Showing 21001 words to 24000 words out of 44631 words
Chapter 8 - KUNDIN QADDARA BOOK COMPLETE By MJay.pdf
fada tanata kuka..."Allah gani gareka, wannan wacce irin kiyayya ce? Yoo aii itama
bata ce tana sonshi ba, dole aka mata. Allah sarki yaa faysal, da shi ta aura da yanxu duk ba
haka ba. Allah dai ya kyauta".
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*8:37pm*
"Taybah! Taybah!! Taybah!!! Where the hell are you you silly bitch!". Saleem ya fada cikin fada.
"Gani fa, na shiga inyi sallah ne fa". Taybah ta fada tana fitowa daga dakinta.
Tana dago kai ta ganshi tsaye da friends dinshi biyu....mukhtar da zayyad. Yanxu a gabansu ya
mata wannan zagin.."bloody bitch"!.
"Kinyi tsayene kina kallona bazaki wuce ki zuba mana abincin bane". Saleem yayi snapping.
"Yaa saleem abincin bazai isa ba, bansan da wasu zaka zo ba, amma bari in dora wani".
Taybah ta fada muryarta na rawa.
Karasowa yayi gabanta tareda kwasheta da mari..."Amma kin raina ni koh? Kin raina ni nace
koh, saboda me zaki dafamun abincin dan kadan a gidan? Ke kika mun cefanen, come on wuce
ki dora kafun in babbalaki a nan".
Dafe da kuncinta tana kuka ta nufi kitchen din.
"Kiyayyah ba hauka bane fa saleem! What the hell is wrong with you? In kana taqama baka
sonta ita tana sonka ne? Da bakinka ka fdamun itada faysal na soyayyah ashe, ashe bazaka
rungumi kaddarar da Allah ya dora ma ba? What type of person are you?". Cewar mukhtar cikin
fushi.
"Malam mind your own business abeg, kaika dage saika zo ban gayyace ka ba, in bazaka iya
kallo ba find your way out". Saleem yayi snapping.
"Ahh....lallai, gaskiya ne, toh nikam nayi nan Allah ya kyauta, amma lokacin da haqqin yarinyar
nan zai kamaka believe me saika ji ba dadi". Mukhtar ya fada sannan ya nufi waje abunshi.
Shima zayyad da mamaki ya cikashi kasa cewa komai yayi kawai ya tafi abunshi.
Washegari da wuri taybah ta tashi ta hada mai breakfast..... Sannan ta gyara gidan tsaf da
badeshi da kamshin turare.
Sai wuraren 9:48am ya fito, direct dinning ya nufa, warmern farko daya bude yaji ranshi ya
mugun baci
"Taybah!!!!!!!" Ya fada cikin bacin rai
*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:55 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
*28*
A yau asabar da misalin karfe 2:00 na rana muka shaida daurin auren SALEEM DA
TAYBAH......Allah bada zaman lfya.
Taybah na sanye cikin lace pale yellow, dinkin ya mata cas a jikinta, ga kunshi ta sha sai baza
kamshi take.
"Iyyee! Kaga amarya a gidan doctor, kinyi kyau fa yan matan likita". Hafsah ta fada cikin
barkwanci.
Taybah ta dago rinannun idanunta da suka rine dan kukan data sha ta zabga ma hafsah harara
sannan cikin jin haushi tace..."kinga bansan iskanci, ki kama kanki kina jina koh".
Sallamar da yasmeen tayi dakin ne ya hana hafsah tankawa.
"Adda taybah, Abba da mammay na kiranki, kizo kuyi sallama anzo daukan ki".
"Na shiga uku! Har sunzo?". Taybah ta fada tana kama baki cikin baqin ciki. Sannan a hankali
ta miqe ta nufi dakin iyayyen nata. Duk inda ta gifta kamshi ne ke sallama yayin da yanuwa da
abokan arziki ake binta da guda.
