Showing 24001 words to 27000 words out of 42034 words

Chapter 9 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf

Advertisement

24 Jun 2025

2301

tashi uwar ba. Duk sun fishi so ma,duk da shi ma yana so.
Fita suka yi wai zasu siyayya suka bar su,su kaɗai ɗakinta Taye ta ja shi.
Dan kafin shigowarshi sun bata wani magani wanda aka tabbar musu yana kwanciya da ita a
lokacin to ba makawa zata ɗau ciki.
Daman da biyu suka kirashi ɗin.
Shi kuma da daman yana cikin yanayin kasala da mutuwar jiki,hakan yasa ya amshi tayinta da
hannu bibbiyu..
Nan suka hau jiyar da juna daɗin rayuwa,saita taye ta tabbar da ta mantar dashi komai ya fita
haiyacinshi,dan duk jarumtarshi wannan faninin susucewa yake yi.
"I love u Taye zan yi rayuwa da ke kaɗai ne,nayi miki alƙawari bazan taɓa bawa wata kai na ba
bayan ke
....u are d only one who have right akai na,am your's har abada,Taye ba wata maccen da zata
kai ki .... Ke ba irin su ba ce...kin fi su...."
Shi dai yaji yana suburbuɗo zance,amma bai san kansu ba.
Ko da ta soma ƴanke ƙauna ga samun nagartaciyyar soyayyar Dany,a wannan fanin take
samun gamsuwar yana son ta,kawai dai shi haka yake baya yin abu da zafi-zafi,domin sosai
take yarda da amincewa da kalamanci,musamman idan ta tuno shi mutum ne me magana ɗaya
da kuma cika alƙawari,shiyasa ta ƙore ta huro take kuma gyara kanta,shiyasa kullum yake jinta
savuwa kuma daban,daɗinta kullum sabonta yake mishi.


*** **** ***
Ban tsaya ba saida na tabbar da nayi duk abunda ya kamata nayi,sannan na tsaya lumshe ido
nayi na gaji ga wata uwar zufa da takw ketomin,"gaskiya aiki da wuya".
Ban tabbatar ba,saida nayi tuzali da agogon dake office ɗin.Zaro ido nayi ƙarfe uku da rabi
banyi sallah ba..
Tsaye na tashi,ina tunanin lokacin da muka fito daga meeting ƙarfe sha ɗaya da hamsin da wani
abu,haka na ɗau lokaci gurin wannan aikin.
Tsaki naja na takaicin rashin jin kiran Sallar da ba'ayi,ai dole kuwa a shafawa gurin yi inba
wanda yaɗau sallah kaya ba,ji dai yanzun ina zaune ina aiki har lokaci yayi haka,irin haka ai sai
ga buɗe ido ka ga ma anyi sallar maqrib.
Ina wannan tunanin ne,ina alwala a vayin da ke office ɗin.
Fitowa nayi aiki ja,wato sallaya ina zan samota,ni kuma ban yarda da wannan gurin ba,abun
haushi kuma ba hijjabi na saka ba,balle na cire ɗan kwalina na shimfiɗa,haka nan na samu nayi
dabara nayi sallar ina idarwa na tadda la'asar.

