Showing 27001 words to 30000 words out of 42034 words

Chapter 10 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf

24 Jun 2025

1953

nace;

“Tofah!, har akwai wani abu da yafi sallah muhimmanci?,au kaima kace ka fara bin ak’idar arnan
nan, nan gaba ma kila sallar ma bazakayi ba”.

Dafe kai yayi yana dariya yace;

“Kai Meenal, ni ba hakan nake nufi ba,Bara naje dai nayi sallar nan”.

Ya k’arashe maganar yana miqewa har lokacin fuskarsa d’auke da murmushi yana kallon
Masifaffiya for real wato Meenal.

Ban ce komai ba nabi bayan su Anty Sadiya da suka bar wurin tin d’azun, yayin da Khaleed ya
fice daga gidan.

Bayan mun qare sallar ne, Anty Sadiya tace zamu wuce gida,sosai Anty Rabi ta nuna bata son
mu wuce, wai abar mata ni na kwana gidan, a raina nace taff a ina zan kwana?,Allah shi kiyaye

ai gidan Anty Sady kawai zan iya kwana injini a salkake, amma duk inda na kwana ji zanyi
kamar na koma arniya nima.

“Meenal zaki kwana ko?”.

Murmushin yaqe nayi mata nace;

“Dayake Anty akwai wani aikin office da na bari a gida,ina so idan na koma in qarasa”.

Kallona Anty Sadiya tayi cike da mamaki, nikuwa na fuske na d’auke kaina kamar gaskene,
inda Anty Rabi’a tace;

“To shikenan Meenal, idan kinyi free promise me zaki zo ki kwanar min”.

Sosa kai nayi don nasan wannan alqawalin bazai yiwuba sam,

“Insha Allah”.

Na fad’a ina miqewa ganin Anty Sadiya ma ta miqe alamar dai tafiya zamuyi, d’aukar Bak’ir nayi
ganin yanata lumshe ido da alama ma bacci yake ji, wata leda Anty Rabi’a ta miqamin tace;

“Ga wannan Meenal, ba yawa”.

Karb’ar ledar nayi ba kunya nace;

“Nagode Anty,Allah saka da alkhairi”.

Da Ameen muka amsa sanna muka nufi hanyar da zata kaimu pallor ta fitar damu waje, banga
Khaleed ba da alama bai dawo sallar ba.

Sallama mukayi ma Anty Rabi’a muka shige motar mu Anty Sadiya ta bata wuta muka fice daga
gidan,saida Anty Sadiya ta biya wani Restaurant ta siya muna Burger da Ice cream sannan
muka koma gida a gajiye.

Bayan Anty Sadiya nabi zuwa d’akin ta domin kwantar da Bak’ir da yayi bacci, ina fitowa na
wuce d’akina, kayan jikina na cire na d’aura towel na shige bathroom domin watsa ruwa don inji
dad’in bacci.

Koda na fito Cream kawai na shafa ma jikina, na zuba wata doguwar rigar bacci, wutar d’akin
na kashe nayi kwanciyata don wani irin lafiyayyen bacci nakeji.

Asuba Ta Gari Meenal

*#Comments*
*#Share*
*#Vote and like*



~Mrsbalarabe✍️~



*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._

*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8




* Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun
so ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin
matsayinki a gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy
ya baki miji na gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_21-22_


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.



Addu'ar Korar Shaidan da Wasuwasinsa:

Ya nemi tsarin Allah daga shaidan.
ُذوُع
َأ
ِهللاِب َنِم ِناَطْيَّشلا .
ِ
ميِجَّرلا
A'uzu billahi minash shaytanir rajeem (3)


​ Ya yi kiran sallah.

​ Yin zikiri (ambaton Allah) da karatun Alkur'ani.


_Bismillahir Rahmanir Rahim_



A B’angaren Sir Daniel shida Taye, sun kwana farantama junansu rai,daga baya bacci yayi
awon gaba dasu k’arshe dai a wurin Taye ya kwana.


Da asuba Anty Sadiya ce ta tasheni kamar dai kullum dak’yar tasamu na tashi saboda baccin
yayimin dad’i sosai, Ina kammala sallar Asuba, na nufi Kitchen don had’a muna abin kari, Arish
da kwai na soya muna sannan na d’ora ruwan zafin tea, Ina dama ma Bak’ir custard Anty
Sadiya ta shigo Kitchen d’in cikin riga da wando sun bala’in matseta, kawar da kai nayi ina jan
tsaki a raina,nace;

“Ina kwana?”.

Saida ta zauna kan kujerar dake kitchen d’in tace;

“Lafiya Lau, kin tashi lpy?”.

