Showing 24001 words to 27000 words out of 44631 words

Chapter 9 - KUNDIN QADDARA BOOK COMPLETE By MJay.pdf

bayanta, sannan kuma tayi applying make-up dinta dan dai-dai. Saleem na
sallama taybah ta miqe da sauri tana cewa....."yaa saleem, sannu da zuwa". Ta fada a hankali
with her sweet voice kamn ana busa sarewa.

"Bari in kawo maka snacks, nasan kila ka fara jin yunwa". Ta fada tareda nufan hanyan kitchen,
yayin da saleem ya bita da kallo cikin tsananin baqin ciki.......Meyasa dad zai mai haka
fisabilikkahi wannan ai tsabar wulaqanci ne, Dan Allah yanzu me taybah ta iya balle ta mishi, shi
dayake son soyayyah, by mere looking ma ba abunda taybah ta iya. Runtse idanunshi saleem
yayi yana tuno happy moment dinsu shida rufaida, how he wish....how he only wish ace har
yanzu tana tareda shi.

Ya bude idanunshi da suka chanja launi daga fari zuwa jajjaye saboda bacin rai. Fes ya sauke
su akan taybah dake nufoshi dauke da tray wanda ta jera samosa da kunun aya a
kai......"Dallah ji wani abu da aka bani wai mata". Ya sake lamenting cikin ranshi. Taybah ta
duqa gabanshi ta ajiye tray din sannan ta fara zuba mai kunun, Saleem wanda zuciyarshi ke
tafasa saboda kallon da kawai yake mata a gabanshi, bai san lokacin da zuciya ta dibeshi ba
harya dauki jug din kunun wanda ta ajiye bayan ta gama zuba mishi ba ya juye mata shi tas a
jiki.

Sheshekar sanyi taybah tayi a dalilin jin kunun mai sanyi ya kwaranya a jikinta, da sauri ta miqe
jikinta na rawa saboda abun ya zomata a bazata, yayin da kowannen su yakema danuwanshi
kallon tsana.

"I hate you taybah! Da kinsan yanda na tsaneki ko kusa da inda nake akace kizo bazaki zoba,
Dammit! Na rasa meyasa su dad suka mun haka, dan Allah ke a tunaninki me zanyi dake? Look
at you...me kikeda shi naso? Babu taybah, you've got nothing dazan soki saboda shi. This will
be the last time dazan gargade ki, karki kuskura ki sake barin in ganki koda ta hanyar da nake
bi bane, kar kisa in aikata wani mumunan abu a kanki, dan yanda nake jinki a raina i can do
anything to hurt you". Saleem ya qarasa maganar jikinshi har tsuma yake saboda bacin rai.

Taybah da tunda ya fara magana take tsaye idanunta cike da tsana tsantsa tana kallon Saleem.
"Saleem kake ko wa? I really don't care, nidai Allah ya qani nayi iyakar kokarina nasan Allah
bazai kamani da haqqin ka ba, yoo aini kila nafi kowa tsanar ka ba a duniyar nan, ce maka
akayi nidin sonka nake balle ka tsaya kana gayamun maganar banza. I've tolerated enough, this
will be the last time zan qara tolerating shits like this, wulakancin ya isa haka malam! Enough of
this bullshits!". Taybah tayi snapping sannan cikin sauri ta juya ta nufi dakinta. Sai a lokacin
hawayen da take boyewa suka samu damar zubowa.....Yaa Ilahii, wannan wace irin rayuwa ce,
mutum kamar an hadashi aure da maciji, aiko macijiya ce ita iyaka tsanar dazai nuna mata knn.

Saleem da tunda taybah ta tafi ya sandare a wurin, yau shi yarinya qarama ta gayama magana

son ranta! A kuwa saita dandani kudarta a gidan nan.

