Showing 6001 words to 9000 words out of 42034 words

Chapter 3 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf

24 Jun 2025

1934


mamakin abunda zan yima ko aljani ne kai wllh nafi ƙarfinka dan haka ma ka gama gabanka,
"cikin tsiwa nake gayamashi magana ba tsoro ba shakka balle fargaba.
" MEENAL ki fahimta ƘAUNAR ki fa kawai nake yi ba komai ba, karki ce haka nasan zaki so ne
nima zaki so ni kamar yadda nake miki", cikin sanyin murya yake maganar cikin harshen hausa.
Rintse ido tayi, tana jin wani irin zafi me raɗaɗi a ranta har gwara da kalamar ƙiyayya yake
gayamata da wannan kalmar ta yana ƘAUNARta.
"Kai wai baka da hankali ne jakin ina ne kai bana ƘAUNAR ka kuma bazan so ka ba, kai infact
ma na tsanake na tsaneka.
Cikin zafin nama irin na jaruman maza ya tashi tsaye tare da bugun teburin gurin da karfi
wanda hakan yasa hankali jama'ar gurin ya dawo gurin.
Nima tashi nayi a zabure idan hauka yake ji nawa ya fi nashi idan dan bala'i ne shi to ni ƴar
guguwa ce. Wani irin gurnani yake yi lokaci daya ya sauya daga me kyau zuwa me muni. Duk
da na fahimci hakan amma na dake ɓacin rai nima ina ciki ai wa zai yi wa hauka dan
mahaukaciya ne shi to nima haka. Ido cikin ido muke kallon juna a inda yake wni irin gurnanin ɓacin rai me ban tsoro dan bai yi
kama da irin na mutane ba, tsabar jarumta ce irin tawa yasa na dake da kuma nima din na
harzuƙa.
Cikin wata irin murya wacce bana ce irin ta mutane ba ya ce, "INA ƘAUNARKI MEENAL," cikin
ɗaga murya a kuma fusace.
Nima fusatar nayi zan nuna mishi hauka na, da nayi fatan kar na nunawa kowa shi na ce "I hite
u," cikin daga murya a fusace da kakkausar murya,dan har ga Allah raina ya mugun ɓaci
matuƙa.
"I LOVE U MEENAL".
"I HITE YOU!"

runtse ido naga yayi ya buɗe duk jarumta ta saida na ja baya dan a iya sani na da halittar Allah
ta ɗan adam idan ranshi ya ɓace idanuwa ja suke komawa ba green ba.
"Dole ki so ni Minel dole ki zo ni".
Duk da ina cikin halin tsoro amma sai da na iya cewa, "Vazan taɓa sonka ba na tsaneka kara
na mutu da na so ka".
Dafa ni naji anyi ta baya, wani irin kududu naji ciki na yayi, a tsoro ce na juyo nannauyar ajiyar
zuciya na sauke tare da lumshe ido ganin Aunty Sadiya ce.
Jiki a mace ta ce, "Meenal!
Jin yadda ta kira ni wani iri yasa na ƙara zuba mata ido.
" Ke da wa? ta faɗa a sanyaye.
Juyawa nayi me zan gani wayam ba mutum ba alamarshi, waige-waige na fara yi ina kalle-kalle.
Ga mutane duk sun zuba min najiyamo.
Juyowa nayi baki na rawa ina son yin magana Yaya miftahu ya tare ni," MEENAL ke da wa
kike?"
To na shiga abunda yafi uku ni Meenal me suke nufi, dakewa nayi murya can na ce, "shi ne shi
ne ya zo".
Gargixa kai Aunty Sadiya ta fara yi dan tunda suka jiyo ƙara hankali su ya dawo gurin basu ga
kowa ba, bayan ita kadai da ke ta zuba masifa da bala'i, wanda duk sauran mutane ma basu ga
kowa ba.
Jiki na ya mutu to kar dai ace Aunty Sadiya basu ganshi ba ne.
"Baki ganshi b ne yanzun ya tafi", na fada can da raunanniyar muryata.
"Ba kowa Meenal ba kowa a nan Meenal tun dazun muke tsaye ke kawai muka gani kina faɗa".
Rass naji gaba ya yanke ya faɗi kallon mutane nayi wanda duk hankali su yana kai na, "Kenan
Aljanin ne", sha naji hawaye ya balle ba shiri suka antayo.

