Showing 9001 words to 12000 words out of 50006 words

Chapter 4 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf

30 Mar 2025

6177

kuma ta girgiea kai tace "Ban sani ba, me ye wannan d'in?"

Nuna kanshi yayi yace "Ni ma kike tambaya?"

Sai kuma ya jinjina kai ya nunasu da yatsa yace "Ku jira a gama taron nan zan ji daku
dukkanku."

A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace "...




*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BAIWATA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ��
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️


_Bismillahir rahamanir rahim_


_5_

A fusace ya wuce ya barsu inda Safiya ta kalli Saleema tace "Me kika masa kuma yanzu?"

A raunane tace "Ba abun da na yi, irin wannan zanen ne fa nake yi."

Ta fad'a tana nuna wuyan rigar Safiya, tab'e baki Safiya ta yi tace "Kin tabbata?"

Jinjina kai tayi tare da cewa "Allah ko."

Jinjina kai tayi tace "Shikenan." Juyawa tayi ita ma ta barta nan ta ci gaba da abinda take. Duk
wannan shagali da abinci da aka shiga rabawa bai wani d'ad'a Saleema a k'asa ba, haka take
abinda take ganin zai fisheta yayin da suma suke wanda ya fishesu, sai da dare ya yi sosai
kafin su fara watsewa daga gidan.

*Mamakin* dalilin da yasa ya kirasu b'angarenshi take da kuma yanda ya taso Saleema a
baccin ta, gashi ya musu tsaye k'erere har da wani rik'e d'amara a hannu alamar dai duka zai yi,
sai dai ba ta san wa zai daka ba a cikinsu, ita ko Saleema ? Indai ita ce abun da bai tab'a
faruwa ba ne, ko mari bai tab'a had'ashi da mace ba, bar shi dai ya rufeki da fad'a idan abu ya
yi k'amari ya k'aurece miki, amma ban da duka.

Zuba masa ido ta yi tana jira ta ji me zai ce, sai da ya gama kumbura da kallonsu sannan ya
kalli Safiya yace "Yaushe ki ka saka yarinyar nan koyon d'inki?"

Da mamaki ta kalleshi tace "D'inki kuma? Ni ban sakata koyon d'inki ba."

Wani kallo ya jefeta da shi yace "Amma ai da saninki take zuwa ko?"

Kallon Saleema ta yi da ta fara tsuru tsuru da idonta tana kakkame jikinta a sakan biyu kuma ta
kalleshi tace "Ban gane ba? Me yake faruwa ne wai?"

A d'an fusace yace "Ni ne ma zan fad'a miki abinda yake faruwa? Safiya yarinyar nan wata uku
kenan ta na zuwa gidan matar can mai d'inki, kina so ki ce baki sani ba ne?"

Sake juyawa tayi ta kalli Saleema da tsantsar mamaki tace "Saleema, d'inki kike koyo?"

Mik'ewa ta yi tsaye ta ja baya tana girgiza kai cike da tsoro tace "Mam...a, da..ma."

"Dama me ?" Ta fad'a a tsawace, zabura tayi ta fashe da kuka tace "Ki yi hak'uri Mama, ba zan
sake muku k'arya ba."

Dafe baki Safiya tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Saleema k'arya kika mana dama?
Da kike cewa za ki tafi karatu, dama ba karatun kike zuwa ba?"

A mugun tsawace tace "Me yasa Saleema? Me yasa kika mana k'arya?"

Cikin kuka ta kalli Alhaji Yusuf dake kallon Safiya yanda ta hahhak'e ta saye bala'in ta kasa
barinshi ya furta komai, da sauri ta girgiza kai tace "Kiyi hak'uri Mama, ba zan sake ba daga
yau, na rantse miki da Allah."

A hassale Safiya ta yi kanta tare da fizgar d'amarar (belt) dake hannunshi, kafin Saleema ta
ankara ta damk'o hannunta rai b'ace zuciyarta na tafasa na k'arya da yanda k'aramar yarinya
kamar Saleema ta yaudareta haka ta shiga labtawa jikinta bulala tana fad'in "Za ki k'ara daga
yau? Ni za ki ma k'arya Saleema? Ni kika d'auka shashasha da ba ta san me take ba? Kin sake
fita a gidan nan da sunan za ki je wajen d'inki ?"

Cikin kuka na bara-bara Saleema dake ta doka tsalle na azabar bulala take fad'in "A'a, A'a
Mama, na tuba wallahi ba zan k'ara ba, na daina zuwa daga yau kar ki kasheni, wayyo ! Abba
ka taimakeni."

