Showing 12001 words to 15000 words out of 42034 words
asiri ya tuno yau kowa ya ganshi,juyowa nayi domin na kuma kallonshi naga yana nan
ko yabi iska ya gudu.Tasss kake ji.
Tagaga naji tare da jin wani irin shuuuu cikin kunnuwana,wani irin wawan mari yabi kyakyawar
fuskarta da shi,ba wanda bai ji marin ba jin yadda sautin ya fita da ƙarfi gashi murjajjen
namiji.Aunty Sadiya kuwa da tana saka ƙafa yana sauke marin taji wani irin raɗaɗin zafi ya saki
ta runtse ido tayi. Ni kuwa da faɗar azabar zafin marin daya kwasamin ɓata lokaci ne ma domin ɓoyaƴƴen abu
ake baiyanawa baiyanne kuwa ba ta yadda za'a baiyana shi,kowa yaga irin yadda na tafi tagaga
zan faɗi har russunawa nayi amman ban kai ƙasa ba tsabar azaba harda jiri naji ya ɗibeni yuuu
gashi marin ta gurin kunnuwa na ya ssukemin su yasa naji shuuu xan iya cewa dodon kunne na
ya samu matsala bani ba kara jin mgna a duniya.
Kama gurin nayi ina jina wata iriii na kuma kai duba na gareshi dan son tabbatar da abunda
nake ji kamar a mafarki.
"How dare u! u rascal wacce irin banza ce ke dabba mara hankali mahaukaciya wawiyace
waya kawomin ke mahaukaciya?"yadda yake mgnr cikin ɗan ɗaga murya ya tabbatar musu
daya fusata dan sun san baya ɗaga murya haka.
Wani irin kallo yayi musu kafin cikar saƙon duk sun watse banda Aunty da take cikin
kwatankwacin halin da nake ciki.
Runtse idona nayi da tuni sun ɓalle da ambaliyan wasu irin ruwa masu azabaɓen zafi
nayi,zuciyata naji tayimin wani irin ɗaci wanda nake jinshi har maƙogaro na,jin waɗan nan
munannan kalamai wanda basu da na biyu yasa na tabbatar da cewa ban rasa ji na ba,saida
kuma yanxun kai na ya kulle kwanyata ta tsaya cik tayama zan iya ɗaukar wannan baƙon lamari
daga Meenal ina ƙaunarki ki so ni,komai naki burgeni yake yi Meenal wllh ƙaunar gaske nake yi
miki wanda ba wanda ya taɓa yimiki irin ta,sai kuma wani azabaɓɓen mari me matukar zafi
mahaukaciya,dabba,hajila wawaiya,runtse ido nayi a daidai nan a tunani na wasu irin hawayen
azaba suka kwaranyomin suna rangaji suna wanke min fuska tausayin kai na ne ya mugun
kamani.
Cikin sanyin murya da yin ƙasa da kai Aunty sadiya ta ce,"Sorry sir!
Ta jani muka bar office ɗin binta kawai nake yi,su kuwa mutane sai gulmar mu suke yi,gurin
parking muka je ta ja motor bata ce min komai har muka isa gida nan ma ita ce ta fito da ni
daga cikin motor ni kuwa da har lokacin hawaye nake yi,riƙe ni tayi muka isa tsakiyar falon kana
ta rungumeni ta fashe da kuka,sautin kukan ta ne ya dawo da ni daga duniyar dana faɗa,nima
fashewa da kukan nayi me ban tausayi na ƙara ƙanƙameta a jiki na.
"Shi ne fa shi nefa!cikin shashsheƙar kuka nayi mgnr.
Zaunar da ni tayi akan kujera ta tashi taje ta ɗaukomin gorar ruwa me sanyi ta kawomin,amsa
nayi tasha dan ina da buƙatar sha ko naji ɗan sanyi-sanyi.
"Shi ne wa Meenal,"ta faɗa bayan ta zauna kusa da ni,ita ma idanuwan na ta sunyi jajir.
