Showing 15001 words to 18000 words out of 50006 words

Chapter 6 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf

30 Mar 2025

6147

dai duk kin iya wannan? Idan ma ba ki iya ba ina fata za ki
koya saboda ni."

Tunda ya fara magana ta zuba masa ido ta na kallo, dogon bayanin nan da ya zauna ya na
mata sai ta ji kanta ma ya fara ciwo, to ita kam ta rasa hadisi na nawa ya karanta mata, a
gaskiya ba ta ma gama fahimtar zancen shi ba, dan haka ta na buk'atar k'arin bayani.

D'an gyara zama ta yi tana kallonshi tace "Bebe ban gane ba, ka min dalla-dalla mana, ka na
nufin ni ma sai na koyi iya tuk'a tuwo kenan?"

Murmushi ya mata yace "B za ki iya ba kenan?"

Kawar da kai ta yi tana nazari na wasu dakik'u, a gaskiya duk yanda take so da k'aunarshi ba za
ta iya wannan wahalar ba, amma kuma sanin waye Huzeifa ya sa ta d'an yi wata shawarar,
tunda dama ba shi ya fara cewa ya na son ta ba, ita ce ta ji ta na k'aunarshi saboda kyawawan
halayenshi har ta masa tayin soyayyarta, da fari kam ya nuna baya ra'ayi saboda kasancewarta
'yar mai kud'in unguwarsu, amma da ta dage ya kuma shawarci mahaifiyarshi sai ya amince har
yanzu suke shirin zama mata da miji nan da kwanakin da ba zasu gaza goma sha biyar ba. Dan
haka ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace "Bebe, ai kasan soyayya ta sa na ce ina sonka,
dan haka ba abinda ba zan iya yi maka ba."

Fad'ad'a Murmushin shi ya yi yace "Nagode sosai, ai na d'auka ba za ki yi ba."

Da irin zolaya tace "Ni na isa? Idan fa ka fasa aurena?"

Dariya ya yi cikin tattausar muryarshi yace "Ba zan fasa aurenki ba, sai dai na miki kishiya
bayan auren."

Zaro ido ta yi ta dafe k'irjinta cike da tashin hankalin da ya ziyarceta lokaci d'aya tace "Bebe,
dan Allah ka daina min irin wasar nan bana so..."

Tsal! Ta taso daga kan kujerarta ta dawo kusa da shi sai dai dake babu wata kujerar sai ta
durk'usa k'asa ta rik'o hannunshi, da sauri ya d'an jaye hannunshi saboda gudun matsala, dan
baya son ya sake shiga halin da ya shiga d'azu daga kallon wata.

Sake rik'o hannun na shi tayi ta rik'e gam tana kallon idonshi da na ta idon da sukayi jajir suka
tara ruwa alamar kuka, cikin rikitacciyar murya ta dinga mitsika hannunshi ta na fad'in "Ka na ji
ko Bébé ? Dan Allah ka daina irin haka bana so, ka ga ba zan iya kishi da wata a kan ka ba,
dan Allah ka min alk'awarin ba za ka tab'a min kishiya ba?"
Da mad'aukakin mamaki ya kalleta sosai ya na nazartarta, daga bisani numfashi ya sauke yana
ci gaba da kallonta yace" Tashi ki zauna, kina ga fa kallonmu a ke."

"Ni ban damu ba su kallemu, ka min alk'awari ka ji mijina." Ta fad'a da alamar fashewa da kuka,
jinjina kai ya yi yasake nuna mata wurin zaman da d'aya hannunshi yace "Dan Allah ki zauna
sai mu yi magana."

