Showing 39001 words to 42000 words out of 42034 words

Chapter 14 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf

24 Jun 2025

1945

firata na
musamman.

Zuwa Yanzu na dawo normal kamar bani bace Meenal da na rame kwanakin baya,hankalina
kwance har na manta da wata abu wai damuwa,a kullum cikin farin ciki nake,nadena jin d’uriyar
dan rainin hankalin nawa nasan hakan yana daga cikin add’u’oin da nakeyine Allah yayimin
gaba dashi.

Rayuwata nake cikin walwala musamman ma da Khalid ya shigo cikin rayuwar tawa don yana
d’ebe min kewar abubuwa da dama,aiki kuwa sam naji ya fitar mun a rai, saidai inga Anty
Sadiya na zuwa,nikuwa kullum ina gida ina hutawa,don yanzu sam bana muradin sake had’a
ido da wannan arnen don gani nake shine damuwata,nisanta kaina da nayi dashi kuma na
samu kwanciyar hankali sosai.


************************************
Sir Daniel yayi kewar Meenal sosai wanda har saida yayi ‘yar rama,yana muradin ganin Meenal
saidai gashi yau tsawon kwanaki masu yawa baiji d’uriyarta ba,duk yabi ya damu da rashin
Meenal,tinani ya shigayi a ransa kodai tabar aikin ne?,Meyasa zata bar aikin?,daga haka ya
yanke shawarar tambayar Anty Sadiya yaji miye dalilin rashin dawowar Meenal wurin aiki.





*Sharhinku shike k’aramin kaimi wurin yimuku typing a koda yaushe,nagode fans abun
alfahri*




*#Vote*
*#Comments and like*







~mrsbalarabe✍️~


*ƘAUNAR ƁOYE!!!*

_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._


*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8




*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_35-36_







✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*



*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.


___________________________
Fitowata kenan daga kitchen Anty Sadiya tace;

“Zo Meenal”.


zama nayi gefenta ina fad’in,

“Gani Anty”,

“Yawwa dama akan maganar komawa wurin aikine,naga kin share zancen”.


B’ata fuska nayi nace;


“Nifa Anty na ajiye aikinnan,wallahi ya fitarmun a rai”.

Da mugun mamaki ta kalleni.


“Kamar ya kin aje aiki Meenal?,Wace irin magana kike haka?,Meye dalilin ki na yin hakan?”.


Turo baki nayi.


“Saboda ajiye aikin shine kwanciyar hankalina,Idan har na cigaba da aiki da Daniel to nasan
bazan tab’a samun kwanciyar hankali ba”.


“Wannan ba hujja ba ce Meenal,kisani cewa Allah shine keyin komai,mutun bai isa ya miki

abunda Allah bai nufa ba,kima cire wannan a ranki”.



Hannuwan Anty Sadiya na kama.


“Ya kamata ace kin fahimceni Anty,Tinda na fara had’uwa da wancen mutumen rayuwata take
cikin matsala,a koda yaushe banida kwanciyar hankali kuma kun rasa naku,zanso ace kin
amince da wannan dalili nawa”.


Shiru Anty Sadiya tayi na wasu sakanni sannan tace;


“Shikenan tinda kin zab’i hakan”.


Tana gama fad’in haka ta mik’e tabar wurin fuskarta ba yabo ba fallasa,da kallo nabi bayanta
harta shige d’akinta,duk sai naji jikina yayi sanyi don koda Anty Sadiya bata fito ta bayyana mini
b’acin ranta a fili ba nasan ranta ne ya b’ace.


Mik’ewa nayi na koma d’akina ina jin duk babu dad’i a raina,shawara nashiga yi da zuciyata
amma sai rayamin take karna koma aikin,wani uban tagumi nayi ina tinanin meyasa zan
b’atawa Anty rai?,bayan ita kullum batada burin da ya wuce taga ta farantamin rai,Indai cigaba
da aikina zai faranta ranta to ba shakka dole nayi hak’uri na cigaba da aiki a k’ark’ashi Daniel
koda kuwa hakan shine zaiyi sanadiyar rayuwata,da wannan k’udurin na mik’e da sauri na nufi
d’akin ta,zaune na tarar da ita tayi shiru alamar tayi nisa cikin tunani sosai, dafata nayi ina
fad’in,


“Anty!”.

Da sauri ta d’ago ta kalleni,tare da sauke ajiyar zuciya tace;


“Ya akayi kuma?”.

Cike da sanyin jiki nace;


“Kiyi hak’uri Anty nasan ranki ya b’aci,Insha Allah zan cigaba da aiki indai hakan zai faranta

ranki”.



Duk da Anty Sadiya taji dad’in maganar Meenal sai bata nuna ba,sai ma kawar da kanta da tayi
gefe kamar bataji mai nake fad’a ba.

