Showing 1 words to 3000 words out of 42034 words

Chapter 1 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf

24 Jun 2025

1952

*ƘAUNAR ƁOYE!!!*


©️ _2021_



*By*
_Fatima Batula_

*Wattpad:mrsbalarabe* .

*Dedicated*
_To My Bilkisu(matar soja) ubangiji Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗaiyiba,y shiga
tsakanin ku daga sharrin maƙiya da mahassada._


*Special gift to;*
_My Ahmed ubangiji Allah ya rayaka ya albarkaci rayuwarka ya shiryar da kai kan tafarkin
addinin tsira addini gaskiya yasa ka zama me kira domin addinin musulunci, Amin Amin._



_Page_
_1-2_



✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi , Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.


_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_

Rass! rass!! zuciyarta ke wani irin bugawa cike da tsananin tsoro da fargaba me illata ruhi da
tunani.
Buɗe rufaffun idanuwanta tayi wanda suka cika da tsantsar tsoro da fargaba, jikinta ne ya hau
ɓari da karkarwa tamkar wacce ke cikin matsanaicin zazzaɓi, ba komai ya haifar mata da hakan
ba, illa sake sauke idanuwanta da tayi a kanshi a karo na uku sau uku a ɗan lokacin da bai fi
awa uku ba. Duk da sanin cewa ita jaruma ce jaruma kuma me jan hali da juriya amma a wannan karan ta
rasa jarumtar ta.
Cigaba da karkarwa jikinta ke yi. Kallon ta yayi yana sakar mata kyakkyawan murmushin shi
na ƙauna.
"Ina ƘAUNAR ki! zan cigaba da bibiyarki har sai kin ƘAUNACE ni kamar yadda nake miki".

Naji kalmar nan sau biyu kafin wannan duk wancan lokacin ko nace ɗazun ban taɓa ɗauka
cewa ƙara jin wannan kalmar zata haibar min da rudewa ba, kalmar zai bibiye ni kuwa na dauka
zan ji ta sau miliyan banji komai ba.
Yunƙurin tattaro jarumta ta nayi wacce ni kai na nasan ni jaruma ce, amma ina ban iya komai
ba bayan rawar da vaki na yahau yi, Allah ya so ni ma a zaune nake da na tabbata yanzun na
daɗe zube a ƙasa.
Wani irin buguwa naji zuciyata tayi wacce lokaci daya naji ta karamin karfin gwiwa tare da haifar
min da wata zabuwar jarumta da karfin hali.Idona cikin nashi na zuba duk da har lokacin jiki na
be gama rawa ba, amma na buɗe bakin da nake ji tamkar na rasa shi na ce, "Malam ka daina
bibiyata haka karka dauka neman ka tsorata ni zai yi tasiri a raina har na ce ina sonka, dan
haka kabar ma bi na dan bazan taɓa cewa Ina ƙaunarka ba", ban dauka bakina yana da saurar
tsiywar da na sanshi da shi ba sai jin ina zaro kalamai cikin tsiwa yasa na tabbatar da cewa ni
din ce dai, sai hakan ya ƙaramin ƙaimi ya kuma cire min tsoro ko ba komai baki na zai kwace ni,
inma shi *MUTUM* ko *ALJANN*.
Bazai taɓa cin galaba a kai na ba, juyawa nayi da nufin nabar gurin naji yana fadin, "Nifa ina
ƘAUNAR ki dan haka dole ke ma sai kin so ni".
Yana daga cikin abunda na fi tsana a duniya wato umarni da gadara cikin iko isa, ko uwar da ta

kawo ni duniya cikin kwantar da kai take umarta ta da lallami da ban baki duk da isarta akai na
amma bata saka ni yin abu cikin isa dan isarta, shi waye da har zai min magana haka cikin isa
da gadara a fusace na juyo gareshi na sauke mishi wani mugun kallo na ce cikin tsiwa, "Dole na
so ka! a matsayinka na wa? tukunna kai waye? to bari ka ji ni *MEENAL* bazan so ka ba, ni
ban ma taɓa jin ƙarfin hali irin haka ba wato dole na soka an gaya ma ana ƘAUNA dole ne da
har kake wani umarta na cikin isa, bazan so ka ba, karka ɓata wa kanka lokaci ni dan bani da
lokacinka, "ina kai aya na juya a fusace dan ya ban haushi da takaici haka ake yi.

Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi masu jan hankali, wannan dalilin ne yasa bazai taɓa barin
ta ba, tun daya ganta a tashar mota tana faɗa da wani me moto yaji kalamanta sun mishi zubun
tsiwarta sun mishi tana da zafi amma bata gayan munanan maganganu duk zafi da tsiwarta
kenan kan giskiya take magana, sai kuma jarumta da karfin hali da juriya da rashin shakka da
rashin tsoron da ya gani tare da ita, ita ce zaɓin shi yaji kaunarta ta shige shi tun kallon farko.

Cikin sarsarfa ta isa cikin garejin motor, hango motar su tayi har ta kusa ciki da hanzari ta je ta
hau gidan baya can inda nan ne daman kujerar mata, bude jakarta tayi ta dauko korar ruwa ta
bude ta sha ko taji sanyi a ranta, lumshe ido tayi ita kanta tasan tayi jarumta tuno irin yadda
haduwarsu ta faru a yau din nan abun tamkar alamara wanda bata tunanin mutum dai mutu ɗan
mutum jikin mutum zai yi hadda yayi, tun fitowar ta daga kano suka haɗu a tashar moto suka
rabu yana me shaida mata kalamanshi akan yana kaunarta ta kaunace ko yaita bibiyarta har sai
ta amsa mishi tana sonshi, anan ta barshi suna tsaka da tafiya motar ta dan tsaya aka sauka
taje shago domin siyan ruwa sai kawai ta ganshi zaune cikin shagon me hade da gurin cin
abinci, a haduuwarsu wannan kuwa da ta kasance ta uku a garejin Kaduna wacce anan zata
hau motar zuwa Lagos ta kara ganinshi.

Duk ganin da take mishi da wasu irin kaya daban na canjin ƙabilu farko dai cikin shigar Fulani
komai da komai harda sanda a hannun shi, amma da ta ganshi a gurin cin abinci shigar nufuwa
yayi yanzun kuma cikin shigar yarbawa.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe ido a ranta ta ce, "Ya Allah karka ƙara haɗani
da wannan mutumin kuma, kasa har na isa Lagos lafiya," tana idarwa ta ƙara hangoshi tsaye da
shigar Fulani ni kuma bayan dazun na yarbawa da ganshi, sannan kuma da rabuwarsu da shi
bai fi minti hudu b ko uku. Rass taji gabanta ya faɗi gashi ta kasa dauke idanunta daga gareshi.
Shi kuwa murmushi kawai yake yi mata hankali kwance cikin nuna so da ƙauna.
Ganin motar su ta tashi gashi a can gafe yana kallon ta yasa taji dan dama-dama, dan duk
rabuwarsu hakan take hangoshi amma ta sameshi a gaba, kafin ta gama wani tunanin motar
har ta fita daga tashar, ajiyar zuciya ta sauke a ranta ta fara addu'o'in tsari kallon ilahirin
mutanen da ke cikin motar tayi taga duk kafirai ne ita kadaice macce musulma sai kuma wasu
maza da ta gani da shigar hausawa wanda hakan ya tabbatar mata cewa musulmai ne su.


