Showing 33001 words to 36000 words out of 42034 words
ta cike da tausayawa,fuskarta ta shafa take k’wallah suka sake cika idonta.
“Meenal menene ya sameki?,Don Allah ki bud’e idanunki Meenal,Duk wani farin cikina yana
tattare dake”.
Shigowar wata nurse ya sanyata yin shiru.
“Kiyi hak’uri kidena wannan kukan da kike,zata iya farfad’owa ko wane lokaci”.
Tana gama fad’in haka ta fara qoqarin cire drip d’in da aka sanya ma Meenal.
Sir Daniel kuwa Kiran Mom d’insa ya addabesa don harta isa ma’aikatar ta tarar baya nan,yana
d’agawa ta balbale shi da masifa,tare da bashi umurnin duk inda yake ya baro yazo ma’aikata
tana son ganin shi, ba shiri ya fice daga Asibitin bayan ya gama tsara komai akan Meenal,don
duk wani abu da zata buqata saida ya bada kud’i a k’asa.
Yana shigowa Company bai zarce ko ina ba sai Office d’insa don yasan Mom tana chan,saida
ya tsaya ya daidaita nutsuwarshi sannan ya tura k’ofar office d’in ya shiga,zaune ya sameta
tana waya tana ganin shi ta sakar mishi wata muguwar harara,shikuwa murmushi ya sakar mata
tare da qarasowa wurinta yayi mata side hug yana kai mata peck a goshi.
“Yaushe ka fara min qarya Son?”.
Ta jefo masa tambaya don sosai tayi mamakin yanda yayi mata qaryar yana office, don qarya
ba halin shi ba ce tin yana yaro.
Sosa kai yayi yace;
“Sorry Mom yau nayi babban laifi ki yafemin,naje wurin wani Meeting ne na sirri,ba kowa ma
yasan bana Office ba”.
Sai a lokacin ta yarda dashi tace;
“Okay,Menene Abinda Meeting d’in ya qunsa”.
Shiru yayi yana tinanin qaryar da zai k’ara zabgo mata don shi sam bai iya qaryaba,har
mamakin kanshi yayi da yayi mata wannan qaryar ta yarda.
“Wai suna son na sanya musu hannun ne akan wata Giya da za’a fara mai cike da sinadarai
masu kyau”.
Murmushi tayi tace;
“Dakyau yarona,ni nasan cewa kai d’in a koda yaushe kaine a gaba saidai a bika a baya,Ina
alfahri da kai sosai”.
Shima murmushin yai mata yana fad’in,
“Nima haka Sweetheart”.
Mik’ewa tayi tace;
“Zan wuce Church yanzu,kasan munada biki yau,k’arfe takwas tayi maka a chan kai da Taye”.
“Okay Mom”.
Ya fad’a ranshi a d’an jagule,daga haka Mom ta fice daga office d’in.
Meenal ta fad’o masa a rai,karo na farko da yaji wani irin matsanancin tausayin ta ya mamaye
zuciyar shi,Wacece ita?,meke damun ta?.
Tambayoyin da ya shiga jero ma kansa kenan,d’an guntun tsaki yaja saboda rashin sanin amsar
wadannan tambayoyin.
Ganin lokacin sallar la’asar har ya wuce ya sanya Anty Sadiya mik’ewa cikin sanyin jiki ta shige
Toilet d’in d’akin tayo alwala, ta cire d’an kwalin kanta ta shimfid’a ta gyara mayafinta ta gabatar
da Sallah, ta dad’e sosai tana yima Meenal addu’a hawaye sai ambaliya suke a idonta.
Haka taci gaba da zaman jugum tana kallon Meenal,sai a lokacin ta tino da Abban Bak’ir da shi
kanshi Bak’ir d’in,Number shi ta lalubo ta danna mishi kira,yana d’agawa ta fashe mishi da
kuka,cikin tashin hankali yake tambayar meya faru,da k’yar ta daina kukan ta shiga fad’a mishi
abinda ke faruwa nan yace mata gashi nan zuwa,tace ya d’auko Bak’ir,daga haka suka katse
wayar kowa da abinda yake sak’awa a ransa.
