Showing 15001 words to 18000 words out of 42034 words

Chapter 6 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf

Advertisement

24 Jun 2025

2304

wacce xanyi ramuwar gaiyya ga wannan halittar ta
ka,Allah kasan ban iya jure abun da ban ɗau fansa ba akanshi,wannan halittar taka in ma dai
mutum ce ko aljanna Allah ka bani ikon yin galaba akan shi Allah ba ruwan Auntyna Allah kasa
kar abun ya shafeta,"hawaye nake yi masu zafin gaske a inda maganar ke fitowa daga can
ƙasan zuciyata,kallon ƙofar nayi wacce suka barta a buɗe bayan fitarsu,ina kudurtawa kai na
duk rintse bazan taɓa bari ta rasa aikin ta ba.
Ga tsanar wannan halittar da ke ruruwa a cikin raina har wani ɗaci nake ji ai ko masoyina nasan
zai ya tayani tsanarshi,shi babban maƙiyi na a duniya har wani ji nake kamar na kashe shi na
huta.


Duk da kasancewar mutane sun yi ɗan mamakin ganinshi,amma basu wani ji ko kawo wani abu
a ranshi dan shi ɗin kamar hanwawa yake me zanja kala da launi.
Yana zuwa Office ya zauna zaman isa da gadara dan yana da fariya da gadara,rufe ido yayi
yana jin wani iri a ranshi baƙon lamari dai kawai idanuwanshi yake so suyi toxali da ita.
Ɗanna wata ƴar ƙararrawa yayi wacce kai tsaye take aikowa office satariya saƙon kiran shi.
Shiru yaji har gurin minti ishirin ba ita ba alamarta.
Ita kuwa Aunty Sadiya da tunda ta shigo jikinta a macce har ta isa office ɗinta ta zauna shiru
bata ga wata alamar sallama ba,dan idan har aka sallami mutum to ko da zai xo gobe zai dai
yaga wani kan kujerarshi.
Kuma bata ji wani labari makamancin hakan ba,hasalima lura da tayi ba wanda ya shiga office
ɗin tun jiyan.
Office ɗin P.A ya ɗanna kira bai kai ga sauke hannunwanshi ba yaji knocking.
"Come in",ya faɗa ƙasa.
Jiyowa tayi,"Goodmornig Sir".
Kallonta yayi sama da ƙasa ya daɗe yana jin sha'awarta saidai shi abu ɗaya ne baya so rai
ni,bazai taɓa iya neman ma'aikaciyarshi ba,bada kai kenan wanda baya jin xai iya bada kanshi
ga kowa,ko matan waje su ke bada kansu gareshi.
Ɗaure rai yayi daman ba ma'abocin fara'a ba ne,"where is secretary?"
"Bata zo ba tun jiyan nan,saidai naga accounter (Aunty Sadiya)ita ta zo yau".
Tana kai aya yace,"call her".
Ta juya ta fita ita kanta tana mugun sonshi,da biyu ma tayi yadda tayi tazo kamfanin aiki
dominshi amma har yau ta kasa samun ko wacce irin dama.
Rass gaban Anty Sadiya ya faɗi jin wanda ke kiranta,haɗiye wani daskararren miyau tayi ta fito
daga office ɗin na ta jiki a mace,tana zuwa tayi knocking ya bata izinin shigowa.
"Where she is?"
"Amm..am she is at home..we thng dt ..thatt".
"Call her bata san dokar ƙin zuwa office ba ne?"
Wani irin sanyi taji a ranta har saida tayi wani irin deepbreath na jin daɗi,"Ok sir thank u Sir",ta
faɗa jiki na rawa bata taɓa tunanin ita kanta xata cigaba da aiki ba,balle kuma Meenal.
Fita tayi cikin jin daɗi jiki na rawa ta shiga kiran Meenal ɗin ringin ɗaya biyu ta ɗauka.
"Meenal wllh ke me sa'a ce,Allah na sonki Meenal".

