Showing 3001 words to 6000 words out of 44631 words
Chapter 2 - KUNDIN QADDARA BOOK COMPLETE By MJay.pdf
abinci, faysal inka gama kaje gidansu taybah ka dauko mun
iyayyenta".
"Toh dad".
Ya riga kowa barin dining din sannan yayi gaba, taybah ta bishi da kallo admiring his outfit.
Yana sanye cikin shadda fara ras data sha aiki ash colour, yasa hula ash colour and a black
swatch.
O Allahna!, ta fada a ranta holding her breathe, what the hell is wrong with her?.
Sun gama breakfast suka zauna a nan main parlor suna jiran faysal su qaraso.
Can sai kawai suka tsinkayo sallamar faysal abbu na biye dashi sannan mammy dasu
yasmeen.
Kana ganin mammy kasan hankalinta ba'a kwance yake ba.
Tana dago kai suka hada ido da alhaji usman.
Cak ta tsaya ko motsi ta kasa yi. Ta saje murxa ido tana kallon alhaji usman har yanxu.
Cikun karfin hali ya furta....
"Ya usman, kaine kuwa"?
*©Mss Mjay*
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY❤*
In dedication to
*sembyy luff*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*06*
"Ya usman"!
Mammy ta sake furtawa a firgice tare da fashewa da wani kuka mai ban tausayi.
"Ya isa samyrah, ba kuka zakayi ba, yanxu duk ku zauna muyi magana" cewar Alhaji usman.
Duk suka zauna, an dauki kusan 20mins ba wanda ya iya cewa komai.
Alhaji usman ne yayi qarfin halin fara magana
"Nayi nadama safiya, nayi nadaman abunda ya faru shekarun baya, kiyi hakuri"
Ya juya ya dubi su faysal da suka zubamai idanu suna kallo kawai.
Murmushi kawai yayi sannan yace "nasan kun matsu kuji abunda ya faru....yanxu kuwa zan
fada muku"
*26yrs back*
"Asalin mu yan garin kaduna ne, a anguwan kanawa. Mahaifinmu riqaqqen malami ne, amma
hakan bai hanashi samu makarantar boko ba. Daga ni sai samyrah Allah ya mallaka musu.
Mahaifiyar mu inna tayi qoqari wurin bamu tarbiyya mai kyau har muka girma.
Bana taba mantawa,lokacin ina university of jos(uj)....na gama 200lvl nazo hutu gida na samu
malam kwance baida lfya. Babu yadda banyi dashi ba akan mi kaishi asibiti yaqi sai umurni
daya bani na inje gidan limamin anguwan mu a daura mana aure da yarshi....shine kawai
abunda yake buqata.
Haka na tafi bawai dan na santa ba kona taba ganin ta...a'a sai dan inma mahaifina biyayya.
Aka daura mana aure da karymah ta tare a wani dan bangare na gidan.
Haka nayi hutuna malam baida lfya. Na koma da sati daya rasuwar malam tazo mun.
Nayi kuka,nayi kuka amma bashi zai dawo da malam ba.a lokacin samyrah ta gama junior
secondary school amma bataci gaba ba.
A kwana a tashi harna gama karatuna na kuma samu aiki saina dauki karymah muka koma
jos....ba yadda banyi da inna akan tazo muje tare taqi.saina barta tare da samyrah a lokacin
tana shekarar tabta karshe a secondaru school.
Inada ya daya lokacin wato rufaida wadda a halin yanxu tana aure a abuja.
Shekarata biyu da komawa jos inna ta rasu. Sai na dawo da samyrah gidana nan jos muka
zauna.
Kwatsam saiga kabir yaxo, dane ga yayan babanmu wai yazo neman aure samyrah, ba yadda
banyi da ita ba akan karta aureshi tace ita shi take so.naji haushi a lolacin faysal nada shekara
daya da yan watanni.
Naji haushi nacema samyrah babu ni babu ita domin kabir baida mutunci ita kuma ta dage.
Hakan kuma bai hanani mata kayan daki ba suka zauna a kaduna a anguwan rimi, na bata
jarin kudi tareda wasika nayi gaba.tun daga ranar ban qara waiwaiyar rayuwarta ba, a cewata
tunda ta batamun rai babu ni babu ita.
Takardar dana bata ita na tsinta ranar dana kade taybah. Ta haka harna gano inda kuke.
Kiyi hakuri samyrah, ki yafewa wannan yaya naki kuskuren shi".
Alhaji usman ya qarasa bada labarin yana kuka.
Falon yayi shiru bakajin motsin komai Sai kukan alhaji usman da samyrah.
"Yaya kayi hakuri...naga kaddara iri iri bayan rabuwar mu....amma na godema Allah daya sake
hada fuskokin mu".