Ni da har lokacin hawayena basu ƙafe ba,gashi ina jin fuskata tayimin nauyi ina jin ta kumbura
ne to ai dole dan ma ni jaruma ce da wata ce sai ta suma ga kukan da na sha.
"kin ganshi ne?"Na faɗa ina hawaye.
"Wake kike nufi Meenal Sir Daniel kike nufi wai".
"A'a aljani na baki ga marin da yayi min ba,"sai na fashe da kuka wannan halittar tsakani na da
ita sai Allah ya isa ban yafe ba,domin duk ramuwar da zanyi bazan taɓa iya raba abunda
tayimin ba.
Cikin rashin fahimtar zance na Aunty sadiya ta ce,"sir daniel ne fa ya mareki Meenal".
Girxiza mata kai nayi ina kuka abuna wato sai ya fito mita a matsayin oganta Allah ya haɗani da
sheɗani.
Waya ta zo dubawa dan ta nunamin hotonshi bada gani ba,sai yanzun ne ma ta tuna da yadda
tayi da wayar.
Tashi tayi taje ɗakin ta ban kula da abunda ta ɗauko ba inacan ina kuka na."Meenal kalli
wannnan ne".
Tashi nayi daga zaunan da nake a tsorace nace ,"eh shi ne shi ne aljanin a ina kika sanshi".
Wata irin raguwar ajiyar zuciya Aunty Sadiya ta sauke zama tayi tare da kama kanta abun da
ɗaurewar kai.
Nima zama nayi kusa da ita na dafa kafaɗunta ban iya cewa da ita komai ba.
Ɗagowa tayi muka kalli juna sosai,"Meenal wanan shi ne *DANIEL KRISTEN* yaron attajirin
ɗan kasuwar da lagos ke ji da shi bayarabe ne sanan kuma manyan kafirai maƙiya Allah,taya
Daniel zai kasance aljanin dake bibiyarki ko mutum dai ma,bayan baya jin hausa ko kaɗan
sanan kuma bai iya faɗin ko zo na kashe ka ba da hausa,ke bai ma taɓa xuwa arewa ba,taya
taya?sam baya son hulɗa da musulmai kamar mahaifinshi bazai taɓa kasancewa shi ba Meenal
kowa yasan wanan irin wannan sanin d na gayamiki,"ta faɗa tana nuna shi a hoton da ke haɗe
da mujalla.
Ban wani bawa kwanyata wanan damar ba balle ta buga haka ma zuciyata na samar musu hutu
dan yin wannan tunain a daidai wannan lokacin daidai yake da tarwatsamin kai yahaifar min da
hawan jini.
Hawaye ne kawai suke ta faman safa da marwa a fuskats,na shiga uku ni Meenal wani irin
lamari ne wannan Allah ka ɗauramin abinda yafi ƙarfina Allah,abunda nai ta rayawa kai na
kenan a zuciya.
Rungume ni Aunty tayi na matukar bata tausayi xata iya cewa tun ƙuruciya rabonda ta ga kuka
na,balle wannan yanayin Meenal jarumce me juriya da jan hali duk lamarin da ya sakata a
wannan yanayin to tabbas da wani ne abun bazai kwatantu ba.
"Kiyi shiru Meenal ɗan Allah kiyi hakuri kin ji".
Abun kuka ya sameka ace kayi shiru to ya ake so kayi da ranka fitinar cikin ranka da ɓoye kuka
ko me,kalamanta na nayi shiru tinzira ni ma suka ƙara yi na sake fashewa da kuka me cin rai da
ban tausayi kukan da zan iya cewa duk tsawon rayuwata ban taɓa yin irin shi ba.
Na daɗe sosai ina kukan cikin haka naji wani irin barcin wahala na fusgata ganin hakan yasa
aunty ta taimaka min na shiga ɗaki na,na kwanta ina kwanciya barci ɓarawo yai awan gaba da
ni.
Aunty sadiya ta daɗe xaune tana kallonta daga bisani ta tashi bayan ta rufeta da bargo,office
ɗin da ita ma bata koma ba kenan.
