Showing 15001 words to 18000 words out of 44631 words
Chapter 6 - KUNDIN QADDARA BOOK COMPLETE By MJay.pdf
zaune ka darduma a garden riqe da hand out tana karatu.
Alal haqiqa ba karatun take ba, tayi zurfi ne cikin tunanin maganganun da faysal ya gaya mata
jiya. Yea, itama tasan deep inside akwai wani weird feeling da take feeling for him, she can't say
what that feeling is truly is or what's all about.
Kamar daga sama tajiyo kamshin turarenshi mai kashe mata jiki,wanda kuma take matuqar so.
Kafin tayi yunqurin yin komai faysal ya tsugunna a gabanta. Kallonta kawai ya tsaya yi...how
beautiful she is just being natural....she's an angel..yet she drives him craxy!.
Shirin da taybah taji yayi yawa ne ya sata dago kanta a hankali....caraf suka hada idanu. A yau
sai taybah ta samu kanta da kasa dauke kanta daga kallon faysal....yea, she can see the pain,
the love deep inside his eyes.
Sunkai kimanin 15mins sitting there, just staring at each other....kowa kuma da abunda yake
sani akan danuwan shi.
A hankali taybah ta dauke fuskan ta daga kallon da suke ma juna......faysal yayi saurin
cewa..."Noo taybah, look at me please, look into my eyes and tell me har yanxu bakiga the pain
am going thru ba....mena miki bakya sona taybah, ko tausayina bakya yi?... Kullum cikin tunani
nake, ga aiki a gabana na kasa nitsuwa inyi....what do you want me to do pretty face? Tell me".
"Yaa faysal, give me time please, i need to think this thru".
"Think thru? Think thru wat taybah....kinga if you hate me ki gayamun kawai in sani...kinsan
sleepless night nawa nayi? Kinsan yanda nakeji cikin raina sbda son danake miki?....Noo! Duk
baki sani ba bcuz thatz not the way you feel".
"Yaa faysal mana!, i'll give you my answer in a week time".
"Nah, in a week mayb na tsufa a asibiti...make it tomorrow!. Abunda kawai yace kenan ya tashi
yabar garden din dafe da kanshi dake barazanar fashewa sbda ciwo.
*9:23pm*
"Am confused gaba daya hafsah, na rasa yanda zanyi". Taybah ta fada in a sad tone riqe da
waya a kunnen ta.
"Listen taybah, kibi abunda ranki yakeso, kin riga kin admitting faysal kikeso, wani dogon tunani
ba naki bane. Tell me the use of soyayyah shi yana yi ke bakya yi?...tunda kinada wanda kikeso
yake kuma sonki fine, go to him with open arms". Hafsah takai karshen dogon sharhin ta.
Ajiyar zuciya taybah tayi bayan sunyi sallama da juna. yea, its time she decides about her
future!.
Washegari taybah na gama hada breakfast ta kuma bacci, dan yau batada lectures sai 12.
Misalin 10:36 ta fito daga dakinta sanye da bakin wando daya kamata da top ja, saita daura
bakin dankwali a kan nata yayin da dogon gashinta yayi kwance a gadon bayan ta.
Rufaida ce zaune a falo tana cin apple, taybah na ganin haka ta kwashe da dariya tana
fadin....."Allah bar mana ke mana biyu..ci fruits da kyau mu samu healthy babies...
Wooo...harna ganni rungume dasu...soo cute". Taybah ta fada tana zama kusa da rufaida akan
three sitter.
Duka taybah ta zuba mata a baya sannan tace.."kiga twins a womb dinki muguwa...kiwa Allah
ki rabani da maganar twins dinnan".
"Ai sai kin haifesu.....shi wannan doctor hubbyn naki ya miki scanning musan me muke ciki
yaqi.....mijin nan naki akwai riqaqqen akida".
