Showing 3001 words to 6000 words out of 42034 words
gayamin abunda ya
faru".
Daki-daki na fara basu labarin haduwata da shi tun a tashar motar Kano har kawo yanzun
kuma da na sake ganinshi a cikin motar bayan bashi na gani na daura da fadin, "Kuma yace
dole sai na so shi indan ba haka ba zai daina bibiyata ba har abada," harda ƴar kwalla ta na
karasa mgnr ina yi, dan na tsinke matuka. Shiru suka yi suna nazartar abun inda su kan su suka sha mamaki yaya Miftahu ne ya fara
cewa, "Ba aljani ba ne Autar Maama kawai yana son ya tsoratar da ke ne, ki kwantar da
hankalinki ba abunda zai faru kina tare da mu, yanzun dare yayi sosai karfe biyu saura ki je ki
kwanta karki ji komai ba abunda zai faru," yakai ƙarshen mgnr yana kallon matar ta shi. " Ehm Auta kawai dai ki je ki kwanta dare yayi karji ji komai abunki ba wani aljanin da ya isa ya
cutar da mu ko kin manta ne? balle shi ma ba aljanni ba ne kawai ki samu muje ki kwanta ki
huta dare yayi".
Tashi na tayi muka nufi wani ɗaki babba ne sosai dan harda kujeru a ciki daga gefe kuwa bayi
ne, Yaya Miftahu na biye da mu tare da jibgin kayan da na jibgo, bakin gadon ta zaunar da ni
cikin tsantsar kulawa ta ce, "Meenal dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kwanta ki huta kiyi
wanka sai kiyi salla ki kwanta". Sai yanzun da naji Aunty Sadiya tayi mgnr wanka na tuno da abunda ya faru da ni na jin fitar
abu ta ƙasa na, wata irin kunya naji, "Na shiga uku ni Meenal waye wannan? tun ina ƙarama
rabona da yin fitsarin kwance balle na tsaye," n gane fitsari ne ta hanyar jin zarnin da naji yana
tashi a jiki na. Runtse idon bacin rai nayi wllh ba abunda yafi min wannan ɗaci a duniya wai ni ce *MEENAL
MANSUR MANGA* da fitsarin tsaye, bazan taɓa yafewa wannan halittar ba inma mutum ne ko
aljann.
Duk sun fahimci halin da nake ciki hakan yasa suka yimin sallama cikin kulawa suka fita tare da
janyomin ƙofar.
Da sauri na tashi na faɗa bayi dan ni kaina naji ina ƙyamar jiki na dan warin da nake bugawa
dan ma su ɗin nawa ne. Na daɗe sosai a bayi ina wanka tare da tunanin shi a rai na, ina fatan
nayi ramuwar gaiyya a gareshi na saka shi yin zawo a wando kamar yadda yasa nayi fitsari,
tsabar rashin hakuri irin nawa da mugun fitina sai naji dama na ƙara ganinshi naci mutuncinshi
na manta da wahalar fargaba da tsoron da na faɗa dazun. Da wannan tunanin na kwana a rai na bayan na gama jeru dukan sallolin da ke kai na dan ma
kasaru zanyi.
Ban ji ma da kwanciya ba barcin wuya ya dauke ni, dan ina da gajiya sosai a rai na, tafiya
yankin azaba.
ASUBA TA GARI MEENAL.
Sama-Sama nake jiyo muryar Aunty Sadiya tana faɗin, "Meenal daure ki tashi kiyi Sallah sai ki
koma".
Cikin barci nace da ita, "to!.
Vata barni ba saida ta tabbatar na tashi sannan ta fiti, ni kuma na je na dauro alwala na dawo
na tada salla ina idarwa na koma na kwanta dan ji nayi ma kamar ina kwanciya ta tashe ni.
Ƙarfe goma sha biyu saura kwata na tashi, tare da taimakon wata irin muguwar yunwa a ciki
na, hakan yasa kawai ina tashi na fito, sakin baki nayi ina duvan gidan gaskiya gidan ya fitino
ainun kamar ba'a nan ba tsari da fasalin gidan bai yi kama da na ƴan 9j.
"Auta kin tashi daman yanzun nake son zuwa na ƙara duboki".
Sagaga nayi ina kallonta ko nace shigar da tayi Aunty na ce haka cikin shigar arna to na arna
mana zance, lagos ta lalatamin ƴar uwa ban kai karshen tunani n ba naji an rungume ni da
karfi.
"Oyoyo Aunty Meenal kin zo lafiya jiya naƙi yin barci na tsaya jiran ki baki zo da wuri ba",da
turanci yake yin maganar cikin kwarewa.