Ko Minti Ashirin basuyi da waya ba sai gashi ya iso,da kanta ta fito zuwa tarbon shi,Karb’ar
Yaronta tayi inda shikuma ya riqo ledoji a hannunsa suna tafe yana tambayar jikin Meenal d’in
da haka har suka iso d’akin.
Sosai Meenal ta bashi tausai,don numfashin da takeyi kawai ze tabbatar maka da tana
raye,zama yayi kan kujera yana kallon Anty Sadiya yace;
“To su Doctors d’in me suka ce ne?”.
Tana cire ma Bak’ir rigar sanyin da ke jikinsa tace;
“Wai lafiyar ta qalau,kawai shock ne maybe taga wani abun da ya firgitata ne da yawa,wa
yasani ko wannan Aljanin ne dake bibiyarta ta gani”.
Girgiza kai Yaya Yayi yace;
“Na rasa gane kan lamarin Meenal,kawai addu’a zamu cigaba da yimata insha Allah za’a dace”.
“Allah yasa”.
“Ameen”.
Daga Haka suka cigaba da tattaunawa akan lamarin Meenal,daga k’arshe dai gida Yaya ya
koma ya d’ebo musu kayan su da duk wani abun da zasu yi amfani dashi.
K’arfe takwas nayi Mom ta danno mashi kira akan ya tabbatar ya iso yanzu,laqe murya yayi
yace;
“Mom Banda lafiya fa,kunnen nan nawa ya matsa min”.
“Oh my god!,Ka kira Doctor d’inka?”.
Ta fad’a cike da damuwa,don tasan yanda ciwon kunnen nan nashi ke basa wahala,ko kad’an
baya raga mishi.
“Eh na kirashi Mom yace zaizo yanzu”.
“Good Boy,Kace mishi ya duba min kai dakyau kaji ko”.
Cikin ‘yar shagwaba yace;
“Okay Mom,Bye”.
“Bye Son”.
Daga haka ya katse wayar yana lumshe idonsa,miqewa yayi ya shiga Bathroom yayo
wanka,yana fitowa ya sanya wasu qananan kaya tare da feshe jikinshi da turaren sa mai
k’amshi,Keys d’in motarshi ya d’auka ya nufin harabar get,horn yayi ma masu gadi da sauri
suka bud’e mishi get ya fice daga gidan,ya kama hanyar Hospital d’in da Meenal take.
Sosai yaya da Anty Sadiya sukayi mamakin ganin shi,tambayar me jiki yayi suka bashi
amsa,nan yace zai wuce sosai suka hau yimasa godiya da zai fita ya ajiye musu wasu
mak’uddan kud’i yayi ficewarsa,Kallon juna Anty Sadiya da Yaya sukayi saidai basu ce komai
ba.
Wasa-Wasa har saida Meenal tayi 2days a Asibitin,har lokacin bata farfad’o ba amma lafiya lau
take fitar da numfashi kamar me bacci,Anty Sadiya tashiga damuwa sosai ganin halin da
Meenal ke ciki don sosai ta tsorata da lamarin,Doctors d’in da Yaya ke lallashinta tare da qarfafa
mata gwuiwa,Sir Daniel kuwa be qara zuwa ba amma labarin ta yana a kunnensa shima duk ya
shiga damuwa da wannan lamari na Meenal.
Anty Sadiya na zaune ita da Anty Rabi’a da tazo ganin Meenal,sukaji kamar Meenal d’in ta
sauke ajiyar zuciya da qarfi,da sauri suka juyo suna kallon ta don tabbatar wa,a karo na biyu ta
sake sauke ajiyar zuciya sai kawai Jini ya fara biyowa ta baki da hancinta.
