Showing 18001 words to 21000 words out of 44631 words

Chapter 7 - KUNDIN QADDARA BOOK COMPLETE By MJay.pdf

ya kira saleem gida da misalin karfe biyar. Falonshi ya kaishi
daga shi dad, sai Ammi, taybah da saleem din a zaune.

Gyaran murya dad yayi sannan a hankali ya fara magana......."Ina qara ma kowannen mu
ta'aziyar rashin ya, mata, yaruwa da duk mukayi. Allah ya bamu juriya da hakurin rashinta ya
kuma haskaka kabarinta. Ba komai bane yasa na taraku a wurin nan face dan in isar muku da
wata shawara dana yanke".
"Kai saleem" dad ya fada yana mauda kallonshi da hankalinshi gaba daya a kanshi...
......"Ina sonka, kuma yanda faysal yake da a wurina haka kaima kake da a wurina, na yaba da
hallayar ka da kuma karamcin ka...saboda wannan dalilin yasa na yanke hukunci, amma sai in

ka yadda ka kuma amince, kar kaji kunyar fada mun in hukuncin dana yanke bai maka ba
domin ni tsakani da Allah nake sonka. Saboda haka....in har ka yadda kaji kana so kaje kayo
shawara dasu alhaji nan da wani sati inka amince zan daura maka aure da TAYBAH!."







*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:55 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG





Written by
*MSS MJAY*



In dedication to
*SEMBYY LUFF*



*This chapter is for you MOMMA, wallahi i lack the perfect words to show you what you mean
to me. But i love you alot....to the moon...the sun round and back❤*




*26*


Tsayawa sukayi suna kallon juna kawai ba tare dasun furta komai ba. Taybah ita kallon shi
kawai take, wondering ko me yasa shi zama haka, looking soo depressed and hurt.

"Taybah, what is this i heard? Wane irin magana naji wai saleem zaki aura? Taybah how can
you do this to me...kinsan yanda nake sonki kuwa? Do you know the sleepless night i went

through before in sameki?. Dan Allah kiji tausayina kije ki fada ma dad ya janye....taybah
pleaseeeeee". Faysal ya fada hawaye na zubowa daga idonshi.

Taybah ma wani kuka ne yazo mata, this is the worst day of her life...zata rasa faysal dinta,
rasawa ta har abada....amma wacce ita taje ta cema dad bazata aure zabin shi ba...no thats not
possible.

"Yaa faysal, dan Allah kayi haquri, ya kakeso inyi ni? Taya kake tunanin zan dubi idon dad ince
banason zabin daya mun?. Muyi haquri kawai mu karbi KADDARAR da Allah ya dora mana.
Kayi haquri dan Allah, nikam na riga na huqura".

"I knew it! Ni dama nasan ni kadai nake haukan sonki you never seem to care about how i
feel...ki fadamun kawai cewa you never loved me...say it taybah". Faysal ya fada cikin bacin rai
yana girgiza taybah kaman zai balla mata kafada......."Stop it yaa faysal! You're hurting me".
Taybah ta fada cikin kuka.
"Aii gwara inyi hurting dinki...the pain kike feeling yanxu ko rabin wanda nake feeling bakya ji.
Haba ni nayi mamaki haka kawai dad yace yaba saleem ke, ashe ke kika je kika ce ya hada
ku....ashe baki taba sona ba!". Ya fada a tsawace.


"Yes! Ban taba son naka ba kuma bazan taba son naka ba! I hate you, i hate you more than
anything i've eva loved....karka qara gani nan kamun magana domin yanxu na riga da zama
rabon wani". Cewar taybah cikin tsananin kuka sannan ta kwace kanta ta nufi gida da
gudu........"Noo taybah, karya kike...ni kike so, you are just saying this to hurt me.
Ta...tay...taybah ki dawo, tell dad ni kike so dan Allah". Ya durkushe a wurin yana kuka(nima
nida momma muna tayashi



WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

Washegari taybah ta tashi idanunta sunyi luhu luhu saboda kukan data sha jiya da daddare. Ko
wayar ta taqi kunnawa tunda faysal ya dinga damunta da kira. Yanzu ma tana kwance tayi zurfi
cikin tunani har bata san lokacin da ummu da kamal suka shigo dakin nata ba, sai ji kawai tayi
suna cewa...."Aunty taybah, dad na kira".