Bayan na idar na zauna nayi azkar kamar yadda na saba,sanan na tashi naje na zauna ina jin
gajiya.
Tunaninshi na fara yi ya kamata yace wani abu ai,wannan kalaman idan har masoyi yaji su to
dole zai ce wani abu.Azalzata xuciyata naji ta fara yi,dan a ɗabi'ance haka ne,ina son sanin shi
ɗin ne?.
Deepbreath nayi bai ƙarfe .
"cool down Meenal!
Na faɗa da ɗan ƙarfina tare da furza isa daga bakina,zanca tunani nayi akan cewa to ko dai
yana so yaja aji ne,ganinshi babban mutum ne ma matsayi da daraja.
"Mtsewww wani girma da daraja ga kafiri".
In badan ina son ɗaukar fansa ai ni da tuni na gama gaba ne,kan me zan zauna ɓata lokaci na
da tunani ga kafira.
Wani tsakin na kuma ja tare da yin fatan Allah ya kawomin lokacin da zan bar garin ma gaba
ɗaya.
"i have to do something",na faɗa bayan na tashi tsaye fita nayi office ɗinshi na nufa tunda banga
ta zama ba.
Banyi knocking ba na kunna kai wayam ba mutum ba alamarsu.
Tsaki na kuma ja iya laɓɓa na.
"ina kuma yaje daman ai duk abunda aka haɗa da jaki sai ya ci kara",na faɗa bayan na juya na
fita.
Securityn gurin na tambaya ko sun ganshi,suka ce min ya fita yana sauri da alama gida za shi
wani abun ne na gaggawa ya tashi,taɓe baki nayi na koma office ɗina na zauna.
Wayata na ɗauko text na rubutawa Anty Sadiya.
"Besty ya aiki?
Murmushi nayi lokacin muna makaranta ita ce besty na,idan nun dawo gida Anty idan muna
makaranta besty.


Daman ita ma ta gama abunda take yi,zama tayi tana ƴan dube-dubenta a wayar,tana jin
shigowar saƙon ta duba,ita ma dariyan tayi .

"Alhmdllh Besty ya naki aikin?ah tunda ke expect ce ba wani gajiyar da zaki yi".

Murmushi Meenal tayi bayan ta karanta.

"Ban kai ki ba ai,gani nan a gajiye yau muna zuwa gida zan kwanta dan barci ma nake ji".
Sai yanzun na tuno da fitar da zamu yiba,muka fasa bayan kuma munce wa matar zamu zo,ya
kamata muje gaskiya.
Kallon agogo nayi wanda ya nuna min ƙarfe shidda da rabi,lokaci naja.
Tunda oga baya nan yanzun ni ce zanyi sallama ta hanyar danna ƙararrawa.
"Zamu tashi da wuri yau,kafin muje gida sai mu biya inda kike ce zamu tunda mun sanar da
ita,bai kamata kuma tashi shiru ba" .
Na turawa anty sadiya.

"Hmm manya aiki fa yazo gurin manya za a saka ya sallame mu kenan da wuri,"dan ita bata
kawo baya nan ba ma.
Ni ban ma duba replay ɗinta ba,na tashi na faɗa bayi dan ɗauro alwala,ina aiyanawa rai na
Sallar isha'i a gida zan yi ta.
Ina fitowa na tada dan lokacinta yayi.
Bayan na idar na gabatar da azkar ɗi na na yamma sannan na tashi.
Lokacin bakwai tayi shiri na fara yi duk da bazan tafi da komai gida ba,dan duk mafi yawan
ma'aikatan da computer suke tafiya gida harda anty sadiya.
Na kimtsa tsab na fito kai tsaye office ɗin nashi na nufa,gurin madannin naje na danna ina
dannawa nai fitowa ta.

Naga alamun mamaki ƙarara tun gurin security ɗin,ni kuwa nai murtsitsi abuna na taka cikin isa
da ƙasaita har office ɗin Anty na.
Tunda taji ƙarar gabanta ya faɗi,ta tambayi wani ma'aikaci da yazo kawota wasu takardu meke
faruwa,ya ce oga baya nan ya fita tun ɗazun sakatariya ce tayi sallamar.

Daman tasan haka Meenal take idan ta ce xata yi abu to fa zata yi shi ne,ba tsro balle fargaba,a
tarihin ma'aikatar bai fi sau ɗaya aka taɓa sallama bakwai da wani abu ba,ana dai yi takwas
tara.

"Ki fito muje,"na katse mata tunanin da ta faɗa.
Firgitt tayi tana cigaba da shan mamakin Meenal da ƙarfin hali.
Ƙarasa shigowa nayi,"bai kamata ace kina mamakin ƴar uwarki har yanzun,trust me kawai
nasan abunda nake yi".

"gaskiya banga alama ba Meenal,baki tsoron abunda zai biyo baya idan yaji".