"Laaa, yanxu dan bakida kunya a gabana kike zagin mijina, kedai bari taybah, kiyi fatan samun
miji irinshi....he's loving, handsome, caring, ga iya love.....nikam anya akwai masoyi irin doctor
hubbyna kuwa". Rufaida ta fada tana runtse ido tareda daura hannunta akan kirjin ta irin tana
feeling love vibe..lol..
"Na shiga darii.....aunty rufy kinyi nisa, yanxu banda kissing din juna da kuke a gabana yau har
wani fannin kika tabo?. To nikam nayi nan..yunwa nakeji". Cewar taybah tana nufan dining.
"Nayi daki in kwanta, inkin tashi zuwa lectures kimun magana". Rufaida ta fada sannan ta nufi
dakinta.
A nutse taybah take breakfast dinta..fish pizza tayi da cottage pie, sai madarar waken suya
datayi.
Ta gama breakfast kenan ta nufi hanyar dakinta taji muryar faysal yana cewa...."Good morning
pretty face, Allah yasa kin gama tunanin naki".
Juyowa tayi a hankali ta kalleshi, yana sanye da baqin wando shima da jan top....laaa, anko
sukayi knn.
Dago ido tayi ta kalleshi taga ba abunda yake banda aikin kallonta.. Sai a sannan ta tuna kayan
jikinta.
Da gudu ta juya ta nufi dakinta, saida ta kama handle din kofan zata bude sannan ta juyo a
hankali tace....."I LOVE YOU YAA FAYSAL". Ta fada tareda fadawa dakinta ta kulle zuciyarta na
bugawa.
*©MSS MJAY*
[12/15/2016, 10:48 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
*This chapter is for you my xoxo...am soo proud of you, you made it and ended your story in a
UNIQUE AND ENTICING manner...THE CHARMING WAS ONE OF THE BEST BOOKS I'VE
EVER COME ACROSS....am so ao proud of you. Allah qara basirah in loads. I love you to the
moon, round and back❤*
*23*
Jingina da kofan taybah tayi zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Dafe saitin zuciyarta tayi
tana murmushi, ashe dai xata iya bayyanah her feelings to him.
Faysal daya sandare a wurin ko motsi ya kasa yi, she left him speechless tsaye a wurin yana
mamakin ta. Baisan lokacin da wani murmushin farin ciki ya subuce mai ba.
Misalin 11:15 taybah ya fito cikin shirin atampa purple riga da skirt, tasa purple hijab dinta ga
make up dinta dan das a fuskan ta.
Tana bude kofar dakinta ta hango faysal zaune kan three sittern dake saitin dakinta.
Daskarewa tayi a wurin saboda batayi tunanin ganin shi a wurin ba. Harta juya da nufin
komawa daki domin yanxu wata matsanan ciyar kunyan shi ne ke damunta.
Da sauri faysal ya tsayar da ita yana fadin...."pretty face, ina zaki kuma? Come back here dan
Allah and lemme have the pleasure of taking you to school today".
Rufe fuskanta tayi da hannunta tana murmushi. Sannan a nutse ta nufi dakin rufaida, koda ta
shiga ta samu rufaida na bacci hankalinta kwance. Sai kawai taybah ta fita tareda rufe mata
kofan dakin ta nufi waje.
A harabar gidan ta hango faysal tsaye a gaban motar shi, yana hangota ya tashi da sauri ya
bude mata gidan gaba. Wata kunya ta rufe taybah amma kuma she's happy beyond words na
yanda yake showing his care akanta.
A hankali yake driving din, yanayi yana kallonta, sometimes su hada ido su sake ma juna
murmushi...sometimes kuma shi kadai yake kidanshi da rawar shi.
A hankali ya tsinkayo muryarta mai matuqar zaki tana cewa...."yaa faysal, ya kamata ka koma
jos hakanan, concentrate on your work yanxu please.... Am all yours". Ta fada tana rufe
fuskanta.
