. Suna haɗa ido ya sakar mata murmushi cike da tsokana yace "Za
ki ci abincin? Ko na ɗura miki?"
Ɗan waro ido tayi da mamakin rashin kunyarshi, sai kuma ta ɗauke kai ta sake kallon Alhaji za
ta nemi izininshi, kafin ta yi magana Mu'az ya sake faɗin "Abba."
"Na'am." Ya faɗa yana maida kallonshi ga gareshi, Mu'az kuma Saleema ya ƙurawa ido ba tare
da yanayi na wasa a tare da shi ba yace "Na ce ko ka yi wa ƴarka miji ne?"
Shi da Hajia Rabi tare suka saki murmushi suna kallon Saleema, inda amarya ta yatsina fuska
ta kalli Mu'az ɗin ta na ganin me ye na wannan tambayar? Sam a ganinta bai ma kamata a ce
Mu'az ya yi wannan tunanin akan wannan yarinyar ba, dan ta na da labarin rashin iliminta da
wayewarta, yatsina baki tayi tana kallon Alhajin da yake faɗin "A'a, me ya sa ka tambaya aboki?
Ko dai ƴar ta wa ta sace tsoka ma fi mahimlanci ne a jikinka?"
Wata ƴar dariya yayi ya sunkuyar da kai sai kuma ya ɗago yace "Ni dai Abba idan ba ka mata
miji ba, to ku taimaka min kar na ƙara zama tuzuru a gidan nan, idan shekarar nan ta wyce ban
yi aure ba gallabarku zan yi."
Saleema da ta yi mutuwar zaune da ido kawai ta ke binshi kamar wani sabuwar halitta ne ta
gani, Alhaji Auwal kuma dariya kawai ya ke sai Hajia Rabi da ta ɗan dakeshi a kafaɗa tace"
Marar kunya kawai, me za ka yi to?"
Saleema ya kalla ido cikin ido ba tare da shayin komai ba yace" Ba zan bari ta zama ta kowa
ba, zan mayar da ita *mallakina* ko ba ta so."
Yanzu kam da ke ranta ya gama ɓaci na takaicin bawan Allahn nan, zabura ta yi ta miƙe da
sauri ta nufi hanyar madafa, dan gani take idan sama za ta hau za ta jima ba ta kai ba, da kallo
duk suka bita har ta ɓacewa ganinsu, cike da izgili da raini amarya ta kalli Mu'az tace "Wannan
yarinyar fa ba ajinka ba ce, ba ta da ilimi sannan ga ta ƴar ƙauye, ka nemi dai-dai da kai mana."
Kallonta yayi irin kallon nan na nidai ban saka bakinki ba, sannan ki min shiru ko ki ji ba daɗi, ya
mata wannan gargaɗin da ido ne dan kar ta hassala shi ya faɗa mata magana Abbanshi ya ce
ya rainata, dan haka yake so ta masa shiru kawai. Fahimtar kallon yasa ta ɗauke kai ta na sake
yatsina baki da tunanin "Ita ina ma za ta yarda Mu'awwaz ya ɗauko mata ajawo irin yarinyar
can?"
Da haka ma ta yanke shawarar tunkarar lahaifiyar yarinyar da maganar, dan ta san su ɗin
amare na musamman ne, idan suka yanke hukuncin to mazan za su ce ya yanku ne kawai.
Alhaji Auwal da farin cikin hakan ya kamashi kallon Mu'az ya yi yace" Karka damu aboki, indai
da gaske kake ka shirya za mu je wajen mahaifinta sai mu nemo aurenta."
Cikin jin daɗi Mu'az ya ba wa mahaifin na shi hannu suka tafa yana faɗin" Yawwa aboki, na ji
daɗi, idan mukayi sa'a ma ya amince nan kawai za ta zauna sai dai na mata lefe da gado."
Dungure masa kai Hajia Rabi tayi tace" Sheɗani, wato ba za ka bata damar sallama da iyayenta
ba kenan?"
Sosa ƙeya yayi yace" Wane sallama kuma Mama bayan ga waya? Ta je daga bayan idan ta
gama jego."
Buɗe baki Hajia tayi da mamaki da kuma kunyar maganar sa, Alhaji Auwal na dariya yace"
Abokina da alama yanzu kam ƴar manuniya ta fara azalzalarka ka yi aure ko?"
Bushewa sukayi da dariya shi da Mu'az sai Hajia Rabi da ta miƙe tana faɗin" Allah ya shiryaku
shirin addinin musulunci."
*Saleema* kuma na shiga madafa ta samu mai aikin nan tana wanke-wanke, a hankali ta rage
saurin da ta shigo da shi na bala'i da gwaramar da bawan can ke haɗa mata da bata san dalili
ba ta fara takawa har zuwa kusa da ita tana kallonta, ƙarara tsoro ya bayyana a matashiyar
kamar za ta arta a guje, saida ta samu tabbacin yarinyar da ta gani jiya ce sannan ta shiga ƙare
lata kallo daga sama zuwa ƙasa.
Bayan abubuwan nan da ita ma Allah ya hore mata guda biyu, wata cikakken ƙirji da mazaunai
ba ta ga wani abu da yarinyar ke da shi da za