Showing 45001 words to 48000 words out of 50006 words
Chapter 16 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
cajeshi yana laluba duka aljijunanshi daga na gefe-gefe
har na baya, ai kam sai ga kwalin sigari da maƙyasta, cirosu ya yi ya shiga ƙare masa kallo
yace "Mu'awwaz bayan neman matan yanzu kula shaye-shaye za ka fara? Wai me ka ke
neman maida rayuwarka ne? Ka kuwa san illar haka?"
Saleema dake gefe tana kallonsu kiran da Mamanta ta mata dan ta tambayeta ko ta ga lambar
ne ya sa ta juyawa da niyyar barinsu nan su ci kansu idan suna so. Mu'az da dama ya ke son
kora mata kashedi a kan tayi nesa da ƙanin na shi a zafafe ya gusa daga wajen Mu'awwaz tare
gabanta yana kai hannu kamar zai riƙe hijabinta, kallon da ta aika mishi yasa shi dakatawa ya
sunkuyar da kai yana ɗaga hannu alamar saranda yace "Shikenan na gane, kinga ni na miki
alƙawarin zan kiyaye taɓaki har sai bayan aure."
Sai kuma ya kalli fuskarta yana sauke numfashi kamar wanda ya yi gudu ya nunamata inda
Mu'awwaz yake da idanu yace "Kinga wannan?"
Wayam! Ba Mu'awwaz har ya bar wurin, ba tare da ta ɗauke kanta ba ta ci gaba da kallonshi da
mamakin shasheƙar da yake, ɗorawa ya yi da "Saleema dan Allah ki kiyaye shi, wallahi bai da
mutumci ko kaɗan, kinga idan kina tsayawa tare da shi komai zai iya faruwa, Saleema ni na san
Mu'awwaz wallahi har ta ƙarfi zai iya yi miki abin da bana so."
Wani kallo ta jefeshi da shi tace "Me ye baka so ɗin?"
Sadda kanshi yayi kamar mai jin kunyarta yace "Zai iya yi miki iskanci."
"Hummm!" Ta faɗa tana raɓashi tace "Nagode da kulawa."
Da kallo ya bita har ta ɗan yi nisa sai kuma ta juyo tace "Wataƙila a gunka ya koya."
Da wani tattausan gudu ya tare gabanta da mamakin maganarta, iska ya feso ya na tunanin
wace irin jarabawa ce Ubangiji ke masa haka? Shin dan ya kasance mai taɓa jikin macen da ba
ta halatta gareshi? Shi ne Allah ya jarabceshi da wannan ƙwaya ɗayan tak? Shi bai ma taɓa
sanin ana son mutum lokaci ɗaya haka ba sai yau, a kwana uku da sukayi gidansu kawai
haukacewa yake neman yi, ba kuma shine farkon da ya fara saninta ba, a'a ya santa jimawa dai
ake ba'a haɗu ba, wannan ikon Allah ya fi gaban wasa kam, gashi sai ta mishi wauta da
katoɓara, amla sai ya ji ya haɗe ranshi bai ɓace ba ko ɗaya. Yanzun ma dai bai ji haushi ba, sai
ma ƙanƙance idanu da yayi cike da son ta yarda da shi yace "Wallahi Saleela ni ban taɓa sanin
wata ƴa mace ba, shiyasa na faɗa miki ki nemi zaɓin Allah a kaina, idan kika ji gamsuwa a kan
hakan ki faɗa min, na miki alƙawarin sanar da ke komai da ya shafeni, kuma wallahi gaskiya
kawai zan faɗa miki, amma ki yarda dani Saleema ban taɓa zina ba, ke ce mace ta farko da na
ke so na fara sani a rayuwata bayan aurenmu."
Wani irin faɗuwar ne ya ziyarceta sakamakon abin da ya faɗa, hakan yasa ta gyara tsayuwa ta
ƙanƙance idanunta tace" Mu'az, yanzu idan aka ce ba na da wannan abun da ka ke tunanin
samu a tare da ni, anya kuwa za ki iya zama da ni a haka?"