Sai gurin ƙarfe biyu da rabi na tashi da ƙyar na iya buɗe idanuwana tsabar nauyin kumburin da
suka yi,ita kanta fuskata ta kumbura tai him da ita.jiki n ma ciwo yake yimin da ƙyar na samu na
lallaɓa na faɗa bayin ganin lokacin sallah ya wuce,wai tamkar bani ba dana kalli fuskata a
madubi ta kumbra nai wani irin muni yatsunshi biyar kuwa gasu nan a fuskata shafa gurin nayi
wasu ƴan tsiraran hawaye suka gangaromin na takaici ba wanda ya taɓa yimin abunda wannan
halittar tayimin a rayuwa,gasa jiki na na fara ina kuka ban yarda da abunda Aunty sadiya ke son
gayamin ba na wannan ba shi ba ne wancan mutum biyu ne ko aljannai biyu anya kuwa,da
gaske wannan baya jin hausa kuma bai taɓa zuwa arewa ba??shi kuwa wancan a kano na fara
ganinshi da hausa raɗam a bakinshi kai ina dole da wani abu,to ko dan nace bana sonshi shi ne
zai ɓullomin ta wata sigar.
Da wannan zancen na gamsu wato dan na ce bana sonshi shi ne ya bijiromin ta wannan hanyar
tuno kalamanshi na ƙarshe nayi inda yske tabbatar da cewa kwara na fara sonshi kafin haɗuwar
mu ta gaba idan ba haka ba abun bazai min daɗi ba Jinjina kai nayi,"ohho shi ne zaka birijomin
ta haka to xamu ƙara haɗuwa ne,zaka gayamin kuma sai na rama marin da kayimin,"da ƙarfi
nayi mgnr kamar yana gaba na.
Na daɗe sosai ina gasa jiki na,sannan na fito wata duguwar rigar na saka sannan na tada salla
ina cikin yi Auntyna ta shigo zama tayi har na idar.
"Kin tashi Meenal ga abinci n kawo miki ki ci,ga magani ki sha nasanki da saurin zaxzaɓi".
Kusa da ita na zo na zauna na ɗauka ta koma gurin aiki gaskiya aunty sadiya tana so na so
mugun so nafi komai muhimmanci a gareta nasan yadda take mugun son aikinta.
"Baki koma ba",n faɗa ina kallon fuskarta.
Buɗe robar man zafin tayi ta lakato ta shafamin a gurin daya barmin taɓon yatsunshi ni ba fara
ba amma gurin yayi jajir.
"Oshhhh!
"Sannu!sai gobe zanje naji yadda ake ciki Meenal Sir Daniel bashi da mutuncin yin yafiya ga
kowa,ina jin ƙarshen aiki na a kamfanin ne ya xo ƙarshe nima na huta".
Zuba mata ido nayi ina ganin yanayin da tayi mgnr da shi yanzon shikenan zanyi silar barinta
gurin aiki,raurau nayi da ido xanyi kuka ta caraf ta ce,"No dont carry is all my fault saida kika ce
baki xo ba zaki iyaba na takura ki..."shiru tayi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,flet ɗin
abincin ta buɗe ta miƙa mata,"ki ci". Ba musu na amsa naci kaɗan na miƙa mata ta miƙomin magani da ruwa na sha.
"Ki samu ki kwanta zaki ji daɗin jikin ki,"ta faɗa bayan ta gƴaramin kwanciyar ta lulluɓe ni da
bargo,rufe ido nayi badan ina jin barcin ba.
Ina son Auntina ina ma tana so na,bazan taɓa bari ta dalilina ta rasa aikinta ba.......
*#Comment*
*#Share*
*#Vote and like*
*Please*
~Mrsbalarabe✍️~
Follow this link https://chat.whatsapp.com/FUiDhNPMi2W2AKSovmsstj
*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_
*Fatima Batula✍*
_Wattpad:mrsbalarabe._
*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_
_11-12_
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.