Duƙawa nayi na rungume shi a ƙirjina ina jin sonshi har raina.
"Am sorry dear nayi dare jiya". Baƙir kenan yaron yayata.
Ban taɓa ganinshi ido da ido ba sai a waya sunkutarshi nayi.
"Muje ki ci abinci nasan kina jin yunwa karki biye Baƙir sarkin surutu".
Ni duk sai naji bana jin yunwar ma tsabar ɗaukin ganin baƙir.
Muna nan tsaye Yaya miftahu ya fito, "Tsiwa Baby kin tashi lafiya ya kwanan legos amma baki
ƙara yin wani fitsarin ba dai ko,kai ni kuwa zan so ganin wanda ya saka Tsiwa baby fitsari," cikin
zolaye yayi mgnr da harshen Hausa.
Wani irin kututun bakin ciki naji ya kama ni ai fa abun nema a gurin yaya Miftahu ya samu na
bani da zolaya bata rai nayi nai kici-kici da fuska nace," Wllh tafiya zanyi gida zan koma abuna
bazan zauna ba kuma bazan kuma dawowa ba," ina faɗa na juya ɗakin duk suka biyo ni.
Da ƙyar suka shawo kai na, na hakuri falon muka fito nan na hau cin abinci haniƙan.
Ina cikin farin ciki sosai ni har na manta da zancen wani can daban wanda ban san shi ba, Baƙir
baya jin hausa ko ƙadan ko zo in kashe ka bai ji abun takaici nai ta fada ina masifa basu son
ƙabilarsu daga zuwa bariki sai su manta da asali,shiru kawai duk sukai min dan idan ina fada na
shiru suke yimin dan ina yinshi ne kan gaskiya.
Haka muka wuni ranar dan ranar yau ta kasance sati ba su da aiki basu fita ko'ina, haka muka
wuni muna firar yaushe rabo.
Sai dare naje dakin da a yanzun ya zama nawa na kwanta.
Yau da kai na na tashi duk da ban ji kiran sallah ba tsaki naja bayan na tashi sam ni legos bata
yimin ba bayan mutane ukun nan wllh kaf legos ba wanda nake so duk na tsane su ba to me
zanyi da arna ina musulma me zanyi da yarbawa ko igala ibra ina bahaushiya, gari duk arna
ace badai kaji kiran sallah na tashi ba, bayan na gama yin mitata a fili sannan na tashi naje da
dauro alwala na dawo na tada salla bayan na idar na koma na kwanta.
Sai bakwai na tashi, wani wankan na ƙara yi na dawo gaban mirrow Light makeup nayi kamar
yadda daman na saba, ina da kyau iya bakin gwargwado dan ni wankan tarwatsa ce abu mafi
kyawu cikin hallitar fuskata sune bakina da dimple dina me lutsawa ko murmushi nayi sai
fararen idanuwa na duk da dai ba manya ba ne amma tarr suke, bani da wani hanci amma
kuma ba gajere ba ne kamar yadda yake ba dugo ba, ina kuma da qiba ta ta fuskar da ta jiki.
A halitta kuwa zan iya cewa bani da wani naƙasu dan ina da zati abu mafi kyawu nidai a gurina
hips dina amma sauran mutane ƙawayena classmate yafi burge su a tare da ni ƙirjina dan Allah
ya azurtani da su tantsan-tsantar irin kuma cikakkun nan masu faɗi kuma a sama suke.
Cikin shigata na hausawa na shirya wato atamfa riga da siket kaya na kenan duk inda za'a je
zanyi irin wannan shigar abu na. Falon na fito wani daddanan ƙamshi ne ya duki hanci ne
lumshe ido nayi da Aunty na ta sauya sosai amma bata sauya gurin hada girki ba, kicin din na
nufa da sauri na kau da kai, wato dai yanzun yaya da Aunty basu da kunya legos ta cire musu
yar kunyar nan ta Hausawa juyowa nayi zan tafi.
"Twiya Baby ya zaki juya kuma ki shigo mana ki ga abunda Honey ke dafa mana".
"Ya bazan juya ba, na shigo kuna haka da alamar yanzun dai baku da sauran kunya gani na
bazai hanaka shafata ba," a zuciya na faɗa a fili kuwa ma na rasa abun cewa.
"Meenal ki shigo waina nake dafawa dan ke nasan kina son waina".
Juyowa nayi tare da arowa fuskata wani murmushin ƙarya.