"Pair! ba ina son zama gwana ba ce,da yasa bana jin tsoro akan abunda zanyi,haka nake i do
wht ever a want to do,me zai faru is my job nifa sakatariya ce,i have right to do my job,ban
karya doka ba,kawai nayi yadda nake so ne",cikin karfin gwiwa nake zaro kalaman da nake
sarrafasu haɗe da hannuwana wanda nake nuna da kai na,da kuma matsayina.
Duk da gaskiya ta faɗa amma ita dai har yanzun jikinta a sanyaye yake,dan tasan lallai sai an
kira an gayamishi tun yanzun.

Jan ta nayi muka fito,"ni muje".

Bayan mun shiga motor ta ja ,"ina so na iya tuƙi ba,ko zaki bani na koya".

Zaro ido anty sadiyar tayi,"wuu rufa ma Ɓakir asiri tausaya mishi yayi ko da wayau ne da
iyayenshi".

Dariya na fashe da ita sosai wacce na manta rabon da nayi irinta.

Ita ma dariyar tayi,muna tafe muna fira,da yake gidan na ɗan nisa hakan yasa muka ɗau lokaci
kafin mu isa,a tanƙamemen get ɗin na alfarma muka tsaya muna hon,saida security ya fito zuge
glss ɗin Anty sadiya tayi.
Murmushi,"Tun ɗazun aka sanar mana da zuwan ku,barka kun zo lafiya",yai mgnr cikin raha.
Anty Sadiya ce ta amsa mishi ni kuwa ko kallo bai ishe ni ba.

Get ɗin aka buɗe mana,wai yadda kasan rana tsabar hasken tsagar gidan wanda ya haska
ƙyayataccen gidan.

A tare muka sauka bayan mun tsaida motor,kallonta nayi muka yiwa juna ɗan murmushi kafin
muka nufi kofar da zata sada mu da falon.


Turuss muka kusa cin karo da juna,ja yayi ya tsaya.
Kyakykyawa ne ajin farko gashi fari tasss zubin fulanin asali,ga hutu da boko zun ratsa shi,ɗan
gaye na na ƙarshe,sakin wannan kyakyawar fuskar yayi wacce daman me annurin
ce,murmushi yayi wanda ya bawa fararen haƙuranshi damar baiyana.


"Munyi fushi tunda sai yanzun kuka zo",da harshen hausa yayi maganar.

Hakan da naji yasa na ɗago mukai two eye da shi,hausa kai yaushe rabon da naji hausa irin
haka.

Wani lafiyayyan murmushi ya sakar mata,ita ma ta maida mishi martani,ya burgeta dubi da
yadda yake ya ga dama yace shi bai taɓa jin hausa ba ma,kuma ta zauna,dan yadda yake
mugun yanayi da indiyawa harda sirintar ma,amma ji hausa raɗam a bakinshi.

"Maraba ku shigo,"ya faɗa bayan yayi gaba,yai mana jagora har tsakiyan tankamemen falon.

"Anty rabi'ah kin gansu wai sai yanzun,"cike da zazzaƙar muryarshi yake kiran na ta".

Juyowa yayi gare mu,"ku xauna dan Allah".

Ni da har lokacin murmushi nake saki dan jin hausa a bakinshi yasa naji ya burge ni ƙwarai.
Zaman muka yi muna zama ta fito.
Babbar macce me jini a jika,ita ma fara ce sol zubin fulanin,fuskarta ɗauke da annuri.


" *Khaleed* su waye kake maga....." bata iya ƙarasawa ba,ganin mu da tayi,da murna ta isa
gurin Anty sadiyar rungumar juna suka yi.

"Haba oum Ɓakir tun ɗazun,muna ta jira ai da kin gayamin sai kun taso daga gurin aiki".

"Kyi hakuri wllh da ba aikin zamu ba,har mun fito sai aka kira mu shiyasa".

Sakin Anty Sadiya tayi tayo kai na,rungume ni tayi,naji wani irin banbara kwai.