Da sauri ta mik'e ta zauna ka kujerar ta zuba mi shi ido ta na kallo kamar wanda take son gano
ta inda yake fitar da numfashi. A hankali Huzeifa ya d'an girgiza mata kai cikin sanyayyar
muryar da hakan d'abi'arsa ce yace mata" Ba zan iya miki wannan alk'awarin ba *Sharha*,
saboda ni d'an adam ne ban san me Allah ya tsara min a gaba ba."
Jin hakan daga bakinshi ya sa ta fashewa da kuka da iya gaskiyarta kawai ta kifa kanta a kan
teburin, cike da damuwa da jin tana muzantashi cikin mutane ya k'ara tausasa murya yace" Dan
Allah Sharha ki daina kukan nan, kin ga tashi mu bar nan in dai kuka za ki min."

Kamar ba ta san ya na yi ba haka ta dakeshi, mik'ewa ya yi ya sake maimaita" Tashi mu je na
ce."

Nan ma shirun ta masa, ranshi ne ya d'an fara b'aci dan haka ya zagaya kusanta ya d'auki
jakarta da wayarta da makullai dake aje, bai tsaya jiran komai ba ya finciki hannunta suka fita a
wajen dan shi fa duk taushinshi mutum ne kuma da baya son iskanci, sam ba zai lamunci ta
mayar da shi wani lusari ba dan baya da kud'i sannan *mad'inki ne* shi, haka kawai ba za'a
raina masa wayo ba, ta ya ma zai mata wannan alk'awarin? Ta san me alk'awari yake nufi a
shari'ance? Ta san me zai faru da shi idan Allah bai nufeshi da cikawa ba? Ba ma duk wannan
ba shi fa gaskiya *mace mai addini* ya ke da burin samu, hakan yasa ya ke tunanin ko ya
aureta idan bai sameta yanda ya ke buk'ata ba to indai ya samu halin k'ara aure to zai k'ara, sai
kuma ta nemi katse masa hanzarinsa da wani tunaninta irin na hayudawa haka kawai.

Tuk'i kawai yake a motar ta ya na kallonta jefi-jefi, yanda ta d'aga hankalinta akan tashin d'aukar
mata alk'awarin nan da irin kukan da ta yi, a ganinshi ko iyayenta aka ce sun rasu iya hakan ne
kawai za ta yi, idonta sun yi jajir sosai sun kumbura abu ga jar fatar da ba ta saba da hayaniya
ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon gabanshi yace "Ki yi shiru Bebe, kukanki fa ya na tab'a

min zuciyata sosai."

"To idan ka hakane ka min alk'awarin mana." Ta fad'a kamar za ta matso daf da shi ta sumbace
shi, d'an tab'e baki kawai ya ui ya girgiza kai bai ce mata komai ba, cikin tausa murya tace
"Bebe me ye a ciki ne wai? Alk'awari fa kawai za ka d'auka da fatar baki."

Wata nauyayyar ajiyar zuciyar ya sake saukewa yace "Sharhasila hadisin Anas d'an Malik fa ya
ji daga bakin Manzon Allah (S. A. W) ya ce" Alamomin munafiki guda uku ne, idan zai yi
magana sai ya yi k'arya, idan ya yi alk'awari ya sab'a, idan aka amince mi shi ya ci amana..."

Kallonta yayi fuskarshi d'auke da damuwa sosai yace" Duka wannan alamomin za su tabbata a
kaina idan na miki abinda kike so yanzu, na farko idan na fad'a miki ni na san k'arya na miki har
cikin raina, idan kuma ban cika alk'awarin ba kin ga na sab'a, sannan na ci amanar yardar da
kika min, to me ye ribar hakan? Me zai sa na jefa kaina a wannan halakar ? Alk'awari d'aya da
zan iya yi miki shine, ko bayan aurenmu zan zama mai mi yi miki uzuri, sannan ko da Allah ya
jarabceni da k'ara aure, to zan ci gaba da kare martaba da kimarki a idon d'ayar, ba zan tab'a
bari ki zubar da hawaye ta dalilina ba kuma da sanina, sai dai abisa rashin sani, wannan
alk'awarina ne gareki."

