Showing 9001 words to 12000 words out of 42034 words
fira bani da ɗan fira, ina jiran ranar Lahadi tayi ranar suna
gida nace musu ni gida zan tafi, dan yanzun har ranar sati fita suke yi saidai bada wuri ba kuma
su dawo da guri. Kasancewar a babban famfani ne dan duk Lagos kowa yasan da kamfanin me kamfanin hamsin
me kudi ne, dan yana da kamfani iri daban-daban.
Yau ta kasance ranar ladi da wuri na fito ban bi takan su ba nai gurin Bakir na shiryashi da kai
na bayan mun gama lokacin gurin goma saura sannan muka fito.
"Aunty tsiwa fitsari wai ina aljaninki yake ne? naga kwana biyu bai kawo miki ziyara ba".
Yi nayi kamar ban san da wacce yake mgnr ba, nai zama na na fara bawa Bakir abinci.
"Zan koma gida na gaji da zama tunda ku rayuwarku haka take bazan iya ba gurin Maama zan
koma".
"Haba Auta kiyi hakuri daman jiya da daddare muka yi mgn da Honey akan haka zaman gidan
zai miki yawa to gurin aiki na za'a ɗibi'i ma'aikata to na tura application letter jiyan".
Zaro ido nayi, "Me gurin aikin ku na ce ina so ne, ki janye ma tun wuri dan bana so".
"Haba MEENAL ya zaki ce haka dabara ce fa kinga kullum sai ku dunga fita tare ku dawo tare
hakan zai fi da zaman gidan da kike yi".
"Hm nidai Yaya gaskiya bazan iya ba," abunda yafi ban haushi shi ne wato duk na rasa inda zan
fara aiki sai a nan na baro arewata na zo nan idan aikin nake so na zauna acan mana, ni sam
bana wani sha'awar fita aiki kamar wata namiji.
Da kyar da ya Allahu suka shawo kai na na yarda shi ma da sharaɗin na wata biyu kawai zanyi
na ajiye na koma gida, na kuma yardan ne dan idan na cigaba da zama cikin kaɗaici gajiya
zanyi n koma gida Maama kuma dariya zata yimin daman tace bazan iya yin ko wata ba,
shiyasa kawai na aminci har ga Allah badan na so ba.
Washegari ranar Monday duk suka wuce kamar yadda suka saba haka nai ta faman xama ni
kaɗai abun takaici nai wata irin qiba ta hutun bala'i.
Yau laraba ina zaune gurin karfe tara na dare ina kallo a falo sai ga su nan.
"Sannun ku da zuwa yau kun dawo da guri".
Washe baki Aunty tayi, "Eh yau shugaban mu ya sallame mu da wuri ne, amma MEENAL
gaskiya ke me sa'ar gaske ce", tana kare mgnr ta kai ga zama kusa da ni.
"Na me kuma?"
"Wllh MEENAL ba wanda ya taɓa zama matsayin Sakatariya a kamfanin mu ba tare da yayi
wani abun ba ko cin hanci ko yai asiri kuma ba ma kai tsaye haka ba, amma ke *MR DANIEL*
da kanshi ya baki wannan matsayin wllh da na gani sai da naji wani irin luu zan faɗa tsabar
mamaki na rasa dalili ikon Allah ne kawai yasa amma abun da mamiki shi da sam baya son
m.... "
Ban bari ta ƙarasa ba na katse ta," Hm ni bar gayamin meye nawa wllh ina ganin ba zan iya va
zan guduwa garin mu zanyi".
"Gaskiya MEENAL sa'arki tayi yawa farko dai ga masoyi ya rako ki har nan, sannan kuna ga
babban matsayi a gurin aiki ina ji a jiki na akwai wani abu".
"Gaya mata dai Honey abun da mugun mamaki wllh".
"Sai da safe! ina faɗa na tashi nabar gurin sai naji kamar na ce na fasa, dan ban hango alkairi
a cikin wannan aikin sam ni dan ƴar uwata kawai yasa na amince amma da ko kusa, gashi abun
jin ma gurin duk arna ne ni da ban son mu'amala da su.
Dariya suka yi sannan suka wuce dakin su.
Asubar fari naji aunty tana tashi na, "MEENAL dan Allah ta ki shirya kinga yau zaki fara zuwa
karki makara".
Bata barni ba saida ta tabbatar na tashi, na shiga bayi sannan ta fita ita ma ta je ta shirya.