Yaya Miftahu ne yaja hannu na mukai waje, ita kuma Aunty ta dauko Bakir. Wani iri nake jina
lamarin da bazan iya cewa gashi ba kawai dai naji ni kamar wata ƴar karamar zautacciya taya
za'ayi haka kenan ni kadai nake ganinshi janye hannu na nayi daga riƙon da Yaya tayi min
bayan mun fito wajen. Baƙir na janyo dukawa nayi gurin har kasa ina hawaye na ce da shi, "gayamin Bakir baka ga
kowa ba dazun da nake mgn?“na tambaye shi ne don son ƙara tabbatarwa amma ina zullumin
jin amsar da zai bayar.
Kallon iyayenshi yayi a inda su ma suka zuba mishi ido don jin amsar da zai basu.
Saida ya dawo da dubunshi gare ni kana ce cikin harshen turanci dan da turancin nima nayi
mishi magana.
"banga kowa ba amma naji kina magana ke".

Rass naji gaba na ya yanke ya fadi saura ƙiris na zube ƙasa Yaya ya tarbo ni, alert message ne
ya shigo wayata wanda duk ya razana mu.
Wayar Aunty ta amsa ta bude sakon.

" _MEENAL KIN KASA FAHIMTA NE KAUNAR KI FA KAWAI NAKE YI ZAI FI MIKI KI SO NI
MA, DAN NI KULLUM KARA SONKI NAKE YI, KARKI MANTA DA WANNAN BAZAN TAƁA

BARIN KI BA HAR SAI KIN SO NI TUN KAFIN HADUWAR MU TA GABA KI FARA SO NA ZAI
FI MIKI DOMIN HADUWAR BA ZATA TAƁA YI MIKI DADI BA, YA KUMA ZAKI TAFI BAN GA
FUSKARKI BA BAKI GA TAWA BA JUYO KI KALLE FUSKAR ABUN ƘAUNAR KI KI KUMA
AJIYE FUSKAR CIKIN KWAKWALWARKI DA TUNANINKI"._
Da ƙarfi Aunty ta karanta sakon dago kai na nayi domin na kalle Aunty wai cikin rashin sa'a ko
na ce aljanan ce ya kai idona can bayan motar ta mu.


"Waaa... innnahuuu... Sulaimanu..... ".

Diff maganar ta yanke, wanda daman ba fitowa tayi ba iyakarta maƙogaro.
Jiki na ne ya hau rawa yana karkarwa fiye da shekaranjiya, sanyi kawai naji ta ƙasa na wanda
hakan ya tabbatar min na kuma. kafafuwan nawa ma karkarwa suke yi, duk ilahirin jiki na ma
rawa yake yi.
Na kuma kasa dauke idona daga gareshi a inda shi kuma yake sakar min wani irin kyakkyawan
murmushi amma a gareshi.

Ganin halin da nake ciki ne yasa suka juyo dan ganin abunda nake gani amma wayam basu ga
kowa ba, gashi dai ni suna ganin alama ina ganin wani abu.

Janyo ni Yaya yayi ya tura ni cikin motar Aunty, tayi saurin shiga bayan ita da bakir jan motar
yayi da gudun tsiya ya bar gurin. A inda ni kuma har yanzun hotonshi bai ɓacewa gani na ba
idona fuskar shi kawai yake hasko min yana sakar min murmushi.



Duk jijjigar da Aunty ke yimin a banza ban ma san tana yi ma.
Sai can har mun isa gida ban ma san mun kai ba sai da muka isa tsakiyar falon sannan na
farga a tsorace.


"Aljani ne Aunty Wllh aljnai ne na shiga uku na mutu!".


Aunty n ita kanta ta ruɗe ta gigice ta ma rasa abun da zata yi kawai dai riƙe ni take yi.


Muna nan tsaye a rude bamu ma san da fitar Yaya ba sai jin da muka yi an kwala sallama
sannan yasa muka kai duban mu.


"Ruƙiyya za'ayi miki MEENAL idan ma aljanni ne zai rabo da ke".

Har maganar tawa tana hardewa gurin faɗin, "To to!'
".


Gaban malamin naje da sauri na tsugunna jiki na sai faman rawa yake yimin".

" Ayi min rukkiyar!".

da rawar naki na ce.

Murmushi Malamin yayi shi da wanda suke tare dan ta basu dariya ma wai ayi mata rukiyyar,
zama suka yi akan kujerar daga can.
Ganin sun yi nisa da ni yass na tashi ina rawar jiki na matsa kusa da su gaff na tsugunna.