“Nima haka”.

Na bata amsa a tak’aice.

Murmushi tasaki tana fad’in,

“Yau me ake had’a muna ne?,naji gidan duk ya k’amsashe”.

Daidai lokacin Yaya ya shigo kitchen d’in shima.

“Tsiwa Baby Me ake dafa muna hakane??duk gidan ya cika da k’amshi”.

Shima ya jefomin kalar tambayar Anty Sadiya.

K’wafa nayi ina kallon shi fuskar nan tawa a tamke nace;

“Arish da Kwai”.

Yanda nayi maganar ne ya sanyasu dariya.

Anty Sadiya tace;

“To a gama lafiya,bara mutafi karmu dameki”.

Daga haka suka fice ita da Yaya suna maganar da bansan me suke cewa ba.

Kayan da na b’ata na shiga wankewa,na jero abinda na had’a a dainy,sannan na wuce d’akina
don yin wanka.


Wani Sihirtaccen k’amshin turaren da nake jin kamar na tab’a jinsa ya doki hancina, amma na
kasa tino inda na tab’a jinsa,chak na tsaya ina k’arema ko ina na d’akin kallo don ba shakka
k’amshin daga cikin d’akin yake fita, wani rass naji gabana ya bada da sauri na fice daga d’akin
ban zarce ko ina ba sai d’akin Anty Sadiya ko sallama ban tsaya yiba na fad’a d’akin.
Mik’ewa tayi da sauri ganin yanda nashigo duk a hargitse.

“Meenal!,lafiya?”.

“Anty ke kika fesa turare a d’akina?”.

“Turare kuma?,Ni ban shiga d’akinki ba”.

“Me yake faruwa ne?”.

Yaya da ya fito daga Bathroom ya tambaya yana kallon yanda mukayi cirko~cirko damu.

“K’amshin turare naji a d’akina,wallahi kamar anyi b’arin turare a ciki”.

Kallon juna sukayi Yaya yace;

“Muje d’akin inji”.

Dukan mu ficewa daga d’akin mukayi zuwa d’akina, ga baki d’aya jikina duk a sanyaye.

“Banji K’amshin komai ba Meenal”.

Cewar Anty Sadiya cike da mamaki.
Ganin yanda jikina yayi mugun sanyi yasanya Yaya yin shiru don naga bakinsa na motsi da
alama dai shima baiji k’amshin ba, nikuwa ga k’amshi inaji kamar ana k’ara kosantoni da shi.

“Kaima Yaya bakaji ba?,Wai Anty Sadiya da gaske kike bakiji ba?”.

Hannuwana ta riqo tana fad’in,

“Eh Meenal, inaga kawai hancinkine ya baki amma mudai bamuji komai ba”.

Kai na gyad’a,Inajin wata irin jarumta tazo min,don nasan ba kowa bane sai aikin wannan d’an
iskan,Yo d’an iska mana tinda dai ya hana rayuwata sukuni.

“Shikenan Anty bara nayi wanka”.

“Ki riqa addu’a kinji Sisy”.

Yaya ya fad’a yana min murmushi, nima murmushin na miyar masa ina fad’in,

“Insha Allah”.

Daga haka suka fice daga d’akin, bathroom na fad’a na watso ruwa

Ina fitowa daga wankan na nufi gaban Mirror na zauna,har lokacin kamshin baibar d’akin nawa
ba, cream na shiga murzama jikina don banada lokacin shafa wasu tarkace a fuskata.

“Masoyiyatah!!!”.

Naji Saukar muryar da ko a cikin bacci zan iya sheda me ita a cikin dodon kunnena,kaina na
dago da sauri karaf muka had’a ido dashi ta cikin Mirror zaune yake kan gadona yana min
murmushi,cikin shigar k’ananan kaya,sak Oga Daniel,ni banga wani bambancin dake tsakanin
su ba,hakan na nufin dai Oga Daniel ne ke rainamin hankali,Kenan tsafi yakeyi?,yana cikin
Qungiyar matsafa?,Meyasa yake bibiyata?,Ko nima tsafin zaiyi dani?,na shiga jeroma kaina
tambayoyi.

Rintse idona nayi tare da bud’e su na saukesu akansa,jikinane ya fara rawa kamar mazari don
iya tsorata nayi ta ba kad’an ba.

Addu’oi na fara jerowa a zuciya ta,sai naji wata nutsuwa ta ziyarceni,tsoron da ya mamaye
zuciya ta ya gushe,cikin dakiya da kawar da duk wata hanyar da zata nuna tsoron sa nace;

“Me kazo yi a d’akina?”.