Murmushi yayi cikin farin ciki, yau yana cikin farin ciki marar misaltuwa....yea, taybah tashi ce.
Wani zafi yaji ya ziyarci zuciyarshi sakamakon tunawa da bello da yayi.
"Noo pretty face, ba gaskiya bane....in har abunda kika fada gaskiya toh ki kira that so called
boyfriend din naki a gabana and end things". Ya fada yana wani shan toka.
"Kaima kasan haka bazai yiwu ba, a hankali zanbi da bello, ba yanda za'ayi lokaci daya in
kirashi in cemai am no more interested.... Thatz not possible yaa faysal".
"Not possible kamn ya? Kinfi son happiness dinshi akan nawa kenan?" Ya tambaya yana
kallonta.
Dagowa tayi da sauri ta kalleshi, idanunta sun ciko da kwalla
"Yea, kinfi son happiness dinshi akan nawa. Am the jealous type pretty face, ni am very jealous
akan abunda nake so and believe me i don't wanna share you". Daidai lokacin yayi parking a
gaban faculty dinsu.
"Kaidai yaa faysal ka cika rigima kaman karamin baby......awww na manta you are my baby
ashe". Ta fada tana kashe mai idanu.
Aii nan da nan mr.faysal ya manta da fadan da yakeyi. Taybah ta kama murfin motan da nufin
budewa ta tafi, sai taji ansa lock.
"Ki tsaya muyi sallama mana, thought kince kin gaji dani, ina komawa gida xan hada jakata in
koma".
"Awwnn yaa faysal...am gonna miss you, ka kula da kanka for me dan Allah.... Karfa kaje kana
kallonta wasu yanmatan fa". Taybah ta fada cikin shagwaba tana turo those sweet lips of hers.
Mutuwar zaune kawai faysal yayi yana kallonta. Admiring every single thing about her.
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah, gashi har soyayyah mai karfi ta shiga tsakanin taybah da
faysal. Domin ni kaina shedah ce akan irin soyayyar da sukema juna.
Duk wainar nan da ake toyawa rufaida bata taba lura ba, balle uban gayyar doctor saleem
wanda jininsu ko kadan bai hadu da juna ba shida taybah.
Yau taybah ta rubuta final paper dinta...an gama first semester exams. Tana fitowa ta kira
faysal....."yaa faysal..ka tayani murna, yau am gonna sleep like a baby". Taybah ta fada cikin
farin ciki.
"Ooo Allah ni faysal naga ta kaina, nayi nayi ki chanja mun suna kinqi ko pretty face, anyway
kice kawai yau am a baby, dan nasan you gonna kill me with love". Ya fada soo sweetly.
Murmushi taybah tayi sannan tace..."kwarai kuwa mine...harsai kace inyi hakuri in barka
hakanan, bye take care of yourself am gonna miss you". Ta fada sannan ta kashe wayar.
Tana isa gida ta nufi ciki da sauri tana fadin "aunty rufy, maman biyu kina ina? Gani na dawo
kizo kimun massage".
Shiru taji ba alamun rufaida sai kawai ta doshi dakin rufaidan dan gannin ko bacci take.
A duqe ta sameta tana riqe da cikin ta sai salati takeyi cikin zafin ciwo.
Zubar da kayan hannunta tayi sanna ta nufeta cikin sauri.
*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:55 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
*25*
A razane su duka biyun suka dago suka dubi dad.........T...Ta....Taybah fah kace dad". Saleem
ya fada in shock yana zare ido.
Taybah kai kawai take girgizawa tama kasa cewa komai, nan da nan hawaye suka fara zuba
kamar famfo.
"Kwarai da gaske, ita nace saleem in kuma baka so ka fada kar kaji komai i understand stuffs
like this". Dad ya fada.