Ta karasa dakin tareda yin sallama sannan ta shiga, a zaune ta samu iyayyen nata cikin
kwalliya mai kyau, Mammy sai fara'a take alamun tana cikin farin ciki mabayyani.
"Malam gatanan fa tazo tun dazu naji kuma kayo shiru baka ce komai ba kuma kasan mutanen
nan jira suke a fito da ita".
"Yoo ni me kikeso ince? Banda abun cemata nida na rage mugun iri a gidana. Allah raka taki
gona". Ya kai karshen maganar tareda tashi ya kade babbar rigarshi sannan yayi gaba.
Taybah ta share hawayen da suka zubo mata masu zafi, ta rasa irin mahaifin da Allah ya basu,
A da tana tunanin zai chanja ya rage tsangwamar da yake nuna musu amma kamar komai kara
gaba yake.
"Ina godiya ga Allah daya nuna min wannan ranar, ba wanda ya kaini farin ciki a yanxu. Dan
haka ki riqe auren ki da muhimmanci, yafi komai a wurinki.
Komai wuya komai dadi ki sani dakin mijinki shine gatanki yanzu. Ki riqe shi da yanuwanshi,
yanzu kin zama su, sun zama ke. Ban yarda matsala ta fito daga gareki ba. Allah ya baku
zaman lfya. In shaa Allah ba zakiyi dana sanin wannan auren ba. Kullum zan kasance cikin
maku addu'a".
Rungume mammy tayi ta rushe da kuka mai tsuma rai..."wayyo mammy ki yafe min, ki yafe min
banason tafiya".
Da kyar mammy ta banbareta tace..."taybah yanzu dakinki shine gidanki, ki kasance mai tsoron
Allah, kullum shi zai yaye miki baqin ciki ya sanya farin ciki, kuma banda wasa da sallah".
Da kyar su hafsah suka samu suka banbare taybah daga jikin mammy, tana rusa kuka mammy
nayi....su yasmeen ma na taya su......awwwnn..so pathetic.
Saida aka kara komawa gida wurinsu dad suma suka daura nasu fadan sannan aka dauki
hanyar abuja da amarya da misalin karfe 5:00 na yamma.
*SALEEM*
Sake sauke ajiyar zuciya mai nauyi yayi cikin baqin ciki da rashin madafa. Yanzu shyknn ya
tabbata taybah ta zama matar shi. Yarinyar daya tsana deep inside to the core.....Dammit!.... Na
tsaneki taybah!!.
Mukhtar ne ya sake dafa shi cikin damuwa yace..."aboki, wannan tunanin da kuncin da kake
won't solve anything, ka rungumi auren nan hannu biyu. Allah kadai yasan dalilin da haka ya
faru".
Furzar da huci mai zafi yayi sannan yace....."bazaka gane bane, na tsani yarinyar, i just hate
her....ni me zanyi da baqar mace dan Allah, ka dubeni da kyau, nayi kamada mijin baqar mace
balle ita lauje". Saleem ya fada cikin fushi.
"Hmmn, saleem kenan, kabi rayuwar nan a hankali, who knows gobe ko you'll be head over
hills for her? Ka dena cika baki my man". Cewar mukhtar.
"Allah ya sauwaqe, me zanyi da ita, abeeg spare me that riddle, abunda kawai na sani shine
saita gwammaci kida da karatu.
Nikam dai nace maji ma gani....namu ido muga abunda zai faru!!!.
*FAYSAL*
A hankali ya zame wayar daga kunnenshi yayin da wasu hawaye masu tsananin zafi suka zubo
mai, yes shyknn yanxu ya rasa taybah for sure....his happiness, his pretty face, his priceless
jewel to someone who doesn't even know her worth!.
Kuka yake wiwi yana fadin...."taybah na rasa ki, Allah ya bani ikon juriyar rashinki, har a yau da
kike matar wani ban daina sonki ba kuma banji ranar dazan daina ba taybah.....i love you and i
still do". Ya fada cikin kuka nima ina tayashi.......yaxo kawai ga doctor sumayyah durln na bashi
ya manta taybah.
