Showing 30001 words to 33000 words out of 42034 words

Chapter 11 - KAUNAR BOYE BY MRS BALARABE.pdf

24 Jun 2025

1955

tare da nace komai ba.

“Wannan ya zamo miki na k’arshe da zakiyi waya a cikin office d’ina, Infact bana ma son na
k’ara ganin kin shigo office d’in nan da waya okey?”.

Da sauri nace;

“Okay Sir”.

“You can go”.

Ya fad’a yana juyarda kujerar sa ya bani baya murmushi d’auke a fuskar sa,nikuwa miqewa nayi
na sakar mishi gwalo aikuwa lokacin ya juyo ya kamani ina masa gwalo,zaro ido yayi cike da
mamaki yayinda nayi saurin ficewa daga office d’in ina k’yalk’yala dariya na shige office d’ina.


Shima Sir Daniel dariya yayi sosai wacce bai sa ran ya tab’a yin irinta a rayuwar sa.

“She’s so funny”.

Ya fad’a yana jin wani farin ciki na ratsa shi,saitin zuciyar sa ya dafe yana fad’in,

“I’m in love with this idiot”.



Wasu yawu masu k’arfi Pa ta had’iye tana bin bayan Meenal da kallo,

“Is he the one that makes this idiot laugh,no no this will never happen,i know how Sir Daniel
hate muslim,so what make her laugh?,i wan’t know”.

Tana gama fad’in haka ta nufi Office d’in Meenal.



*Idan naji ruwan comments zanyi wani page anjima*�








*#Comments*
*#Share*
*#Vote and like*




~Mrsbalarabe✍️~





*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._

*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8




*Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun so
ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin matsayinki a
gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy ya baki miji na
gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_25-26_


https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ

*DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*



*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.








Na duk’ufa sosai ina aiki a laptop ina shigar da wasu bayanai,naji an turo k’ofar office d’in an
shigo ba tare da sallama ba,dayake na ba k’ofar baya shiyasa banga wanda ya shigo
d’inba,sharewa nayi na cigaba da aikina don sonake in kammala shi a yau d’innan,duk da kuwa
shigomin Office da akayi babu sallama ya batan rai.

“Hey Muslim girl, Excuse me”.

Tiny ta fad’a tana tsaye daga bakin k’ofar.

Banjuyo ba saida na karasa shigar da wani guntun bayani sannan na juyo ina kallonta,tamke
fuska nayi kamar an aikomin da sak’on mutuwa nace;

“What brought you here?,What do you want?”.

Yarfe hannayenta tayi tana tab’e bakinta mai kama da na aladu tace;

“Nothing,I just wanted to ask you some questions”.

“Which questions?,do you have any business with me?”.

Na fad’a ina b’alla mata harara.

“Menene ya sanya ki dariya lokacin da kika fito office d’in Sir Daniel?”.

Tiny ta fad’a tana cire glass d’in dake fuskarta,mamaki taban sosai don har nayi niyya zan
mayar mata da maganar da zata iya sanyata kuka sai kuma na saki wani murmushi don dama
ina lure da take-takenta tin ranar da tasan nice Secretary d’in Sir Daniel take min wani
matsiyacin kallo, hakan ya tabbatar min da sonshi take ba ko shakka.
Juyi nayi akan kujerata kamar yanda naga Sir Daniel yayi nace;

“Do you want to know what make me laugh that time?”.

Na k’arashe maganar ina juyowa saitin da take na zuba mata idanuna,cikin sauri ta gyad’a kai
tace;

“Yes”.

Gira na d’age mata,tare da nuna mata kujera ina fad’in,

“Okey well,have a seat”.

Ba musu ta zauna cike da zumud’in son jin abinda ya sanyani dariya.

Miqewa nayi daga kan kujerar na nufo inda take zaune,fuskata d’auke da shu’umin murmushi
nace;

“Can you believe that?”.

“What?”.

Ta fad’a tana min wani kallo marar ma’ana.

“Can you believe Sir Daniel falls in love with me?,So that’s what makes me laugh”.

