Showing 33001 words to 36000 words out of 50006 words

Chapter 12 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf

30 Mar 2025

6144

wa da ita."

Ko kallon Nafissa bai yi ba ya ci gaba da aikinshi dan ba zai iya abin da suke buƙata ba, sun
ɗauki mintin da ya kai goma zaune wata mace ma ta zo karɓan ɗinkinta, a mutumce ya gaishe
da matar da kuma alamar sani a tsakaninsu, kujerar da ke gaban wata tela ya nuna mata yace
"Zauna ko, bari a ɗauko kayan."
Zaune tayi shi kuma ya leƙa ta tagar da ke gabanshi wajen samarin dake zaune yace "Kai zo
nan."

Jim kaɗan matashin nan na ɗazu ya shigo yace "Gani."

Kallonshi yayi yace "Ka ɗauko kayan Hajia."

Ƙarasa shiga shagon ya yi ya buɗa drower da suke aje kayan, a sauƙaƙe ya ɗaukosu tare da
ɗaukar leda ya saka a ciki ya bata, godiya ta yi ta fita shi ma saurayin zai fita Saleema tace "Kai
ma ka iya ɗinki?"

Kallonta ya yi yana dariy yace "Sarauniyar jin kai, ɗinki ai a jininmu ya ke, a nan shagon Babana
ya rasu, yanzu haka idan kika shiga gidan can za ki samu ƙannaina suna yanka wasu ɗinkuna
ko suna gamewa, yayin da ƙanena ke saka mana duwatsu idan akwai buƙatar hakan."

Kallon gidan da ya nuna mata tayi tace" Can ne gidan na ku?"

Ɗaga kai yayi yace" E."

Da sigar tausayi tace" Allah sarki, Allah jiƙan Babanmu."

Da fara'a ya amsa da" Ameen. "

Huzeifa kuma saida ya kalleta sanda ta ce *Babanmu*, ko a ina kuma ya za ma na su? Amma
ko ba komai girmamawarta ga na gaba da ita ya birgeshi, uwa uba yanda ta kwatanta tsohon
wasu da na ta, har matashin zai fita tayi saurin faɗin" Ba ka ji ba?"

Tsayawa yayi yana kallonta, a ɗan kunyace tace" Dama ina da sha'awar koyon ɗinki ne, ko zan
iya koya a wajenku?"

Cike da lura ta fahimci ya kalli Huzeifa, sai kuma ya kalleta yace" To ki yi magana da babban
Yaya, idan ya amince ba damuwa."

Da sauri Saleema ta juya ta kalli Huzeifa da za ka rantse ba ya gane yarensu, dawo da kallonta
tayi ga matashin tace" Yayan ka ne?"

Ɗaga kai ya yi yace" E, shi na ke bi wa, shi kuma shi ne babba a gid..."

Ɗan gyaran muryar da Huzeifa ya yi ya ankarar da shi ya kalleshi, rufe baki yayi da tafin hannu
yace" Yi haƙuri Yaya."

Ficewa ya yi a shagon hakan yasa Saleema juyawa ta kalli Huzeifa ranta ɓace kamar ta ce" Wai
me ye matsalarka?" Sai dai sam babu fuska a tare da shi bare ta yi maganar.

Yanzu kam ba wani jimawa ya gama ya miƙe tsaye, cikin drower ya ɗauko sauran an gogesu
tsaf ya haɗa da wanda ya ida ya saka a leda, miƙawa Nafissa ya yi yace" Gashi, dan Allah ki
basu haƙuri na jinkirin da aka samu."

Karɓa Nafissa tayi tace" Ba komai, ga ragowar kuɗin." Ta faɗa ta na miƙa mishi, karɓa ya yi ya
sa aljihu yace" Ki musu godiya."

Miƙewa sukayi suka fita a shagon, Saleema ba ta sake juyowa ba bare su kalli juna, shi kuma
yana tsaye har suka tsallaka titin suka shiga kwanar da mota ke jiransu yana kallon hijabinta da
ke taɓa diga-diginta duk in ta ɗaga ƙafar, saida suka ɓace mi shi ya koma ya zauna kan kujera
yana godiya ga Allah da ya bashi damar cika alƙawarin da ya ɗauka na ɗinkin nan tunda ga shi
har ya kammala ya bayar.