Sai ana kiran isha'i suka shigo garin abuja, gidan nanan yanda yake sai sabon fenti daya sha,
daga gani ansan wannan gidan amarya ne.
Allah bada zaman lfya amaryar likita!.... Nida seeyermerh mun kwashi shoki wurin biki...lol.
*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:14 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
*31*
"Taybah! Uban meye wannan?". Saleem ya fada not wanting to believe what his eyes are
seeing a cikin warmer din.
Taybah da tsoro ya gama kamata, cikin rawar murya tace...." Dumame ne faa".
"Du what? Dammit! Ke tunda kike kin taba gani naci dumame.....ohoo, so kinaso ki nuna mun
cewa kin girma tunda an sani dole na auri bagidagiya irinki, you even have the guts kimun
dumame, dumamen ma na tuwo for goodness sake....how dare you!". Ya fada a tsawace.
Taybah tsoro duk ya gama kamata, barin inta tuno marin data sha jiya. Cikin rawar murya ta
fara cewa...."k..kai fa...ka..ce i..in j...j..je in dora wani abincin daka dawo, s...sai kuma baku ci
b...ba, nikuma bansan ya zanyi dashi ba, naba bala driver da tasiu mai wanki harda baba me
gadi shine na ajiye ma saura".
Kasa cemata komai ma yayi banda tsayawa yana kallonta, dukanta zaiyi ne ko me? Noo yama
san me zeyi.
"Kinga dumamen nan da kika bani, yau shi zaki wuni kina ci a gidan nan, in kika kuskura kika
bari na dawo na samu kin dafa wani abincin kinci sai kinji jiki, kinji na gaya miki". yana gama
fadan haka ya juya ya tafiyan shi aiki ba tare daya ci tuwon ba.
"Aii kuwa tunda bakason cin dumame da safe yanxu na fara, saidai kata zuwa aiki baka ciba ba
abunda ya dameni". Taybah ta fada cikin fada kaman yana gurin.
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Zaman nasu taybah gashi nan dai, wulakancin yau daban, na gobe daban....saleem ya fara
qure haqurinta. Tana kwance a falo kan kujera tana waya da hafsah....."kin san Allah, haqurina
ya fara qarewa, sai kace shi kadai akama dole. Na rasa yanda zanyi bestiee....am lost, kullum
kina cewa inta haqura for how long kikeso inta haqurin, yanxu almost 4weeks da resuming
school amma yaqi cewa in tafi. Ta yaya zan iya wannan zaman hafsah? Yanxu haka idan baki
sani ba da kyar nake numfashi a gidan saboda duk ya fice min a kai ya gundureni". Taybah ta
fada cikin kuka.
"Kinga taybah, kinada dalilin zama, ki tuna rufaida mana, ko dan ita da kamal ki qara haquri. Aii
ba sai na fada miki ba already kin mallaki komai na jan hankalinsa, kece bakiyi amfani dasu ba,
keda ko magana kikeyi sai mai wucewa ya tsaya yaji, ke din ce za'a nuna ma janye hankalin
miji". Hafsah ta qarasa cikin sigar kwantar da hankali.
Da yammacin ranar kuwa taybah ta cancada adonta cikin wani olive green lace mai laushi
wanda yasha dinki mai kyau ya kuma bi surar jikinta.
Biyar da yan mintuna kamar yanda ya saba dawowa kullum yauma haka ya dawo. Taybah najin
tsayuwar motarshi ta miqe tana gyara zaman rigarta, this time around taci alwashin saita kwaci
yancinta.
Sallama yayi ya shigo, saidai a maimakon ta ganshi shi kadai saita gansu su biyu.
Da sauri ta koma daki ta yafo farin gyale babba, sannan ta qara fitowa.
Koda ta fito suna zaune akan kujera. Durkusawa tayi dan nesa dasu sannan ta gaishe su.
"Amarya kinsha kamshi, ya amarci ya gida?". Abokin nashi ya fada cikin raha.