"Meenal muna ta jiranki tun ɗazun,Khaleed daga jin nace zaku zo,ke daga arewa kike yaƙi fita
shi dole zai ya jira ki ya ganki,ya samu abokiya ƴar arewa,wacce zasu na hausa, daman baya
son hausarshi ta gudu....."

Kallonshi nayi,wanda shi ma daman idonshi na kai na,murmushi na sakar mishi......


_Kai wai ya naji sai typing nake yi,ba gajiya,hmm ban gaji ba haka zan dai barku idan naji
ruwan comment na dawo.Amm gaskiya duk grp ɗin da nake tura muku da kaina baku yin
comment yasin dainawa zanyi,dan lada ake sallah a to._

*I do love u my people,ƙaunar ɓoye fans,ku huta ku saki ranku kuna raina,ina mugun jin daɗin
addu'o'inku gare ni.*



*#Comment*
*#Share*
*#Vote and like*
*Please*



~Mrsbalarabe✍️~


*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._

*Telegram*

https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8




* Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun
so ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin
matsayinki a gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy
ya baki miji na gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_19-20_


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*



*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.



*Addu'ar Nema Wa 'Ya'ya Tsari.*

Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan

da Husain tsari da wannan addu'ar:
اَمُكُذيِع
ُأ
ِتاَمِلَكِب ِهللا ،ةَّماَّتلا ْنِم ِّلُك ٍناَطْيَش ،ٍةَّماَهَو ْنِمَو ِّلُك ٍنْيَع .ٍةَّمَال
O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin
lammah.

Ina neman muku tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan shaidan da wata dabba mai dafi,
da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa.




_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_




_Previously_

Kallonshi nayi,wanda shi ma daman idonshi na kai na,murmushi na sakar mishi.....



_Continueosly_


Shima Khaleed d’in wani k’ayataccen murmushi ya sakarmin mai d’auke da wasu sak’onnin da
suka rikitamin dukkan lissafi nah.

Lumshe idona nayi tare da sake bud’e su a hankali na d’ora su akan kyakkyawar fuskarsa mai
cike da haiba tare da kwarjini.

“Barka da zuwa”.

Na jiyo saukar sihirtacciyar muryarsa a cikin dodon kunnenah.

“Yawwa,Mun sameku lafiya?”.

Nima na fad’a cike da farin cikin jin hausarsa mai birgewa, kallon gefen da su Anty Sadiya suke
nayi ashe wai harsun bar wurin sun wuce d’akin Anty Rabi’a,wata nannauyar ajiyar zuciya na
sauke,ina jina normal.

“Bismillah, Ga ruwa kisha Meenal”.

Khaleed ya fad’a yana ajiye min tray mai d’auke da robar swan da cup d’aya.

Dariya nayi nace;

“Nagode da wannan karramawa”.

Murmushi yayi min,

“Karki damu,kinsan ance baqonka Annabin ka,gaskiya naji dad’in had’uwa dake”.


“Nima haka,Barin ma da naji ka iya Hausa sosai,tinda nazo banji Hausa irin taka ba”.

Na k’arashe maganar ina d’aukar ruwan na b’alle murfin robar da zummar zubawa, da sauri
Khaleed ya riqo hannu na wanda yin hakan yayi sanadiyar jin wani irin shock tare da wani
bak’on yanayi,saurin janye hannun nayi ina kallonsa cike da mamaki.

Murmushi mai sauti yayi yace;

“Nine ya dace na zuba miki ba keba,karki wahalar da kanki”.

Sai a lokacin na saki wata ajiyar zuciya,jin inda manufarsa ta dosa.

“Okey nagode”.

Na fad’a ina karb’ar cup d’in da ya mik’o min wanda ya tsiyaya ruwan a ciki.

Ina qoqarin kai cup d’in bakina wayata ta hau ruri, dubanah nakai kan wayar naga number Anty
Sadiya murmushi na saki sannan na d’aga wayar ina fad’in,

“Anty Sady yane?”.

Dariya tayi tace;

“Lallai Meenal Sannunki,to Anty Rabi’a tace in tambaye ki wurin ta kikazo ko wurin Khaleed?”.