A mugun firgice suka nufi inda take kwance,jijjigata Anty Sadiya ta shiga yi tana kiran sunan ta
cike da tashin hankali amma shiru,sakinta tayi ta fice daga d’akin da mugun gudu ta nufi wurin
Doctor.
A tare suka shigo d’akin da Dr d’in tare da wasu nurses,suma cike da mamaki suke kallon jinin
dake fitowa daga Bakinta da hancinta,nan take suka shiga yimata aune-aune don ganin abinda
ya haddasa mata wannan bleeding d’in, babu abinda suka iya ganowa,dubararsu ta likitoci suka
shiga yimata dak’yar suka samu jinin ya tsaya, suna k’ara aunata sukaga jininta yayi qasa
sosai,tana buqatar jini cikin gaugawa.
Kuka kawai Anty Sadiya keyi,Anty Rabi’a na lallashinta.
Number Sir Daniel Doctor ya kira ya sanar dashi abinda ake ciki,babu b’ata lokaci sai gashi ya
iso Asibitin,Ana auna jininsa aka ga yana yimata nan aka d’iba aka zo aka sanya mata,sai kuma
numfashinta ya fara barazanar d’aukewa take aka sanya mata Oxygen,haka suka cigaba da
zama Asibitin babu wani cigaba,don sau uku ana qara mata jinin Sir Daniel,abunda yayi
matuqar d’aurewa su Anty Sadiya kai kenan.
*After One Week*
Duk kaga halin da Meenal ke ciki dole ka tausaya mata,don kuwa duk ta rame kamar wacce ta
shekara tana ciwo,Anty Sadiya ma ta rame sosai don ko bacci bata samunyi.
Ta b’angaren Sir Daniel ma sai a hankulla,babu abinda yake tsinanawa a office, ga baki d’aya
baya jin d’ad’in komai,sai a lokacin ya qara tabbatar da yana k’aunar Meenal bada wasa ba.
***************************************
“Ina sanki Meenal,kece farin cikina”.
Sassanyar muryarshi ta daki dodon kunnena.
Fuskata d’auke da murmushi na juyo na kallesa,yana tsaye kusa da wata bishiyar fulawa mai
kyawawan furanni masu launin kala,hannu ya miqo min yana fad’in,
“Kizo gareni Meenal,nazo miki da wani muhimmin labari”.
“Dagaske?”.
Na fad’a ina kallonsa.
Kai ya gyad’amin alamar eh,wurinsa na nufo ina cigaba da yimasa murmushi, inda ya riqo
hannuna muka zauna akan wata lallausar capet.
“Kinsan labarin da zan baki?”.
Girgiza kai nayi ina fad’in,
“A’ah sai ka fad’a”.
“Kalli nan”.
Ya fad’a yana nunamin tafin hannunsa,
Zaro ido nayi ganin Sir Daniel zaune a office yayi tagumi.
“Sir Daniel!,Meyasa kuke kama dashi?”.
B’ata fuska yayi yace;
“Banason tambaya,Inason ki saurari duk abinda zan fad’a miki a yanzu,idan har kikayi amfani
da abinda zan fad’a miki to tabbas kin tsiratar da rayuwarki daga fad’awa halaka,idan kuwa kika
qi to lallai kuwa kina cikin had’ari Meenal”.
Ban iya cewa komai ba na zuba mishi ido,ina son jin abinda zai fad’a.
*#Comments*
*#Share*
*#Vote and like*
~Mrsbalarabe✍️~
*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_
*Fatima Batula✍*
_Wattpad:mrsbalarabe._
*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8
*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_
_29-30_
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.
