Showing 18001 words to 21000 words out of 42034 words
wulaƙantata kaci mutuncinta,kayi mata ƙazafi ka nuna mata ƙiyayya",Momyn ta faɗa
cikin jin daɗi.
Yaƙe yayi wanda ko fuskarshi bata gamsu da shi ba,balle zuciyarshi..
Fira suka shiga yi suna nan Taye ta zo,kan cinyarshi ta ɗare,sai wani shafashi take yi,ai ba
maganar kunya ga fariki.
Shi ma yana biyeta cikinta ya shafo har gurin ƙirjinta,lumshe ido yayi a duniya ba abunda suka fi
ɗaukar hankalinshi zama da nonowan macce,ita kuwa Momy washar baki kawai take yi.
Jan shi Tayen tayi suka bar gurin dan sun fara fita haiyacinsu,ɗakin suka koma romance sosai
suke yiwa juna cikin tsananin ƙwarewa take sarrafashi da abunda yafi so,haka shi ma yana
mugun nishaɗantu da soyayyar Taye me mantar da shi komai da komai ta kai shi duniyar daɗi.
Murzar juna suka yi iya iyawarsu ita kanta ta yarda da jarumtarshi har gajiya take yi ta fara
neman guduwa duk maitar ta kuwa yana bata jikin ta....
***** **** *****
Da zaxzaɓe sosai na kwana a jikina,sai gurin asuba muka samu barci ni ta Aunty Sadiya,ina jin
sallah amma na kasa tashi dan jiki na ciwo yake yimin ga wani irin ciwon kai na azabar
hawayen da nai tayi.
Ina jin Anty Sadiya ta tashi tayi sallah ta idar.
"Meenal ɗaure ki tashi na haɗa miki ruwan zafi,ki watsa sai ki fito kiyi sallah ki koma barcin".
Bata barni ba saida ta tabbatar na tashi da ƙyar sannan.
Fita tayi taje gurin mijinta suka gaisa ya rakata kicin ta ɗafa indomi da ƙwai ta suya dankalin
turawa,ɗaki ta kawomin nawa tare suka shigo harda Baƙir muka gaisa.
Ina son wannan ahalin so me lafiya ma,zan so cigaba da zama da su amma ina bazan iyaba
lagos tafi ƙarfina.
Saida suka sa naci sosai,na kuma shan magani sanan yaya yace a barni na huta.
Ban ce su tsaya ba,dan ni kaina ina buƙatar hutu ina buƙatar kaɗaici ko na samu na dawo da
tunani na da kwakwalwa ta aiki,dan tun shekaran jiya suka tsaya da aiki.
Lamo nayi na zurfafa tunani na can iyakar shekarun da na fara ajiye abubuwa a memory na.
*MEENAL MANSUR MANGA* shi ne dai asalin tunana,ban san tarihi da asalin mu ba,nidai
kawai na buɗe ido na gamu a garin kano,na kuma gan mu a cikin ƙabilar hausawa sanan kuma
cikin addinin tsira da aminci addinin musulunci,mu uku kawai na buɗe ido na gamu mama
mahaifiya masoyiya a gare mu kuma ƙawa,Mama bata magana haka muka buɗe ido muka
ganta amma muna mgnr mu ta kurame da ita,tana ma ji raɗau saidai bata mgn,ba muga wani
uba a gaban mu,kuma har yau bamu san yadda lamarin yake ba,yana raye ne ko ya mutu,waye
shi ɗan ina ne,duk wannan amsoshin bamu san su ba,ba kuma mu taɓa tambayar mama su ba.
Abu ɗaya ne dai wanda muka saka a ran mu,shi ne mu ƴaƴa ne,dan maa tana mugun son mu,a
bata aikin komai to aikin me zata yi ma bata gani,ba kuma mu san ko tun haihuwa b ne rashin
ganin.