Wata arniyar harara ta maka masa ta gefen ido dan ita sam abinda ya fad'a ta kunnen da ya fi
kusa da shi ya shiga ko d'ya kunnen bai kai ba ya fita abunshi, ya zai tsareta da wasu
zantukanshi na daban kawai da wasu tatsuniyoyi? Ba ta ce mishi k'ala ba har suka isa k'ofar
gidansu.
Fita duk sukayi inda ta zauna mazaunin dreba shi kuma ya kalleta yace "Ni zan idasa gida a
k'afa, sai da safe."

A shagwab'e tace "Ba za ka kirani ba?"

Shafa sumar kanshi ya yi yace "E to...kin san fa jibi za mu fara jarabawarmu (BAC) karatu yayi
zafi sosai, amma dai zan kok'arta na kiraki."

Turo d'an k'aramin bakinta ta yi tace "Tom, sai na ji ka."

Da haka suka rabu ita ma ta shige k'aton gidansu kowa da abinda yake ta sak'awa da
warwarewa a zuciyarshi, inda Huzeifa ya fi maida hankali kan irin zaman da zaiyi da yarinyar da
take ganin mahaifinta mai kud'i ne, shi kuma d'an ladanin da ya rasu ya barshi da nauyin
k'annanshi da mahaifiyarsu wanda ya ke ciyar da su ta hanyar d'inkin da yake d'an samu idan
ba ya karatu, yarinyar da aka ma hanya duk da takardunta ba su kai ba amma take aiki a
babban reshen kamfanin shiga da fitar kud'i na *Al'izza*, shi kuma yanzu ne ma yake karatun,
dan ko ya samu jarabawar nan yana da burin ci gaba da karatunshi.

*Ku yi hak'uri da rashin ganin update jiya, hakan ya faru ne sakamakon wasu uzurirrika.*



*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BAIWATA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ��
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️


_Bismillahir rahamanir rahim_


_8_




Kiran da aka mana cewa mu zo mu ci abinci ya sa Saleema fitowa daga ɗakin bayan idar da
sallah isha'i, rufe ƙofar ɗakin ta yi ta fara takawa a hankali, cikin nutsuwa ta ke saukowa daga
matakalar benen har ta sauko ƙasa, za ta nufi teburin cin abincin da ta hangi mutanen gidan ta

dan tsaya saboda jerawa da sukayi da Mu'az shi ma zai nufi teburin.

Ɗan satar kallonshi ta yi ta gefen ido ta taɓe baki, Mu'az dake kallonta ya na so ya san wacece
wannan? Cikin shan-ƙamshi da tsareta da ido yace "Sannu."

Kallonshi ta yi sosai, haɗaɗɗen saurayi mai ilimin boko da wayewa irin ta zamani, sa kawai ta
ɗan ɗaga masa kai alamar "Kai ma sannu."

Da mamakin yanda ta amsa mi shi ya bita da kallo sanda take ƙarasawa wajen teburin, tana isa
ta dan dakata tare da faɗin"Ina wuninku."

Alhaji Auwal ne ya fara amsawa da fara'a yace" Lafiya lau ma puce, kin sauko?"

Cike da kunyar sunan da ya kirata da shi ta ɗan jinjina kai sannan ta ja kujerar da Hajia babba
ta nuna mata ta zauna. Dara-daran idonta ta ɗaga ta kalli Mu'az da shi ma ya ja kujerar da ke
fuskantarta ya zauna ya na binta da ido kamar maye, ɗauke kai ta yi tana ɗan gunguni ciki-ciki.

Ummeeta ta kalla da suke maƙale da juna ita da Hadeeya tace "Sannu Ummee."

Yatsina fuska Ummee ta yi tace "Sannu."

"Abba ita ma wannan ƴar tonton ce?"

A sanyaye sosai ta maida dubanga zuwa ga wanda ya yi maganar, wato ɗaya sheɗanin ne ba?
Mu'awwaz ko? Haɗa ido su ka yi hakan yasa ta yi saurin ɗauke kanta, Alhaji Auwal da ke
murmushi ne yace "Wai ba ka ganeta ba abokina? Mai sunan Hajia ce fa."