Wata mahaukaciyar dariya Tiny ta saki tana nunani da yatsa tace;

“You are lier,Do you know how Sir Daniel hates your ditty religion?,he’s..”.

“Shut up!!!,and Watch your words”.

Na daka mata wata tsawa mai firgitarwa wadda tasa Tiny yin shiru ba shiri.

“This should be the last time da zaki fad’i wata banzar kalma gameda da addinina,I don’t care If
you believe or not,you can leave my Office”.

Na fad’a ina komawa kan kujerata na zauna,raina fess don nasan yau bacci ma sai ya
gagareta.

Miqewa Tiny tayi da sauri ta fice daga office d’in,nikuwa na saki wats shak’iyiyar dariya,bag d’ita
na bud’e na feffesa turare a office d’in don wani irin warinta naji ya mamaye office d’in,Kai Allah
ya shiryeni ni Meenal, duk banji warin ba saida ta fice daga office d’in lol.

cigaba nayi da aikin da nake a laptop d’in,ban tashi ba sai k’arfe d’aya naje nayo alwala na
gabatar da sallar azahar.

Wani k’ugi naji cikina yayi alamar ina jin yinwa,da sauri na fice daga office d’in na nufi hanyar da
zata kaini Office d’in Anty Sadiya.

Dakatar da aikin da take yi tayi ta d’ago ta kalleni Fuskarta d’auke da murmushi tace;

“Harkin kammala aikin naki kenan?”.

“Wallahi Anty yunwa nakeji,zan d’an fita nasai ko Fresh yo nasamu nasha”.

“Okay,amma kije ki d’au Excuse wurin Boss don bakida ikon fita saida izininsa”.

Da sauri na zaro ido nace;

“Kai!,Yunwa fa nace miki ina ji,ai ba wani gu zanje ba nasan ko shi dole idan yaji yinwa ya fito
neman abinda zaisama cikinsa”.

Girgiza kai tayi tana fad’in,

“Nasan da haka Meenal,bana son ku k’ara samun wata matsala ke da Sir Daniel,please kiyi
yanda nace kinji my sis”.

Harga Allah raina baiso ba,amma ganin yanda Anty Sadiya ta dage yasa ni fad’in,

“Shikenan,bara naje”.

“Okey,ki dawo lafiya”.

Harna kai bakin k’ofa na juyo nace;

“To ke Anty me kike so na siyo miki?”.

“Bana jin yunwa Meenal,kema nasan don kawai bakiyi wani karin kirki bane yasaki jin yinwa da
wuri haka”.

Ban tsaya jin k’arshen zancen ta ba na fice daga Office d’in kamar in fasa ihu nakeji,wai d’an
fitar ma da zakayi saika nemi izinin wani shirgegen Arne,mushiriki,ina gunguni a raina har na iso
k’ofar Office d’in nasa,tsaye nayi abunda ya faru a tsakanin mu d’azun ya dawo min a kai.

“yanzu fa idan na shiga zai iya zabga min mari”.

Na fad’a a raina.

“Hmm wallahi bazata sab’u ba,ina wannan daa ne yanzu kam saidai mu kwashi ‘yan kallo
bazan yarda lafcecen arne yana zabgamin mari a banza da wofi ba”.

Na k’arashe maganar ina d’aure gele na a qugu na don yau na d’au alwashin duk ya bugeni
wallahi saina rama,da wannan tinanin na fara nock d’in k’ofar Office d’in.

Shiru banji alamar yama san ina wurin ba,a hankali na murd’a k’ofar na tura kaina kad’an don
ganin ko baya cikin Office d’in ne,fincikoni akayi da k’arfin tsiya wanda zan iya rantsewa da
Allah banji hannun mutum a jikina ba saidai na ganni zaune a tsakar Office d’in, kalle-kalle na
fara banga kowa ba,take naji hanjin cikina sun hargitse,ba b’ata lokaci na fara jero addu’oin tsari
a raina.


K’amshin turaren d’azun da safene naji gaf da hancina,da sauri na k’ara kallon ko ina na d’akin
babu kowa a ciki bakajin komai sai k’arar Ac.