Shiruu bayan munyi tafiya me nisa mun fita daga cikin garin Kaduna munyi nisa sosai mun dau
hanyar Lagos amma bamu yi rabin isa ba, tun ina duba lokaci har n gaji tun ina

muskuce-muskucen gajiyA da zama har na kife kai na wani irin barcin gajiya ne naji yana son
kama ni, tun biyar da na baro gida zuw.
Har barci ya fara fusgata naji ringin din wayata wacce ke cikin jakata tashi nayi cikin jin daɗina
dan ringin din ya sanar min da me kiran tawa.
"My sweet Aunt!"
Da sunan da ya baiyana akan screm din wayar kenan. Murmushi tayi tare da daukar wayar tare
da fadin, "Hello Aunty waiyo Allah na Aunty haka daman Lagos din ke da nisa, kamar n koma
gida ma". Wata sabuwa inji yan caca ashe masu tsiwa sun iya shagwaɓa haka, to gani nayi tayi
mgnr cikin wata irin shagwaɓa kamar ƴar shekara sha shidda.
Daga can ɓarin naji ta ce, "Sorry Autar Maama gani nan muna ta murna haba Autar Maama
shekara nawa rabon mu da juna, baki son ganin Aunty ki ne da yaronki".
Ƙara shagwaɓewa tayi, "Ina so mana amma kin san ban iya jure zama guri daya duk na gaji,
gashi yanzun kusan goma fa".
"Sorry kinji ai kun kusa nan da 12pm zaku iso, ko da zaki iso muna tashar muna jiranki".
Ji nayi kamar nayi kuka har ga Allah n gaj iya gajiya kuma ace yanzun a hakan ina da zaman
awa biyu tabb.
A hakan muka gama waya da Aunty na wacce na dau shekara shidda har da rabi ba tare da na
saka ta a cikin idona ba, bayan kuma ita ce ni nice ita yayata ce ina mugun sonta so mara
misali ita tai min komai, tun bayan aurenta da shekara daya mijinta aka dawo da shi legos da
aiki yanzun haka ita ma ta aikin take yi, ban taɓa zuwa ba sai yau munyi munyi Mama tabar ni
inje taki sai yau bayan nima na kammala karatu na na H N D. Ji nake kamar zani Makka za bar
murna da zumudin haduwa da farinciki na.

Dan a zahirin gaskiya Lagos bata min ba ko kadan garin arna garin matsafa duk wani bariki
sunyi kaurin suna, amma yau gani ina daukin zuwa daran jiya tsabar murna ko barci ban yiva
fatana da Allah yasa kamar yarda nake lfy n dawo lafiya.
Munyi nisa sosai har barcin wuya ya dauke ni ƙiii naji motor ta tsaya da sauri na ɗago kai na
dan ganin abunda ke faruwa mun isa ne ta tsayan ko kuwa yaya. Hayaniyar da naji ita ta ƙara
tabbatar min da cewa mun isa kenan, dan guntun tsaki naja jin yaruka iri daban daban ina da
ƙavilanci matuƙa bana so ko sha'awar wata ƙabila bayan tawa ta Hausa hasalima ni haushi
ƙabilu suke ban.

Juyo da kallo na zuwa jikin motor naji, juyowar da zan sakata a shafin farkon shafukan
rayuwata.
Wani rasss naji tare da jin tsull ta kasa ne, fitsari ne ko zawo ba zan iya tantancewa ba ko da
kuwa duvawa nayi, dan ina cikin yanayin da yafi tsoro tsoro, tsoron da ke haddasawa kai da
ruhi zuciya kwakwalwa tsoro wannan ƙaran ban ma iya runtse idon na sake buɗewa ba zuba
mishi ido kawai nayi ina kallon shi yana yimin murmushi "Daman tun can yana cikin motor ko
kuwa? kai ina bazan manta ba ina kallon shi a ƙasa aka kulle motar bayan kuma ta cika
sannan kuma duk na kalle mutanen da ke ciki ba ko me kalar kayan fulani balle na fulani, oh ni
*MEENAL* na shiga uku ta tabbata kenan Aljani ne meye nai mishi yake son dagulamin lissafi.

Ban iya dauke ido na a kanshi ba, gashi ina jin abunda ke fita ta kasa na yana ta ƙara fitowa
jikin nawa ma yayi sanyi libes balle na yi wani irin yunkuri ina cikin wani irin hali wanda ganin
wannan halittar cikin motor ce yahaifar min da hakan kuma wai a gabana a zaune.
"Ina ƘAUNARKI *MEENAL* ki amince da ni kaunar gaskiya nake miki ki amsamin kina so na",
yana kallonta yana mgnr bai damu da ganin halin da take ciki ba.
Bana ce banji ba ji ma kai ma isarwa dan hatta hancin ciki na saida suka shaida naji, ji nayi
wllh kamar na yi me n ɓace n ganni a gida a kwance ko me ma ni?