Tsurawa fuskarta idanu yayi yana kallo, saida ya mayar da wasa gefe cike da bata tabbaci
yace" Ban san ta ya ne zan kwatanta miki yanda na ke ji ba, amma nan..."
Ya faɗa yana ɗora hannunshi na dama akan daidai zuciyarshi sannan ya ce" Gabaɗaya na ke
jinta ta ki ce, duk wata bugawarta ɗaya da sunanki take amsawa, ƙwaƙwalwata a yanzu ba ta
tunanin komai sai ke kawai, a yanda na ke ji Saleema zan iya rayuwa da ke ko babu wannan
abun da kike tunanin shi ne kaɗai na ke so, ban taɓa sha'awar macen da ban ga jikinta ba,
amma ke jinin jikina a sanyaye yake tafiya idan na ganki, ina da sauri a kan komai, amma akan
lamarinki sanya nake tamkar gajiyayyan matafiyi, Saleema, a duk duniyar nan ke kaɗai ke da
alhakin gajiyar da ni."
Ita ba *dutse* ba ce, hakan yasa a karo farko maganganun Mu'az sukayi matuƙar tasiri a
zuciyarta, dan hatta da tsigar jikinta saida ta dinga tashi, saƙon ya ratsata matuƙa, babban abun
tunaninta shine, dama a haka da mahaifinta ke kusheta akwai wani namiji da zai so ta a haka?
Yanzu duk kalaman nan nata ne ita kaɗai? Son da yake mata har ya kai haka dama? Yadda ta
ke kallonshi ne ya sa shi ƙyasta yatsunshi biyu yace "Matata ya dai?"
Da sauri ta zabura tana kallonshi, sai kuma ta kalli wayar dake hannunta ta nuna masa tace
"Zan...ina zuwa, zan amsa waya."
Da sauri-sauri ta raɓa ta wuceshi shi kuma ya bita da kallo, saida ya ga shigewarta ɗakinsu
kaɗai ya juya ya fita shi ma fatanshi ɗaya Allah ya ɗorashi a kan yarinyar nan dake wofantar da
shi, irin yanda mata ke mararinsa suna kawo kawunansu gareshi, da yadda idan ya na wasa da
mace take baje basirarta dan son ganin ya isa babbar fada, babu irin salon munafurci da
kisisinar da ba'a masa ba dan ya faɗa tarko, amma ya dage ya nuna a'a fa, har saida ya taɓa
samun kanshi yana daf da afkawa amma ya ce a jira sai ya nemo kororon roba saboda tsaro,
daga ranar bai kuma haɗuwa da yarinyar ba dan a ganinshi wani abun ta ke da da yasa ya kusa
wuce gona da iri ranar.
*Duk* abin da ke faruwa a idanun Hadeeya wacce ke sama fitowarta daga ɗakin amarya kenan
ta hangesu, laɓewa ta yi tana kallonsu, irin yanda Saleema ke mishi magana kamar da gadara
da isa, shi kuma yana ta wani sussunkuyar da kai, hakan sai ya sata tunanin to me ye a
tsakaninsu? Ba ta iya samun amsa ba dan ba ta jin me suke faɗa, saida ta ga kowa ya bar
wurin sannan ta sauko ita ma da tunanin me ye wai? Soyyaya suke? Ko kuma dai wani abun ne
na daban?.
Lambar Khairat ta kira, bayan sun gaisa ta faɗa mata ita ce, ɗorawa tayi da cewa "Yawwa
Khairat, ai nan da kwana huɗu ne saukar makaranta ko?"
Daga ɓangaren Khairat ta amsa da "E, muna ta shirye shirye ma."
A nutse tace "Yawwa, Khairat dan Allah ki min wata alfarma, ki samu malam ki faɗa masa na
amince yanzu a saka sunana a jerin masu saukar."
Da mamaki Khairat tace "Amma me yasa? Na ga da fari ke kika ce ba kya so saboda Abbanki,
yanzu kuma kin ce a saka, Abban ya amince ne?"