Shidai malam kamal yayi mudus, ya kasa cewa komai.
"Toh kamal, so nake ka barmun taybah a hannuna, zan riqeta". Cewar alhaji usman.
"T..tt..toh ba komai yaya, yanda kace haka za'ayi". Malam kamal ya amsa.
Faysal kuma haushi yaji, shi dad dinnan ya rasa wadda zaice a bashi sai baqar yarinyar nan.
Taybah ma tunanin ta kenan, yanxu shyknn ya faysal zan dinga ganinshi kullum.
Tana cikin tunanin ne ta tsinkayo muryar dad yana tambayar ta aji nawa take a school
"Ss3 abbah, saura sati biyu mu fara waec" .
Ta amsa shi a nutse.
"Toh shyknn, in kin hama exams sai faysal ya kaiki abuja wurin rufaida kusan juna koh".cewar
alhaji usman.
Aka watse taro lfya su mammy suka tafi gida bayan sunyi lunch a gidan.
*8:04pm*
Taybah ta fito daga kitchen cikin sauri tana jera abinci a kai, ta sake komawa ta dauko 5-in one
friut juice datayi.
Sannan ta haura sama cikin sauri tayi wanka tareda sake wata red arabian gown da ammi ta
bata daxu. Rigar me robace gashi tabi jikinta tayi das.
Bata shafa komai a fuskanta ba sai kawai tayi rolling kanta da baqin gyale, ta fesa arabian pef
dinta"oud al-abha" sannan ta fito.
Tana saukowa falon ta hadu da faysal shida abokin shi a azaune suna hira, dad da ammi
kuma na dining a zaune suna jiransu.
Gani tayi kaman ya faysal ya qara kyau, looking soo muah cikin wani black wando da white top
wadda ta fito mai da shape din chest dinshi.....(woo koni na fola balle maman nawal).
Taybah shagala kawai tayi da kallon shi ba tare data lura shima kallon nata yake ba.
Ba make-up ne a fuskan ta tayi kyau haka??tabb!!! Yayi maganar a cikin ranshi.
Sai tsinkayo muryar abokinshi yayi yana cewa "abokin who's this charming damsel?? Dan Allah
in yar uwarka ce ka bani ita". Ya fada witjout taking his eyes off her.
Faysal bai samu damar ansawa ba yaji dad na cewa "kuzo muci abincin mana".
Taybah tayi saurin wucewa ta barsu a gurin tare da kara rikita suda kamshin pef
nata.
*©Mss Mjay*
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY❤*
In dedication to
*Sembyy luff*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*07*
Taybah ta qarasa dining din tare da gaida dad da ammi, sannan ta fara serving dinsu.
"Faysal, kuzo muyi dinner mana". Cewar ammi ganin basuda niyyar miqewa.
"Barshi kawai ammi, anjima zanci yanxu zamu dan fita ne". Faysal ya fada tareda miqewa.
"Jira yaruwarka ta gama cin abinci kuje can gidan ta dauko uniform dinta and wasu abubuwa
da take buqata". Dad ya fada ba tare daya dago kai daga cin abincin shi ba.
Kafin faysal yace komai ummu talkative(kaman hafsy) tayi saurin magana "Dad nima zan bisu".
Ta fada tareda barin dining din gaba daya ta koma wurin faysal wai karsu gudu su barta.
*Monday....7:16am*
Taybah na hango tana saukowa da sauri cikin shirinta na makaranta. Wando baqi tare da farar
riga da farin hijab dinta tayi das.
Ta tarar da ammi a dining tana jera breakfast din da taybah tayi.
"Yi maza ki karya kafin yayanki ya fito....daddynku ya riga ya fadamai shi zai dinga kaiki
makaranta". Ammi tafada tana serving dinta itada ummu.
"Ai wallahi nima ya ne zai dinga kaini". Ummu ta fada tana turo baki.
Taybah tayi murmushi kawai batare data ce komai ba. Kanta a duke a kasa taji wani irin kamshi
ya ratso falon.
Da takalman shi ta fara cin karo yana saukowa daga steps cikin sauri.
Tana dago kai ta sauke idanunta fes suka sauka a kanshi. yana sanye cikin suit baqi ta red
shirt a ciki...ga turtle neck tie dinshi.(awwwnnn....he's just soo handsome harna fola❣)
Ya qaraso dining din tareda aje briefcase dinshi a gefen shi sannan ya zauna. Taybah ta gaida
shi tareda miqewa dan tayi serving dinshi.
"Kin gama kallon nawa kenan" ya fada absent mindly.
Ummu tayi caraf tace "Laaa ya faysal, kaima fa ina kallonka lokacin da kaketa kallon ta. Aunty
rufaida ma kafin ta auri ya bello haka suke kallon nan shine dad ya musu aure, kuma aure za'a
muku kenan koh yaya?.