Da sauri saleem yayi saurin amsawa da.." Amarya fa bata nan, tana jos, daka fadamun zakaxo
ai dana kirata ta dawo, ganinka kawai nayi kwatsam a office dina....wannan yar aiki ce". Saleem
ya fada ya kawar da kai.
A razane taybah ta dago tana kallon saleem, lallai ba karamin tsana ya mata ba tunda har zaiyi
denying existence dinta a matsayinta na matar shi. Great, in game yake so sai su buga aii.
"Whow, amma batayi kamada yar aiki ba aboki, irin wannan black beauty haka?" Abokin ya
fada admiring her.
"Bismillah, muje kuci abinci". Taybah ta fada a hankali....Dr shuriem saiya kara zama lost aii jin
irin muryarta da zaqinta, ashe dai ya dawo Nigeria a saa'a....daga zuwanshi yaga
mata......lmoa...mata kam likita.
Taybah tayi serving dinsu tuwon nikakkiyar danyen shinkafa da miyar eguhsi data sha ganda
and stockfish. Dr shureim santi kawai yake zubawa a ranshi yana rayawa inya auri wannan aii
ya more.
Koda ya tashi tafiya kuwa harda kyauta 20k yaba taybah sannan ta tafi.
"Keh, kallenk, in kika bari yasan kece bagidajiyar matar da aka bani nida kene a gidan nan, dan
saina miki dukan tsiya". Saleem ya fada in a warning tune bayan abokinshi ya tafi.
"Mtsssswww....toh mene abun birgewa inna nuna kaima mijina na....ai naji kunya". Taybah ta
fada sannan ta nufi dakinta tana rangwada.
Tsayawa galala kawai saleem yayi a wurin tareda binta da kallo.
*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:14 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
*32*
This is not taybahn daya sanu, yarinyar da in yana magana tsabar tsoron shi nitsuwa take tana
sauraronshi, amma yau itacae harda mai tsaki. Tab! Ashe da matsala kuwa.
Wani sabon saln da taybah ta dauko shine...dressing in alluring outfits ta kuma caba make-up
na daukan hankali. Sannan duk lokacin daya dawo gida daga office babu abunda taybah take
banda qoqarin ririta shi, abinci ma intayi serving maimakon ta tafi a'a zama take saiya gama ci
tana mai hira mai dadi. Dukda shidai saleem baya tankawa, amma the changes in her ya fara
sashi some strange feelings. A kuma koda yaushe cikin fara'a take da gayamai daddadan
kalamai.
Yauma kaman kullum ta gama girkinta da wuri inda ta dafa plantain porridge, wanda yasha
kidney da liver sannan tayi chicken pepper soup dinta a gefe kuma ga rapsberry and strawberry
juice. Tana sanye cikin wani jan lace mai kananan zane purple and dark blue, dinkin ya amsheta
sosai. Gashi ansha make-up an kuma kashe dauri. Loose fitted ne rigar da skirt dinta, dama
taybah yaya balle an dau kwalliya.
Tana zaune a falo tana kallon t.v amma alal haqiqa ba kallon take ba, tana jiran isowan saleem
gida ne. Ko minti goma batayi da zama ba taji tsayuwar motarshi, yau kuma haka kawai a
ra'ayin kanta taji bari ta tarbo shi tun daga waje.
A hankali take taku harta fito harabar gidan, daidai lokacin kuma likitan nata ya fito daga motar.
Tsayawa yayi galala yana kallon taybah, yayin da ita kuma taybah ta kashe shi with hr best
smile wanda yayi dalilin lobawar duka kuncinta(dimples). Ya dauki kusan daqiqa uku a tsaye ba
tare dayasan inda yake ba, kodai an chanza taybah ko kuwa yau asalin kyawunta ya gani a
bayyane.
Take a wurin yaji wani irin kishi ya rufeshi, to akan wane dalili zata fito waje cikin wannan irin
kwalliyar ga bala mai wanki da kuma tasiu mai gadi duk suna zaune a wurin, kuma da alama
duk sunga kwalliyar datayi.