Haka kowannensu ya kwana zuciyarshi ba dadi, washegari da wuya taybah ta tashi tayi chores
dinta saboda tanada lectures, ta kammala aikinta ta hada lafiyayyen breakfast dinta daidai
cikinta sannan ta kwashe tas ta nufi daki, a ranta ta riga da qudiri indai ita zata ba saleem abinci
to lallai ya tabbata cikin yunwa kuwa. 8:15am saleem ya fito daga dakinshi, direct dining ya nufa
saboda wata mahaukaciyar yunwa dayake ji. To his surprise dining din was empty ba komai, me
take nufi? Bata tashi ta hada mai breakfast ba kome?. Yana nan tsaye yana tunani taybah ta fito
daga dakinta. Zaro idanunshi yayi yana kallonta a dalilin hangota da yayi riqe da warmers da
plate, da alama abinci taci kuma ta gama. Wani kallon banza ta watsa mai sannan ta dauke
kanta ta nufi kitchen.

Yana nan tsaye harta fito daga kitchen din ta nufi dakinta ta dauko hijabin ta da handbag dinta.
Still koda ta fito yana nan tsaye a wurin, ganin ta nufi hanyar barin parlorn batare data cemai
komai ba ya sashi saurin shan gabanta sannan yace...."keh, ina breakfast dina?". Ya fada yana
daure fuska tareda yatsina ta kmn yana magana da kashi.
Ita taybah dariya ma yaso ya bata yanda ya wani tsare gidah shi a dole bayason raini. Ai kuwa
saida ta murmusa dan ta kasa riqe dariyar sannan ta dogo kanta itama cikin shan mur
tace..."Au, ana cin abincin wadda aka tsana ne? Malam get out of my sight kaje ka nemo cook
abeg, kona maka kamada chefs ne?". Taybah ta fada turning in circle dan ya kalleta da kyau ya
tabbatar ba kalan kitchen bace.
Wani irin baqin ciki neh ya tasoma Saleem, amma ba qaramin raina shi taybah tayi bah, be
ankara bah yaga tabi ta gefen shi ta wuce bayan ta jamishi dogon tsaki.


Haka ma'auratan suja cigaba da zama da juna, kowa burinshi ya samu abunda zaima
danuwanshi danya kuntata mai. Ita taybah kwata kwata ta daina abinci dashi a gidan, ko a ina
mr.saleem yake cin abinci yanxu oho, sometimes dai koda zata dawo daga lectures zata
sameshi a kitchen yana girki.

Yau saturday wanda yayi daidai da wata uku cif da aurensu, amma har yanxu ba abunda ya
chanja a zamansu. Wuraren 12:03pm wayar taybah dake gefenta tayi qara alamun saqo ya
shigo, koda ta duba sai taga numbern saleem ne...."ki dafa mna abinci, inada baqi bayan
la'asar". Abubda ya rubuta knn, lallai na, taybah tace a ranta, wato yana cikin gidan yazo kawai
ya fada mata neh baze iya ba, lallai kuwa, yau zega abinci.

Tana nan kwance a dakinta taji fitar motarshi, sai wuraren 2:35pn ta gama jera komai a kan
dining din, daki ta nufa ta watsa ruwa sannan ta shirya cikin material ja, tasa baqin hijabinta ta
fita salon abunta

4:42pm motar saleem tayi parking a harabar gidan, su uku ne harda shi, wato saleem, mukhtar

and aminu. With confidence yayi directing dinsu dining din, yayin da mukhtar yake faman kwala
mata kira...."Amarya! Kina ina ne? Ki fito ki tarbi angonki mna".
"Malam, ka zauna kaci abinci abeg, yau qarshen wata nasan ta riga ta tafi salon". Saleem ya
fada yana zama a daya daga cikin kujerun dining din........" Ahh!, kace kai zakayi serving
din......." Maqalewa maganar mukhtar tayi a dalilin arba da abincin da aka aje musu. Saleem da
yayi turus yana kallon warmer din yayi saurin bude dayan warmern dake gefenshi.
Behold! Danyen shinkafa ne a warmern farko da spices harda mangyada. Yayin da dayan kulan
danyen kazane a yayanke a ciki a jera dasu tattasai. Nan da nan naga jikin saleem ya fara rawa
saboda bacin rai.