Waro ido sosai Mu'awwaz ya yi yana kallon Saleema yace "Abba Saleema fa? Ita ce ta koma
haka?"

Wani mugun kallo ta aika masa cike da takaicin rashin sako hijab ɗinta da ba ta yi ba, hakan
kuma ya faru ne da tunanin doguwar riga ce jikinta kuma ban da samari ake cin abincin,
murguɗa masa baki tayi duba da shi kan shi fa shekara biyu zuwa uku ne ya bata, amma abu
ga ɗan hutu ya zama wani karbcece masha Allah, ka rantse ba su yi wasar ƙasa tare ba.
Hajia babba ma dake murmushi cike da dattako tace "Girman mace ai ba wuya, kai ma da ke
namiji ba gashi ka haɗemu wajen tsayi ba."

Mu'az da ke ta kallonta yana taunar leɓe ne yace "Gaskiya kam, gashi ta girma...sosai."

Da sauri Saleema ta kalleshi, amma sai ya dinga aiko mata da wani kallo irin na iskanci a
ganinta yana kashe mata ido ɗaya, ɗan cire takalminshi ya yi daga ƙafa ya zuro ƙafar ta ƙasan
teburin ya zunguri ƙafarta, da sauri ta jaye ƙafar ta na waro ido ta kalleshi sosai, sake kashe

mata ido ya yi hakan ya hassalata ta wurga masa harara.

Hajia ƙarama da ta miƙo masa abinci amma bai kula ba ne tace "Mu'az."

Da sauri ya kalleta sai kuma ya girgiza kai yace "Um um! Zan sha kayan marmarin nan kawai,
kun san sun fi..."

Sai kuma ya kalli Saleema yana ɗaukar tuffa dake kusanshi sannan yace "Sun fi daɗi da ƙara
lafiya ko ya ki ka ce mai sunan tsofaffi?"

Buɗe ɗan bakinta tayi kamar za ta yi magana, sai kuma ta yi shiru dan bata san me yake nufi da
abinda ya faɗa ba. Hadeeya da kujerarta ke kusa da ta shi a ɓangaren ce ta kalleshi tace "Yaya
ka ci abinci fa, wannan ba zai riƙeka ba."

Kallonta yayi da fara'a a fuskarshi yace "Hadeeya ko?" Jinjina kai tayi alamar e tare da sakin
murmushi, hannu ya miƙa mata alamar su gaisa yana faɗin "Kina lafiya?"

Ba tare da tunanin komai ba ta miƙa masa hannun suka gaisa, hannayen na su Saleema ta
kalla sai kuma ta kalli Hadeeya, girgiza kai ta yi ta sunkuyar da kanta ta fara wasa da cokalin
hannunta, babban abun takaici shine yanda ya yi haka a gaban iyayenshi amma ba wanda ya
nuna ya damu.
Muryar Alhaji Auwal ce ta saka ta ɗaga kanta sanda yake faɗin "Mu'awwaz idan kun kamala ka
tafi da su alimentation idan akwai abunda suke da buƙata sai ku siyo."

Jinjina kai Mu'awwaz yayi yace "To Abba."

"Ka barshi ma ni zan kaisu." Cewar Mu'az yana ci gaba da kallon Saleema, bai san me yake ji
ba a kanta ba, sai dai ya ji yana sha'awar komai na jikinta, duk da ba kyawun fuska ne da ita ba
na nunawa a jarida, ba kuma jar fata gareta ba kamar ƴan uwanta, amma dai komai na ta ya
birgeshi musamman da ya fahimci ya fi sauran ƴan uwan na ta nutsuwa da kamun kai.
Wani kallo Mu'awwaz ya masa dake nuni da bai ji daɗin abinda Yayan na shi ya masa ba,
wannan ai katse hanzari ne, ya na tunanin ya fita da ƴan mata su shanawarsu, musamman ma
Hameeda da ta fi ɗaukar hankalinshi, sai kawai ya ce shi zai kaisu? Wallahi ba dan ya na tsoron
ya yi magana ya kabta masa mari ba, da ya masa magana sai dai a yi duk wacce za'a yi. Da
harara ya bi Mu'az ɗin da ya miƙe yana faɗin "Ummee ina jiranku a waje."