*Suna* isowa kai tsaye ɓangaren suka tunkara, daf da za su shiga motar Alhaji Auwal ta danno
kai cikin gidan, dakatawa Saleema ta yi yana gaba biyu daga cikin mutanenshi na bin shi a
baya, tarbanshi tayi cike da ladabi tace "Sannu da zuwa Abba."

Da fara'a sosai ya amsa da "Yawwa sannu Baby, ya gidan?"

Cike da kunya ta amsa da "Lafiya lau Abba, ya aiki?"

Cikin jin daɗi ya amsa da "Aiki da wahala yarinyata, amma tunda na dawo gida yanzu zan ɗan
huta."

Murmushi tayi tace "Allah ya baku ladar ɗawainiya da mu."

Jim ya yi yana kallonta kamar mai son gano wani abu a fuskarta, sai kuma ya jinjina kai yana
murmushi yace "Ɗawainiya da ku Baby ai dole, iyalinmu ne ku fa."

Ganin ba ta da niyyar shigewa ciki yasa ya nuna mata yace" Mu je ko."

Nuna masa hanyar bayan gida ta yi cike da son karkato hankalinshi tace" Abba zan je na ga
Papi ne."

Ɗan zabura ya yi kamar wanda ya manta da tsohon, sai kuma ya mata murmushi yace" To

shikenan, ni ma zan shiga yanzu na gansu idan na yi wanka."

Jinjina kai tayi alamar to ta juya ta nufi bayan gidan, shima ƙarasa shiga ya yi ya samu Hajia
Rabi na mitar ina Saleema ta tsaya, shi ne ya bata amsa" Ta shiga wajen Baba ne za ta
ganshi."

"Baba kuma?" Ta faɗa da mamaki kafin ta ɗora da "Me ya sa ba za ta zo ta huta ba?"

Taɓe baki ya yi alamar bai sani ba ya nufi ɗakinshi, fitowar amarya daga ɗakinta ne ta kalli Hajia
babba tace "Kamar Alhaji na ji ya shigo?"

"E, ya shiga ciki." Ta bata amsa ba yabo ba fallasa, dan tsakaninsu ba wani shaƙuwa ba ce
tsakaninsu da ake ma juna dariya ko sanin sirrin juna, ganin ta nufi ɗakin yasa ta faɗin "Ga
kayan nan an karɓo daga ɗinki."

Da fara'a ta dawo da baya tana faɗin "Dukansu kuma?"

"Um." Ta amsa mata tana zama kan kujera, kayan ta buɗa ta shiga dubawa tana cewa "Kai!
Gaskiya Huzeifa ya na da kirki, kin san ban ɗauka zai gama aikin nan a ɗan lokacin nan ba?"

Ɗan murmushi kawai tayi tace "Ai ya wuce haka."

"Gaskiya kam, kuma ga shi kamar dai yanda mu ka faɗa masa ya mana."

Kallon ɗinkunan da hirar da suke taɓawa musamman kan bikin da za'a yi jibi wanda kayan
shigar bikin ne na yasa har Alhaji Auwal ya fito ba ta sameshi da maganar da ta yi niyyar zuwa
su yi ba, dan ba za ta bari ta yi sanya ba, dole ta daki ƙarfe da zafi-zafinshi.

Juyawa sukayi a tare suka kalleshi yana fitowa sanye da doguwar riga, cike da kissa da
kwarkwasa amarya ta shagwaɓe fuska tace "Baby, shi ne ka fito ba ka jirani ba? Gashi kuma
ina son magana da kai."

Ɗan murmusawa ya yi yace "To ai ba guduwa zan yi ba, wajen Baba zan shiga, tun jiya rabona
da su."

Hanyar fita ya kama ta bishi da kallo cike da jin ƙarfin gwiwar tabbas zai amince da abin da za
ta zo mi shi da shi.

*Ya na* zuwa ya samu Saleema da mahaifinshi a ɗakin suna ta hira da dariya, da mamakin irin
dariyar da take ya ƙarasa yana zama bakin gadon yace "Me ki ke ma dariya haka?"

Wata dariyar ta ƙyalƙyale da ita ta nuna tsohon tace "Wallahi Papi ne ya ke ta cika min ciki da
dariya, labari suke bani."