*©MSS MJAY*
[12/21/2016, 7:29 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG





Written by
*MSS MJAY*




In dedication to
*SEMBYY LUFF*






*34*

Kasa cewa komai saleem yayi, yanabzaune still akan kujerar yana qarema warmers din kallo.
Mukhtar da aminu ma ba'a barsu a baya ba wurin tayashi bin warmers din da kallo.
Yaa rabb!, wannan wane irin wulakanci taybah ta mishi haka? Dafe kanshi yayi wanda ba shiri
yaji ya fara mai ciwo mai tsananin gaske kuwa. Mukhtar dayake yasan yanda lamarin yake
zama yayi kusa dashi tareda dafa shi yayin dashi aminu ya musu sallama kawai ya tafi,
zuciyarsho cike da tambayoyi.
"Aboki, what is the meaning of this? Am very sure wani abu kama yarinyar nan hartayi
disgracing dinka haka...tell me me yake faruwa". Mukhtar ya tambaya cikin sigar lallashi.
"Aboki, you know very well na tsani yarinyar nan, am telling you i hate her to the core man,
yanzu ji irin wulaqancin datamun, ta disgracing dina a gabanku wanda kuma hakan ya qara
assasa wutar tsanar danake mata". Saleem ya fada muryashi muryarshi har choking take
saboda bacin ran dayake ciki. "Cool down man, wannan maganar tsana duk bata taso ba, you guys are married yanxu, bound
to live together forever har ranar da zaku bar duniya in Shaa Allah, all this while i thought kun
rungumi qaddarar data saukan muku kuna zaune lfya, ashe i was wrong, abunda nake tunani
daban abunda kuke aikatawa daban.....why can't you.......". Shiru yayi sakamakon sallamar da
taybah ta doka musu.

Wani lallausan murmushi ta sake musu sbda hango Warmers din a bude, wani dadi taji ya
lullubeta, koba komai yau ta kuntata ma saleem. Karasawa dining din tayi tana wani murmushin
mugunta...."Ahh lallai, kuce harkun gama cin.....". Tasss! Tasss!! Tasss!!! Marin da saleem ya
zuba mata ne har uku yayi dalilin yanke maganar data fara. Mukhtar ne yayi sauri ya riqeshi
ganin yana qoqarin cire belt dinshi ya daketa.
"Ka barni inyi maganin yar iskar yarinyar nan, ni zata kawoma iskanci? I hate her the more ma
yanxu, she disgust me, nikam gaskiya tsakani da Allah su dad sun cuce ni da suka kakaba mun
wannan jarabar".

"Hey! Hold it right there malam, ka mareni kaji dadi koh? Great wait for the consequences i
promise you you'll regret this". Taybah ta fada cikin kuka sannan ta juya da nufin barin parlorn,
mukhtar ne yayi saurin shan gabanta yana cewa.."Taybah wait, tsaya muyi maganah please".
Juyawa yayi yana kallon saleem Wanda har yanxu jikinshi rawa yake...."Man zauna, zoka
zauna, kema madam ki zauna muyi magana in a matured way, wannan fadan da kuke won't
solve anything. Dukkanmu nan mun girma fa". Mukhtar ya fada cikin sigar lallashi.

"Dawa zan zauna muyi maganan? Ba dai wannan abun mai kamada laujen ba, imagine irin
wulakancin datamun yau a gabanku, Aboki tell me abunda zanma yarinyar nan in huce".
Saleem ya fada.

"Ai kadan ma ka gani malam, duk abunda kamun saina rama, yanda ka mareni ranar a gabansu
ka wulaqanta ni haka kaima na maka, and believe you me, expect the worst dan this time
around sai kayi kuka akan abunda zan maka. Inba KADDARA bah, me zanyi dakai fisabilillah,

na tsaneka nima morethan anything I've ever loved!". tana gama fadan haka ta juya da gudu ta
nufi dakinta tana rusa kuka.
Koya suka qare saleem da mukhtar oho! Nidai naga sun fita sun bar gidan



*9:14pm*

"Taybah, me kike cewa haka? Kina nufin mijinki kikama wannan cin mutuncin? Tell me what the
hell has gotten into you!." Hafsah tayi snapping through her phone.