A tausashe tace "Ko ɗaya Khairat, yanzu ma zan yi ne ba tare da saninshi ba, sai dai ban damu
da ko me zai faru ba, ban ci jarabawar ba bai kamata na bari wannan damar ma ta wuce ni ba."
Khairat ce ta amsa da "Gaskiya kuma hakane, to amma ta ya zakiyi sauka bai sani ba?"
Kamar za ta fashe da kuka tace "Khairat ke dai ki faɗawa malam, in dai har ya amince za'ayi
dani, to zan samu kuɗi a hannun Mama ko da na iya wainar da za'ayi sadaka ne."
"To shikenan." Cewar Khairat tana ci gaba da faɗin "Bari na faɗa masa dama yanzu ya shigo
gida zai ci abinci."
"Yawwa nagode, yanda kukayi ki kirani da wannan lambar, amma anjima da yamma za mu
koma gida."
Da haka suka rabu ita da Khairat, bai fi minti 15 ba ta sake kiranta da lambar malam ɗin dan ita
wayarta ba kuɗi ta sanar mata ai ya amince kuma ya yi farin ciki sosai, wannan magana ita ta
saka Saleeema farin ciki marar misaltuwa tana jin ko ba komai dai za ta kafa tarihi a zuri'arsu
cewa ita ce ta farko da za ta sauke Alƙur'ani kuma a haddace.
Dreban da ke ta jiransu Alhaji Auwal ya kalla ya musu nuni da shi yace "Ku je yarana, Allah
muku albarka."
Sai kuma ya kalli Saleema yace "Amma dai za ki dinga kawo mana ziyara ko?"
Ɗaga kai tayi alamar e, da yatsa ya nunata yace "Da gaske?"
Da murmushi ta amsa da "Allah ko Abba."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan to na yarda."
Juyawa Saleema tayi ga Hajia Rabi tace "Mama sai anjima."
Shafa kuncinta tayi tana fara'a tace "Allah ya miki albarka ƴata, ki gaishe da Mamanki."
Jinjina kai tayi alamar to, Papi dake gefe Saleema ta ƙarasa gareshi, riƙo hannayenshi tayi duka
biyun tana kallon fuskarshi tace "Papi nagode sosai da goyon bayan da ka bani, mu zamu tafi,
sai wani lokaci kuma."
Jaye hannunshi ɗaya yayi ya ɗora a kanta yace "Allah ya miki albarka, Allah ya baki miji na gari,
Allah ya saka farin ciki a rayuwarki, Allah ya baki zuri'a ta gari wacce za ta zama sanyin
idaniyarki."
Ɗora hannunta tayi kan na shi tana murmushi tace "Ameen Papi, nagode sosai, kai ma Allah ya
ƙara maka lafiya da nisan kwana."
Ummeeta dake tsaye kusan Hameeda da kallon ƙyama take binsu har saida suka shiga mota
suna ta ɗaga musu hannu suka bar gidan, duk da Saleema na jin za ta yi kewar mutanen,
amma dai ta fi farin ciki da komawarta gidansu dan shine kwanciyar hankalinta.
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_18_
Tunda suka shigo gidan sai suka ga kamar sun yi watanni ba sa nan, cike da kewar iyayensu
duk suka zube falo, daga iyayen har su kansu yaran sun girgiza ganin irin tarin tsarabar da aka
saka musu bayan mota wacce sai yanzu da dreba ya yi ta shigowa da su suka gani, wani kwali
na daban dreba ya miƙawa Saleema yace "Wannan Alhaji ne ya ce na baki."
Karɓa tayi tace "Ka min godiya sosai."
Duk tarin kayan dake gabansu wanda komai aka saka daidai da na kowa, hatta da takalmi dake
wurin kowa da lambar da ƙafarshi ke ɗauka, dan Saleema talatin da takwas take anfani da shi,
Hadeeya kuma arba'in daidai ƙaramar lamba, sai Hameeda talatin da tara, amma Hadeeya da
ta ƙwallafa rai tana son sanin me je cikin kwalin, saida ta matso kusan Saleema tace "Mu ga
miye a ciki?"