“Please Anty,Kiyi hak’uri”.

Na sake fad’a fuskata d’auke da damuwa,ba tare da ta kalleni ba tace;


“No raina bai b’aci ba,Bazan takuraki ba Meenal kinsan komai saida ra’ayi kuma kin nuna baki
ra’ayin aikin shikenan ai babu damuwa”.


Daga yanda take maganar ma ya k’ara tabbatar min da tsantsar b’acin rai take wannan
maganar,ban ankaraba sai kawai naji k’wallah sun gangaromin a kunci,durk’ushewa nayi a
gabanta ina fad’in,


“Don Allah Anty kiyi hak’uri,Nasan ranki a b’ace yake,wallahi namiki alk’awalin zan koma aiki”.


Na k’arashe maganar kuka na cin k’arfina don har wani zafi nakeji a raina wai Anty Sadiya tana
fushi dani?Ni Meenal insa kaina a ina?.


K’yalk’yalewa da dariya Anty Sadiya tayi tace;


“See you!,Miye na wani b’are baki kina min kuka sai kace wata baby girl,na zata ai ban isa
dakeba ban kai matsayin da zansaki kiyi ba”.


Da sauri na girgiza kai ina fad’in,

“A’ah wallahi Anty,kin ma wuce hakan”.


Murmushi ta sakarmin tare da rik’o hannuwana na mik’e ta sharemin hawayen dake kwance a
kuncina,sannan ta matsamin gefen ta na zauna kaina a k’asa ina wasa da yatsuna,cikin sanyin
murya tace;

“Inaso ki fahimci cewa Sir Daniel bayada niyyar cutar dake,duk da kasancewarshi ba musulmi
amma baya zalunci,ko kinsan cewa shine da kansa ya d’aukeki a jikinsa ya kaiki asibiti?,Kin
kuwa san yanda yake k’yamar musulmai amma ko kad’an bai nuna k’yama a kankiba ya kaiki
asibiti abunda yai matuk’ar bawa mutane mamaki har yanzu zancen ake a company,zaki yarda
idan nace miki jinin Sir Daniel ya gauraya da naki?”.



Sai a lokacin na d’ago na kalleta cike da tsantsar mamaki don sam ban fahimci abinda take nufi
ba,kai ta girgiza min tana fad’in,


“Tabbas jinin sa ya gauraya da naki,domin kuwa sau uku yana bada jininsa ana sanya
miki,sannan ya d’auki nauyin komai a hospital,kinga kuwa Sir Daniel ya taka muhimmiyar rawa
a cikin rayuwar ki,gode masa ya kamata kiyi ba bayyana k’iyayya a garesa ba,don haka ki
zauna kiyi tunani,Bari kiji Meenal wallahi jiya Sir Daniel da kansa ya sameni a office d’ina yake
tambayata meyasa har yanzu baki dawo aikiba?,abinda bai tab’ayi ba wato shiga office d’in
ma’aikatan shi saidai mutun ya sameshi,amma a kanki ya d’auki k’afafuwansa yakai office
d’ina,ga baki d’aya mamaki ne ya cika zuciyata daga k’arshe dai dole na masa k’arya nace kinyi
tafiya ne,da kin dawo zaki cigaba da aiki”.



“Gaskiya nayi matuk’ar mamaki Anty,amma shid’in ya kasance yanada kyakkyawar zuciya tare
da tausayi kawai fahimtarshi ce banyi ba,In Allah ya yarda zanje in gode masa tare da cigaba
da aiki a k’ark’ashin sa har zuwa lokacin da zan bar garin Lagos”.


Murmushin jin dad’i Anty Sadiya tayi tare da rungumeni tace;

“Nagode Sister,Ina matuk’ar alfahri dake a koda yaushe”.








*Kuyi manage da wannan please Insha Allahu zuwa gobe zaku ga new update*

*#Vote and like*
*#Comments and Share*







~mrsbalarabe✍️~


ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*


Marubuciyar
~Bugun Zuciyata
~Nida Malamata
~Saif ko Maleek
~Alfarma
~Okhasha Dan Malan
~Billionaire Bilkisu-Paid Story
And Now
~K’aunar B’oye(The Secret Love)



_Wattpad:mrsbalarabe._


*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8

*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_37-38_







✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*



*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.

———————————————

Fuskata d’auke da murmushi nace;

“Nima haka Anty nah ta kaina,Allah ya barmin ke”.

Anty Sadiya na dariya tace;

“Ameen Qanwata”.

Daga haka muka b’arke da fira cikin matsanancin farin ciki tare da annashuwa,a haka Yaya ya
dawo ya samemu munata firar mu,inda shima ya zauna aka cigaba da kaftawa dashi.