"Ai ina gayamiki kadan ma ya gani in beyi hankalu dani bah, nagaji da daukan wulaqancin
dayake mun, danma dad yana turomun kudi every month dasu nake laluran school ai da
bansan yanda zanyi ba. Ni duk haqqi na da suke kanshi ya sauke ne balle kice ni saina mai, tell
me if you were in my shoes ya zakitu?". Taybah ta fada
"Mezanyi kuwa banda incigaba da haquri ina biyyayah, haka kika ha iyayen mu nayi ne? Baki
koyi darasi da rayuwar gidanku ba knn, wanne wulaqanci neh abbab baya ma mammy, daidai
da raba daya kin taba ganin ta daga muryarta akan tashi? Naah! Baki taba gani bah, that
doesn't mean tana jin dadin yake treating dinta daku baki daya, haquri kawai take, kina ganin
haqurin nan da takeyi zai tashi a banza neh?
Shiru taybah tayi, yayin da wani kuka mai ciwo ya taso mata..."Bestiee, haka rayuwata zata
qare cikin baqin cikin maza? Na baro gidanmu cikin kunci kalma me dadi bata shiga tsakanina
da abba ba, a gidan auren nawa ma bazan samu kwanciyar hankali bah? Ni wacce irin marar
sa'a ce a rayuwa?". Hafsah ma saida ta zubar mata da hawaye..."karki ce haka swthrt,
KADDARAR ki kenan, daurewa zakiyi kawai kita haquri, duk abunda zai miki ki dena kulashi,
kedai kawai abunda nakeao dake kiyi haquri dan Allah, pleasesss". Hafsah ta fada pleadingly.

Haka dai hafsah taci gaba da kwantar mata da hankali da kuma mata wa'azi masu shiga rai,
hakan kuma bai tausasa zuciyar taybah ba, balle harda ta tashi da safe ta hada breakfast ta
bashi ba.Wuraren karfe 10 na safe taji saleem na kwala mata kira, saida gabanta ya fadi amma
ta daure ta fita ta sameshi a parlor. Sanye take da leggings baqi wanda ya kamata tsam tareda
wata sleeveless vest fara, gashin kanta wanda yasha gyara jiya a saloon sai sheqi yake kwance
a gadon bayanta. Fuskarta fayau ba kwalliya which made her look soo damn cute just being her
natural self.

"Lafiya wannan kiran kaman kana bina bashi". Taybah ta fada sweetly tana wani kada idanu.
Saleem da tunda ta fito yayi mutuwar tsaye ganin shigar dake jikinta.....haka dama yarinyar nan
takeda diri?......whoa! Abeeg see body. Taybah ta lura da irin kallon da yake mata, aii kuwa saita
qara gyara tsayuwarta tana girgiza jikinta......"malam, ka kirani kuma ka tsaya kana kallona,
baka taba ganin abu mekyau bane a rayuwarka ba sai yau?. Taybah ta fada tana murguda
baki. Da alama dai yau da rashin kunya ta tashi.

Zaro kyawawan idanunshi saleem yayu sanan yace.."meneh abu me kyau din? Badai ke kike
nudi ba? Duniyar nan akawi abunda ya kaiki muni ne? Dallah malamah wuce kije ki gyaramun
daki, ki kuma wanke mun toilet dina, inner wears dina na nan ajiye tas ki wanke su. Tsayama
kiji, daga yau duk randa kika kuskura na shiga dakin nan na ganshi da datti sai jikinki ya gaya
miki".

"Kutcee!!...duk wa kake nufin ya maka wannn aikin? Na maka kamada masu aiki neh? Abeeg
mr.man go look for house maid, kai kasan ni ba kalar aikin nan bace aii". Ta fada cikin tsiwa.
Dammit! Look how cute her lips were da tana magana, nan da nan yayi imagining kanshi
kissing her widely... Soo passionately.... In a sense da ita kanta will go wild in kissing him back.
Tsakin data ja ne yayi dalilin dawo dashi daga duniyar tunanin daya fada.
"Kinsan Allah, koki wuce kiyi aikin nan ko yanxu jikin ki yayi tsami". Ya fada yana qoqarin cire
belt din shi. Wup taybah tayi ta wuce dakin nashi jin anyi naganar duka, tsaf ta gyara dakin
tareda wanke toilet din sanna ta zaune wanki inner wears dinshi. Sai ana kiran zuhr taybah ta
kammala aikin daya sata, shi kanshi daya shiga dakin ba qaramin burgeshi yayi ba, ga wani
qamshi kuma mai dadi dake tashu.