"Allah na son kuwa ai Aunty Sadiya".
"Eh haka ne amma ke me sa'a ce,kinyi abunda ba wanda ta taɓa yi ya xauna".
"Ya aka yi gayamin tsinannen ya koreki ne,bari na zo na bashi hakuri dan Allah yayi hakuri ni ya
hukunta ni,"a gaggauce nake yin mgnr kamar ta kusa ƙarewa.
Dariya Anty Sadiya tayi,"A'a Meenal be kore niba kuma ke ma yace ki dawo bakin aiki,ki shirya
yanxun ki fito",ƙil ta katse wayar. Wani irin sagaga nayi,"meye manufar mutumin nan akai
na?idan bashi aljanin ba ai kurata zaiyi kamar yadda suka faɗa",hura hanci nayi cikin ɗaga
murya nahau faɗin,"Yau kuwa dole ayi ta ƙare zai ka gayamin manufarka akai na...."tamkar ina
gabanshi yadda nake maganar "Ai daman nasan duk kai ne,kana son ka saka ni a cikin ruɗani
ne dan ka ga ko xan so ka, soyayya dai banyi duk kuwa tsiyarka..."ina faɗan ina shiri.Daman
tun safe nayi wanka na shirya,cikin duguwar riga baka da ratsin fari,gyalen rigaar babba ne na
yafa abu na,na saɓa jaka..
Na fito fuska a murtuke,ina zuwa na je direba yaja ni gurin,kansutuwar ba wani nisa yasa muka
isa da wur,na fito duk da naji gabana yana faɗuwa amma ban yarda hakan yayi min tasiri ba,na
fito ban ko biye ta mutanen da naji suna saƙin ƙananun maganganu ba,ko Office ɗin Aunty
Sadiya ban waiwaya ba,kai tsaye office ɗinshi na nufa,knocking nayi. "Come in,ban ji abunda yace sosai ba amma nasan umarnin shigowa zai bani hakan yasa na
faɗa,"Ai ko baka faɗa ba shigowa zanyi,"na faɗa da ɗan ƙarfi tsakiyar office ɗin naja na tsaya
ina hura hanci da baki.
Dany kuwa da tunda ta shigo ya bita da wani irin kallo wanda shi kanshi bai san na meye.
"Kai malam ya isa haka,ka fito muyita gaba da gaba,idan mutum mutum idan aljann aljanna".
Bai san lokacin da ya sake wani irin murmushi ba,"such an idiot girl".
"Idiot!na furta da ɗan ƙarfi na haɗe da zare ido.
Kalaman daya xuburbuɗamin jiya ne suka dawo kwanyata tare da haifarmin da wata irin
muguwar tsanarshi.
"am not an idiot u are ,idan hauka nake yi ka fini,jahila dabba kuwa wllh duk kai ne su,ni ko a
jikin hajilar ban taɓa jin larabin takkuli irin ka ba,dan na ce bana sonka,ka mare ni ka tsorata ka
kuma xage ni,for wht?i have never see person like u in my life,i say it and i will say it again i hite
u r...... Tasss wani lafiyayyan sauti ya duki kunnuwana ban an ƙare ba sai gani na nayi a zuƙunne a
kasa,ɗagowa nayi a razane a kuma tsora ce,raɗaɗin da naji a kunci ne ya tabbatar min da mari
na yayi,hawaye shaaa kuka na fashe da shi,"Who do u think u are? da zaka mare ni haka
Allah ya isa ban yafe ba wuta ballal kuma sai na rama,i hite u wllh bazan taɓa sonka ba,ko
kashe ni xaka yi tsinnan ɗan a bura uba. Ɗan balaja'u ɗan batsula..,"cikin tsantsar kuka nake
xagin nashi da.