_Monday_


Tinda safe muka tashi,muka yi ‘yan aikace-aikacen da muka saba,yau ni na had’a muna
breakfast Kunu na dama na soya k’osai don yau da marmarinsu na tashi,daga Yaya har Anty
Sadiya sunji dad’in kunun da k’osan,don bazasu iya tuna rabon su dasu ba,ko banza Anty
Sadiya tafi karkata wurin girkin turai,sam bata fiye yin abincin mu na al’ada ba,bayan mun
kammala break d’in Yaya ya fice zuwa aiki don dama shi a shirye yake,Niko da Anty Sadiya ko
wanka bamuyi ba,muma d’akunan mu muka wuce domin yin wankan muyi shirin zuwa aiki.



Shigar wani tsadadden bulan leshi me ratsin fari nayi wanda d’inkin yayi mugun amsar jikina,sai
zuba k’amshi nake,gaban mirror naje na shafa powder tare man baki,sannan na yafa gyalena
fari a kafad’a,na zura takalmina suma farare,pallor na nufa inda na tarar da Anty Sadiya na jiran
fitowata,itama ta shirya cikin wasu riga da wando tayi rolling gyale a kanta.
Mik’ewa tayi tana murmushi.

“Masha Allah Auta,Kinyi kyau sosai”.


“Nagode Anty,Kema haka”.

Na fad’a ina d’aukar yaronta daketa min dariya,kumatunshi na lakuce nace;

“D’an albarka,gaskiya Anty yaron nan yanada hak’uri sosai wallahi,Shikenan shi kullum bakuda
lokacin shi saina aikinku,indai ya rab’eku to weekend ne”.

“Ai Bak’ir beda lak’uwa ne,jiya ma munyi magana da Dady shi yace za’a kaishi wurin

lesson,kamin dai yakai lokacin shiga school”.

“Gaskiya kam hakan ya dace,nidai gani nake ba wanda zai hanani zuwa da yarona wurin
aiki,idan kuwa akace bazan je dashi ba,saidai in bar aikin wallahi”.

K’yalk’yalewa da dariya Anty Sadiya tayi tace;

“Ai nasan zaki iya,rigimatu,nidai muje a kaishi mu wuce lokaci na tafiya”.

Ban k’ara cewa komai ba don nasan Anty Sadiya bakin rai take da aikin nan nata,amma ina
dalili yaro tun yana k’arami baisan dad’in iyayenshi ba?,to inaga ya fara zama babba?.


Wurin da take kaishi reno muka ajiyeshi sannan muka wuce Company,hakanan kawai nake jin
gabana na fad’uwa,fitowa mukayi daga motar muka nufi public elevator.


Nafi minti uku tsaye a bakin k’ofar office d’in,gabana sai fad’uwa yake,abinda ya faru ranar naji
ya dawo min sabo akai,da sauri na fara jero addu’oi a raina,dak’yar nasamu hankalina ya d’an
kwanta,nasamu natsuwa.a hankali na tura k’ofar na shiga don ganin nake idan na tsaya neman
izini zan b’ata lokacina.

Zaune yake shida wani Mutun,suna magana,fararen suit ne jikinshi da necktie ja,kayan sunyi
mugun mishi kyau,yana ganin shigowarta ya mik’e da sauri yana kallonta,irin kallon mamakin
nan,sai kuma yayi d’an murmushi tare da komawa ya zauna idon shi a kanta,ya kasa yarda wai
itace yau a office d’insa,abinda bai kawo nan kusa ba.

Kaina na miyar k’asa,saboda wani irin kwarjini naga yayimin,ina isowa inda suke ba tare da na
koma kallon shi ba nace;

“Good Morning”.

Daidai lokacin Mutumen ya mik’e ya mik’ama Sir Daniel hannu suka sake gaisawa,sannan ya
nufi hanyar fita.

“Good Morning Sir”.

Na sake fad’a,ganin bai amsa na farkon ba,nanma shiru yayimin hakan yasa nayi saurin
d’agowa na kalleshi,yana zaune ya kafeni da rikitattun idanuwanshi fuskarshi d’auke da
murmushi mai tattare da tsantsar farin ciki,baiyi zato ko tsammanin ganinta ba,wani sanyi yakeji
a cikin zuciyarshi,tabbas yayi kewarta sosai.saurin janye idanuna nayi don gabaki d’aya ya

kashemin jiki da kallon shi,dama haka yake da kyau?,na fad’a a zuci,don kuwa yau yayimin
wani mugun kyau,amma kuma naga ya rame,dama indai ba sani kayiba bazaka kirashi arne ba
domin kuwa siffar musulmai gareshi sam beda kama da arna,shi kyakkyawane,ina ruwana da
kyaunsa?,nayi saurin tambayar kaina.
“Hey,Have a seat”.

