Showing 36001 words to 39000 words out of 42034 words
Chapter 13 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf
_31-32_
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.
Cikin sanyin jiki na fito daga Toilet d’in ina kallon Anty Sadiya da wasu nurses dake tsaye suna
kallona wanda nake tinanin kallon mamaki ne,basarwa nayi Ina gyara d’aurin Towel
d’ina,murmushi Anty Sadiya ta sakar min tana fad’in,
“Meenal kin fito?”.
Zama nayi a kusa da ita sannan nace;
“Eh Anty”.
Daga haka ban sake cewa komai ba,akwai abinda nake son tinawa a raina amma na kasa.
Cikin halshen turanci Nurses d’in suka ce min,
“Sannun ki,Ya kike jin jikin naki yanzu?”.
Kallon su nayi sannan na kalli kaina,sai chan nace;
“Lafiya”.
Ficewa sukayi daga Office d’in inda na samu damar sanya kayan da Anty Sadiya ta mik’omin.
“Karfe nawa?”.
Na tambaya don inaso in gabatar da Sallah,wayarta ta duba tana fad’in,
“K’arfe biyu da rabi,zakiyi sallah ne”.
“Eh”.
Hijab ta d’aukomin tare da shimfid’amin darduma,ba b’ata lokaci na fara gabatar da
Sallar,bayan na sallame ne ta zubomin Abinci tana fad’in,
“Ki samu kici ko kad’an ne”.
D’an guntun murmushi na saki,don kuwa ni yanzu bata abinci nake ba,ina da muradin komawa
gida,don a yanzu banida burin da ya wuce in ganni a garin Kano kusa da Mama nah,farin cikin
rayuwata.
Anty Sadiya na k’ok’arin magana aka turo k’ofar d’akin,dukan mu daga kai mukayi muna kallon
k’ofar Yaya ne hannunsa d’auke da Bak’ir,tsantsar farin cikine bayyane a fuskarsa har ya iso
inda muke.
“Meenal!,ya jikin ki,fatan kin samu sauk’i sosai?”.
Rungume Bak’ir da yayo kaina nayi ina murmushi cike da Qaunar wannan ahalin nace;
“Alhamdulillah Yaya”.
Murmushi yayi yace;
“Masha Allah,Gaskiya tsiwa baby rashin lafiyar nan taki ta tayar muna da hankali sosai,dubi
yanda Sweetheart duk tabi ta rame kamar itace mara lafiyar”.
Turo baki nayi,ina b’alla mishi harara nace;
“Kanka akeji wallahi,ni nan da kake ganina bar muku garin ma zanyi don bazan k’ara koda
kwana biyu ba a garin nan”.
Nan take naga fuskokin su sun sauya cikin mamaki Anty Sadiya tace;
“Kamar ya?,Ban fahimceki ba Meenal”.
“Ina nufin jibi zan koma gida,saboda ina kewar Mama da yawa”.
“Haba Meenal,ai inace mun riga da mun kai k’arshen wannan maganar tunda nace miki tare
zamu tafi kamin Sallah”.
Anty Sadiya ta fad’a fuskarta d’auke da damuwa,kawar da kai nayi daga gareta don banajin zan
iya fasa tafiyar nan,akan me?,akan wane dalili za’a wani bi a rik’eka garin arna?,akan me zasu
hanani tafiyata,gaskiya nikam jibi sai Kanon dabo,duk a raina nake wannan zance.
“Zaifi kam kibari kuje tare,inada tabbacin Mama zatayi farin ciki da hakan”.
Cewar Yaya yana kallona,cike da ba matarsa goyon baya,shiru nayi ina nazari a raina,daidai
lokacin Dr ya shigo tare da Nurses d’in da suka fita.
Tun kafin ya k’araso garemu yake min murmushi nikuwa na wani had’e rai don bansan me
murmushin nashi ke nufi ba.
“My Patient ya jikin naki?,Akwai wani wurin da ke miki ciwo?”.