Runtse ido yayi,a kaff duniya ba wanda ya taɓa kiranshi da mahaukaci,wacece ita da xata kalli
cikin idonshi ta kira shi mahaukaci,wani irin zafi yaji har cikin ranshi.
"Mahaukaci kawai wawa dabba jahili....ta uwa ta uba nake zaginshi zagin da ni kai na ban san
na iya ba..
Duk da baya jin take cewa amma yadda take mishi mgnr cikin ɗaga murya ya ƙara kai shi
ƙarshe wacce irin yarinyace wannan mara hankali,buɗe ido yayi wanda har sun sauya kalla
tsabar bacin rai ya ƙara shatata mata wani uban marin.

Wata irin gigitacciyar ƙara na sake da dukkan ƙarfin muryata......



*Hmm...this is just d begining...yanzun wasan zai fara,sai ku gyara zama.*


*Mu tashi lfy fans*


*#Comment*
*#Share*
*#Vote and like*
*Please*



~Mrsbalarabe✍️~


*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._


*I Dash d whole page to u MASOYIYAR Marubuta�haƙika kin nuna mana ƙauna kin yabe
mu,kin saka munji cewa mu ƴan baiwa ne,kin mana yabon da mutane basu yi mana,mun gode
bai isa zama tuƙici gareki ba saida muyi miki addu'a Allah ya cika miki burikan ki na duniya ya
baki sa'a akan duk abunda kika saka a gaba,ya yiwa rayuwa albarka ya kuma haɗamu a
firdausi kamar yadda kika yi fata,Batula ƴah ga Umar mata gurin Yaya Balarabenta,ta gaidake
tare da jinjina miki Dear yabonki agare mu ya saka ni jin daɗi har raina,fatan Alkairi Mosiyiyar
mu,Allah yabar ƙauna.*


*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na

gari. Amin thumma Amin.*

_Page_

_13-14_


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.


_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_



Rufe kunnuwanshi yayi da hannayenshi duk biyu,amma hakan bai hana ƙarar ihunta shiga cikin
kunnuwan shi ba.
Kafin cikar saƙon Office ɗin ya cika dam da mutane ihun da suka ji,a ruɗe Aunty Sadiya ta nufo
ni,"Meenal..Meenal.."Abunda ta iya faɗa kenan duk ta ruɗe.
Security ne suka kamo ni,nan Aunty Sadiya ta ruɗe ta shiga yi musu magiya tureta suka yi,suka

ja ni,ni kuwa da gaba ɗaya bana tare da wannan duniyar ma,nadai ji alamun rike ne aka yi irin
riƙon ɓara yin nan.
Fituwa yayi daga office ɗin kallo ɗaya zaka mishi kasan yana cikin wani hali me wuyar
kwatantuwa,huci yake yi kamar mafaraucin zaki.

Kai tsaye gurin motorshi ya nufa,daman shi ke tuƙin motor da kanshi,yaja ta da ƙarfin
tsiya,bazai taɓa iya misalta ɓacin ran da yake ciki ba,idanuwanshi sam basu gani tsabar ɓacin
rai.
Wani irin sautii yaji ƙiiiii sannan yaji kanshi na juyawa yana hajijiya wanda hakan ya tabbatar
mishi da cewa haɗari yayi.


Kuka Aunty Sadiya ke yi muraran tana basu hakuri su ƙyale ni,amma ina basu ji basu gani,inda
ake kulle masu laifi kafin a yanke musu hukunci suka kai ne,jefa ni suka yi sannan suka saka
key suka ƙulle ƙofar.
Kallon gurin nayi ina zubda wasu irin hawaye masu zafin gaske na kasa gane yadda zan kira
wannan lamarin da shi,illa kawai nace ina cikin goma sha tara,ina cikin hau ina cikin iftila'i
wanda wannan halittar ne ya jefa ni a ciki,xama naje nayi kan wata ƴar duguwar kureja,har
lokacin ina dafe da kunci na. Ina jiyo kukan Aunty Sadiya to bani da baki balle nayi magana.