Cikin tarbiyar islama muka ta so dan ni hafiza ce,na haddace littafin Allah kuma nasan tafsirin
kwata daga cikinshi,haka ma Aunty Sadiya zan iya cewa ma ban taɓa ganin me son addini irin
na Maama ban taɓa ba,har mamaki nake yi,kuɗi kuwa bamu san inda take samo su ba,mundai
san ta fi mu sanin meye halal meye haram shiyasa bamu damu ba,balle mu nemi ba'asi,haka
muka ta rayuwa cikin jin daɗi da ƙaunar juna bamu wani damuwa da rashin dangin da muka ga
bamu da su ba,dan Maa cikin tarbiyyar tauhidi da ihisani ta raine mu.
Lokaci yana ja muna girma yadda muke amfani da kuɗi ya ragu wanda hakan ya tabbar ta
mana da cewa kuɗin sun yi ƙasa kenan ƙuɗin da take ɗiba.
Bata da wata kalma a gare mu kullum bayan cewa,mun yarda da ita,mu kuwa mu bita da amsar
eh ke yardaddiyace Maa.
Nifa tun ƙuruciya nake jarabbiya ƴar bala'i ina da tsiwa ta fitina,ga rashin hakuri dan ban san
cewa na yafe ba,ina kayimin nayi maka shiyasa ban fiye shiga sha'anin mutane ba,duk wanda
ya taɓani ya taɓowa kanshi.
Ban iya shanye abu sam,daman Maa bata bamu damar yin ƙawaye ba,hakan yasa ba ruwan
mu tun ƴan unguwa na tsegumi har sun gaji sun daina.Ana haka Yaya ya shigo rayuwar
mu,mutumin arzƙe ne sosai ya jure kawaicin Maa har ya shiga ran mu ya zamar mana ɗan uwa
tun Maa bata so ya fara yi mana hidima har ta hakura,tundaga nan shi ya cigaba da ɗawainya
da mu har yanzun kuwa,shi masoyine na gaske duk ya jure tsagumin mutane akan mu na
cewar mu shegu ne,nidai ya zamemin yaya.
Haka fa har Aurensu shekara shidda da rabi kenan,wanda bayan bikin basu yi shekara ba suka
dawo wannan garin,na lura da Maa bata son lagos sosai amma haka nan ta haƙura,nima
zuwana wannan saida muka sha fama da magiyar da bamu taɓa yi mata ba,ta barmu muka zo
badan ta so ba. Wannan kenan taƙaitaccen tarihin rayuwata.
Juyawa nayi tare da sauke wata irin ajiyar zuciya wannnan tunanin ya dawomin da abunda na
rasa,tun zuwa na legos ya kuma haskomin wani abu,sannan kuma ya tunatar da ni ni
wacece,ya kuma kunnamin injin kai na daya mutu.
*** *** ***
Yau ma haka ya tashi yana son ganinta har wani ji yake yi kamar ya shekara,dariya ma yake ba
kanshi da kuma mamaki yaushe ya santa kwana biyu kawai amma ji yadda yake missing ɗinta
ko Taye baya jin haka,tana nan kwance ya shirya tsaff abunshi ya fito.
Bai yi niyyar zuwa gurin Momynshi ba dan yasan zata hanashi zuwa ne,shiyasa ya waske sai
cin karo suka yi a falo.
"Dany!ina kuma zaka ne?muje ka cire kaya yau ba zuwa office",cikin nuna kulawa tayi maganar.
Shi daman abunda yake gudu kenan,kafin ya ƙwaƙwulo ƙaryar d zai gayamata yaji ta ja
shi,"Muje ba inda zaka wai yaushe ka fara son aiki haka da nasan baka son aiki ko kaɗan sai
sa'a".
"ina son ganin wa...shiru yayi jin abunda ya faɗa wanda shi kanshi jin maganar kawai yayi ta
fito.
Tsayawa tayi,"Wa zaka gani?"
"Eh Momy akwai su costomer ne sun sha zuwa basu samu na".
"To meye amfanin ma'aikatan?"
"Ehm ..amm eh suna nan amma nayi musu alƙawari ne zamu haɗu da su ne".
"Ina sakatariya ta sanar da su baka da lafiya ko a soke meeting ɗin sai nextweek"...