“Ziyara na kawo Masoyiyata abar qaunata”.

Ya fad’a idonsa a kaina,da sauri na juyo domin qara tabbatar da kodai gizo ne yake min,
Mutumen da ko zo in kasheka da Hausa bai saniba?,saidai banga koda alamar mutum akan
gadon nawa ba,sake jiyowa nayi akan madubin still yana zaune inda yake.

“Kidena jin tsorona, bazan tab’a cutar dake ba saboda ke abar sona ce”.

A mugun fusace kamar me shirin dambacewa na mik’e tsaye ina juyowa saitin gadon nace;

“Wallahi qarya kake, da kana sona da baka rik’a takurawa rayuwata ba,mugu azzalumi,Yau
Asirinka ya tonu kana cikin qungiyar matsafa to wallahi Daniel nafi k’arfin ka, Arnen banza
k’azami d’an iska,Sai na toni asirinka mushiriki kawai maras tsoron Allah”.

Sautin dariyarsa kawai nakeji amma bana ganin sa,Tinanin na farayi meyasa wannan mutumen
zai takurawa rayuwa ta ne,’yar baiwar Allah dani mai na tare masa a duniyar nan,Tabbas dole
na k’ara damara wurin ganin na kwato ‘yancin kaina, in kuma d’au fansar zaluncin da yayimin,
saina zame masa masifa a rayuwarsa.
“Na barki lafiya masoyiyata”.

Najiyo Muryarsa yana fad’a,Mirror nayi saurin kallo sai naga wayam, wata nannauyar ajiyar

zuciya na sauke ina dafe kaina a hankali na furta,

“Ya Allah gani gareka, kayimin katangar k’arfe da wannan azzalumin”.

Jiki a sanyaye na shiga sanya kaya a jikina, agogo na kalla naga lokaci ya tafi kuma nasan Anty
Sadiya nachan na jirana,duk abinda nake buqata na d’auka don bana marmarin dawowa
d’akin,sannan na fice zuwa pallor.


Anty Sadiya kawai na hango a dainy Bak’ir na kan cinyarta, alamar Yaya har ya fita aiki da sauri
ta d’ago tana kallona tace;

“Me ya tsayar dake Meenal,sai jiran ki nake tin d’azun”.

Murmushi nayi mata nace;

“Bakomai Anty”.

Na k’arashe maganar ina zama gefenta, a gurguje muka gama yin break d’in duk da nidai ba
dad’in abincin nakeji ba,saida muka biya Inda Anty kekai Bak’ir sannan muka wuce wurin aiki
lokacin har 8:00 ta buge.

Koda muka isa kowa office d’insa ya nufa, banbi ta kansa ba duk da banada tabbacin yazo ko
bai zoba,na cigaba da ayukkan da ban k’arasa ba.


Sai 9:30 Sir Daniel ya shigo ma’aikatar,fuskarsa a sake bayada burin da ya wuce ya d’ora
idonsa a kan k’yakkyawar fuskarta ta.

Koda ya shiga Office d’insa baiga alamar shigowar ta office d’in ba, kan kujerar sa ya zauna
yana k’allon saitin qofa ko zata shigo amma shiru,tinanin meya faru a jiya bayan yabar
ma’aikatar ya fara,waya sallami ma’aikata?,Itace ko kuwa Pa sa?.