Murmusawa ya yi ya kalli mahaifin na shi yace "Baba, ya jikin na ku?"

Cike da tsantsar ƙauna da kulawa dattijon ya amsa da "Alhamdulillah Auwalu, ka na lafiya?"

A tausashe ya amsa da "Lafiyata lau Baba, ka ci abinci?"

Cikin sarƙaƙƙiyar murya yace "Ban ci ba, amma kai ka ci ne?"

Da alamar damuwa da tambayar mahaifin na shi yace "Baba, sai ka dinga min tambayoyi kamar
wani ƙaramin yaro, hakan ya sa wasu lokuta bana son mu haɗu."

Shiru dattijon ya yi sai kuma a sanyaye sosai yace "To ka yi haƙuri, na saba ne idan ban
tambayeka ba bana jin daɗi."

Da sauri Saleema ta katsesu ta hanyar dafa hannun dattijon tace "Papi, na kawo ma ka abincin
ne?"

Ɗaga kai ya yi alamar e, miƙewa ta yi Alhaji Auwal yace "Ki haɗo da maganinshi."

Jinjina kai ta yi ta kama hanyar fita, ta na buɗewa Nafissa na shigowa ɗauke da abincin, karɓa
ta yi ita kuma ta koma dan wasu ayyukan. Dawowa ta yi ta zauna ta zuba da kanta sannan ta
ɗago ta miƙowa Alhaji Auwal da ke shirin tashi ya tafiyarsa, kallonta ya yi da alamar jiran ƙarin
bayani yace "Uhum?"
Saida ta yi takwaf-takwaf da fuskarta cike da sigar ladabi da biyayya a tausashe sosai tace
"Abba, na yau kawai ka ba wa mahaifinka abinci da hannunka, a shekarun nan na shi zai yarda
ka ciyar da shi ne ta hanyar bashi abinci a baki kamar yadda ya baka kana yaro, ba wai ta
hanyar saka mai aiki ta dafa ba sannan ta kawo masa ya ci, na san an ɗauki shekaru rabon da
ka ji shauƙi na mahaifi na fizgarka, ka fizgo wannan shauƙin ko hakan ya sa ka tuna da
mahaifinka na buƙatar kulawarka, *kai kaɗai kawai* ya ke da buƙata."

Sadda kanta tayi ƙasa ta saki murmushi tace" Abba, ka na damuwa saboda yawan tambayarsu
gareka, ba komai ya kawo hakan ba sai *soyayyar mahaifi ga ƙaramin ɗansa*, shi a wajenshi
har yanzu kulawarsa ka ke buƙata, ba zai zama cikakken mahaifi ba idan har ya na nauyin baki
wajen tambayar abin da ya shafi lafiyarka, harkokinka, farin cikinka da ma damuwarka, sannan
abun farin ciki ne yau a rayuwa a ce kana da wanda ya damu da kai, Abba, wallahi duk
soyayyar da iyalin nan na ka suke taƙamar suna maka bai kai rabin soyayyar da bawan Allahn
nan ya ke maka ba, hatta da ƴaƴan da ka haifa..."

Tunda ta fara maganar alamun komai na ratsashi ne ya bayyana a tare da shi, dan jikinshi yayi
sanyi kuma kanshi a ƙasa yake sai dai wani lokaci ya kan ɗago ya kalli mahaifin na shi da
alamar jin kunya, amma yanzu da ta ce wai har yaranshi sai yasa ya kalleta da mamaki, kamar

ta san me kallon ke nufi sai kuwa ta ce "E Abba, soyayyar da yake maka ta fi wacce suke maka,
sai dai idan muka kalla a zahiri shi ya na sonka ne saboda shi ya haifeka, su ma kuma suna
sonka ne saboda kai ka haifesu, ba fata na ke maka ba Abba, a yanzu ba na jin akwai wata
larura da za ta saka tsohon nan ya gujeka, amma yanzu Mu'az ko Mu'awwaz da za ka hanasu
auren wacce suke so, to fa idan ba Allah ya shirya maka su ba, tsaf za su bijire maka a kan
mace, kenan soyayyarsu ba haɗi da ta wanda ya kawoka duniya."