Shi waye da dad zai mai kyauta yaqi karba, ai da kunya ma inya ce bazai karba wannan
kyautar da aka mai ba. Taya zai dubi idon dad ya fada mai bayason niece dinshi....naah thatz
not possible.........."Na yadda na amince dad, nasan su Alhaji basuda matsala, zanje musu da
maganar yanxu inna koma gida". Saleem ya fada murya na rawa saboda bacin rai.
Duk kokari taybah nata hana kukan dayake son kufce mata ta kasa, nan da nan wani kuka mai
ciwo ya kucce mata......bata jira me za'a kara cewa ba ta tashi ta nufi dakinta da gudu. Faysal
wanda ke shigowa gidan lokacin ya hango sanda take shiga dakin nata da alama kuma kuka
take.
Ganin su dad zaune a parlor dinne ya hanashi binta yaji abunda ya faru. Gaida iyayyen nashi
yayi sannan suka gaisa da saleem.
"Nagode saleem, ka nuna mun cewa inada iko a kanka, Allah ya maka albarka ya albarkaci
rayuwar kamal....zan kira Alhaji da kaina mu tattauna...tashi ka tafi". Faysal dai yayi zaune ne a
wurin kaman gunki ya kasa cewa komai, wa kuma za'a aura mai?.
Saleem ya isa gidansu cikin mawuyacin hali, ko gabanshi baya gani da kyau ya qarasa shiga
cikin gidan. Hajiya sadiya mahaifiyar shi na zaune a kan kujera da hisnul muslim a hannunta
tana karantawa.
Sallamar dan nata data jine da kuma yanayin data hango shi yasa ta ajiye littafin gefe sannan
ta bishi da idanu bayan ya kwantar da kashi a gefen cinyanta tareda runtse ido. Ba tare data ce
komai ba ta fara sha lallausan gashin dake kwance a kanshi sannan a hankali ta fara karanto
mai suratur rahman.
A hankali yanayin da yake ciki na tsantsan bacin rai ya fara gushewa har ya koma suna
karatun tare, saida suka kai karshen surar sannan suka shafa addu'oin da sukayi.
"Auta, zaka iya magana yanxu". Hajiya sadiya tayi tambayar cikin kulawa.
"Wai daddyn rufaida ya bani niece dinshi in aura, Taybah dake zaune tareda mu a abuja". Ya
qarasa maganae kwalla na fitowa daga idonshi.
Hajiya sadiya ta lura dan nata baiyi na'am da auren ba, amma aii da kunya Alhaji usman ya
musu kyauta suqi karba.
"Inaso ka gane wani abu auta, ita rayuwar nan daka gani kowa da nashi KADDARAR, a
KUNDIN kowa an rubuta mai irin tashi KADDARAR, fatan mu kawai shine Allah ya dora mana
KADDARAR da zamu iya dauka. A naka KUNDIN an riga an rubuta cewa zaka rasa rufaida
sannan ka auri taybah, addu'a kawai zamu tayaka da ita, Allah ya baka farin cikin zama da
taybah fiyeda yanda kaji dadin zama da rufaida". Hajiya sadiya ta qarasa dogon sharhinta tana
goge kwallar data taru mata.
Rungume mahaifiyar tashi yayi sosai yana kuka mai han tausayi, sai yau ya qarajin dacin
rabuwa da rufaida, she was the best, infact perfect to him.
Saleem ne kawai da namiji a gidansu, yanada yayu mata har guda hudu, samyrah, kausar,
iklimah da khadeejah.
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Taybah tunda ta shiga daki ba abunda take banda kuka, kuka kuwa mai tsanani, shyknn yanxu
burin auren da suja ci itada faysal ya rushe, yanxu duk soyayyar da sukema juna ta tashi a
banza. Ya ilahi! Wannan wacce irin KADDARA ce ta hau kanta.