Ace wai har mutane cikin motar sun sauka Meenal bata sani ba me motar yayi mgn su sukai zai
yi gaba ne ita ina ta ji tayi nisa cikin duniyar saƙau.
"Zan tafi Meenal amma zan dawo zaki yi ta gani na har inda bazaki yi mamaki va, zan cigaba da
bibiyarki ne har sai kin amsa min kina so na", yana gama faɗa ya tashi ya fita daga motar bayan
ya gama yi mata kallon tsantsar so.
Taji jin daya ƙara rikitar da ita duk da a zaune take amma yadda jikinta ke rawa tamkar wacce
aka tsirawa wutar lantarki.
Jijjigar na naji anyimin da karfi yasa na juyo da sauri tare da sakin wata irin ƙara wacce wllh
zan rantse ban iya irin ta ba.
"Meenal lafiya na shiga uku lafiya kike kuwa Meenal," a ruɗe take yi mata mgnr.
Janyota suka yi daga motor ita da kyakkyawan mijin ta shi ma faɗi yake, "Tsiwa baby lafiya
kuwa meye sameki?"
Ganin bata cikin halin da zata iya yin mgn yasa suka ja ta gurin motarsu suka shigar da ita, shi
ya dawo ya kwashe uban akwati nan da ta jibgo kamar wacce zatai hijira....


*~Mrsbalarabe~ .*


*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._



*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*

_Page_
_3- 4_



✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.


_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_

Duk yadda suka so da na buɗe baki nayi magana na kasa, badan kuma bana jin su ba sai dan
kawai na rasa baki na dama abunda ke sarrafa magana.
Kuka sosai Auntyn ta fara yi, "Dan Allah *MEENAL* kiyi magana meke faruwa ne? meye ya
same ki?". Duk a ruɗe take jero tambayoyin.
Mijinta da yake gaba yana duƙi shi kan shi ya ƙara tsorota sanin wacece Meenal, "to ko zamu
wuce asibiti ne," y faɗa jiki a mace.
Ji nayi kamar an hura min isa a ido hakan yasa na ƙifta su, wanda hakan yasa tunani na yai
nasarar dawowa jiki na.
"Aljani ne Aunty bibiyata yake yi, na shiga uku ni zan koma gida gurin Maama wllh Aljani ne

shi", n fashe d kukan tsoro dan har ga Allah n tsorotan tsoro ma me ban tsoro.
"Aljani kuma wani irin aljani kuma Meenal? shi waye shi? a ina kika san shi da har kika san shi
aljani ne??“
Idanuwanta cikin nawa ta dafa duk kafaduna biya take yimin maganar cikin kulawa da nuna
damuwa dan Aunty Sadiya tawa ce ni kuma ta ta ce.
Ban kai ga buɗar baki ba naji ƙii alamar tsayawar moto, in kai kallo na na gan mu cikin wani
gida babba duk da kasancewa dare ne sosai amma na ga kyawun gidan.
"Ku fito mu shiga," yana faɗa ya fito riƙo ni Auntyn tayi muka fito nima nayi lamo jikin ta a tsora
ce gani nake zan ƙara ganinshi.
A babban falon gidan muka tsaya a ina Auntyna Sadiya ta zaunar da ni kan daya daga kujerun
daka dakin itama ta zauna.
Yaya Miftahu kuwa(Sunan d nake kiranshi da shi kenan) yake ya dauko min ruwa me sanyi ya
kawomin.
Amsa nayi dan ina da bukatar shan ruwa na sha sosai sannan na miƙa mishi kurar ina ta sauke
ajiyar zuciya.
Shi ma zama yayi kusa da ni cikin kulawa ya kalle ni ya ce, "Tsiwa baby

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login