*#Comments*
*#Share*
*#Vote and like*

~Mrsbalarabe✍️~




*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._

*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8




*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_23-24_


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*



*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.


```WANNAN PAGE KYAUTACE TA MUSAMMAN GA DUKKANIN MASOYA LITTAFIN K’AUNAR
B’OYE,INA GODIYA SOSAI A GAREKU DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN
LITTAFI NAWA,ALLAH YABAR K’AUNAR�ALKHAIRIN ALLAH YA ISKEKU A DUK INDA
KUKE MASOYAN AMANAMRSBALARABE NA GODIYA DA JINJINA A GAREKU```





Yana cikin wannan tinanin ne yaji ana neman izinin shigowa office d’in nasa,baisan lokacin da
ya saki wani k’ayataccen murmushi ba don yasan itace ba wani ba,mayun idanunsa ya zubama
k’ofar na ‘yan wasu seconds sannan yace;

“Come In”.

Yana gama fad’in haka yayi juyi akan kujerar sa fuskarsa d’auke da murmushi.

Pa ce ta shigo cikin wata irin arniyar shiga,matsatsun riga da wandone sanye a jikinta,fuskar
nan tata anci uban makeup ga wani katafaren glass da tasa,kanta yasha kitson attach har
gadon bayanta,burinta kawai Sir Daniel ya juyo ya kalleta don tasan dolene sai ya k’yasa.

Fuskarta d’auke da wani shu’umin murmushi tace;


“Good Morning Sir”.


Muryar Pa ta d’aki dodon kunnensa,wani irin bacin rai ya ziyarce shi nan take,a mugun hasale
ya jiyo yana kallon ta baima tsaya tantance shigar dake jikinta ba yace;

“Hey who permits you to come in?”.

Jikinta na rawa ganin yanda yake kallonta ranshi b’ace tace;

“Am..ehm Sir You ar...”.

“Get out of my office!!!”.


Ya daka mata wata razanannar tsawa,wadda tasa hanjin cikinta hautsinewa,da sauri ta bud’e
k’ofar ta fice daga Office d’in ta nufi nata office d’in.

Nidai naga Pa ta fito daga office d’insa da sauri saidai ban tsaya lura da yanayin ta ba don kuwa
bata isheni kallo ba,nayi shigewata office d’ina don a lokacin na dawo daga office d’in Anty
Sadiya ne.


Pa na shiga office d’inta ta rik’e qugunta tana fad’in,

“Jesus christ!!!,What’s wrong with him?,did i do something wrong to him?,No i didn’t,Sir Daniel
he’s never do this to me”.

Zama tayi kan kujera tana fad’in,

“I will find out what caused this to me”.

Sir Daniel kuwa yana ganin Pa ta fita ya mik’e ransa a mugun b’ace,yafara zagaye tsakiyar
Office d’insa,

“What she’s mean?,Tana nufin bazata shigo office d’insa ba ya ganta ko zai samu sassauci a
cikin zuciyarsa”.

Turo K’ofar da akayine ya sanyashi d’ago kansa da sauri yana kallon wane isasshene ze shigo
masa Office babu izininsa,Karaf idanunsu ya sark’e a cikin na juna,lumshe idanunsa yayi ya
sake b’ud’esu a kanta yana cigaba da kallonta.

Nikuwa murmushi na sakarmasa a raina nace;

“Munafuki,zakaci ubankane”.

A zahiri kuwa cewa nayi,

“Good Morning Sir”.

Har lokacin ina tsaye a bakin k’ofar Office d’in kuma ban rufo k’ofar ba don nasan ba qaramin
aikinsa bane yace na fita.

“Come in”.

Ya fad’a tare da komawa kujerar sa ya zauna yana cigaba da kallon Meenal dake k’ok’arin rufe
k’ofar.


Bayan na rufe k’ofar na juyo cikin wani irin taku mai jan hankali nake tafowa wurinshi,file d’in
dake hannuna na ajiye mishi a kan table d’insa, cikin wata fitinanniyar murya nace;

“Ina buqatar sa hannunka Sir”.

“Okey, have a seat”.

Ya fad’a yana nunamin kujerar dake ajiye tana kallon table d’in nashi tare da janyo files d’in
zuwa gaban shi ya bud’e.

Ba musu na ja kujerar na zauna,duk da kuwa nayi mamakin hakan,naci gaba da kallon shi,wani
tinani nayi a raina tare da sakin wani murmushi ina kara wayata a kunne nace;

“Hey darling I miss you”.

Da mugun sauri naga Sir Daniel ya d’ago yana kallo na,nikuwa na maze na cigaba da fad’in,

“I love you too,i can’t imagine life without you..”.

“What the hell you are doing here?”.

Sir Daniel ya fad’a a mugun fusace yana buga table d’in dake gabansa.

Da sauri na cire wayar daga kunnena ina kallon sa,ina k’ok’arin gimtse dariyar dake son
kub’uce min nace;

“I’m sorry sir”.

“Shut up!,and leave my office”.

“But Sir wh..”.

“Out!!”.

Ya katse ni da wata irin tsawa.

Miqewa nayi na nufi k’ofa har na d’ora hannu kan handle d’in k’ofar naji yace;

“Come back”.

D’an murmushi nayi sannan na juyo nadawo gabansa nayi tsaye, kallo d’aya yayimin ya d’auke
kansa yana fad’in,

“Seat”.

Ba tare da na kalleshi ba na zauna,ina mamakin murd’ad’en halin wannan mutumen.

Tsawon 5 minutes ya d’auka yana singing d’in sannan ya turo min su gabana ba tare da ya kalle
ni ba.

Nikuwa da sauri na d’au files d’in ina k’ok’arin miqewa yace;

“Excuse me”.

Kallon sa nayi, ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login