Duk da shi ma ranshi a b'ace yake na turbar da Saleemar ke neman d'auka, amma kuma
haihuwa ta fi gaban wasa, sai ya ji na shi b'acin ran ya fece inda zuciyarshi ta fara suya na
yanda ya ga Safiya na dukanta. A sukwane ya nufosu ai kafin ya kai mata agaji Saleema da
dama neman ceto take ta yi ram da k'ugunshi ta na lab'ewa bayanshi.
D'aga bulalar da Safiya ta yi za ta sake zuba mata yasa shi rik'e hannunta ram tare da jawota
gaba d'ayanta ta fad'a jikinshi, tsit ! D'akin ya d'auka har Saleema dake kuka ma wacce ta tsura
musu ido da tunanin kar dai dukan Mamanta zai yi? Ido cikin ido suka kalli juna duk idonsu sun
yi jajir na mabambamta b'acin rai, sake damk'e hannunta ya yi sosai hakan ya tilasta mata sakin
d'amarar ta na d'an rintse ido na zafin da ta ji, cikin tattausan murya yace mata "Dukan ya isa
haka, kamar kin samu wata jaka za ki dinga narkar min 'ya a gabana, to kar ki k'ara."

Zamewa ta yi daga jikinshi cike da kunya tace "Ka ga ka mik'o min yarinyar nan na farfasa mata
jikinta, gobe ba za ta sake min k'arya ba."

Harara ta dalla mata yace "Wallahi kika sake tab'a min yarinya ranki zai b'ace, ko ma me ta yi ai
laifinki ne, shi ne za ki wani zak'alk'ale ki juye a kan ta dan kar na hukuntaki."

Kawar da kanta tayi gefe tana d'an gunguni, d'an k'aramin bakin na ta ya bi da kallo tare da
lashe leb'enshi na k'asa, dafa kafad'ar Saleema ya yi ya mata alamar ta fita, dan ya kula yau
Safiyar namansa take da fitina, har shi ne ma take ma gunguni haka? Cikin shashek'ar kuka
Saleema ta ari na kare ta bayan mahaifinta ta fice a d'akin da gudu.
Bin ta da kallo Safiya ta yi tace ta nunata da yatsa cikin d'aga murya tace "Ai zan sameki d'akin

dan ubankkkk...."

Tsit! Ta yi dan sai da ta tasan ma fad'a ta tuna irin sub'ul da bakan da ta yi, wato a gaban shi ta
zageta. K'in juyowa ta yi a hankali ta fara jan jikinta za ta fice a d'akin da sauri ya nufeta ya k'ara
jawota jikinshi, tsura ma fuskarta ido yayi yace" Sofee dama tsaurin idonki ya kai haka? Hajiar
ta wa? Kuma a gabana?"
Marairaicewa ta yi tace" Ka yi hak'uri dan Allah, wallahi sub'utar baki ce na manta."

Jinjina kai yayi yace" Ni dai ko? Hajia ta kika zaga a gabana, ba komai." Ya fad'a yana sakinta
tare da fad'in" Je ki yi shirin bacci ki zo, na gode Allah da ya sa ranar kwananki ne kika zagar
min uwata, hakn shi zai bani damar d'aukar fansata."

Turo baki ta yi ta juya za ta fita dan zuwa d'akinta ta shirya ta zo kamar yanda ya ce. Da kallo ya
bita kafin ya girgiza kai ya na murmushi ya zauna bakin gadon.


*Washe gari*


A ladabce ta shigo d'akin tana fad'in "Asaalama alaikum."

Safiya dake kwance da k'yar ta tashi zaune tana amsawa da "Wa'alaiki salam."

Kusan gadon ta k'arasa ta tsuguna tace "Mama, kin ga safiya ta yi kuma ba inda muke zuwa,
yanzu kinga na fad'a miki gaskiya, zan iya tafiya wajen aunty Hafsatu?"

Harara ta watso mata tace "Saleema jiya ya mukayi da ke? Ban ce kar na sake ji ko gani ba?"

A shagwab'e Saleema tace "Dan Allah Mama ki barni na tafi."

A tsawace tace "Ke tashi, tashi ki bani wuri, kuma wallahi kika sake min maganar nan ranki zai
b'ace."

Mik'ewa tayi ta juya za ta fita ta bita da harara ta na fad'in "Ka ga min yarinya, ina zaman
zamana ki hassalani kuma ba daman na zageki yanzun nan ubanki ya sake titsiyeni."

Gyara kwanciyarta ta yi tunda dai yau ba aikinta ba ne tana fad'in "A bar ni na ji da abinda ke
damuna mana."

Alhaji Yusuf da ke jinme take fad'a yana daf da shigowa ne yace "A ma sake kuskuren zagar
min uwata wallahi."