“Naji sauk’i”.
Na fad’a ina hararar shi k’asa-k’asa,bai k’ara cewa komai ba ya fara aunani domin k’ara
tabbatar da lafiyata,murmushi yayi ganin yanzu kam komai lafiya,nan ya shiga rubuce-rubucen
sa bayan ya kammala ya mik’ama Yaya takardar Sallama,bayansa Yaya yabi suka fice daga
d’akin.
Wani sanyi naji a raina don duk takure nake zaune a Asibitin,Mik’ewa Anty Sadiya tayi ta fara
harhad’a kayan mu,Yaya yazo ya kwasa ya kai mota,cikin d’an k’ank’anin lokaci muka gama
komai,Yaya yajamu muka koma gida,dukan mu a pallor muka yad’a zango muna fira jefi-jefi
daga bisani Yaya ya fice daga gidan ya barmu.
Hannayena Anty Sadiya ta kama tana fad’in,
“Ina son in tambaye ki Meenal”.
“To ina jinki Anty”.
Na fad’a ina murmushi.
“Wai menene ya faru dake ranar a ma’aikata?”.
Dummm naji k’irjina ya buga,a mugun tsorace na kalleta, take naji abubuwan da suka faru a
baya suna dawomin a kai,wani shahararren tsoro naji ya mamaye zuciya ta.
“Kinyi Shiru Meenal”.
Mik’ewa nayi da sauri ina girgiza mata mai,da gudu na nufi hanyar d’akina,ina isa na fad’a kan
gadon ina dafe saitin zuciyata da nake jin yana bada dam!dam!!.
Cike da dana sanin wannan tambayar Anty Sadiya ta nufi d’akin ta tana ji inda ma bata tambayi
Meenal ba,yanzu shikenan idan wani abu ya faru da ita kuma?,duk ita ce taja,fashewa tayi da
kukan tausayin Qanwar tata.
Sai k’arfe Shidda Na falka daga b’arawon baccin da ya saceni,da sauri naje nayo alwala nayi
sallar la’asar,bayan na kammala na d’auko Al-Qur’ani na fara karanto suratul Kahfi,Ina gaf da
kammalawa Anty Sadiya ta shigo d’akin zama tayi akan gado har saida na kammala karatun
sannan na juyo ina kallonta fuskata d’auke da murmushi nace;
“Ina yini Aunty”.
“Lafiya Lau,Meenal”.
“Ya kike?”.
“Alhamdulillah”.
“Masha Allah,ki taso muje ga Abinci can muci”.
“To Anty nah,muje muci”.
Na fad’a ina mik’ewa duk da banso hakan ba,saidai nayi ne don kawai faranta ranta,kan dainy
muka isa inda ta zuzzuba muna abincin muka fara ci,sosai abincin yayimin dad’i inaci ina santi
sai dariya ta Anty Sadiya keyi,bayan mun kammala cin abincin muka koma pallor muna kallo
tare da fira jefi-jefi,sosai na saki jikina don fitar da su daga cikin yanayin damuwar da suke,da
dare Yaya ma da ya dawo mukaita kaftawa dashi, sai firar da dariyar mu mukeyi cike da Qaunar
junan mu.
*Washe Gari*
Cikin shirin zuwa aiki Anty Sadiya ta shigo d’akina,inda ta sameni zaune inata karatun
Al-Qur’ani na don yanzu shine ya zamar min maganin damuwata,saida na kai aya,na ajiye ina
mik’ewa nace;
“Anty har kin shirya?,gashi ni ko wanka banyi ba”.
Zaro ido tayi tace;
“Idan da kinyi wankan ina zakije?”.
Cike da rashin tunanin komai nace;
“Wurin Aiki manah”.
“Hmmm Meenal kenan,ai Boss ya baki hutun aiki har sai kin murmuje sannan zaki koma,nima
naji dad’in hakan”.
“To shikenan a dawo lafiya”.
“Yawwa Meenally tah,to kizo muje muyi break ko”.