Shiru yayi tunanin yadda zai ɓuluwa Momy ta barshi ya fita ,yana son ganinta har wani ji yake
kamar shikenan bazai ƙara ganinta ba.....
*#Comment*
*#Share*
*#Vote and like*
*Please*
~Mrsbalarabe✍️~
*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_
*Fatima Batula✍*
_Wattpad:mrsbalarabe._
*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_
_15-16_
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.
_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_
Kan ya ankare sai ganinsu yayi a ɗakin Momyn,"kin yarda da ɗakin ki?" . Ya faɗa yana kallon
cikin idanunta cikin tare da tattara dukkan tsanuwarshi a kanta.
Idonta cikin nashi ta ce,"na yarda da kai".
"To ki bari na fita zan dawo da guri abunda zanyi yana da muhammanci sosai".
Tana son naxartar wani abu daga cikin kalaman nashi tasan waye ɗanta kuma a sanin da tayi
mishi sam bai ɗauki aikin shi da wannan muhammancin ba,kuma ta hango wani baƙon lamari a
cikin idonshi naashi, wani abu ne me matuƙar muhammanci haka?.Katse mata gundun tunanin
da ta faɗa yayi,"Yana da muhimmanci ",shi kanshi zuciyarshi yaji tana janshi ga hakan. Ɗaga mishi kai kawai tare tayi tare da faɗin,"Take care".
Kiss ya manna mata a goshi sannan ya fita yana sauri kamar wanda zashi bangon duniya.
Binshi kawai tayi da ido,ta kuma kasa yin tunanin komai.
****** **** *****
Ko da Aunty Sadiya ta isa office ɗin jiki a mace,gashi taji labarin har motor ta begeshi fitan da
yayi,jikinta ya ƙara sanyi ,takardar barin aiki ta rubutu ta zauna tana da kallon takarda wani irin
ƙunci take ji dan tana son aikinta bata shirya barinshi ba,amma kuma duk duniya bata da wani
abu me muhimmanci sama da Meenal,dole zata yi domin Meenala, wannan tunanin da tayi
yasa ta tashi cikin ƙarfafawa kanta gwiwa akan abunda zata yi shi ne daidai,office ɗinshi ta
nufa,daman ta san bai iso ba,hakan yasa ta shiga kai tsaye ta ajiyesu inda yana zuwa zaiyi
tuzali da su ta fita,bata tsaya tabi takan kowa ba ta fito abunta taja motor,tana fita motorshi na
shigowa,saida ya kalli motor duk da dai bai shaidi waye me itan ba.
Yana zuwa ya fito ya hau saman left ɗin wanda zai kai shi babban gurin ma'aikatan inda a nan
office ɗinshi yake.
Ba ƙaramin mamaki mutane suka sha ba,gashi kuma sunga bandge a kanshi,abun ya basu
mamaki haka nan ma dan hudu yaƙi zuwa office sai gashi abun ƙin zuwan ma ya kama ya zo,su
dai na su kallo.
Suna gaidashi bai ko san suna yiba,daman kullum aikinsu kenan su gaida shi,shi kuma yayi
banza da su,ba kowa ne ma ya taɓa jin maganarshi bs tsabar rashin son yin magana.
Yana isa office ɗin yaje ya zauna abunda ya faru jiya ya soma bijero mishi,"i wnt to see her,"ya
furta can ƙasan maƙogaro,tare da kai dubanshi kan tebur ɗin,tozali yayi da dakardun inda ya
gane cewa na barin aiki ne,bai wani damu daya duba ya gani ba,dan basu ne a gabanshi
ba,duk da cewa yana wuya mutum ya ajiye aiki da kanshi. Computer ya buɗe camarar tsaro ya shiga,wacce ke ɗaukar komai na office ɗin shi da ma
sauran opisoshin.ganinta yayi ta shigo office ɗin nashi,ta ajiye takardun,cikin sauri ya janyo su
ya fara dubawa,bai ma san lokacin daya miƙe tsaye ba,saidai ganinshi a tsayen yayi.