Saida ya ƙara matsowa kusan Saleema ya ɗora hannayenshi a kan teburin ya sunkuyo sosai
kamar zai sumbaceta, jaye fuskarta tayi daga kallonshi tana yatsina fuska cike da kunya, duka
mutanen kallonsu suke, su Hadeeya mamakin yanda ya ke ma Saleemar su ke, ko bai gane ita
ɗin ba mai aji ba ce? Yayin da amarya ta ke taɓe baki da tunanin "Ɗan iska kawai, a gaban
mutane ma sai ya nuna halin iskancin da tambaɗewa."

Hajia babba kuma murmushi take a ran ta tana ayyana "In har Saleema za ta zama alkairi
gareka zan fi kowa farin ciki." Dan kuwa ta fi kowa sanin ɗanta, ba ta taɓa ganin ya wa mace
haka ba, shi Alhaji Auwal kuma murmushi kawai ya ke saki a fuskarshi, ko ba komai ƴaƴan
Alhaji Yusuf za su ji daɗin zama gidan.
Cikin sanyin murya Mu'az yace mata" Ina jiranki, ki fito da wuri."

Juyawa ya yi kawai ya fice a falon, kasa ɗaga kanta tayi bare ta kalli mutanen wurin, sai da ta ji
sun maida hankulansu kan abincin sannan ta ɗan ɗago ta kalli Alhaji Auwal, cikin taushin murya
da ladabi tace" Am! Abba."

Cike da kulawa ya kalleta yace" Na'am ƴata."

A sanyaye tace" Ina ganin su tafi kawai, ni zan zauna a gida."

Da mamaki a fuskarshi yace" Me yasa? Ke ba kya buƙatar komai ne?"

Ɗaga kai tayi alamar e, wata harara Hadeeya ta jefo mata cike da takaicin me yasa wau ita take
da kidahumanci ne? Kuɗi ne fa za'a kashe musu, ɗauke kai ta yi cike da baƙin ciki, Saleema
kuma da ta kula da kallon ba ta biyata ba bare ta samu damar faɗa mata wata maganar marar
daɗi.
Hameeda a da saida ta harari Saleema cike da rashin kunya tace "Abba ka ƙyaleta ita dama
haka take, mu za mu je mu siyo abinda mu ke so."

Kallon Hameeda ya yi da mamakin yanda ta ke magana akan Yayarta haka, shi fa duk bokonshi
da iskancinshi ya na so ya ga ƙarami na girmama babba, girman da ubansu ya ke bashi ne
matsayinshi na wanda ke sama da shi a komai ya sa suke kamar abokai, ko Mu'awwaz da ke
namiji bai yarda ya raina Mu'az ba tunda ya na gaba da shi, bare ita wannan da ba ita ke bi ma
Saleema ba. Ɗauke kai kawai ya yi da tunanin idan ya ƙara ganin haka zai tsawatar mata, dan
sam ba ya lamuntar irin haka.

Shigowar wata matashiyar yarinya da ba za ta wyce tsarar Hameeda ba yasa Saleema kallon
ƙofar, Alhaji Auwal ma cike da kulawa ya kalleta yace "Kin kai musu abincinsu?"

A ladabce yarinyar da sai yanzu Saleema ta fahimci ƴar aiki ce tace "E Alhaji na kai musu, sun
tafi masallaci ma sai da na jirasu."

Jinjina kai ya yi yace "To da kyau, kin gama aikin ki ne yanzu?"

Cikin ladabi tana ta rarraba ido tsakanin Alhaji Auwal ɗin da kuma amaryar sa da ke binta da
kallon ƙyama a ɗan tsorace ta amsa da "E na idar."

"Shikenan za ki iya tafiya." Ya faɗa yana ci gaba da cin abincin shi, tsaf Saleema ta kula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login