"Kun tashi lafiya? to tunda ga gwani nan yana tayaki bari ni naje gurin Baƙir, kuma naji wainar
bata yi dadi ba sai ka sake yinta tunda ba zaka barta tayi ita kaɗai ba", ni dai nasan bazan canja
ba duk yadda naso kar nayi mgn makamciyar hakan sai da nayi tsabar rashin gani a ƙyale.
Dariya yayi harda sauti, "Idan bana kusa ne ma zata yi ta ba dade idan ina kusa kuwa duk
abunda zata yi shi zai fi domin....
" Am ni kam na tafi, "na fada lokacin ma har na kusa barin gurin dan Yaya ba kunya ne da shi
ba dukkan su ma.
Dariya suka yi sosai, su kansu sun san sun sauya to ya zasu yi aka ce idan gaje garin da ka ga
suna yawo da bindi samu igiya kai ma kayi bindin da shi, wannan shi ne cin ribar zama a legos
da mutanen cikin ta.
Dakin Baƙir na dufa wani tanƙamemen daƙi ne yakai nawa abun takaici wannan dan shekara
shiddan ne ke kwana a ciki ko da naje y a tashi hakan yasa nai mishi wanka na shirya shi tsaf
sannan muka fito.
Tana kan cinyarshi yana bata wainar a baki, guntun tsaki naja iya laɓɓa abun takaici a gare ni
dan a gare ni kam mutanen da sun manta su hausawa ne.
Ban iya ko kallon su haka na samu naci wainar abun takaici kuma suna a gaban Vaƙir yaron ma
da alama ya saba da ganin hakan dan ko a jikinshi.Su kuwa wani abun dan ganin ta ne yasa
basu yi.
"Tsiwa Baby ya kamata mu fita dake ganin gari".
"Am kamar wani garin arziƙi me zan gani bayan tsiya".
dariya yayi yana kallon fuskarta ita kuwa kanta na ƙasa gudun kar ta ga wani abun.
"Tsiya ko baki zo ki ga yadda tsarin garin yake da mutanen ciki".
Taɓe baki nayi, " hm Arnan ni me zan gani a gurin arne".
"Ke waya gaya miki wai duk arna ne a garin da musulmi sai da ki ce yare ne".
"To ni me zan gani a gurin yare kuma, ni wllh bayan ku da bazan tava zuwa legos ba".
"Zaki zo mana ina ji a jiki na bayan mu da wani abun alkairin da ya kawoki legos".
Bai jira na kara bude baki ya ce, "Karki cika min baki yau gobe naji kin ce min kin fara son wani
a nan zaki zauna tare da shi kuyi rayuwa", cikin zolaya ya ƙarasa mgnr yana ƴar dariya abunshi.
"Wllh Allah ya kyauta Allah ma ya tsare ni wllh dan ku ne kawai na zo garin nan, duk fadin
duniya na rasa wanda zan so sai dan legos naci baya wllh Allah ya tsare ni ma", na faɗa cikin
tsiwa kamar yadda na saba.
"Kyaleshi kinji auta daman haka yake so ai yaga ya ɓata miki rai, tashi ki shirya mu fita
shoping".
Tashi nayi Bakir na rike a hannun na bar gurin, ba canja kaya zanyi ba kawai mayafi zan dauka
na zaro wani farin gyale cikin kaya na, na dauko flatshoe fari na saka da farar jakata ta rikewa
na fito hayaniyarsu naji a waje hakan yasa na biyo bayan su.
Ya isa na daina mmkn su amma n kasa dainawa yanzu dan Allah a haka zasu fita yadda suke
dai a daki, gida da waje ya zame musu daya kenan.
Kau da kai nayi basu tsaya bi ta kai na ba suka shige cikin motar, shiga baya nayi ni da Baƙir
yaja motar direba ya bude mana wangalelen get ɗin.
Bana da ra'ayin wani kallon gari hakan yasa na maida hankali gurin wasa da Baƙir abu na, ƙarar
saƙo naji ya shigo wayata ban kawo komai a rai na ba na ɗauka na shiga karantarwa.
_Haba MEENAL ya zaki min ruwar ganin fuskarki bana so kuma na shigo cikin gidan,amma ba
komai tunda yanzun gashi zaki fito zai na ganki. daga me ƘAUNAR ki fiye da kowa da komai a
duniya Meenal ki yarda da ni son gaskiya nake yi miki ki amince da soyayyata. Sai mun haɗu
ina fatan dai kin shirya cikin shigar fararen kayan da suka fi yi miki kyau"._
Na duba number na ga an ɓoye tsaki naja me karfi wanda har yasa su Aunty ji na Yaya ne ya
fara cewa, "Lafiya Meenal?" kusan a tare suka haɗa baki da Aunty sadiya.