Wayarta dake gefenta a ajiye ta fara ruri, tana dubawa kuwa taga faysal ne yake kira. Nan da
nan wani kuka mai ciwo ya qara zuwa mata, in komai ya daidaita wani sati ta zama matar
saleem kenan. Tana cikin tunanin ne taji message ya shigo wayarta........" Ki sameni a BQ dan
Allah, ina jiranki".
Tun daga nesa ta hango shi a tsaya ya juya bayanshi yana saqale da hannuwanshi ta
baya...qarasawa tayi a hankali sannan tace...."yaa faysal, gani".
She was shocked at what she was seeing,hawaye ne kwance shabe shabe a fuskarshi,
idanunshi sunyi jawur saboda bacin rai da tashin hankalin dayake ciki.
*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:55 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
*24*
Dago rufaida tayi cikin tsananin kidima. Hango jini tayi yana zuba daga jikinta kaman pampo.
A gigice taybah ta dauko wayarta tayi dialing din numbern saleem.
"Yaa saleem, aun...aunty rufaida na bleeding". Ta fada muryarta na rawa.
"What?....ki tsaya gani nan zuwa gidan". Ya fada a rikice.
Ko mintuna goma musu kyau ba'ayi ba taji motar saleen ta qaraso gidan. Saleem wanda yake
a gigice ya nufi cikin dakin tareda dauko rufaida suka nufi asibiti.
Emergency ward aka nufa da ita saboda yanda take bleeding, shi saleem tsabar kidima yama
kasa tsayawa ya duba ta da kanshi.
*2hrs later*
Dr. Sameer ameer ne ya fito cikin sauri daga ganinshi hankalinshi a tashe yake. Taybah dake
zaune sai rusa kuka take ta qasa shiru tunda aka shiga da rufaida labour room.
"Ina mijin nata yake?" Dr sameer ya tambaya.
"Gani nan doctor". Saleem ya fada a hanzarce.
"To my office". Ya fada tareda nufanoffice dinshi. Taybah ko gayyatar ta ba'ayi ba amma saida
tabi bayansu.
"Kowa da irin kaddarar shi a rayuwa, khairan aw sharran...kuma kowacce kaddara da
dalilinta...a kullum addu'ar mu Allah ya daura mana kaddarar da zamu iya dauka.....sai kunyi
hakuri da abunda nake shirin fada muku". Dr sameer ya fada idanun shi sun ciko da kwalla.
"Dr, dan Allah ka fada mun meya faru? Tell me what the hell is wrong". Saleem ya fada
impatiently.
"Am sorry to say, matarka ta haifi twins duka mata, kuma Alhamdulillah they are healthy....
Amma...". Sai kuma yayi shiru.
"Amma kuma me doctor? Ka fada mun menene matsalar dan Allah". Saleem ya fada yana
hawaye.
"Kayi hakuri doctor, kayi hakuri, Allah ya baka jurar rashinta.....amma munyo iyakar qoqarin mu
we couldn't save the mum".
Sandarewa saleem yayi a zaune a wurin yayin da taybah ta sulale a wurin tana salati.
Rufaida is gone? Rufaidar shi ake nufi ko wata? Noooo!!! It can't be, rufaida bazata tafi ta
barshi ba. Girgiza kai kawai saleem yake kaman qadangare ba tare daya samu damar cewa
komai ba.
*RIP RUFAIDA*
*43 days later*
Mutuwar rufaida ta taba kowa mussam man ma da bayan rasuwarta da kwana biyu twins dinta
suma suka bita
Saleem ya chanxa, duk ya zama abin tausayi, gaskiya ne, yayi rashin mata dan rufaida mata
ce tagari wadda yake alfahari da ita kuma a ko yaushe.
A bangaren taybah ma haka abun yake....zaman watanni takwas da tayi da rufaida ta koyi
abubuwa da yawa dangane da rayuwa. She has lost a sister and a friend.
A takaice dai both tje two families, na rufaida dana saleem kowa mutuwar ta gigita shi.
A yammacin ranar asabar dad