Sake baki kawai sukayi suna kallon ummu, faysal ne yayi saurin shan toka tareda cewa
"Come on swthrt, yaushe kika ga ina kallonta, bakiga na fita kyau bane shiyasa take kallona?"
Ya fada yana murmushi.
"Malamin islamiyyan mu yace bakyau qarya fa, kuma gashi kayi qarya ya faysal. Naga lokacin
da kake kallonta fa. Kuma nikam wallahi Adda taybah ta fika kyau".
Taybah tace "ya isa cute sisterna, ci abincinki mu yafi school kar muyi latti koh".
Faysal ya dago ua harareta, ita kuma tamai tongue out tare dama ummu murmushi.
Su oga faysal a kiyayi aunty ummu.
*kuyi hakuri da wannan,am very busy ne yau. Love ya all from the beginning to the end of
seven seas❤*
*©Mss Mjay*
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*08*
Faysal ba gama breakfast dinshi ya tashi yayi waje tareda fadin
"Duk wadda bata fito ba tafiyata zanyi".
Ta sauri taybah ta aje spoon dinta tareda miqewa tsaye taja hannun ummu sukayi waje, koda
suka fita harya tada motar shi.
Cikin sauri taybah ta qarasa tareda shiga bayan motan bayan ta budema ummu gaban motan.
Suna isa bakin gate ta hango hafsah a tsaye, daga gani cikin damuwa da fargaba take kar
taybah taqi xuwa.
Ta yunkura da nufin bude motar ta fita tajita a kulle. Batare daya kalleta ba taga ya miqo mata
200 naira sannan ya cire jam lock din.
Tamai godiya sannan ta fita ta tafi. Da sauri ta qarasa wurin hafsah tareda rungumeta......"i
missed you soo much yaruwa....a whole lot much".
"I missed you more hun, jiya da yamma naje gida yasmeen take cemun wai kin koma gidan
uncle dinku, dagaske take ko wasa? Dan yasmeen ta raina ni wata rana". Hafsah ta qarasa
maganar tana kallon taybah.
"Ki wuce mu tafi abeg, in kin fara surutu ba comma ba full stop. Am gonna gist you later about
everything". Taybah ta fada tana jan hannun hafsah suka qarasa cikin school din.
*3 months later*
Su taybah har sunyi waec dinsu sun gama. Sai jiran results.
Satinsu biyu da gama exams dad ya shirya musu tafiya abuja, tare da umartar faysal akan shi
zai kaisu.
Ana sauran kwana uku dad ya bata sabuwar waya dal a kwali "iphone 6".
"Nagode dad, Allah ya saka da alkhairi ya qara budi". Taybah ta fada tana sunkuyar da kanta
kasa.
"Bakomai daughter, anjima yayanku zai kaiki kima mammynki sallama ko". Dad ya fada.
Faysal yayi caraf yace "Dad, inada uziri fa, su usman suna jirana, kasa driver ya kaita kawai".
Yanayi yana kawar da fuska dan karsu hada ido da taybah.
"Dad nima zan rakata, kuma gaskiya ya faysal ne zai kaimu". Cewar ummu tana tsalle.
"Dolen shi aii princesses, kyale shi kawai" cewar dad.
Sannan ya juya ya dubi faysal yace
"Ka tashi kaje ka shirya kaxo ka kaisu, daga nan ka kai taybah shopping tayi siyyaya kuma a
matsayinka na babba kai zaka mata siyyayar".
Faysal ya dogo kai, karap suka hada ido da taybah ta mishi gwalo tare da juya kanta gefe.
Ammi dai na zaune tana murmushi ba tare data ce komai.
Faysal haushi ya cika shi cikin ranshi yana cewa......"Am gonna deal with this girl. Dammit, i
hate you taybah".
(Kut!!, kuji malam faysal dai abeg).
*Afuwan sisters, am very busy this dayz.....kuyi hakuri......i love you all.
*Team taybah lovers*
*©Mss Mjay*
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY luff*
*09*
Taybah ta fito cikin shirin wata green and baby pink atampa, an mata riga da skirt.
Tayi using baby pink gyale sai yar pos din data sa wayan ta(hhh...su taybah anyi waya).
Tana cikin saukowa qasa ta hango ya faysal an dauki wanka, tsayawa kawai taybah tayi tana
admiring dinshi.....unknown to her shima admiring nata yake.
"Laa ya, kaima kana kallon yadda aunty tayi kyau koh". Cewar ummu da babu wanda ya lura
da tsayuwarta a gurin sai tsinkayo zazzakar muryarta da sukayi.
Da sauri faysal ya kawar da kanshi tareda jan tsaki.