Burinta bai wuce kar ya ga zaƙewarta ba, ba ta so su ga ta cika shiga shirgin da ba na ta ba, sai
dai kuma akwai kurakuren da take ganin ya kamata su gyarasu, saida ta ɗan faɗaɗa murmushi
a ladabce tace" Dan Allah Abba kar ka fahimceni ba daidai ba, na yi magana ne saboda girma
da mahimmancin iyaye garemu, idan har shi kaɗai ya rage maka a rayuwa, ya dace ka ɓata ɗan
sauran lokacin da ya rage maka wajen kula da shi, duk rayuwarsa ya ɓata ta ne wajen kula da
kai, a yanzu da ya kawo ƙarfi yake kuma neman tallafi, kulawarka kaɗai yake buƙata, duk abin
da ka ke nema da yake ɗauke maka hankali daga nesantar mahaifinka, ba zai zama mai
albarka gareka ba saboda mahaifinka ba ya farin ciki da halin da ka ke sakashi a ciki.."

Sai kuma ta kalli tsohon da ya ƙureta da ido ya ma rasa akan me zai auna yarinyar, cikin kulawa
tace" Papi, ko kana farin ciki da zaman wurin nan kai kaɗai?"

Da sauri Alhaji Auwal ya kalleshi da son jin amsar da zai bayar, shi ma kallonshi ya yi da
tunanin ko ya masa kara? Sai kuma ya sunkuyar da kanshi ƙasa saboda ba ya so ya sosa
ranshi ko kaɗan, wani murmushi Saleema ta yi mai ciwo ta kalli Alhaji Auwal tace "Wani shirun
ma amsa ce."
A hankali ta rusuna ta aje farantin abincin sannan ta miƙe tsaye tana kallon Alhaji Auwal tace
"Idan har ka yi yaƙi sheɗan kuma ka yi nasara, to na san za ka yi abin da ya dace kan
lamarinshi, sannan za ka ci gaba da yi har sanda mai rabawa za ta rabaku kuna mai cike da
alhini da ƙaunar junanku."
Idonta cike da hawaye ta matso kusa da Alhaji Auwal ta ɗan riƙe hannunshi tace" Abba, kafin
kai ko shi wani ya bar duniya, ya kamata ya shaida arziƙi da ikon da Allah ya baka ta sanadiyar
jajircewarshi a kan ka har ka zama hakan."

Juyawa ta yi ta kalli tsohon da fara sharar hawaye saboda taɓo masa ciwon da ya jima yana
gwaguyarsa, cike da tsokana ta marairaice ta kama kunnuwanta tace" Ayya! Papi ya na kuka
saboda na taɓa masa ɗan gudaliyarsa."

Da sauri ta riƙe hannunshi ɗaya tace" To a gafarceni ba zan sake ba, na barku lafiya."

Ta faɗa tana ficewa a ɗakin da sauri-sauri, jiki a matuƙar sanyaye tsohon ya bita da kallo yana
mai saka mata albarka, ko ba'a samu canji ba aƙalla dai ta sauke nauyin da ya hau kanta na
faɗin gaskiya da gyara kayanka, Alhaji Auwal kuma kanshi na sadde ya kasa ɗagawa saboda
tsananin kunya da nadama da kuma ƙudirin gyarawa da ya ɗarsu a zuciyarshi yanzu yanzun

nan.


Tsugunno ya yi a gaban mahaifin na shi ya riƙo hannayenshi kanshi a ƙasa cikin muryar da ke
ɗauke da amon nadama yaxe "Baba ka yi haƙuri ka yafe min, na tuba Baba ba z..."