Yayi nisa cikin tunani har baisan lokacin data karaso kusa dashi ba....sai kamshin turarenta na
valence da oud daya bakunci hancinsa.
"Welcome home yaa saleem". Taybah ta fada sweetly tareda karban jakan hannunshi....."muje
ciki". Ta fada sannan ta juya ta nufi cikin gida.
Binta yayi da kallo cikin tunani sannan yabi bayanta. Yana shiga dakinshi ita kuma tana fitowa
daga toilet dinshi...."yaa, ka shiga ka watsa ruwa, abincinka na jiranka inka gama". Ta fada
tareda barin dakin.
Ya dauki kusan 30mins sannan ya fito sanye cikin wando three quarter milk color da wata black
top. Sai yau taybah ta qare mai kallo, Dogo ne mai kakkauran jiki, daka ganshi kasan yana
samun kula ta hanyar motsa jiki. Karfaffa ne kuma tsayayye, sannan farine shi danya fita haske.
Kyawunsa ba irin sumul din da kowace mace zata masa duba daya ta gane bane, zamu iya
cewa haduwarsa irin boyayyar haduwace wacce kwarjini ya kara masa ado da kima. Ga wani
kwantaccen gashi a kowane gefe na fuskarshi wanda ya qara fiddo da siffarsa ta cikakken da
namiji...(bily, rufe baki hakanan mana)
A hankali tabar kallon da take masa yayin dashi kuma ya nufi dinning ya zauna. Yana zama ta
miqe cikin fara'a ta fara serving dinshi sannan taja kujerar kusa dashi ta zauna.
Saleem was lost, ya rasa yanda zaiyi, this days wasu strange feelings ne akan taybah suke
ziyartar shi wanda ya kasa tantance ko wane iri ne, for all he knows shine, this days baya cikin
nitsuwarshi.
Gyaran murya yayi a dalilin shaqewar daya kusa yi, da sauri ta miqa mai ruwa da hannu biyu,
yasa hannu ya karba lokacinda idanunsu ya hadu dana juna. Itako tasan miqa ruwan datayi
baya cikin acting din data shirya, wannan dalilin yasa tana miqa mai ruwan ta miqe da nufi dakin
shi.
Binta da kallo saleem yayi yana ayyana abubuwa da dama cikin ranshi.
*©MSS MJAY*
[12/20/2016, 6:07 PM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
Written by
*MSS MJAY*
In dedication to
*SEMBYY LUFF*
*This chapter is for you Dr sumayyah....i love you beyond words. Allah barmun keh❤*
*33*
Koda taybah ta koma dakinta, shiru tayi cikin zurfin tunanin abubuwan da take aikatawa this
days, ita kanta it disgusts her yanda take qasqantar da kanta a gabanshi. Amma yata iya, babu,
hakanan dole zata cigaba dayi indai tanaso ta cimka burinta.
Saleem sat there stunned, har yanxu ya kasa yadda taybah ce this days, sometimes in tayi abu
sai yaga kmn rufaida..."Oh yaa Allah!" How he seriously missed his lovely wife kamn hauka, if
only ana chanja KADDARA daya chanja tashi, da yanzu yana nan rungume da rufaidan shi,
tana feeding dinshi like a baby he has always been to her. Dammit!, yanzu yanzu yana nan
zaune da wata baqar halitta a matsayin mata which to him is not fair ko kadan. Sanadin wannan
dogon tunanin da saleem ya zauna yi, ya assasa cikin dalilan da suka sa yayi loosing apatite
dinshi. Dole ya sama wannan salon data dauko mai this days full stop!.
Koda ya dawo daga masallaci bayan sallar isha, taybah na zaune a parlor wannan karon sanye
cikin wata doguwar riga ash colour, wadda tabi surar jikinta ta lafe ga gashin nan yasha gyara
kwance a gadon