“Meenal dagaske zaki iya dambe da masoyin ki?”.

Na jiyo sautin muryar da dukkanin wani sashe na jikina ya gama haddaceta.

Miqewa nayi da sauri,ina fad’in,

“Meye zaka wani b’oye kanka,ka fito idan ba tsoroba,na rantse da girman Allah duk ka tab’ani
sai na baka mamaki”.

Sir Daniel da ya fito daga Toilet tsaye yayi yana kallonta,dawa take magana?,ya tambayi kansa
yana cigaba da kallon yanda tayi d’amara,dayake ta bashi bayane shiyasa bata ganshi
ba,takowa yayi zuwa gareta a hankali ya d’ora hannunsa a kafad’arta yace;

“Hey..”.

Juyowa tayi ta daka wani uban tsalle tare da zabga mishi wani lafiyayyen mari a kunci, tana
fad’in,

“Me na fad’a maka?,wallahi yau koni ko kai a Office d’innan”.

Ta k’arashe maganar tana ja da baya,hannuwanta dunk’ule tana shirin kai masa bugu.

Mamaki da al’ajabi suka taru suka cika Sir Daniel ya dafe kuncin da ta maresa yana kallon
ta,anya wannan yarinyar tanada hankali?ni zata mara?,tambayoyin da yake ma kansa kenan.


“Zakiyi nadamar wannan marin Meenal”.

Naji saukar muryarsa a gefena,kallon Sir Daniel nayi naga yana nan tsaye a inda yake har
lokacin hannunsa dafe da kuncinsa,sannan na juyo na kalli gefen da naji saukar maganar shi,
Tsaye na ganshi cikin shiga irinta jikin Sir Daniel ranshi a matuk’ar b’ace wanda ganinsa cikin
wannan yanayin ba k’aramin razanani yayi ba,sake kallon Sir Daniel nayi still yana nan yanda yake,iya rud’ewa nayita wacce bansan
yanda zan misiltata ba.

“Meke shirin faruwa dani ni Meenal?”.

Wani irin jiri naji ya d’ebeni Shuuu na zube a k’asa sumamma ban k’ara sanin inda nake ba
kuma.

Da mugun sauri Sir Daniel ya
nufota, hankalinsa tashe yana mamakin abinda ke damun wannan yarinyar,bai tsaya b’ata
lokaci ba ya sunkuceta yayi waje da sauri,ta Elavetor d’insa ya shiga ta saukesu a chan k’asan
ma’aikatar, ganin yanda Ya fito d’auke da Meenal ya sanya ma’aikatan nufosa suna tambayar
lafiya? babu wanda ya kula a cikinsu ya sanyata a motar shi ya shiga yaja motar ya fice daga
ma’aikatar a tamanin,Bayansa Security’s d’insa suka bi,yayinda duk jama’ar ma’aikatar sukayi
cirko-cirko suna mamakin abinda ke faruwa?,inda akaita cecekuce har labari ya kaima Anty
Sadiya.

A rud’e ta shige motar ta tabi bayan su Sir Daniel duk da ko alamar motarsa bata gani ba,haka
ta yanki tikiti tabi hanyar da zuciyarta ke bata a chan ya nufa.









*#Comments*
*#Share*
*#Vote and like*

~Mrsbalarabe✍️~





*ƘAUNAR ƁOYE!!!*
_(THE SECRET LOVE!)_



*Fatima Batula✍*

_Wattpad:mrsbalarabe._

*Telegram*
https://t.me/joinchat/GxqDXvsOyg0Xr4s8




* Dedicated to my Anup(my happines) Allah ne kawai yasan irin son da nake yi miki, ke abun
so ce dole duk wanda ya raɓeki ya soki, baki na bashi da kalaman godiya da nuna irin
matsayinki a gurina sai dai kawai na ce ke ta musamman ce a cikin rayuwa ta, Allah yabaki lfy
ya baki miji na gari. Amin thumma Amin.*
_Page_

_27-28_

*HAPPY BELATED BIRTHDAY MUHAMMAD KHAREEMWISHING YOU LONG
LIFE AND PROSPERITY,MORE MONEY IN YOUR ACCOUNT AND MATA TA GARI I
PRAY*


✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

*w̶̶є αr̶̶є вєαr̶̶єr̶̶'s̶̶ σf̶̶ s̶̶σ  g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶*
*w̶̶є w̶̶r̶̶ít̶̶є αs̶̶s̶̶íd̶̶íσu̶̶s̶̶l̶̶ч p̶̶єr̶̶c̶̶єív̶̶є n̶̶σ p̶̶αín̶̶,*
*s̶̶σ m̶̶αg̶̶íc̶̶αl̶̶ σu̶̶r̶̶ c̶̶r̶̶єαt̶̶ív̶̶є g̶̶σl̶̶d̶̶єn̶̶ p̶̶єn̶̶* ✍ *,вєh̶̶σl̶̶d̶̶ σu̶̶r̶̶ w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶.α p̶̶r̶̶σd̶̶u̶̶c̶̶t̶̶ σf̶̶ σu̶̶r̶̶ p̶̶єn̶*̶  *,s̶̶αv̶̶σu̶̶r̶̶ σu̶̶r̶̶
w̶̶σr̶̶d̶̶s̶̶, f̶̶σr̶̶ ít̶̶ w̶̶íl̶̶l̶̶* *c̶̶αu̶̶s̶̶є чσu̶̶ n̶̶σ p̶̶αín̶̶.*

*INA MASOYAN LITATTAFAN ƘUNGIYAR GOLDEN PEN?*

*NESA TA ZO KUSA, TUNANIN RASHIN SAMUN NEXT PAGE YA ƘARE!.*

Kasance mutum na farko da zai fara karanta sabbin littattafan marubutan mu, a duk lokacin da
muka yi typing. Kina/Kana iya samu, ta wannan damar ce kawai idan ka bi wannan links tare
danna *LIKE* a shafin mu na Facebook zaka/zaki iya samun cigaba ko kuma ki samu duk
littafin da kike buƙata namu daga farko.
https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Sai kun zo, kar ku manta a koda yaushe comments da sharhin ku yana ƙara mana ƙarfin gwiwa
a wajen rubutu mai yawa.





Wata tsadaddar Hospital Sir Daniel ya kai Meenal,yayin da Likitocin asibitin suka shiga
tambayar abinda ya sameta amma ina bai rabasu da kalma d’aya ba,da yaga ma zasu raina
mishi wayo su kuma b’ata mashi lokaci ya shaqo wuyan wani babban likita ya hau kifa masa
mari cike da b’acin rai,dak’yar aka kwaceshi suka hau ba Sir Daniel hak’uri,inda nan take aka
shiga bata taimakon gaugawa.

Tare dashi aka shiga d’akin da aka kaita,sam ya kasa zama sai kai kawo yake yana tinanin
meke damun wannan yarinyar haka?,ga baki d’aya ya rasa duk wani sukuni nashi,wayarsa ce
ta fara qara dak’yar ya iya cirota cikin aljihu,sunan Mom ya gani,ficewa yayi waje sannan ya
d’aga wayar yana k’ok’arin saita muryarshi don baya son ta fahimci yanayin da yake ciki.
“Hey Mom”.

Ya fad’a cikin muryar nan tashi mai kama da an mishi dole.

“Where are you”.

D’an sosa kai yayi yace;

“Ina Office Mom,meya faru?”.

“Jikina be bani kana Office ba Son,Please kana ina?”.

“Mom meyasa zan miki qarya?,Ina Office”.

Ajiyar Numfashi ta sauke tana fad’in,

“Shikenan,zanzo ma’aikatar don in tabbatar”.

Daga haka ta katse wayar,Sam shi bema da damu da zuwan da tace zatayi ba,ya komawarsa
d’akin da Meenal take kwance,har lokacin bata farfad’o ba.