Tunda na tashi nake jin ƙirjina na bugawa kamar zai fashe na kuma rasa dalili da kyar na fito na
tada sallah bayan na idar nazo gaban mirrow tunanin kayan da zan saka na fara yi, nasan idan
na saka riga da siket abun kallo zan zama kuma ni su ne kayana. Tashi nayi na janyo wata
duguwar riga navy blue ithopian abaya ce me kyawun gaske tasha adon stone na zura ta,
kamar yadda na saba yiwa fuskata Light makeup yanzun ma shi nayi, ni kaina nasan nayi kyau
na dauko farin kyale nayi rolling din kai na da shi da farar jakata na saka takalmi na fari me dan
tudo.
Tashi nayi tsare ina karewa jiki na kallo ba laifi shape dina bai fito sosai ba, turare na fesa bayan
na mulke humra a jiki na.
Ina tsayen Aunty ta shiga.
"Waw MEENAL kin hadu zaki kwashi ƴan kallo yau a office kuwa".
Ni daman akwai ni da basarwa na ce, "Naje mu je", nai gaba abuna kamar wata wacce ta kware
gashi ina jin gaba na faduwa.
Ina isa harabar gidan motar su Yaya na fita.
Gaban motar ta na shiga, ita ma ta shigo ita zata ja motor, bude mana get me gadi yayi muka
fice daga cikin gidan gabana na kara tsananta faɗuwa.
"MEENAL! Aunty Sadiya ta kira ta cikin kulawa.
Yadda naji ta kiran yasa na amsa nima cikin kulawa domin irin wannan kiran tana yimin shi ne
idan zata gayanin mgn me muhimmanci.
" MEENAL ki kula sosai nasan zaki ga bambanci sosai amma ki kula sosai cikin arna zaki shiga
tsamo-tsamo kuma yare, ki kama kanki abun jin ma ina fatan Allah yasa Sir *DANIEL* ya barki
ki shigaba da saka irin kayan nan, me kamfanin baya son musulunci baya son musulmai, ban
ce ki juya ki nuna ke ba musulma va ce no ko baki ce ba an ganshi a fuskarki amma ki kula ki
kama kanki".
Tashin Hankali tabb aiki ja, "To me yasa Aunty Meyasa sai nan baya son musulunci baya son
musulmai kan me to? wani irin kamawaye kike nufi nayi? Aunty kin san ni kuma kin san abunda
zan iya?.
" Ohh more no taya zan saka ki fahimta MEENAL".
"Bana jin zan fahimta Aunty wllh idan har sai na koma yin shigarsu arna sai nayi basajar ni
wacece sannan zan cigaba da aikin wllh a shirye nake na juya tun yanzun bazan iya b sannan
kuma....
Ƙii naji alamar tsayuwar moto kai duba na nayi a inda naji wani irin rass saida murfin zuciyata
ya rufta ciki, ambaton Allah na fara yi a zuciyata ya tsare ni ya kuma kare ni.
Sauka tayi, ganin hakan yasa nima na fito.
*REAL FUTURE HOPE IND. LTD.*
FUGULE ESTATE, ISHERI IJEGUN LAGOS NIGERIA.
nai tuzali ta sunan a can saman kamfanin me bene kusan shidda.
Dauke kai na nayi na cigaba da kallon gurin to nidai ba maƙiyiya Allah bace da sai nayi ƙarya
nace gurin bai yi kyau ba, amma da yake bashi a rai na sai naji be min kyawun ba.
"Muje! Aunty Sadiya ta ce min da yarensu da turanci binta nayi a baya ina kallon ikon me sama.
Wllh idan ba kasan hasken musulunci da ke baiyana a fuskar musulmai ba, bazaka taba cewa
Aunty Sadiya musulma ba ce.
Jiki na naji ya mutu libis ga shi sai famam kallo na ake yi, kamar a hadiye ne left hawa na biyar
muka hau.
Waiyo ni MEENAL ina zan saka raina kallo ne ya dawo gare ni ita kuwa Aunty Sadiya sai
gaisawa take da mutane cikin sakin fuska dan ta saba da su sosai shekara biyar tana aiki a
kamfanin.
Da yake akwai kama sosai a tsakani na da Sadiya shiyasa mutanen duk suka gane ni, gashi
duk sun san ni ce yanzun sabuwa sakatariyar Sir Daniel, kallon mamaki suke yimin a inda wasu
ke raya ma ransu tafiyar tamu tare baza ta yuwa ba domin baya son musulmai kuma ni daga
ganin alama musulmace ta kwarai wacce ke kishin addininta, wasu kuwa suna raya tafiyar zata
so daya dan ina da kyau ga sura shi kuwa mutum ne mayen me kyau mayen mata ne na karshe
karshe,wasu kuwa su ce idan na bada kai zan zauna lfy naci riba nida yayata duk da
kasantuwar ni musulma ce, idan kuwa naƙi na ja mana wahala.