_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_
Daman barcin ba isata yayi shiyasa ina kwanciyar ya tafi da ni bayan na gama ƴan tunani na.
Ita kanta Aunty Sadiya jikinta duk ya mutu,dan a zahirin gaskiya ba wani aljani dake jikinta ko
yake bibiyarta,mutum ne dai to kuma idan mutum ne sai ya zamto Dany kai ina bazai taɓa
kasancewa shi ne ba ta hakan zata kasance,mutumin da ko hausa baya ji bai kuma taɓa zuwa
arewa ba,hulɗa da musulmai ma baya yi,to taya zai kasance shi?
Binciko wannan amsar daidai yake da binciko halittun cikin ruwa,da yawansu wanda kuma yin
hakan badai bawa ba sai ubangijin da yayi su a ciki,dan haka wannan zancen ma bashi da
amfani Allah ne kawai masanin gaibu.
⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️
Idan ka kalleshi zaka ɗauka barci yake yi,yadda ya rufe ido luff yana kuma sauke ajiyar zuciya
irin ne barci,amma a zahiri ita yake tunowa murmushi kawai yake saki tuno yadda take kallon
cikin idonshi tana gayamishi magana ƙara lumshe ido yayi a inda kwanyarshi ke ƙara
haskomishi hoton ta,bazai iya dakatar da kanshi yabo da begen halittar da ta kasance jaruma a
cikin mata ba,duk kuwa ta kasancewar ita ba ƙabilarshi ba ce,lokaci n farko yaji wani abu
akanta yana son macce mara shakka da tsoro da tsiwa,ɗan ɓata rai yayi ba tare da ya sani ba
tare da jin wani irin abu wanda zai iyacewa zafi a ranshi tuno yadda yaga hawaye na zirya akan
fusksrta sai kuma ya sake sakin wani irin murmushin ko na meye??
Cikin salo ta fara shafa shi salon da tasan yana jan hankalinshi,"Aure fa xamu yi amma na rasa
dalilin dayasa nake ganin kamar u are not interested,Dany u know i lov u morethan anythings
,we have to get a baby before we marriged,baka son k..."
"Shiii!
Ya faɗa ba tare daya buɗe idonshi ba,baya tare da ita hasalima ba jin abunda take faɗa yake yi
ba.
"Am not in dt mod”,ya faɗa can ƙasan maƙogaro ,"leave me alone pls".
Duk da yarbanci suke maganar. "Momy ce ta aiko ne fah,"ta faɗa kamar zata yi kuka.
Shiru yayi mata baya son yawan magana tafi kowa sani.Naci ne ma da ita kamar maiya tasan
idan yana yanayin buƙata tana zuwa yake biye mata.
Cigaba da shafa shi tayi cikin salon karuwanci,ɓalle mishi buturen riga ta shiga yi.
Buɗe idanuwanshi yayi tare da riƙe hannayenta duk biyu,wani irin wawan kallo ya bita da
shi,tashi tsaye yayi daga zaunan da yake kamota yayi har wajen ɗakin ya turata ya janyo ƙofar
ya rufe.
Kuka ta fashe da shi,bata son ta rasa shi,shi ne burinta shi ne mafarkinta.
"Taye meye faru?"
Juyowa tayi ganin momyn yasa ta faɗa kan jikinta,"Momy Dany baya so na,baya son aure
na".Ta faɗa cikin kuka
Lumfasawa Momyn tayi,"Ba haka ba ne Taye,Dany naki ne ki saka a ranki bashi da wata matar
bayanke dole zai so ki ne ma,u are my only inlaw Taye ki share hawayenki kibarni da shi muje ki
kwanta tunda ya rufe ɗakin shi,"cikin sigar lallashi take yi mata mgnr tare da kulawa da nuna
soyayya. Goyan bayan Momyn akanta shi ke ƙara mata gwarin gwiwa,akan duk rintse ita ce zata zamto
tashi.
Janta Momyn tayi suka bar gurin.
⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️
Ko da yaya ya dawo Aunty Sadiya tayi mishi bayanin abunda ya faru yasha mamaki sosai,shi
kanshi abun ya ɗaure mishi kai matuƙa,kwantar mata da hankali yayi akan karta ji komai tayi
hkr insha Allhu ba zata bar aikin ba,bazai kore ta ba,duk da shi kanshi ya faɗa ne kawai amma
baya tunanin Sir Daniel yana da mutuncin da zai iya barinta. Juyi kawai nake yi akan gadon na rasa wacce irin kaddace haka ke bibiyata,ba abunda yanxun
yafi damu na illa aikin Aunty sadiya bana so nayi silar rabuwarta da aikin da take mugun so,ya
xamar min dole nayi wani abu,dole zan kuma haɗuwa da shi zan roƙeshi a madadin naci
mutumcin shi akan barazanar da yai tawa rayuwata a madadin nayi ramuwa zan bashi hakuri
dole na ɗuka domin Aunty na,da wanan tunanin barci yai awan gaba da ni.
⚜️⚜️⚜️⚜️⚜️
A ƙa'idarshi ƙarfe takwas yake tashi ya shirya zuwa tara ya gama shiri sai ya tafi gurin
aiki,saɓanin yau da ta kasance ranar farko a gareshi daya tashi ƙarfe bakwai saura,shi kanshi
ya rasa dalilin daya kawai yaji yana son zuwa office da wuri,duk da wata zuciyar shi tana
tsokalarshi akan dan yana son ganinta ne,amma yaƙi yarda da hakan.cigaba da shirin shi yayi
cikin navy blue da farar suit ya shirya yana matuƙar son farin abu.
Kallon kanshi yayi a madubi,ko ba'a faɗa ba shi kanshi yasan shi classic guy ne yana kyau na
gaban kwatance ga haiba da ƙwarjini,zubin jaruman maza gareshi masu faɗin ƙirji,bai tsaya
ƙarewa kyawunshi kallo ba ya zura farin glas ɗin shi wanda ke ƙarawa kyawunshi kyau.
Ita kawai take faɗu mishi a rai,yana son ganinta fiye da tunaninshi ita ce yaji ya kasa samun
natsuwa tun daran jiya feel somtings strong about her,breifcase ɗinshi ya ɗauka ya fita daga
cikin ɗakin wanda zan ce aljannar duniya.
Bai haɗu da kowa ba,tunda ya fito,wata hanya yabi wacce ta sada shi da steps kaɗan yana kai
ƙarshen ya ci karo da wani ɗaki,nufar ɗakin yayi ba tare da shakkar komai ba.
"Goodmorning Swt heart,"can ƙasa yayi maganar.
Kasancewar ta saba da jin mgnrshi yasa taji abunda ya ce,juyowa tayi daga gurin da take
zaune.
Murmushi tayi wanda ke nuni da tsantsar ƙaunar da take yi mishi,tashi tayi ta nufe shi,"Morning
my Dear har ka shiga fita haka da wuri?yauwa Dany meyesa jiya ba kabar Taye ta kwanta a
ɗakin ka ba,ita ce matar da zaka aura nan da wani ɗan lokaci ya kamata ta samu ciki....."
"Ina sauri ne Momy idan na dawo kinyi maganar,"ya faɗa tare da xame jikinshi daga rungumar
da tayi mishi,bai ko tsaya ya waiwayeta ba,ya fita ,"Sai na dawo Momy".
Kallon mamaki ta bishi da shi,ganin yadda yake sauri haka tasan ko wani abun gaggawan ne ya
taso ai akwai secretary,to ko saurin me yake haka ohho???
Tun asuba na tashi jiki a macce duk jina nake yi kamar ba niba,shiryawa na fara yi,ina cikin
shirin Anty Sadida da Yaya suka shigo,ta ce bari ita taje taji abunda zai faru,jiki na ya ƙara
mutuwa domin ƙwaroƙwaro naga ƙaraya a cikin idanun su.
"Ya ubangiji ka ɗaura ni akan wata dama