Wayar na miƙa mu su hankali kwance dan a shirye nake dana ƙara ganinshi sai ya gayamin shi
waye mutun ko aljann, sai na raba alaƙa ta da shi ko shi waye kuwa.........
~Mrsbalarabe~✍
*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_
*Fatima Batula✍*
_Wattpad:mrsbalarabe._
*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_
_5- 6_
_Tnx for d correction *Queen Indo* (Missparrot) baki abun magana ki huta na gaishe kyauta._
✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍
*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶ *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*
*Yadda Annabi, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A gareshi, Yake Kirga Tasbihinsa.*
Daga Abdullahi bn Amr, Allah ya yarda da shi, yace; Na ga Annabi tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi, yana kirga tasbihi da (yatsun) hannun damansa.
*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*
*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*
Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.
_*Bismillahir~rahamanir~rahim*_
Dariya naga sun fashe da ita, "ah lallai wannan masoyin gaske ne MEENAL, ke fa kinyi kamo
Allah yasa ma dan Lagos ɗin ne".
Cike da zolaya yayi maganar.
Shiru Aunty Sadiya tayi tana son fahimtar wani abu, wasu daga cikin kalamanshi abun dubuwa
ne taya to aka yi ya san yanzun zata fito? Saurin kauda zancen tayi dan bata so ta karaya balle
kuma ƙanwar tata.
"MEENAL wannan mutum ne fah amma dai da dukan alama masoyi ne na gaskiya, ya kamata
ne ma ki saurare shi ki ji".
Sai naji na gamsu da abunda Aunty Sadiya ta ce, tabbas hakan ne kuwa. Ɗaga kai nayi alamar
to.
Dan ban kawo komai a rai na ba, na cigaba da wasa da Baƙir abu na.
Bayan mun yi ƴar tafiya naga an tsayar da motor su ne suka fara fita sun wani rike juna kamar
za'a raba su.
"MEENAL ku fito".
Ya faɗa da turanci, har da nayi niyar cewa a'a na tuno idan ban fito ba a ina zan ganshi. fitowa
nayi rike da Baƙir a hannu na.
Gurin yayi kyau, shoprite ne babba, ya ƙawato daman ai ko naƙi Allah bazan kushe kyawun
lagos ba.
Su gaba suka yi abunsu ni kuwa ina baya kadan ni da Baƙir.
Duk sai naga an fara kallo na, na san shigata ce ta jawo hakan, duk da bana son kallo yana
kashe min jiki idan kuma tafiya nake yi naji ina hardewa, amma duk da naji ina hardewan bai
hana ni cigaba da tafiya abu na ba, kallon yayi yawa hakan yasa na fara hardewa dan har saida
naci tintiɓe, da Allah yaban sa'a muka haɗa ido da wani yana kallo na na banka mishi uwar
harara har da murguɗa baki.
Su wato idan mutum ba irin shigarsu yayi ba bai waye ba shi kenan ya zama abun kallo.
Wani guri na hango can ba kowa naja Baƙir dan idan har na cigaba da tafiyar nan faduwa zanyi,
muna zuwa na zauna.
"Kai Allah wadai! Sai mutum yayi shirgarsu ne zai waye tir kuma ni wallahi ba zan taɓa canjawa
ba kun dade baku kalle ni ba," kamar da wani nake yi yadda na bararraje ina sakin faɗa abuna
hankali kwance.
"Shiyasa nake sonki shiyasa nake ƘAUNARki MEENAL".
Rass naji gaba yayi wani irin mugun faduwa taya zan iya mantawa da wannan muryar ɗago kai
na nayi domin kallonshi naƙara tabbatarwa ido cikin ido muka yi wanda hakan ya ƙara faɗarmin
da gaba. Murmushi ya sakarmin ya zauna akan kujerar da ke fuskarta ta.
Rintse ido nayi, "Ya isa haka dole na fuskance shi ko shi waye".
"MEENAL ina ƘAUNAR ki MEENAL komai naki burgeni yake yi".
"Kai waye? meye matsalarka da ni, Meyasa kake son ka tsoro ni?? Malam bari ka ji ni
MEENAL magana ɗaya nake yi ba biyu ba bana ƘAUNARka kuma bazan taɓa ƘAUNAR ka ba,
dan haka kabar wahalar da kanka bana son na ƙara ganin fuskarka, idan ba haka ba zaka sha