Bin bayan ta nayi zuwa cikin office din da naga ta kunna kai ina shiga na tura kufar jiki na mace
, zama taje tayi akan kujerarta ni mamaki ma take ban.
"Aunty bazan iya yin wannan aikin ba".
"Zaki iya ya zama dole ma, MEENAL kenan taya zan fahimtar da ke sa'ar da kika yi a gurin nan
ki daure zKi iya ba ina nan ba".
Shiru nayi bayan na zauna naji duk rayuwata ta jagule na rasa abunda ke min dadin ina zan
saka kai na ni MEENAL.
Dafa ni Aunty Sadiya tayi cikin sanyin murya da sigar ban baki ta ce, "MEENAL karki ji komai
zaki saba nima haka naji da farko ba kuma abunda zai faru ba ina nan ba, kuma ki kula dan
canji zaki ga canji zaki ga mutane iri daban daban masu halaiya daban daban sai kin lura kin
kula sannan". Daga mata kai kawai nayi.
"Good my sister u are smart girl u know how act".
Nidai lamo nayi ina jin wani iri taya zan saba cikin mutanen da ba ƙabilata ba ba kuma addini na
va, anya kuwa zan iya irin wannan sabawar kuwa??
Waya naga ta kira tana ajiye wayar wata ƙasurgumar arniya ta kunno kai cikin offiice din kallo
daya zaka mata ka tabbatar wannan ko a arnan ma ita ƙasurguma ce.
Wani irin kallo naga tayi min mara kai, ban san lokacin da na maida mata raddinshi ba, dan ni
ban da hakurin wannan.
Da turanci sukai mgn akan ta tunamin yadda aikin yake da office dina da komai da komai na
kamfanin.
To tace da ita kawai ta kalle tace na biyo ta tare da, tashi nayi jiki a mace na bi bayanta har na
kulle kofar aunty ta tsayar da ni wai muje tare.
Naji dadi kuwa ina ma da a office daya ne zamu yi aikin nasan da na rage jin wani abun.
Yawo sosai muka yi duk idan muka je suna sunanin yadda komai yake da yadda ake amfani da
shi da komai da komai ina fahimta dan ba ƙarya ni gorowace by nature not by son a iya, duk
inda muka gifta naji ana ta mgnata akan sa'ar da nayi wasu naji suna cewa anya da akwai wata
a ƙasa ba yadda za'ayi Sir. Daniel ya dauke ni aiki, ohoo dai ni duk wannan maganganun basu
gaba na hakan yasa ban basu muhimmanci ba, daga su har ogan na su.
Duk mun zagaya ko'ina yanzun guri daya ya ragemin offiice dina wanda sai naje gurin oga
sannan zan shiga nawa office din, tunda muka nufa office din naji faduwar gaba na ya tsananta
na jure na cigaba da tafiya ina ambaton ubangiji na.
Tiny suna da naji Aunty ta kirata da shi kenan ita ce ta fara knocking din kofar a hankali tun tayi
sau daya ta tsaya gashi dai ba'a bamu izinin shiga ba, a rai na nace bai ma ji ba, gashi dai naga
sai tsayuwa muke yi ni har na fara gajiya da tsayuwar ma har na bude baki zanyi mgn taji ance,
"u can come". Ban wani ji ba illa dai kawai nace naji anyi mgn amma banji abunda aka ce ba, na gane cewa
yayi a shigo ganin ta murɗa kofar ta shiga.
Bin bayan ta nayi dan Aunty ta koma gurin aikinta office dinta.
Dan taɓe bakin nan nayi da na saba, ganin yadda ya bawa kofa baya kenan mu ma bayan ya
basu. bayani tayi mishi na kan cewa ni ce sabuwar sakatiyar na zo, tana gama faɗa ta juya.
To ni me zan tsaya yi juyawar nayi, har nayi taku ɗaya na tsaya cikk tare da yin nazarin kamar
fuskar aljani na na gani, a zabure na juyo.
Ni MEENAL taya zan iya mantawa da wannan fuskar ai har abada bazan taɓa mantawa da ita
ba.
"Aljani na! na furta can ƙasan maƙogaro.....