Da sauri yace masa "Shikenan Auwalu, ya isa haka ka ji ko, ni dama ban taɓa riƙeka a zuciyata
ba, saboda na san illar hakan, bana so mutuwa ta riskeni ina mai hushi da kai, shiyasa duk
yanda raina ya ɓace a game da halin ko in kula da ka ke nuna min sai na yi gaggawar yafe
maka."
Hannayen mahaifin na shi ya ɗago ya sumbata har sau uku sannan ya durƙusa gwiwoyinshi ya
rumgumo tsohon na shi ya sumbaci wuyanshi, shi kuma da abun ya zo masa da rashin sabo sai
ya ji kunya ta kama shi, rintse ido ya yi sai dai yana jin ƙaunar ɗan na shi na sake narkuwa a
cikin jikinshi, ɓangare ɗaya kuma soyayya yarinyar nan ya ji ta mamaye zuciyarshi da kuma
saka mata albarka. Alhaji Auwal ma albarkar ya ke saka mata tare da ba wa kansa tabbacin
wannan dole ma ta zama surukar gidanshi, wata zuciyar kuma na raya mi shi ba dan ɗanshi ya
rigashi ba ai da shi zai so samun wannan *zinariyar waliyiyar*, dan babu wanda ba ya son
alkairi wa kansa? Amma a hakan ma idan har ta zama matar ɗanshi, to shakka babu za ta ci
gaba da ɗorasu a siraɗin rayuwa miƙaƙƙiya.

Bai fita a ɗakin nan ba sai da ya ba wa mahaifinshi abinci a baki ya sha maganinshi, wani abun
farin cikin kuma yanda suke hira tsohon na taɓo yarinyar Alhaji Auwal wanda shi bai san ya yi
ba, wani kuma ya sani amma ya manta saboda shekaru, sai ya sake yarda da abin da Saleema
ta faɗa cewa har yanzu shi a ƙaramin yaro yake kallonshi tunda shi ya haifesa, to in ba haka ba
har fa labarin lokacin da ya yi bayan-gari yake bashi daga makaranta, haka ya ɗauki awa biyu
suna nishaɗi kuma har zuciyarshi sai ya ji kamar ya sauke wani nauyi mai girman gaske da ya
jima yana dakonshi a kai.


A farfajiyar gidan suke zaune kowa ya na abin da ya fisheshi, motar Mu'az ce ta shigo gidan ya
nufi inda ake aje motocin, da gudu Hamdeeya ta tunkareshi dan tarbanshi, kamar an kirata ita
ma sai kuwa ta miƙe duk da kayan da ke jikinta. Ta wutsiyar ido Saleema ta kalleta sai kuma ta
maida dubanta ga gyaran persil ɗin da take taimakawa Nafissa, har ya fito daga motar yana riƙe
da hannun Hamdeeya, ita ma Hadeeya ta na ƙarasawa ta riƙo hannunshi tana kallon kyakyawar
fuskarshi tace "Sannu da zuwa Yayana."

Kallonta yayi da fara'a ya amsa da "Sannu budurwata, kina lafiya?"

Farrr! Ta masa da ido alamar e, ƙare mata kallo yayi ya kanne mata ido ɗaya yace "Uhum! Kin
ganki kuwa? Gaskiya kin yi kyau sosai."

Murmushi tayi tace "Dama kai na yi wa."

Da mamaki yace "Da gaske?"

Jinjina kai tayi, ɗan kallon Hamdeeya yayi ya miƙa mata wayarshi yace "Je ki ina zuwa."

Karɓa tayi da farin ciki ta juya shi kum ya kalli Hadeeya ya saki hannunta ya riƙe haɓa yace "To
juya na gani in dai ni aka wa kwalliyar."

Rufe fuska tayi da tafukan hannaye alamar kunya, a haka kuma ta juya masa bayanta sannan
ta juyo, daga sama har ƙasa ya ƙare mata kallo, irin ɗan guntun siket ɗin dake jikinta da rigar,
ba ƙarya kayan sun mata kyau, matsowa ya yi kusanta sosai ba tare da ta ankara ba ta ji ya
shafo mazaunanta cikin wani irin yanayi yace "Gaskiya ƙanwata ke babbar yarinya ce..."
Da sauri ta kalleshi amma yanda ya yi narai-narai da ido kamar zai yi kuka yace "Ba ki ban
amsa ba har yanzu, ko dai..."

Sai kuma yayi shiru ya jawo hannunta gaba-ɗaya ta faɗa ƙirjinshi ya tsare fuskarta da kallo,
kallon fuskarshi ita ma take tana ganin idan fa ta samu guyen nan ba ƙaramin kamu ta yi ba,
masha Allah son kowa ƙin wanda ya rasa, ga wata ƙasumba da gemu irin na ƴan zamani da ya
ma fuskarshi ƙawanya. Da sauri ta dawo hayyacinta sanda ya sake faɗin "Ina jinki mana cheri,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login