Wata kunya naji ta kamani wacce bansan ma’anar ta ba, sannan naji wata irin fad’uwar gaba ta
riskeni,da sauri nace;

“Wurinta nazo wallahi,kuna ta ina ne?”.

“Ki shigo d’aki mai kallon ki muna ciki”.

Aunty Sadiya ta fad’a sannan ta katse wayar.

Miqewa nayi ina gyara mayafina, ganin hakan Yasa Khaleed kallona yace;

“Ya haka kuma?,ina zakije gashi ko ruwan da na kawo miki baki sha ba”.

D’an murmushi nayi sannan na d’au ruwan nayi kurb’a biyu na ajiye tare da fad’in,

“Thanks, bara na samesu”.

Ban jira amsarsa ba na wuce hanyar da zata kaini cikin d’akin Anty Rabi’a,ina jin yanda
idanunsa ke yawo a kaina.


Ina shiga Bak’ir yayo kaina ya rungume ni yayinda idon su Anty Sadiya yake a kaina wanda har
saida naji na tsargu da kallon da suke min,d’aukar Bak’ir nayi muka zauna gefen Anty
Sadiya,basu cemin komai ba sukaci gaba da firar su, nikuma naciro wayata na kamo muna
game d’in Candy Crush nida Bak’ir,.
Saida suka sha firarsu mai isarsu, sannan Anty Rabi’ah tace muje dainy don cin abinci, dukan
mu dainy muka nufa achan muka tarar da Khaleed zaune yana danna wayarsa da alama chart
yake,Anty Rabi’a ce tayi sarving d’in mu kowa ya fara cin Abincin shi, inda suka dasa wata
sabuwar fira kamar wasu ‘yan jarida, ni haushima suka fara ban jin duk yawancin firar tasu da
turanci suke, kuma ba akan al’adar mu suke tattaunawa ba,haba gaskiya Lagos batayi
ba,mutum d’an bahaushe amma kaga ya juye baki ya koma inyamurin k’arfi da yaji,haba me
ake da qasar arna?marasa tsalki.

Jikinane ya bani ana kallona hakan yasa ni d’ago fuskata, idanuwanmu ne suka sark’e cikin na
juna wanda ya haifar min da wata irin fad’uwar gaba,da sauri na janye idanuna na sadda kaina
qasa ina mamakin wannan bak’on yanayin dake neman rikitamin lissafi.

“Meenal!,haka kike dama bakya fira?”.

Anty Rabi’a ta fad’a fuskarta d’auke da murmushi.

kamin inkai da magana Anty Sadiya tayi saurin fad’in,

“Chapp aikuwa Meenal gwana ce wurin surutu, bata dai ga damar yi ba”.

Murmushi kawai nayi bance komai ba,inda Anty Rabi’a tace;

“To maybe kunyata takeji shiyasa bata fira da ni”.

Dariyar da ban shirya ba nayi nace;

“Ke Anty nah ce,mezaisa naji kunyarki?,kamar yanda Anty Sady ta fad’a banajin yin firar ne”.

Dukan su dariya sukayi,Agogon dake manne jikin bangon d’akin na kalla naga lokacin sallah
yayi.

Guntun tsaki nayi cike da jin haushi,ace ga lokacin sallah yayi amma baka jin kiran
sallah,wannan wane irin bala’i ne haka?.

“Zanyi sallah Anty”.

Na fad’a ina kallon Mamallakiyar gidan,wato Anty Rabi’a.

“Au anyi sallar kenan?,bara muma muje muyi”.

Anty Rabi’a ta fad’a tana miqewa muma miqewa mukayi a tare, inda na kai kallona wurin
Khaleed naga ko alamar motsi baida ballantana yayi zummar tashi zuwa sallar hasalima
hankalinsa na kan wayarsa,tsayuwata na gyara nace;

“To Oga, kai bazakayi sallar ba ne”.

D’agowa yayi ya kalleni tare da sakar min murmushi yace;

“Zanyi,akwai abinda nakeyi ne”.

Zaro ido nayi a mamakance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login