Najiyo muryarshi yana fad’a,da sauri na zauna kujerar dake kallon shi,saidai nakasa d’ago
kaina.

“Ya jikin naki?”.

Ya tambaya cikin halshen turanci,Nidai hakanan kawai na tsinci kaina da fad’in,

“Alhamdulillah”.

“Alhamdulillah”.

Ya maimaita cikin muryar shi ta inyamurai,da sauri na d’ago na sake kallon shi da mugun
mamakin yanda ya maimaita duk da nasan bai san mai nace ba,murmushi yayi min yace cikin
turanci;

“Menene Ma’anar hakan?”.

“Thanks God”.

Na fad’a,ina kallon yanda ya maida idanuwansa ya lumshe tare da bud’esu ya sauke a kaina.

“Okay,Na d’auka kin barmin aiki”.

Samun kaina nayi da murmushi,don tunda naji irin taimakon da yayimin naji haushi da tsanar
shi sun gushemin a zuciyata.


“Meyasa zan dena?”.


D’an shafa kyakkyawan sajen fuskarshi yayi yana fad’in,

“Dunno,kawai nayi zaton zaki dena ne”.

“A’ah bazan dena ba”.

“Well,naji dad’i sosai”.

Ya fad’a yana k’ara sakarmin wani k’ayataccen murmushi.

A hankali nace;

“Nagode sosai da taimakona da kayi,Naji dad’in hakan”.

“Karki damu”.

Ya fad’a,tare da janyo wasu files dake gabanshi ya turosu zuwa gabana yana fad’in,

“Ko zaki taimaka ki mik’ama Pa wannan”.

“Okay,babu damuwa”.

Na fad’a tare da mik’ewa na d’au files d’in,saida nakai bak’in k’ofar fita naji yace;

“Thanks You,Alhamdulillah You’re coming back”.

K’yalk’yalewa nayi da dariya,nace;

“Baka iya fad’a daidai ba fa,amma idan kanaso zan koyama”.

Da sauri ya girgiza kai yace;

“Yes why not?,dagaske zaki koyamin?”.

“Eh”.

Na fad’a tare da ficewa daga office d’in ina dariya,sai yanzu nake k’ara fahimtar kyawawan
halayenshi,shi mutun ne mai sauk’in kai,daidai office d’in Pa Tiny na tsaya nayi knock.

“Yes Come in”.

Najiyo muryata,maras dad’in sauraro,tura k’ofar office d’in nayi na shiga,tana zaune da wasu
figaggin kaya jikinta,shisha na rik’e a hannunta tana zuk’a,da mugun sauri ta mik’e tana
kallona,tace;

“Kin dawo kuma?”.

Tambayar ma dariya taban,irin ta gaji da ganina a company,saikace company ubanta,amma sai
nayi murmushi nace;

“Yeah,ga files nan Boss yace na kawo miki”.


Na k’arashe maganar ina aika mata da wani matsiyacin kallo sannan na fice daga office
d’in,yayinda Tiny tabi bayan Meenal da wani mugun kallon tsana,don ita duk a zaton ta Meenal
tabar aiki a ma’aikatar,ganin yanda ta dad’e bata dawo ba,Lallai ashe mayyar bata bar aikin
ba.Ta fad’a a ranta cike da takaici,don tasan shikenan ita da sake shiga wurin Sir Daniel sai
wani hali,don duk a ‘yan kwanakin nan duk ita ke aikin da Meenal keyi,da hakane take samun
ganin shi,sai gashi yanzu Meenal d’in ta kuma dawo.


Office d’ina na wuce,nayi mamaki sosai da ban tarar da aikin komai ba,sannan office d’in a
share kamar ina ciki,zama nayi kan kujerata ina jujjuyawa sanyin Ac na ratsani ta
ko’ina,idanuwana na lumshe daidai lokacin wayata ta fara ruri,a hankali na sauke idanuwana
akan Screen d’in wayar,wani murmushi nayi ganin me kiran nawa wato friend Khalid sunan da
nayi save number d’inshi kenan.


“Hey Meenal,kina gida kuwa?,inzo muje ki rakani wani wuri?”.

“A’ah wallahi,ina office kasan na koma wurin aiki yau”.

“What!?,kin koma wurin aiki shine bazaki sanar dani ba ko?,Yayi nagode”.

Yana gama fad’in haka ya katse wayar,daidaituwa nayi akan kujerar ina bin screen d’in wayar
da kallo,k’yalk’yalewa nayi da dariya nace;


“Tofah!,Irin ubana d’in nan”.

Wayar sa na gwada kira amma tana ringing yak’i d’agawa,nanma dariyar nayi ina fad’in,

“Lallaima wannan Khalid d’in,Zaka sani ne”.

Daga haka na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login