Ba tare da tunanin komai ba Saleema ta miƙa mata wanda saida Safiya ta kalli Saleema da
mamaki, dan ita ta san abin da ba'a ba kowa ba ne aka ba ƴarta. Hadeeya na buɗewa jikinsu
har rawa yake ita da Hameeda wajen ciro kayan ciki, wata mahaukaciyar lafiyayyar abaya kalar
pink Hameeda ta buɗe tare da yin tsaye tana gwada rigar a jikinta, Hadeeya kuma wasu takalmi
dake ciki kalar rigar ta ɗauka tana gwada a ƙafarta wanda takalmin da ganinsu ta san masu
tsada ne kuma sabin kalar da ba kowa ya sansu ba.
Hameeda dake tsaye da rigar a hannu ce ta hango kwalin da ya saka gabanta faɗuwa, da sauri
ta saki rigar ta durƙusa ta ɗauki kwalin tana buɗewa, Hadeeya ma da ta gani zaro idanu tayi ta
furta "IPhone 14 pro max."
Ardiya ma zaburowa tayi tana ƙwalalo ido dan jin wai da gaske suke ko dai wasa? Uban wa zai
ba Saleema wayar da ta haura million ɗaya? Ta na ganin camera ɗin wayar ya tabbatar mata da
gaskiya, Hadeeya riƙe wayar ta yi gam tana ta dubawa tana jin ina ma ta zama ta ta, take ta
kalli Saleema tace "Bari na tura miki abubuwa, ba komai a ciki."
Saleema ko a jikinta, yo ita me zata yi da waya? Miƙewa ma kawai ta yi ta barsu nan ta shige
ɗakin Mamanta dan yin wanka, Hadeeya da Hameeda ai sai suka shiga ture-ture da ɗaukar
hoto suna turawa a wayoyinsu suna nuna fa da IPhone 14 aka ɗauki hoton, wayar da har yanzu
su dai duk yanda suke tare da ƴaƴan masu kuɗi kuma maƙaryata ba su ga wanda ya yi jarumtar
riƙeta ba bare su da har yanzu Abbansu ne ke siya musu idan suka birgeshi.
*Suna* zaune kan sallaya Saleema ta kalli Mamanta tace "Mama, kwana huɗu ya rage saukar
makaranta, kuma na roƙi malam ya saka sunana, yanzu kuɗi nake so a wajenki da zan ɗinka
sabon hijabi irin na sauran ɗalibai, sai ka inda hali ki min waina da za'a yi sadaka."
Ajiyar zuciya Safiya ta sauke tace "Me yasa kikayi haka? Kina so mahaifinki ya wulaƙancemu
ne?"
Turo baki tayi da alamar shagwaɓa tace "Dan Allah fa Mama, kinga wannan ce kaɗai damar da
nake da da Abba zaiyi alfahari dani, baki ga ba ɗazu gidansu Yaya Mu'az yanda yake hararata."
Buɗa ido Safiya tayi tace "To, Yaya Mu'az kuma? Yaushe ya zama Yayan na ki?"
Cike da kunya ta sunkuyar da kanta amma ba tace komai, jin shiru yasa Safiya nisawa tace
"Shikenan, amma yanzu dai kinga bana da kuɗi gaskiya, kuma ko da za'ayi saukar nan sai dai
mu ja baki muyi shiru kar kowa ya ji, dan bana son fitina a halin da na ke cikin nan."
Marairaicewa Saleema tayi tace "To amma Mama ina zan samu kuɗin?"
A tsanake ta kalleta tace "Karki damu, bari Abban na ki ya shigo, zan san yanda zan yi na samo
miki."
Fara'a tayi tace "Nagode Mama."