“A’ah Anty,je kiyi abinki ni sai anjima zanyi”.
Ficewa tayi daga d’akin inda nikuma na cigaba da Karatun da nakeyi inajin wata nutsuwa na
wanzuwa a cikin zuciyata tare da wani nishad’i wanda na dad’e banji irinsa ba.
_Sharhi mai tsayi shine ze bani k’warin gwuiwar antayo muku typing ba tare da na gaji ba_
*#Vote*
*#Comments and like*
~mrsbalarabe✍️~
*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_
*Fatima Batula✍*
_Wattpad:mrsbalarabe._
*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8
*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_
_33-34_
*Wannan page nakune K’AUNAR B’OYE FANS GROUP da kuma FATIMA BATULA PALACE.
Mrs balarabe na godiya sosai da nuna soyayya ga littafina na K’aunar b’oye,Ina alfahri daku a
koda yaushe,son so fisabilillah♥️*
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.
<><><><><><><><><><><><><>
A b’angaren Sir Daniel ana sallamar su Meenal,Likitan ya buga masa waya ya sanar dashi,yaji
dad’i sosai da samun lafiyarta,don sosai yake missing d’inta,beda burin da ya wuce ta dawo
office ya d’ora idanuwansa akan kyakkyawar fuskarta.
Yau da wuri Anty Sadiya ta dawo daga wurin aiki,nidai ban tambayeta daliliba duk da nasan bai
rasa nasaba da rashin lafiyata,A tare mukayi girkin rana duk da tayi qoqarin hanani amma nak’i
hanuwa dole ta barni muka gama tare,wanka naje na sake yi na sanya wata Arabian gown
bak’a wacce tayi mugun amsar jikina,kallon kaina nayi a mirror duk na rame nayi k’assa kamar
ba niba saida nayi sallar la’asar sannan na wuce pallor,Ina fitowa Anty Sadiya ta hau kod’ani
akan nayi kyau sosai,nidai murmushi kawai nayi mata na baje kan Capet inda ta baje muna
abinci,muna cin Abincin muna fira,wayar Anty Sadiya ce tayi k’ara ta d’aga,banji mai aka
cemata ba naga dai tayi murmushi tana fad’in,
“Okay Sai kunzo”.
Tana katse wayar ta kalleni tace;
“Anty Rabi’a ce da Khalid ke tafe”.
Sosai naji gabana ya fad’i ambatar sunan Khalid da tayi don ni harna manta da wani Khalid,d’an
guntun murmushi nayi mata nace;
“Allah ya kawo su lafiya”.
Daga haka muka cigaba da cin abincin,tsawon 20 minutes mukaji ana k’wank’wasa
k’ofa,Mik’ewa nayi naje na bud’e,Anty Rabi’a ce ta fara shigowa tana ganina ta saki murmushi
tana fad’in,
“Masha Allah,Meenal Kam jiki yayi sauk’i,Ya k’arfin jikin naki?”.
Nima ina murmushi nace;
“Alhamdulill....”.
Na kasa k’arashe zancen sakamakon sark’ewa da idanuwan mu sukayi wuri d’aya,inda ya
kafeni da rikitattun idanunsa kamar wani tsohon maye,da sauri na janye idona,na matsa gefe
don basu hanyar shigowa,saida suka wuce nasamu damar rufe k’ofar na biyo bayan su,inajin
kamar in shigewata d’aki saidai nasan Anty Sadiya zata tuhumeni akan hakan.
Gaisawa suka shiga yi da Anty Sadiya inda Anty Rabi’a ke k’ara tambayar k’arfin jikina,naji
dad’in hakan a raina saboda matar ta nunamin k’auna,Anty Sadiya ce ta kalli Khalid tace;
“Bakazo ganin Meenal a hospital ba”.
D’an Sosa kai yayi yace;
“Wallahi Anty naje kotono sai jiya na dawo,Shine Anty take fad’amin Meenal batada lafiya”.