“Meenal Ina son kisan cewa Daniel ya kasance Amini a gareni,Tin yana qaramin yaro nake
jikinsa saidai babu wanda yasan da hakan saboda bana yin duk wani abun da zai nuna ina
jikinsa,amma nakan fito masa muyi ta wasanni lokacin yana yaro,daga lokacin da ya cika
shekara 10 na dena fito masa muna wasa saboda tilastani da iyayena sukayi akan dole sai na
rabu dashi saboda ni musulmi ne shikuma arne,ya shiga damuwasa sosai lokacin da yadena
ganina kamar yanda nima na shiga,amma a koda yaushe ina tare dashi domin kiyaye lafiyar
shi,Ina k’aunarshi ne shiyasa na rab’esa,na zauna a jikinsa duk da ya kasance shid’in maras
tsalki da tsalkake ubangiji mahalicci, saidai duk k’ok’arin rabani dashi da iyayena sukayi hakan
be yiwuba domin kuwa ina so na zame masa wani haske a rayuwarsa ta hanyar d’orashi akan
tafarkin tsira wato addinin musulunci,bana son ya mutu cikin kafurci saidai gashi shikuma ya
kasance mai taurin kai da tsananin qin musulunci da musulmai,Tin ranar da na ganki naji a
raina kece wacce zaki iya bani goyon baya wurin kawo haske a cikin rayuwar sa,saboda naga
ko kad’an ke bakisan miye tsoro ba sannan kinada Hankali da kuma hikimar iya magana bugu
da qari kinason addininki kuma kina matuk’ar kishin addinin ki,wannan ne dalilin da yasa na fara
bibiyar rayuwarki da sunan ni masoyinki ne kuma ina fito miki da siffar sa har saida nasamu na
had’aku,nine na cilastamasa a ransa dole sai ya d’aukeki wurin aiki duk da ko kad’an matsayinki
bai kai kiyi aiki a k’ark’ashinsa ba,wanda hakan yayi matuk’ar ba mutane da dama mamaki tare
da sosa ran wasu”.
Cike da tsananin mamaki nake kallon sa,don gabaki d’aya jikina yayi sanyi,mik’ewa yayi ya
cigaba da fad’in,
“Yanzu haka Daniel ya fad’a tsundum cikin kogin k’aunarki,wanda zan tabbatar miki bai tab’a
son wata ‘ya mace ba bayan ke kuma bazai tab’a son wata ba sai ke,Meenal ina so ki karb’i
soyayyar sa,ki fitar da shi daga hanyar b’ata ki janyosa cikin hasken musulunci idan kikayi haka
to zakiga sakamako mekyau a wurin Allah,sannan zaki samu lada mai d’umbin yawa,a halin
yanzu kinada babban muhalli a cikin zuciyarsa,inada tabbacin zai iya yin komai a kanki”.
Nima mik’ewa nayi ina kallonsa don na kasa gasgata abun da yake fad’a min,na kasa yarda da
kalamansa don nasan wannan bazai zama gaskiya ba,saidai idan akwai wata manufa.
“Ni Meenal bazan iya soyayya da arne ba,taya kake tsammanin zan yarda da duk wannan
bayanai da kake min?,Na farko dai ni bazan tab’a amincewa da wannan k’uduri naka ba
sam,abu na biyu bazan iya ba,kai me zai hana ka musuluntar da shi?,ai kaima musulmi ne,abu
na k’arshe ina so ka fita rayuwata ga baki d’aya saboda tin lokacin da ka shigo rayuwata na
kasa samun sukuni a kullum cikin tashin hankali nake, ka hanani jin dad’in rayuwa”.
Na k’arashe maganar cike da takaici don ganin nake wannan ai rainin wayo ne,taya za’ace duk
fad’in duniyar nan saini zai jibgama wannan babban aikin da nake da tabbacin bazai tab’a yin
tasiri ba ballanta akai ga zancen nasara.
“Meenal bijirewar ki shine zai zamo babban kuskure a rayuwarki,zan hanaki farin ciki na har
abada idan har kika bijirema maganata,ga baki d’aya saina zamo miki masifa a rayuwarki”.