Harara ya dalla mata yace "Yar rainin wayo." Da mamaki ta kalleshi tace "Ni d'in?"

"Ke d'in mana, ko akwai magana ne?" Girgiza kai ta yi alamar a'a, Saleema da ba ta yi nisa ba
ya k'wala ma kira ta dawo d'akin, tana zuwa ta tsaya tana kallonshi, cike da gargad'i da jan
kunne ya zaro mata ido yace "Kina ji na? Daga yau sai yau kar na sake jin kin yi maganar zuwa
wajen koyon d'inki, idan ba haka ba kuma wallahi da kaina zan hukuntaki."
A tsawace yace "Kin ji me na fad'a?" Da sauri ta d'aga kai alamar e, nuna mata k'ofa ya yi yace
"Wuce."

Juyawa ta yi jiki a sab'ule ta fita a d'akin ta na jin ba dad'i sam, saboda burinta ne ake neman
hanata cimma shi, amma ya zata yi da ya wuce ta hak'ura kawai.


*Tafiya* ta yi nisa, amma har yanzu babu abinda ya canza daga rayuwar su, islamiya sun cire
rai da sake komawa, saidai Saleema dake mai wayo ce har yanzu ta na d'aukar karatunta
wajen kanwar malaminsu, wanda a shekarun nan ta k'ara sanin abubuwa dayawa, musamman
da yanzu ta k'ara wayo da shekaru, sai ya zama har wayar mahaifiyarta take d'auka ta kira
malamin su sake tattaunawa kan karatunta. A karatunta na boko ma har yanzu ba abinda ya
sauya, duk yanda take son ta birge mahaifinsu ita ma wajen ganin ta yi k'ok'ari abun ya ci tura,
sai ma k'ara lalacewa da lamarin ke yi saboda ta hak'ura ta d'auke hankalinta daga karatun na
boko, tana yi ne kawai ba dan ranta na so ba sai dan mahaifinsu, hakan ya sa shekara biyu ta
na maimaita wani ajin har Hadeeya ta risketa, shima kuma sai Hadeeyar ta yi gaba tana neman
barinta, abinda Alhaji Yusuf bai tab'a yi bane ya yi a wannan karan, wato bayar da cin hanci da
kuma neman alfarma aka izasu tare da Hadeeya dan baya so ta barta a nan.

Yanzu dai haka suna ajin zana jarabawar BEPC, ya ma ta k'wak'waran kashedi in har ba ta ci
jarabawar nan ba to shi kad'ai ya san me zai mata, hakan yasa ta d'an sake maida hankalinta ta
na son ganin bai mata abinda ya bar wa ran na shi ba, sai daia inda ta koyi abun a nan take
tashi ta barshi, ta na shiga d'aki za ta nemeshi ta rasa.
*Farkawa* ta yi don yin fitsarin da ya addabeta, ta na tashi zaune idonta suka sauka kan
Mamanta ta d'ora goshinta k'asa ta na kai kukanta ga sarkin sarakuna mai kowa mai komai, da
alama ba ta kwanta ba kenan tun da suka rabu da sai da safe, dama kuma idan ba kwanan
Mamanta ba ne d'akinta take kwana dan ta fi jin dad'in hakan. Sauko da k'afafunta ta yi ta na ci
gaba da kallon mahaifiyarta wacce ta ke da yak'inin ita kawai take wa addu'a, dan watannin nan
ta cika saka damuwa a kan ta wanda ba ta san dalili ba, haka kuma da ta ga tana yawan
tsayuwar dare da azumin nafila sai ta ce ta na yi ne saboda ta na so ta yi nasara a karatunta ita
ma mahaifinta ya yi alfahari da ita.

Mik'ewa ta yi ta shiga ban d'akin ta yi abinda za ta yi ta fito, zaune ta sake yi bakin gadon ta na
kallon mamanta da sai yanzu kad'ai ta d'aga. Bayan wasu mintuna ta sallame sallar dan ta ji me
ya sa Saleema ba ta koma ta kwanta ba? Kallonta ta yi murya a tausashe sosai saboda daren

da ya tsala yace "Lafiya ba ki koma ki ka kwanta ba?"

Numfashi sosai Saleema ta ja kafin tace "Mama, ki kwanta ki huta mana, gobe za mu fara
jarabawar, idan Allah ya k'addara zan samu zan samu."

Ajiyar zuciya Mamanta ta sauke ta na d'an murmushi na dattako tace "Ko da kun gama
jarabawa Saleema ba zan daina yi miki addu'a ba, ina so na ga kema mahaifinki ya baki kyauta
ko sau d'aya ne."

Girgiza kai Saleema ta yi tace "Mama, wai me yasa ni Abba ba ya so na ne? Saboda ba na da
k'ok'ari a makaranta?"