Ya k’arashe maganar yana kallon inda nake zaune yace;
“Meenal Ya jikin?”.
Ba tare da na kalleshi ba nace;
“Naji Sauqi Alhmdlh”.
Fuskarsa d’auke da murmushi yace;
“Masha Allah,Allah ya k’ara sauki”.
Dukan mu muka amsa da Ameen, nan su Anty Sadiya suka shiga duniyar su wacce a koda
yaushe basa gajiya da fira kala-kala,nikuwa duk na tsargu da kallon da Khalid kemin wanda har
kallon ya fara zama na wulak’anci,wulak’anci manah,to miye mutum zai rik’a kallon ka tun daga
k’asa har zuwa sama sannan ya d’auko daga saman zuwa k’asa?,hak’urina ne ya k’are na
mik’e da sauri zan bar wurin Anty Sadiya tace;
“Yauwa Meenal,Please ki d’auko Musu Drinks”.
Kamar in fasa ihu naji,a dak’ile nace;
“Uhum”.
Sannan na wuce zuwa kitcheen k’afafuwana sai hard’ewa suke kamar zan fad’i,nasan ba komai
ne ya haddasa min hakan ba sai kallona da Khalid keyi wanda na rasa tantance wani irin kallo
ne yake min,plate biyu na d’auko na jera drinks d’in a ciki na kaimusu sannan nashige
d’akina,kan gado na fad’a ina nazarin wannan kallo da Khalid kemin.Bansan tafiyar su Khalid ba
sakamakon baccin da yayi awon gaba dani,saida na fito pallor kallo ne Anty Sadiya ke cemin ai
sunyi jiran in tashi bacci ban tashi ba suka wuce,murmushi kawai nayi bance komai ba.
Washe gari
Tin safe muke faman aikace-aikacen gyaran gida Dayake weekend ne Anty Sadiya bata fita
aikiba,ko ina na gidan yayi fess gwanin birgewa.bayan mun gamane muka dawo pallor muna
kallon shirin Asintado a tashar d’ad’in kowa.
“Anty akwai inda ake saloon nan kusa?”.
“A’ah,amma kibari anjima muje inda nake zuwa”.
Ta fad’a hankalinta na akan kallon da muke don Anty Sadiya na mugun son shirin Asintado.
“To shikenan,wallahi duk banajin dad’in kan nan”.
Na fad’a ina mik’ewa zuwa d’aki,don dama ni kallon ba wani damuwata yayi ba,harna kai k’ofar
d’akina bugun k’ofar da najine ya tsaidani,juyowa nayi na kalli Anty Sadiya ko zataje ta bud’e
amma naga batada alamar tashi,hakan yasani juyawa na koma wurin k’ofar na bud’e tare da
d’an lek’awa ina fad’in
“waye?”.
Yana tsaye fuskarsa d’auke da murmushi ga wasu uban manyan ledoji da ke rik’e a
hannuwanshi,manyan kayane sanye a jikin shi farar shaddar tayi mugun amsar farar fatarhi,sai
zuba k’amshi yake na fitar rai.Da sauri nayi baya ina fad’in,
“Au ashe kaine?,Sannu da zuwa”.
Murmushi ya sake min yace;
“Nine kuwa,ko na koma?”.
Dariya nayi nace;
“Inhar komawar bazatayi maka wuya ba shikenan”.
Na k’arashe maganar ina yin gaba.
“Keda waye Meenal?”.
Anty Sadiya ta tambaya tana kallo na,gefenta na zauna kafin na kai da bata amsa ya shigo
yana fad’in,
“Khalid ne Anty”.
Cikin fara’a Anty Sadiya tace;
“Sannu da zuwa”.
Bayan sun gama gaisawa ne,Anty Sadiya ta mik’e don ta d’an fahimci wani abu,bin bayanta
nayi da kallo harta shige d’akinta,me Anty ke nufine?,meyasa zata tafi ta barni?,Na shiga
tambayar kaina.
“Ya k’arfin jikin naki?”.