Cike da dauriya tare da nuna jarumta mai tattare da rashin tsoro nace;
“Ni nasan cewa Akwai Allah kuma shid’in ba azzalumin sarki ba ne,shine zai sakamin akan
cutarwar da kake min,don inada tabbacin baka fi qarfinsa ba,kuma kai baka isa ka cutar da ni
ba saida izini da yardar sa”.
Ina gama fad’in haka na fara waige-waige saidai bansan inda zan dosa ba,duk inda na duba sai
inga ruwa masu yawan gaske a kwance.
Wata mahaukaciyar dariya ya bushe da ita yace;
“Bazaki tab’a samun kub’uta a gareni ba har sai kin amince da maganata,idan kuwa kika qi zan
cigaba da azabtar da rayuwar ki ko yanzu kinsan irin wahalar da kike sha a gadon Asibiti,kuma
wannan duk yana daga cikin aikina”.
Kallonsa na ke idona sunyi jawur,da qarfin gaske na furta,
“Ka mayar dani inda ka d’aukoni,idan ba haka ba jikinki zai gayama”.
K’ara sakin wata dariyar yayi yana tafa hannayensa,nan take ya rikid’a ya koma wani irin
balagaggen zaki majiyin k’arfi,banyi auneba naga ya fara tunkaroni gadan-gadan.
Ja da baya na farayi don na tsorata ainun,addu’oin tsarin ubangiji na fara karantowa domin
kuwa nasan shine kawai zai iya kub’utar dani daga hannun wannan azzalumin.
“La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,Wala ya’uduhu hifzuhuma wa huwal
aliyyul azim,Wallahu galibul ala amrihi wa la’ilaha ilallah wallahu akbar”.
Take naga fuskarsa ta chanja,inda wata bak’ar guguwa ta turnuk’esa rawa jikinsa ya fara kamar
mazari daga k’arshe ya fad’i a qasa,nima wani irin jiri naji ya debeni na fad’i a k’asa har lokacin
ban dena addu’o’in da nake ba.
Fitowar Anty Sadiya daga Toilet kenan ta tarar da Meenal na kwararo addu’oi,da mugun sauri ta
iso gareta tana fad’in,
“Meenal kin samu lafiya?,Alhamdulillah,Allah abun godiya”.
A hankali na bud’e idanuwana da suka min mugun nauyi ga wani irin nauyi da kaina
yayimin,dishi-dishi nake ganin Anty Sadiya,dak’yar na iya d’aga hannayena na mik’o mata da
sauri ta rik’ani nasamu na zauna ina kallon Anty Sadiya da farin cikin ta ya gaza b’oyuwa.
“Sannu Meenal,Yanzu meke miki ciwo?”.
Ta fad’a tana zama kusa da ni cike da kulawa,Murmushin dole na sakar mata don Ko kad’an
bana jin zan iya magana saboda wani iri da naji bakina yayi duk babu d’ad’i,ganin kallon da
nake bin jikina dashi ya sanya Anty Sadiya fad’in,
“Bara naje na had’a miki ruwan wanka Meenal”.
Tana gama fad’in haka ta mik’e da sauri ta nufi Toilet,ba jimawa sai gata ta dawo hannunta
d’auke da Towel,da taimakonta na cire kayan jikina ta rik’ani zuwa Toilet,saida ta tabbatar zan
iya wankan da kaina sannan ta baro Toilet d’in fuskarta d’auke da murmushin farin ciki,wayarta
ta d’auka ta kira Yaya domin sanar dashi.
Saida na fara yin brush sannan na yi wanka,abubuwa da damane chunkushe a
k’wak’walwata,na rasa wanda zan tunkara in sanar dashi ainahin abinda ke damuna,inason
tunano abubuwa da dama a raina amma na kasa tuno komai.
Idan naji ruwan comments zakuji new update a gobe.✋
~mrsbalarabe✍️~
*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_
*Fatima Batula✍*
_Wattpad:mrsbalarabe._
*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8
*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_