"_wannan bakin naki ko princess....hmmmmn"
Yayi gaba kawai batare daya qara cewa komai ba.
Ajiyan zuciya taybah tayi sannan ta qarasa saukowa daga stairs din ta qaraso gaban ummu ta
durkusa tareda cewa,
"Princess kinyi kyau....."
Ummu ta bata rai ta juya fuskanta sannan tace
"Bawani nan aunty kin fini kyau aii, gashi yaa harda kallonki ya tsaya yi. Amma ni ko kallona
baiyi ba balle yace nayi kyau".......ta fada muryarta na rawa alamun tanaso tayi kuka.
"Come here princess"
Suks tsinkayo muryar faysal kamn daga dama yana ambata.
"Kinfi kowa kyau princess, who told you wancan abun ta fiki kyau, you are soo beautiful
especially when you give me that big smile of yours"..........Ai nan da nan ummu ta washe her 36
jin ance tafi taybah kyau.
"Now give me five". Ji kake tasssss an kashe hannu.
"Toh oya wuce mu tafi". Ya fada yana jan hannunta ita kuma ta yafito taybah da tayi tsaye
kawai tana kallon su.
Kuyi sorry...... School a kwana thats why.love you all❤
*©MSS MJAY*
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
in dedication to
*SEMBYY LUFF*
*09*
Cikin nitsuwa yake tuqin har suka qaraso kofar gidansu taybah.
Ta bude kofa a nutse ta fito sannan ta juya tana cema ummu
"Princess mu tafi ko".
A nutse take tafiya yayin da faysal ya bita da kallo harta kule.
Tana shiga ta samu mammy dasu yasmeen a zaune, ai nan da nan suka ruga da gudu suka
rungume ta.
Salimah auta ta dubi yayar tata tace "adda taybah, kinga yadda kikayi kyai, nima ki tafi dani
gidan uncle usman inyi kyau irin naki".
Tana fada tana taba kayan yayar tata. Taybah taji kwalla ta taru a idon ta, kafin ta samu damar
cewa komai ummu tace....
"Aunty taybah yaya fa yana waje.
Sai a lokacin ta tuna tare sukazo.
Mammy ta dubeta sannan tace "dama tare kuka zo kika barshi a wàje? Wannan ai sakarci ne
taybah. Kinga yi sauri kije ki shigo dashi yasmeen".
Yasmeen ta fita da sauri, cikin lokaci qanqani suka shigo tare.
Faysal ya durkusa a gaban mammy sannan ya gaishe ta.
"Ya kuka baro su yaya? Cewar mammy cikin kulawa.
"Lfya qlw mammy,sunce a gaida ku dakyau" Ya juya ya dubi taybah dake hira da yanuwanta
cikin farin ciki sai dariya take.
"Sister, bari inje in dawo sai muje shopping din ko?.....before then i guess kun gama sallama".
"Ea yaya, saika dawo". Taybah ta fada cikin murna, zata je taga hafsah kenan ta nuna mata
sabuwar wayarta ta kuma mata sallama.
Faysal ya ajema mammy rafar 500 tareda mata sallama ya tafi.
Taybah ta juyo cikin kulawa ta dubi mammy tana tambayarta....."Mammy, akwai improvement a
halayyar baba kuwa?".
"Taybah, addu'a kawai zaku taya mahaifinku da ita, Allah ya ganar dashi gaskiya. A bar
maganan kawai kinji.
"Toh mammy, Allah ya kyauta. Dama dad yace inzo in muku sallama, jibi zan tafi Abuja wurin
aunty rufaida in mata hutu kafin results dinmu ya fito".
"Ma shaa Allah, Allah ya nuna mana. A jamb dinki wacce university kika cika?"....cewar
mammy
"University of abuja dad yace in cika, saj in dinga taya aunty rufaida zama".
Yan uwanta suka taya murna tareda mata fatan alkhairi. Sannan tace ma mammy zataje tama
hafsah sallama.
"Toh kiyi sauri ki dawo amma karya dawo bakya nan".
Itada yasmeen kawai suka tafi, suna tafiya suna hira har suka qarasa gidan nasu hafsah.
Da gudu hafsah ta fito daga daki tareda rungume taybah cikin farin ciki.
"I missed you sis, gashi ke ko yar wayan nan bakida balle mu dinga communicating".
Taybah ta harare ta tareda fadin..."huta damun gori, daxu dad ya dalle ni da sabuwar waya.
Nidai matsa mun in gaida mama tukunna".
Bata baro gidansu hafsah ba saida ta bude mata WhatsApp da facebook, su kadai taybah tace
tana so. Gaba in taji tana ra'ayin wani zata bude. Sukayi exchanging contact sannan taybah ta
tafi suna kewan juna.
Ta koma gida bada