~Mrsbalarabe~✍
*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_
*Fatima Batula✍*
_Wattpad:mrsbalarabe._
*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_
_9-10_
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.
_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_
Komai nisan shuɗewar lokaci banjin zan iya mantawa da wannan halittar wacce ta kafa tarihi a
kundun rayuwata,hotonta ya shiga kwanyata ya zauna tamkar rubutu akan dutse,ai faɗa ma
ɓatawa ni *MEENAL* taya zan manta da shi wanda ban sanshi ba sai dai kawai na iya kiranshi
da *ALJANINA* zuba mishi milky eyes ɗina nayi tunda nake haɗuwa da shi ɓan taɓa ganin
yayimin kyau da cikar haiba ba irin yau ban wani damu ba sanin iya surkulen aljani.
Kaɗan- kaɗan nake jin zuciyata na bugawa a inda tunani na ya shiga karantomin abubuwa iri
iri,cigaba da kalle shi nayi tsaf ƙiff na kafe idanu na akan zarɓeɓiƴar saƙar kurus ɗin dake
maƙale a wunyanshi.
Nufarshi nayi a fusace cikin ɗaga murya da masifa irin tawa nahau faɗin,"Yau kuma da wannan
aka zo?ohoo ma zuwanka kafiri ko musulmi bai dame ni ba,kawai yau ina son insan kai waye
dan na gaji da barazanar da kake yimin ayita ta ƙare soyayya dai nace bana yi kuma ko kai ne
sarkin aljannan kafirai bazan soka ba,dan haka ayita ta ƙare kawai....."cike da tsiwa nake mgnr
murya kuma a ɗage.
Tundaga halittar yatsun kafafuwanta Daniel ke binta da kallo karo na farko ga baƙuwar fuska a
gareshi yaji yana son kallonta bai taɓa ganin ko da me kama da ita ba a duniyarshi,tunda suka
haɗa ido yaji ya kasa ɗauke idonshi akanta,shiruu yayi tare da zubawa bakinta ido yana kallon
yadda take sarrafa su duk da baya jin abunda take faɗa amma ya fahimci faɗa take yi,murmushi
kawai yake saki a fakaice Yadda ta ke faɗa ko da me meye confidence ɗinta ya matuƙar burge
shi yasan shi me kwarjini ne ya yarda da wannan ba duk mace ba,kunsan duk matan da yake
hulɗa da su basu iya kallon cikin idonshi su gayamishi ko da kalmar soyayya balle kuma ita da
yake ganin kamar faɗa take yi mishi,ta burgeshi for the first time yaji takai inda mata da yawa ba
su ko nufar gurin balle su burgeshi .
Ganin yadda yake ta sakin mata murmushi yake yi ya ƙara ƙular da ita.
"Dariya ma nake baka dole zan baka dariya tunda ka maida ni mahaukaciya yau sai na tuna
maka asiri",daa ƙarfin zaxxaƙar muryata ta ce,"ihhhhu jama'a help!help me!!!
Runtse ido yayi a yayin da yaji wani irin abu chuuu ya duki dodon kunnuwanshi shi mutum ne
mara son hayaniya a rayuwarshi duk wanda yasanshi yasan hakan gashi yana da matslar
kunne baya son ayi mgn da ƙarfi sam yana jin kamar laudspeak ake zuwa daidai kunnuwanshi
ana yin mgnr da ita Kasancewar ba wani nisa a tsakanin mu da ofisoshi ne yasa duk suka jiyo
ihu na,karo na farko kenan da suka taɓa jin irin haka ta faru duk abunda yayiwa macce bata
mishi ihu balle ta nemi taimako shiyasa duk suka ruɗe jin irin ihun da take yi.
Aunty Sadiya kuwa da sai da ta ƴarta wayarta dake hannuwanta a zabure ta fito da gudu ta nufi
office ɗin ganin hakan yasa ssuran ma'aikatan biyo bayanta dan ganin abunda ke faruwa.
Shi kuwa Sir Dany tunda ya rufe dukan kunnuwanshi da hannunshi ya kuma runtse ido amma
ina hannunwanshi sun kasa tsaida muryata ga shiga cikin kunnuwanshi suna dukanshi.
Ni kuwa ban tsaida yin ihuu na ba saida naga mutane sun shiga office ɗin dam sanan na tsaya.
Juyowa nayi na kalle mutanen da ke ciki Aunty Sadiya kawai nafi buƙata na gani dan ta shaida
yau dai