Miƙewa tayi ta buɗa wata ƙaramar drower ta ɗauki chocolate a cikin tsarabar da aka basu ne,
da kallo Safiya ta bita har ta fita a ɗakin, murmushi ta saki tana fatan Allah ya kareta a duk inda
take, har yanzu wayar nan tana hannunsu Hadeeya, amma ita ba ta damu ba, sannan tsarabar
ma na sauran kayan Ardiya ce ta raba ta aiko Hamdeeya ta kawo wai na Saleema, kayan ba su
taka kara sun karya ba, ta san za suyi tunanin ai ita an bata wannan babbar kyauta, amma
abun mamaki Saleema karɓa ta yi sam alamu ma ya nuna hankalinta ba nan yake ba bare ta yi
ƙorafin wannan ɗan abun za'a bata? Tabbas halin ko in kula na abin da ya shafi ci ko na duniya
mai ƙarewa halinta ne, sai dai ƴar ta ta tafi ta halin ko in kula akan abun, dan ita tana gane an
cuceta sai dai kawai ta yi shiru, amma ita Saleema sai dai ka ga alamar bata san abun a kai ba
bare ya dameta, gale da kyautar da mahaifinsu ke ba ƴan uwan ita ya hanata kaɗai take ɗan
damuwa, shi ma da an kwana biyu ta shiga sabgar gabanta.
Suna zaune kan teburin cin abincin ya fito cikin farar jallabiya, zaunawa yayi inda ya saba zama
kullum, Saleema dake kusa da shi ta sadda kanta saboda kallon da ya mata, miƙewa Safiya tayi
a kasalance ta fara zuba masa abincin, shi kuma hakalinshi na ga Saleema yace "Na faɗa miki
idan har ba ki samu jarabawar nan ba dama zan ɗauki mataki na ƙarshe a kanki."
A hankali ta ɗaga idanunta ta kalleshi a ladabce tace "Ka yi haƙuri Abba, a gaba zan yi in s..."
Tsawa ya daka mata da cewa "Ke! Ni sa'an wasanki ne?"
Da sauri ta sadda kanta ƙasa saboda alamar da Safiya ta mata da idonta, cike da masifa yace
"To bari ki ji Saleema, idan ma aure kike so ki fito da miji na aurar da ke, amma ki sani na daina
asarar kuɗina a kanki, wallahi na daina zuba miki ƙwandala da sunan karatu, dan haka ba ke ba
sake fita a gidan nan da sunan za ki tafi makaranta, *na dakatar da ita daga yau*."
Duk zuba mishi idanu sukayi har Safiya dake tsaye, sai kuma ta girgiza kai tana lumshe
idanunta, Saleema ma idanunta cike da hawaye ta kalleshi sai kuma ta kalli mahaifiyarta da
tunda ta zo ta fahimci kamar har yanzu jikinta ba ta jin daɗinshi, abin da take son faɗa masa
tsoro kuma ya hanata dan kar ya bigeta, sai kwatsam mahaifiyarta ta yi tambayar cewa "Amma
Alhaji ka hanata zuwa islamiyya shekara takwas da suka wuce, ka hanata ɗinki tun tana
ƙarama, yanzu kuma ka dakatar da bokon ma, toe za ta yi idan ta zauna a gidan?"
Kallonta yayi a zafafe yace "Wannan hukuncina ne kuma na gama yankewa, ta zauna a gidan
ta dinga kama muku aiki har ta fito min da wanda ta ke so nan da wata biyu na aurar da ita."
Da sauri Saleema ta furta "Aure Abba, amm..."
Kallon da ya mata ya sa ta yi shiru, ƙwafa yayi tare da faɗin "Idan la ba ki da saurayin ni zan
miki, kuma ma ai ba zaki rasa ba tunda har kika ƙi maida hankali ga karatu, na san soyayya ce
ke hanaki."
Ardiya da take jin daɗin haka cike da kissa tace "Ai shekarunta sun isa na aure, ba ka ga duk
wata wahalar da take sha kafin ganin al'adarta ba?"
Kunya ce ta sa Saleema duƙar da kanta, inda Hadeeya da Hameeda suka yi dariya a tare,
Safiya kuma kallon Ardiya tayi tace "Me yasa kike min hakane? Dan ba ƴarki ba