Murmushi suka yi a karo na biyu, cikin dattako malamin ya ce, "To MEENAL za'ayi miki ki
kwantar da hankalinki yau zai bar jikinki gaba daya".

Naji sanyi a rai na, amma dai na ƙagara ayi na huta ya fita daga jiki na na huta.
Kallon su Yaya yayi yace, "Ku zauna".
Alama Aunty tayi wa ƴar aikin gidan ta ta janye Bakir su bar gurin. Zama suka yi su ma jiki a
mace musamman ma Aunty Sadiya.

Wata gorar ruwa malamin ya ciro a yar jakarshi har ganin nawarshi nayi gurin bude gorar na
ƙagara ya watso min ruwan na fashe da ihun da naga ana yi.

Basmala yayi bayan yayi yan tufe-tufenshi cikin ruwan ya watso min dauke numfashi nayi jin
sanyin ruwan nai shiru ina jiran sakamako na kuma runtse idon gama yadda duk abunda zai
faru ma ba zan gani ba.


"MEENAL Meenal! malamin ya kira ni".
Ban san lokacin da nace na'am ba sai jin sautin da nayi ya fito dan bude ido nayi naga ko wani
abun ne.


" Meenal ke ce?".

"Eh ni ce Meenal".

Na bashi amsa a takaice.
Kallon wanda suke tare yayi yai mishi alama, naga ya fito da littafin Allah littafin me girma da

daraja kariya waraka magani ga duk wani abu a duniya, kogin azava a gurin shaidanun
aljanai........




~_Mrsbalarabe_~✍


*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._



*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_7-8_


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*

Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.


_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_


Duk wata ayar ruƙiyya dake cikin alƙur'ani ba wacce basu karanto min ita ba, ni kuwa nai lamo
sakon baya sakon yace MEENAL ke ce nace eh ni ce.
Yace da Aunty ta kawo burner za'a kunna hayaƙi sannan ta kawo bargo.
Rufe ni aka yi da bargon bayan an zuba hayaƙn ya tashi, dayake nima ina so shiyasa nayi lamo
a ciki duk yadda yace nayi, nayi wai ni Aljannai.
Na fi minti uku sannan aka buɗe ni, na fito duk nayi zufa, bayan wata lafiya da naji inaji ba
abunda nake ji a jiki na.
"MEENAL baki ji komai ba".
Kallon shi nayi murya zaun nace, "Banji komai ba".
"Ko ciwon kai?"
"Eh!
Lumfasawa yayi sannan yakai dubanshi gurin su Aunty Sadiya," To a zahirin gaskiya yarinya
nan bata tare da wani aljanni sannan kuma ba aljannin da yake biyayyarta dan daya kawo
kanshi, duk wani abu nayi amma sam ba ko alamar aljannai a tattare da ita".

Ni wllh zai fimin ma da yace aljannin ne, to yanzun da bashi ba ne waye? ina kawai dai bai gano
ba ne shi kuma ba zai iya cewa bai gano ba kar mu raina iyawarshi abunda na barwa raina
kenan.
Ita kuma Aunty Sadiya da sai jinjina kai kawai take yi, daman tasan abunda zai faru kenan dan
zu gaba daya zuri'ar su aljanni bazai iya shiga jikin wanin su ba, to amma abun da ruɗarwa.

Ina jinsu suna firar cewa ba aljanni b ne mutum ne kawai yana son tsorata ni ne ta tashi nabar
gurin nai ɗaki na, jiki na a jiƙe da fitsarin da nai tayi bayi na shiga na sakarwa kai na shayaaa.
Ina tunanin taya zai kasance mutum anya kuwa ina gaskiya bazai taɓa kasancewa mutum ba
ina?? dole na je gurin malamin gaskiya daman yan Lagos akwai wani malamin arziki ne me
ilimi.... tunani dai iri-iri nai ta kawo wa a rai na har na fito daga bayin nazo na shirya ina cikin

shirin ne Aunty Sadiya ta shigo zama tayi kan kujera har na shirya sannan nazo nima na zauna.
"Me kike tunani? ta jefomin tambayar ban kalle inda take ba na ce," malamin ƙarya ne bai iya
komai ba kawai zan koma gida naje na samu musu ruƙiyar gaskiya".
Dariya Aunty Sadiya ta fashe da shi, kallon ta nayi rai a ɓace.
Yaya Miftahu ya shigo, "Honey yadai meye faru?"
"Honey kaji abunda MEENAL ta ce kuwa?“
Tashi nayi a fusace," Idan na bar muku gidan sai kuyi ta dariyarku daman ai saida Maama ta ce
min bazan ji dadi ba nace zan zo a haka... "Nai ta mita duk na sauke musu guntun haushin da
nake ji.
Da ƙyar suka iya shawo kai na na fasa, ni daman haka nake saurin hawa saurin sauka.
Da lallami da ban baki suka ban hakuri akan idan har wani abu ya kara faruwa sai a nemi wani
malamin, jinsu kawai nayi dan na saka wa raina ƙara ganinshi zanyi.