Dak’yar Anty Sadiya ta gano Asibitin da ya kai Meenal d’in,koda ta iso bakin get d’in cike yake
da matsara wanda hakan ze tabbatar maka da akwai wani hamshaqi a cikin Asibitin,fitowa tayi
daga motar ta don batama ga fuskar tunkaraso da mota ba,neman izinin shiga asibitin tayi
amma fafur suka k’i barinta,daga k’arshe suka ce saita nuna musu ID card d’inta sannan zasu
bari ta shiga,da sauri ta koma mota ta d’auko ta nuna musu sai a lokacin suka bata izinin
shiga,sauri-sauri gudu-gudu take had’awa sai kuka take zuciyarta na zafi, bata sha wahala ba ta
gano d’akin da Meenal d’in take,daidai lokacin Sir Daniel ya fito shida wani Doctor suna tafe
yana ma Sir Daniel bayani akan sufa basuga wani abun dake damunta ba,hasalima lafiyarta lau
batada wani rashin lafiya.

D’agowar da zaiyi suka had’a ido da Anty Sadiya da keyi mashi wani mugun kallo,duk danniyar
da take ma zuciyarta amma ina hakan yacitura saida ta tako gaban sa tana fad’in,

“Yanzu ma ka k’ara marin nata ko?,To wallahi bari kaji duk hakan yayi sanadin samun matsalar
sister ta sai nayi k’arar ka, kai wane irin mugune?,Azzalumi wanda baisan darajar d’an Adam
ba”.

Wani daga cikin Security’s d’inshi ne ya katsa mata tsawa,yana k’ok’arin jan hannunta ta d’auke
shi da wani lafiyayyen mari tace;

“Karka k’ara kuskuren tab’ani,ni musulma ce kuma matar Aure”.

Security d’aga hannu yayi da nufin zabga mata marora Sir Daniel yayi saurin riqe hannunsa
yace;

“Kar kayi wannan kuskuren,ku b’ace min da gani”.

Jikinsu na rawa suka bar wurin,dubonsa ya maido kan Anty Sadiya kamar bazaiyi magana ba
sai kuma chan yace;

“Idan zaki iya ki biyoni zuwa office d’in likita”.

Da sauri tace;

“Bana buqatar jin komai daga garesa,Ina son ganin Sister na”.

Ta k’arashe maganar tana tinanin wane irin hali Meenal ke ciki,bata da burin da yawuce taga
wane hali Meenal ke ciki.

Sai a lokacin Doctor d’in yayi magana.

“Sorry Madam,amma zuwanki yanada matuk’ar amfani,ki daure muje don kiji abinda zan fad’a”.

Da yake Anty Sadiya akwai saukin kai bata k’ara cewa komai ba tabi su zuwa Office d’in.


Zama sukayi akan kujerun office d’in suna kallon likitan da ya fara rubutu a takarda.

Lumshe ido Sir Daniel yayi ya sake bud’e su yace;

“Wannan itace Sister d’inta,zata tsaya anan har lokacin da zata dawo normal”.

“Wai meya faru da ita ne?”.

Anty Sadiya ta fad’a tana tsare shi da idanunta da sukayi jawur.

Gyaran Murya Doctor d’in yayi yace;

“Babu abinda ya faru da ita Madam illa shock da ta samu akan wani abun da tagani,Sakamakon
binciken da mukai mata ya bada hakan,so amma yanzu dai mun yi iyakar yin mu mun gano
lafiyarta qalau babu abinda ke damunta,ko wane lokaci muna sa ran zata iya farfad’owa”.


Sai a lokacin hankalin Anty Sadiya ya d’an kwanta,ta sauke ajiyar zuciya tace;

“Nagode Doctor,amma zan iya ganin ta yanzu?,hankali na bazai tab’a kwanciya ba idan banga
Meenal ba”.

“Eh zaki iya ganinta”.

Ya k’arashe maganar yana mik’o mata wani green card yace;

“Ki nuna wannan za’a baki damar shiga d’akin”.

Da Sauri Anty ta karba ta mik’e tare da fad’in,

“Thanks You”.

Sannan ta fice daga d’akin,inda tabar Sir Daniel zaune suna cigaba da magana da Doctor d’in.


Koda ta shigo d’akin kwance ta hango Meenal idanunta a lumshe,da sauri ta k’araso wurin ta
tana kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login