Na tsinkayo muryar Khalid,murmushin yak’e nayi nace;
“Nifa naji sauk’i sosai,harma na fika lafiya”.
“Taya zan iya tabbatar da hakan?”.
Ya fad’a yana d’age min gira d’aya fuskar nan tashi d’auke da murmushin dake k’ara bayyanar
da kyawunsa,haka dai muka tsinke da fira nida shi,sai labarai yake bani,sosai na tsinci kaina a
cikin nishad’i saboda na fahimci shid’in mutum ne mai son barkwanci,cikin dubara ya amshe
number wayata nikuwa ban kawo komai a raina ba.
K’arfe uku dai-dai Khalid ya mik’e yace zai wuce,hakanan kawai sai naji a raina kamar ya tsaya
mu cigaba da firar mu bansan dalili ba,nima mik’ewa nayi nace;
“To bara na kirama Anty kuyi sallama”.
“A’ah kawai ki barta,idan ta fito kyace mata na wuce”.
“Shikenan”.
Na fad’a,har ya fara tafiya ya juyo
“Bazaki rakani ba?”.
Ya fad’a yana kallon yanda nayi tsaye ina jiran fitar sa,bance komai ba nabi bayan sa,a bakin
kof’a nayi tsaye ina fad’in,
“Nagode sosai”.
“Karki damu,sai munyi waya”.
Ya fad’a yana sakemin wani murmushi mai wuyar fassarawa sannnan ya wuce,rufo k’ofar nayi
daidai lokacin Anty Sadiya ta fito d’auke da yaronta Bak’ir da ya tashi daga bacci,harara na
b’alla mata nace;
“Sannunki da tafiya ki barni”.
K’yalk’yalewa da dariya tayi tace;
“To ai naga bak’on naki ne shiyasa”.
Zaro ido nayi nace;
“Kamar ya bak’ona?,Duka yaushe na sanshi ma har zai zamo bak’ona?”.
Zama tayi tana murmushi tace;
“Nidai rabani da wannan tambayoyin naki,bara muga me aka kawo munane kayan dubiya”.
Daga haka ta janyo ledojin ta fara bud’awa,d’ayar ledar shak’e take da kayan marmari dangin
su Apple,ayaba,lemo,gwanda da dai sauran su,d’ayar ledar kuwa gasassun kajine guda biyu.
“Lallai abun nayine,wannan hidima haka”.
Anty Sadiya ta fad’a tana rik’e baki,nidai ina tsaye ina kallonta na kasa cewa komai,saboda
wani tunani da naji ya d’alsu a zuciyata,da sauri na kawar da tunanin don banason yayi
tsawo,da haka na d’auki Bak’ir ina mishi wasa.Mik’ewa Anty Sadiya tayi ta nufi kitchen ta dauko
plate,ta fasaltamuna naman muka ci.muna kammalawa ta sanya sauran a fridge tare da fruits
d’in,Saida muka gabatar da sallar la’asar sannan shirya muka fice daga gidan zuwa wurin
Saloon,bamu dawo ba sai k’arfe bakwai saboda layin da muka tarar a wurin Saloon d’in.
Da dare Ina k’ok’arin kwanciya naji wayata ta fara k’ara,bak’uwar number nagani hakan ya
tabbatar min da Khalid ne,wayar na shirin katsewa na d’aga,shid’in ne kuwa,bayan mun gama
gaisawa nanma muka d’inke da fira sai k’yalk’yala dariya nake sai kace sabon kamu,sai da
nafara jin bacci sosai mukayi sallama na katse wayar daga haka bacci ya d’aukeni.
Cikin d’an k’ank’anin lokaci mukayi mugu-mugun shak’uwa da Khalid,don kusan kullum sai
munyi waya,ko kuma yazo wurina musha fira,tuni Anty da Yaya suka halbo jirgin Khalid nikuwa
ban kawo komai a raina ba har zuwa yanzu,don ni na d’aukesa a matsayin abokin