Haka muka wuni ranar a gida muna ta fira ganin abun nasu yayi yawa bazan iya cigaba da gani
ba dan zai su suka na rasa kunyata yasa naja Bakir mukai daki na.

Na dade sosai a falon ina kallo dan su suna da nasu a daki kuma Yaya baya barinta da dukan
alama maye ne, sai can na tashi na koma ɗaki.
Tun asubar fari na tashi lumi hankali kwance naje nayi sallah ban koma barci ba alqur'anin
wayata na bude na fara bita.
Da yake yau ta kasance Monday ranar aiki. Gurin bakwai saura na tashi zan koma Aunty na ta
shigo cikin shigar gayan aikin ta. "Amma Aunty wannan bai dace ba wllh kalli fa shigarki yanzun
kuma a hakan zaki fita gaskiya da sake".
"To ya zanyi MEENAL dokar gurin aikin kenan ba yadda zanyi ne".
"To ba sai kibar aikin ba ba wani ne sai shi".
"Hmm MEENAL kenan ba zaki gane ba, bari naje Honey na jira na sai mun dawo daga nan
zamu sauke bakir a makaranta," tana idasa faɗa ta fita da sauri karewa shigar nayi kallo
matsatsen wando ne a jikinta da ƙaramar riga sai hula da tarkacen kayan aikin.
Wani uban tsaki naja wani irin bala'i ne wannan mace yar musulma da shigar arna kai, duk sai
naji na ƙara tsanar garin da duk mutanen da ke ciki ma.
Komawa nayi na kwanta naita barci gurin goma na tashi na fito gidan wayam ba kowa sai naji
wani iri kenan haka zan dunga zama ni kadai kamar maiya, ga me aikin arniya ni kuma na tsane
Arna wari ma suke min vazan iya sakewa da ita ba balle ta shafamin ƙazanta.
Haka na wuni ranar zungur ba dadi bani daki bani falo nayi barci na tashi nayi na tashi.

Sai dare suka dawo lokacin har bakir yayi barci ma, a tsatsaye muka gaisa suka wucewarsu
daki, ta nan kuma suna burge nidaki daya suke kwana abunsu.
Haka ma washegari.

Tare suka leko harda bakir sukai min sallama suka wuce. Kullum haka nake wuni ni kadai
zungur a gida gashi ina jin tsoron fita duk sai naji na gaji gashi ni ba saurayi ba, ba abun kuma
na kira mama ba, abu duk ya hademin goma da ashirin.
Haka kullum nake wuni a gida, yau dai na gaji nace duk abunda zai faru ya dade bai faru ba sai

na fita abuna, na ko shirya na sa direba yaja ni cikin gari. Abun har ya ban mmk dan ban taɓa
dauka har naje na dawo ban ga aljani na ba.

Haka har yau sati na biyu a garin Lagos wanda na zo dominsu basu takai na dan wata rana ma
ko salamar basu yimin ranar da suka yi latti da dukan alama dai gurin aikin nasu suna da zafi
duk da basu gayamin ba amma nasan cewa me kamfanin ƙasurgumin arne ne, kuma kamfani
daya ne ita Aunty a ƙaramin kamfanin take aiki shi kuma Yaya a Babban yake aiki a duk da ni
ras'ayina irin nawa na hausawa ne amma hakan bai hana naji suna burgeni ba.

Ni da aljani na kuwa har yanzun shiru, nakan karanta sakon shi nayi dariya abu na kuma sai
naji ina fatan kara haduwa da shi, gashi shiru kike ji dan yanzun kullum sai na fita da idan na fita
bana sauka ko ina har na gaji da yawon nace a dawo gida amma yanzun kam sauka nake yi
naita yawo guri guri yau tsabar karan bani na cewa nayi yakai ni shoprite din na muka hadu har
gurin naje amma shiru bashi va lamarinshi.

Ni har na fara mantawa da shi ma, hutu kuwa nayishi har na gaji da yinshi sai kuma naji garin
ya fita rai na dan bani da me tayani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login