Girgiza kai Mamanta ta yi tace "Ba haka bane, ya na so dai ya ga ke ma kina k'ok'ari ne."

Cike da damuwa a fuskarta tace "To amma Mama ilimi ba na Allah bane? Na yi iya k'ok'arina
dan ganin nima na zama kamar su Hadeeya, amma abun ya gagara."

Cike da gasgatawa maman tace "Hakane Saleema, ilimi na Allah kula ya na ba wa wanda ya
so, amma wasu lokutan idan ka sa wasa sai Allah ya bar ka da shirmenka."

Da tuhumammen kallo ta bita tace "Mama kina ganin ni ba na jajircewa ne? Ina fa k'ok'ari sosai,
kawai dai abunda na sani na fi son karatun islamiyya saboda shi na fi ganewa a sauk'ak'e."

Murmushi ta sake yi cike da dattako tace "To shikenan, Allah dai ya bamu nasara wannan
karan."

"Ameen Mama, zo ki kwanta to." Girgiza kai ta yi tace "A' a, ke ki je ki kwanta, ni zan ci gaba
daga in da na tsaya."

Ita ma girgiza kai ta yi tace "A'a, ni ma bari in tayaki, ba zan iya bacci ba alhalin ki na tsaye a
kaina."

D'an murmushi ta sake yi ta mik'e tsaye dan ci gaba daga in da ta tsaya, ba jimawa Saleema ta
fito bayan ta d'auro alwala ta zo ta shinfid'a sallaya ita ma ta bi sahu a gefen mahaifiyarta.



*Saboda comment d'in da ku ke suburbud'awa* ga mai so ta yi magana dan shiga *grp
d'ina*



*Alhamdulillah.*

24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BAIWATA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ��
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️


_Bismillahir rahamanir rahim_


_6_




*12:20* suka fito daga aji sun gama zana jarabawarsu, ranar da ake kwantsamawa ya sa ta
nufi inda ke da ruwa dan sha ko ta ji sanyi saboda kakarewar da jarabawar ta mata a aji, dama
dai ita ba wasu k'awaye gareta ba, to ta ya ma za su yi k'awaye? Bayan mahaifinsu ba kowace
k'awa ya ke barinsu da ita ba sai mai ilimi irin na su, idan kuma ba ki da to ko kin zo wajensu zai
sa mai gadi ya hanasu shiga, hakan ya sa ma tsakaninta da k'awa makaranta a gaisa a yi raha
kawai a wuce wurin, ita ba waya gareta ba duk da shekarunta *goma sha takwas* a duniya,
amma mahaifinta ya hana mata waya ya ce a haka za ta ji haushi ta yi k'ok'ari ita ma saboda ya
ga yanda waya ke da tasiri a rayuwar matasan yanzu, hakan yasa ya siya ma su Hadeeya
manyan wayoyi uta da Hameeda amma ban da ita, wai a dole sai ta ji haushi, amma abunda bai
sani ba shi ne ko a jikinta, tunda dai ta na aiki da ta Mamanta ai shikenan.

Ta na zuwa gaban fanfon sai da ta aje yar jakarta k'arama sannan ta cire hijabinta ta zauna
bakin dandamalin ta fara d'aura alwala, a iya saninta da ganinta dai ba kowa wajen, dan haka
ma ta dinga alwalarta a tsanake har da ture d'an kwalinta ta shafa kai.
Ta na idawa ta mik'e ta na karkad'e hijabin na ta da ya d'auki lemar ruwa, a cikin karkad'eshin
da take ne ta d'an juyo da kan ta kad'an. *Kwatsam* idonta su ka sark'e da na balagaggen
namijin da ba ta tsammaci ya na wurin ba, da mugun sauri ta durmiya hijabinta ta juya bayanta
cike da mad'aukakiyar kunyar da ta kasa misaltawa, gaban Mamanta kad'ai ta ke iya zama da
yar rigar nan da ke jikinta, gashi yau ta yi saken da waccen *Alhudahuda* ya gama kalle mata
jiki.


Da k'yar ta sunkuya ta d'auki jakarta ba tare da ta yarda ta sake kallon wajen ba, dan irin kallon
da ta ga ya na mata abun ya bata tsoro, gashi ta na jin kunyarshi sosai, saboda wasu lokuta
ana turoshi ajinsu ya kula da su idan babu malami, dalilinta na kiranshi alhudahuda kuma shi ne
irin darasin da yake koya musu na lissafi mai matuk'ar wuya, hakan ya sa da an turoshi ajin za
ka ga yan mata da samari kowa na kawo masa rub'abb'en lissafin da ya kakare masa a kwanya
dan ya warware masa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login