Daki ta nufa ta watsa ruwa sannan tayi sallah, ta fito sanye da atampa orange color wadda
akama dinkin fitted gown wanda ya kama jikinta da kyau. Kitchen ta nufa dan ba qaramin kiran
ciroma cikinta yakeyi ba. Arabian chips ta dafa sannan tayi shary kibab ta dama kunun gyadan
ta wanda yaji madaa. Dining ta nufa ta aje abincin sannan ta koma dakibta danta dauko wayeta
ta kuma dauko handout dinta dan yau a parlor zatayi hiran ta. Tana fitowa daga dakin idanunta
suka sauka akan dining din wanda yake wayam babu komai a kanshi. Kamar daga sama tajiyo
karan spoon a gefen ta, tana juyawa kuwa idanunta suka sauka akan Saleem wanda ya
hakimce akan two sitter harda crossing legs yana kwasan girki!!








*©MSS MJAY*
[12/22/2016, 8:50 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG



written by
*MSS MJAY*

In dedication to
*SEMBYY LUFF*




*This chapter is dedicated wholeheartedly to you Deeylerh A.A Rasheed I lack the perfect
words to show you my appreciation, but i want you to know that ina SONKI a whole lot much.
Na saki cikin KUNDIN ZUCIYATAH na kulle. Thank you for everything❣*





*35*


A zuciye ta nufeshi, yayin dashi kuma ya sake hde rai kaman be taba dariya ba. Tsayawa tayi a
gabanshi hands akimbo tana faman girgiza jiki sannan tace..."Malam, what is the meaning of
this? Taya zanyi girki ka wani je ka dauka, who gave you that right". Taybah tayi stating angrily.
Dariya saleem ya kwashe dashi, duniya ba abunda yakeso kamn yaga ran taybah a
bace.,.."gani nayi ke matata ce, dan kin dafa abinci naci kuma aii ba laifi bane young lady ki
tashi a gabana karkisa inyi loosing apatite dina sbda ugly face dinki". Saleem ya qarasa ya
kautar da kanshi daga kallonta.

Haushi ya gama kashe taybah, ga uban yunwa dake cinta, kuma shikenn iya abunda ta dafa
daidai Tommy dinta, gashi wannan mugun ya dauko kuma sai gabza loma yake a gabanta.
Hawaye masu zafi ne suka zubo mata saboda takaici, sheshekar da saleem yaji neh ya sashi
juyowa da sauri. Ganin tana kuka ya sashi sakin smile, a very big smile kuwa....."Awwwn lil
sisturh, kuka kuma? Come on am sorry zoki dauki sauran ki cinye. Without second thoughts
taybah ta qarasa kusa dashi da sauri don ta dauki plate din......Tasss ya juye mata kunun
gyadan dake cikin wani dan babban cup a jikinta sauqinta daya kunun ya huce. Bai kuma tsaya
nan ba, haka ya sake daukar plate na chips da kibab din ya watsa mata akan kunun......."
Whoaaa! Sistoh irin wnnan kyau haka, kici abincin mnah. Oh! And in kinga dam kar kiyo dinner
dani kinji". Ya fada da wata killer smile a fuskarshi yana faman shafa sajen shi.
"Badai ni kika wulaqanta a gaban friends dina bah? Believe me sai kinji jiki a gidan nan, hadn't
been kinsan adadin qin danake miki a raina you wouldn't have tried abunda kika yi jiya, wait and
see the consequences amma". Ya fada yana snapping fingers dinshi sannan ya juya ya nufi
dakinshi.
Taybah yau tama rasa abun cewa, kuka kawai takeyi a wurin, mugunta saleem ia beyond her
thoughts. Allah gani gareka, nikam wannan aure bansan ya zai qara bah. Da zancen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login