******* *** *******
Shi kuwa cikin gaggawa akai asibiti da shi,tare da yi mishi taimakon gaggawa.
Kiran Momy aka yi,a ruɗe ta zo tana kuka kamar zata mutu shi ne kawai ɗan ta duniya tana yi
mishi wani irin mugun so lallashinta likitocin suka yi suka kuma tabbatar mata da abun yaxo da
sauƙi bai ji ciwo ba,zai kuma farka lafiya zasu iya tafiya gida ma,sannan taji ɗan sauƙi a ranta.
Taye ma kuka take yi sosai.
Ƙarfe huɗu ya farka,meyeasa yake jin wani iri a ranshi a madaɗin yaji yana jin haushinta sai ma
jin da yayi be ƙyauta ba,meye laifinta bata san yana da matsalar kunne ba ne,ya tsinci kanshi
da bata uzuri.
"Ka tashi ba abunda ke ma ciwo ko?",a ruɗe Momy take tambar nashi.
"meye ya faru?na hanaka tuƙi amma ka ƙi ji,kana tunanin idan wani abu ya faru da kai xan
yafewa kai na ne?siraran hawaye suka hau zirya akan fuskarta.
Murmushi yayi kaɗan tare da yunƙurin tashi zaune,maida shi tayi.
"Ai ba abunda ya farun?ba abunda zai faru da ni Momy,muje gida".
Ya faɗa can ƙasa.
Tashi yayi yana jin kanshi na wani irin sara mishi amma ya jure baya so hankalin ta ya
tashi,kama shi tayi suka fito har harabar asibitin suka shiga moto direba yaja su.
Suna isa ta kawoshi har ɗakinshi,"bari n kira Taye na gayamata mun dawo gida ta zo nan".
Ɗaga mata kai kawai yayi,ya tashi ya shiga toilet ya daɗi yana watsawa jikinshi ruwa,duk wani
tunanin da xaiyi da ita,ko taye da yace yana so sam baya tunaninta haka.
Yana fitowa wayarshi na ringin daman tun ɗazun yaji tana ta yi,da kamar karya ɗauka sai kuma
yakai hannu ya ɗauka.

"Hello sir ga yarinyar nan an kamata me kake so ayi mata".
Shiruu yayi yana saurar zuciyarshi yaji ko zata raya mishi wani abun amma yaji ba abunda take
raya mishi illa a saketa taje gida ta huta.
"hello Sir!
Maganar ta dawo dashi daga duniyar daya faɗa.
"A sake ta",yana faɗa ya katse wayar faɗawa kan kafitar yayi tare da yin wani irin deepbreath.
Yasan shi dai ba me sauƙi ne haka ba,amma kawai yaji yana sauƙaƙa mata ai tun jiya ya
kamata a hukunta ta,meke faruwa ne haka tun kallon farko yaji yana jin wani abu akan ta.
Murɗa ƙofar dayaji anyi ne yasa ya juya,tun kan ya ɗauke idanshi akanta ta iso gareshi ta
rungumeshi a zaune.
"Ba abunda ya sameka naji daɗi,bazan iya jurar wani abu ya sameka".
Lumshe ido yayi yana jin kalamanta har ranshi musamman sigar da tayi mgnr da shi.Ganin
jikinshi ya mutu yasa ta ƙara samun damar manne mishi tana shafa kwantaccen gashin
ƙarjinshi wanda ya jiƙe da ruwa.
Kiss takai mishi akan ƙirjin yirr yaji tsigar jikinshi ta tashi,kwantar da shi taye akan gadon ta haye
jikinshi.
"I lv u to,i wnt to u in my life with u,u are my heartbeat".
"i lv u too taye",y tsinci kanshi da faɗin hakan duk da dai ba yau ne na farko ba ,amma sai yaji
wani iri kamar bata cancanci ya so ta ba.
Cikin shauƙin so da sha'awar juna suka hau jiyar da juna daɗi,Taye ta ƙware gurin iya sex
shiyasa yake mugun jin daɗinta.