"Wht?
Ya faɗa da ɗan ƙarfe,sun ajiye aiki kenan shikenan,bai gaji da ganinta ba yana son
kasancewarshi a tare da ita.
Komawa yayi ya zauna cibir,tare da ɗan runtse ido,duk abunda suka yi mishi bai kore su ba,sai
su ne zasu ajiye aiki da kan su,wyar tafi d gidanka ya yanjo kai tsaye office ɗin PA,yana ɗauƙo
ya kira ta zo bai jira ta bakinta ba ya katse wayar.
Ko da Aunty Sadiya ta koma gida ina zaune a falo na rangaɗa wanka ne hankali kwance rai
fess.
"Kin dawo ya hanya",na faɗa hankali kwance domin na dawo Meenal ɗita.
"Zauna kinga muyi kallo the evil eye suke yi,film ɗin mu".
Zama tayi ita ma ba tare da ce da ni komai ba,ajiyar zuciya ta sauke kamar zata ce da ni wani
abun dan har na juyo naji.
"kawomin ruwa me sanyi da abun taɓawa ko cake ne,yau ina so mu fita".
To kawai nace na tashi ita ma tashin tayi tayi ɗakinta ta canja kaya ko kan na dawo har ta
canja,murmushi nayi har raina ganin aunty Sadiya cikin shigar riga da siket na atamfa kayan
gida yau an tuna gida kenan.
Zama nayi bayan na miƙa mata,"Wai daman kina da atamfa a kayanki".
Dariya ta ɗan yi kaɗan ita kanta sai ta tsinci kanta cikin jin daɗi da farinciki.
"Har kamfala da shadda duk ina da su".
"Au shi ne baki sakawa".
A madadin ta bi zance na sai ta yanke da faɗin,"Meenal yau zamu gurin Yayar Abban Baƙir" .
Tana kai aya ta shiga kiran wata number wacce nake ganin kamar ta wacce tayi mgnr akan ta
ne.
Ringin biyu ta ɗauka.
"Baban Baƙir kenan yau an tuna da mu?" daga can ɓarin ta ce haka.
"A'a ba haka ba ne Aunty Rabi'a,kin san abubuwan ne sai a hankali bamu samun time sai
sunday,ita kadaice ranar da muke samu,amma yanzun komai ya daidaita ina nan zuwa ma ni da
ƙanwata Meenal",takai maganar tana kallo na.
"Kai amma naji daɗi to shikenan sai kun zon".
" yauwa mun gode sai mun zo",ta katse wayar.
"Tashi ki shirya muje,"ta faɗa tana kallo na.
Nima kallonta nayi na kasa fahimtar yanayin da take ciki,dan nasan tunda naga ta dawo ta ajiye
aikin ne.
To kawai na iya ce mata na tashi nabar falon mayafi kawai zan yafa dan a shirye nake,ina
fituwa itama ta fito yafe da babban gyale.
Murmushi nayi,"Kinyi kyau maman Baƙir.
Dariya ita ma tayi ita fuska ta ce,"ke ma haka antyn baƙir muje.
Tana rufe baki kira na shigowa wayarta,banga wanda ya kiran ba,amma naga duk tayi sanyi.
Saƙale tayi tana saurarar abunda ake ce mata wanda jinsu ya sauya mata yanayi.
Har na kagara ta gama naji ko meye.
Ana katse wayar ta zauna kan kujerar jiki a sanyaye.
"Lafiya anty?waye?meye ya faru? Ajere nai ta yi mata tambayoyin.
"Shi ne! ta furta a takaice
Tsaye na tashi daga tsugunnen da nake.
Bana mukatar ƙarin bayani da zasu tabbatar min da wanda take nufi.