*****
Gaba ɗaya cikin su ba wanda ya iya cewa da kowa komai,kuka Aunty Sadiya take yi
ƙasa-ƙasa.
Ni kuwa da nake kwance rufi cikin bargo ina ta rawar sanyi , wani irin mugun zaxzaɓi ke
tambaliya da ina son nayi mgn amma ba hali.
Ɗafata yayi,"ya isa haka Dear saidai kawai mu godewa Allah da komai ke zuwa cikin
sauƙi,abunda za'ayi gobe kawai ku ajiye aikin da kanku sanan bayan kwana biyu ku shirya ku
tafi kano".Cikin sigar ban baki yayi maganar.
Share hawaye Aunty sadiyar tayi wannan ita ce mafita su ajiye aikin kawai ba zata iya jure duk
wani abu da xai faru da Meenal ba.
"to zan kwanta a nan,sai da safe".
kiss yai mata,"to ku tashi lafiya Meenal sannu zaki ji sauƙi kinji",yana faɗa ya juya ya fita.
Kwanciya tayi kusa da Meenal ɗin wacce har yanzun bata daina rawar sanyi ba.

Su kuwa barci ne yai gaba da shi bayan sun gama jiyar da juna daɗi,sai bakwai ya tashi duk da
ba wankan tsarki yake yiba,amma duk ya gama saduwa da macce sai yayi wanka,bai tashe ta
ba,ko da ya fito ya shirya cikin gajeren wando da riga ya fito,ɗakin hutawar momy ya nufa yana
zuwa ya sameta zaune,tana ganinshi ta taso. "Ka tashi ya kake jin jikin ka?"
100% normal".

Ya faɗa yana maida mata martanin murmushin da tai mishi zaunar da shi tayi,ba musu ya
zauna.
"Taye bata tashi ba ko?"
"Eh!
"Taye na sonka da yawa".
" i know".
"ina so na ganta da ciki ne sai a ɗaura auran ku,ina son ganin jika na,ka dunga kulata yadda
za'a samu cikin ".

"Okk!ya faɗa a fakaici shi kanshi yana son yaro fiye da komai.
"Dany meye ya faru ne a office?" ta jefo mishi tmbyar.
Shiru yayi me zai ce to.
"Naji kuma ance a sababbin ma'aikatan daka ɗauka musulmai sunfi yawa,u know very well
bana son musulmai bana kuma son kana hulɗa da su, kuma ka san waye mahaifinki fiye da
kowa?

Ita ce ta faɗo mishi a rai,"musulma ce,"ya faɗa a ranshi,yana jin wani irin connection me ƙarfi
game da ita,wanda kuma yake jin bazai iya nisanta kanshi gareta ba,yasan iyayenshi basu son
musulmai sam,kuma shi ma haka,duk da cewa saka mishi ƙiyayyar aka yi....

"naji ance secratary ka musulma ce ka kureta".
"What ya furta a ɗan zabure.
"Ka cire ta na ce".
Wani irin abu ya haɗiye kutt duk yaji ya dabure bazai iya kurarta yana son ganinta kusa kamar
wata ɓari a gareshi.
"tunanin me kake yi?
"Nothing zan cire ta..but for wht reason kike son na kureta me too i hite muslim kina tunanin
zan kulata ne ko me?ƙazamace fah im just hiting her ma,tunda na fara ganin yanzun haka ma
na saka an kulle ta,i wnt to make her life misrable cos ita ta kasance musulma ina jin daɗin
ganin ta kuntaka,I wnt her to realized yadda musulmai suke gurin mu,yadda zata ji ciwon
kasancewarta musulma...." shiru yayi yana jin wani sabon lamari,shi dai ba wani ma'abocin
ƙarya ba ne,amma ji yadda ya sake baki yana faɗin mayaudariyar ƙarya to,sam waɗannan
kalaman nashi na ƙarya ne shi kanshi ya shaida hakan,ko ɗis baya jin ƙiyayyarta a ranshi sai
ma wani irin feelling da yske ji akan ta wanda bai san ko na meye ba,and kuma bazai iya
ganinta kuntaka ba,tuno yadda yake jin zafin ganin hawayenta,duk taya ya iya shirya wannan
mayaudariyar ƙarya?tambyar da yake yiwa kanshi kenan,duk domin me?.
"good ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login