Wanan mutumin na rantse da sarkin daya busa min lumfashi sai na saka rayuwarshi cikin
kwalekwale,zai na saka yayi hawaye sai na saka yayi kukan da ba sauti sai na hanashi rintsawa
sai na ɓata mishi lissafi sai na tsoratar da rayuwarshi kamar yadda ya jefani cikin tsoro,duk da
hakan ma nasan bazan huce va. Cikin dakewa nace ,"Muje!na faɗa ba tare da na kalli inda take ba,nasan daman dole abu ɗaya
zai faru cikin biyu,idan har shi ne ki maƙaryacin aljani dole bazai bari mubar aiki ba,domin ai bai
cin ma burinshi akai na ba.
"Je ki maida kayan aikin,bari nima na canja,"ina faɗa na juya.
Sagaga anty Sadiyar tayi,ya akai tasan akan ƙin amincewarshi ga barin aikin sukai
maganar??meye kuma nufinta da su shirya su je?ta amince zata cigaba da aiki a ƙarƙashin ne
ko kuwa?.
Tana nan zaune har naje na dawo,tsaye anty sadiya ta miƙe baki a sake tundaga sama har
kasa ta tsaya kallo na.
Cikin baƙar riga duguwa iya gwiwa da pinki ɗin wandoa,sai rolling ɗin kai na da nayi da pink ɗin
mayafi,na rufe idanuwana da bakin glass ga dugun bakin takalmi da na saka.
Ban tsaya jiran ta gama yimin kallon mamaki ba,nai gaba abu na,"Ina jiranki kiyi sauri pls",na
faɗa cikin wata irin murya wacce ke nuni da ina sauri.
Me hakan ke nufi?ta shiryawa aikin kenan ta shiryawa zama a ƙarƙashin shi kenan ko me?Anty
sadiya ke jerowa kanta waɗan nan tambayoyin.
Ni kuwa da tuni har na shege motor abuna,a shirye nake?waye shi da bazan fuskance shi
ba?dole zamu fuskanci juna gaba da gaba domin sanin manufofin juna,dole zan ɗau fansar
fitsarin da yasa nayi dole zan rama marukan da yai ta min,dole na rama disgen da yayi min,dole
na tsorata shi,wannan shi ne ƙalubali na akanshi,i will take my revegen. Nida zuciyata muke wannan zancen,ganin shiru yasa na yi hon da ƙarfi wanda nasan zata jiyo.
Ita kuma da ta faɗa duniyar tunani jin hon ɗina yasa ta dawo daga inda taje.
Ɗaki ta koma a gurguje ta shirya cikin kayan aikin ta fito,a gaban motor ta zame ni,bata ce min
komai ba taja motor muka bar gidan.
Tuƙin kawai take yi amma hankalinta baya tare da ita,"wani irin abu ne haka,taya zai ce ba zasu
ajiye aiki ba,sannan kuma harda barazanar faɗa musu suna yadda kenan ba zasu taɓa samun
wani aikin ba,tsabar mugunta anya bashi da wata manufa kuwa akn Meenal,"takai ƙarshe mgnr
tana sauke dubanta a gare ni. Murmushi nayi mai aminci na ce,"Yadai ?"
Girziza min kai kawai tayi,ban damu ba duk da nasan cewa da wani abun a ranta,cigaba da
latsa wayata nayi hankali kwance.
Kafin cikar minti sha biyar mun isa cikin kamfanin,ni na fara fitowa ban ma wani tsaya jiranta ba
nai gaba abu na,cikin natsuwa da ƙasaita nake tafiyata.
Ita kuwa Anty Sadee binta kawai take yi da kallo,yadda take ƙwonbo kamar wacce ta shekera
tana aikin.
Mutane sai faman bin mu da kallo suke yi,ni kuwa tsaɓanin yadda na saba, naji duk na tsargu
ina ɗariɗari, amma yanzun kuwa ko a jiki na,banda ma ji nayi kamar zuga ni suke yi,suna
ƙaramin ƙarfin gwiwa,hakan yasa ma na ƙara wani larkewa ina zuba isa da ƙasaita kamar wata
matar me kamfanin,ni na fara kunna kai banyi wani abu wai knocking ba. Jin an buɗe kofa kai tsaye yasa ya ɗago da sauri,idanuwanshi suka harɗe cikin