A zaune ta samu dad shida ammi a parlor, durqusawa tayi ta gaida su sannan ta nema guri ta
zauna.

"Taybah, bakida lfya ne?. Ammi ta tambaya........"lfyata qlw ammi".

"Kodai hukuncin dana yanke ne be miki ba? Tell me taybah in har bakya son saleem zan kira
shi a fasa maganar". Dad ya fada cikin kulawa.......da sauri taybah tace"A'a dad, ba haka bane
kawai banajin dadin jikina ne".

"Toh shyknn ki shirya anjima saleem nanan zuwa ku gana da juna". Cewar dad. Wani daci ya
xiyarci zuciyar faysal dake tsaye bakin kofan tun daxu. Lallai da gaske taybah take data ce bata
sonshi, inba haka ba ga dama dad ya bata amma ta zubar musu da ita. Wasu kwalla masu zafi
ne suka zubo mai ya juya da sauri da yabar falon.


*5:03pm*

Taybah ta qarasa parlorn baqi inda saleem ke jiran ta. Tanansanye ne da atampa baby pink
riga da zane sauta sa baqin hijab dinta. Ko powder babu a fukan ta balle akai ga zance kajol.
Sallama tayi ciki ciki kamar wadda akasa dole. Saleem ya dago a hankali tareda amsa
sallamar. Sai yaga kamar ba taybahn daya sani bace, dan ta chanja mai. Durqusawa tayi ta
gaida shi sannan ta nema wuri ta zauna. Gyaran murya yayi a hankali sannan yace..."nasan
kinji hukuncin da aka yanke, ni bazan iya tunkarar dad incemai bazan aureki ba. Amma zan miki
kashedi guda daya, kika yadda kika bari aka kaiki gidana da sunaa....hmmmn, am sorry to say,
sunnanki sorry taybah. Danni i totally hate you!". Saleem ya fada cikin wata kakkausar murya.

Wani daci taybah taji cikin ranta, to shi cemai akayi ita son nashi take? Damn him! Gashi
saboda shi yanxu bazata auri wanda takeso ba.

"Yaa saleem kenan, duk abunda kaga dama kamun, i really don't give a damn! In kaga dama
ka yayyanka naman jikina da dawoma iyayen namu dashi, sai lokacin zan tabbatar cewa ka
tsane ni".

"Great!, yarinya zaki raina kanki kuwa". Saleem ya fada sannan a fusace ya tashi yabar dakin.

Taybah ma haushi ne ya isheta tare da wani baqin ciki daya toshe mata zuciya. Ta miqe cikin
sanyin jiki da nufin barin dakin, tana kai baqin kofa taci karo da faysal yana shigowa.






*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:55 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*

WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG




Written by
*MSS MJAY*


In dedication to
*SEMBYY LUFF*





*27*


"Taybah, kinfi so ki aure shi yana wulaqanta ki daki je ki fada ma dad Yayi haquri ya janye ba
taybah? Taybah me yasa kike wahalar dani haka dan Allah....why all this pain? I deserve some
happiness taybah.... I love you taybah, you know that.....wannan wane irin abune haka?".
Faysal ya fada sadly.
Kuka kawai taybah take ba tare data ce komai ba, shi kuma yayi tsaye kawai yana kallon
ta.....sun kai kusan 10mins a haka sannan taybah ta fara magana a hankali....."Yaa faysal, na
rasa gane kokai wane irin mutum ne, kayi haquri mana, nima fa haquri nake...KADDARAR mu
kenan, muyi haquri mu rungumeta dan Allah. Leave. Me. Alone!". Taybah snapped. Sannan ta
raba ta gefenshi ta wuce cikin gida. Yayin da faysal yayi tsaye a wurin dafe da saitin zuciyarshi.



Washegari musalin karfe 1:08 na rana taybah ta fito cikin shirin atampa army green da strips na
fari a jiki....si tayi using white veil, shoes and bag....tayi applying simple make up dinta...dukada
damuwar da take ciki hakan bai hanata yin kyau ba, ba kuma komai ya kawo hakan ba sai
rabuwa ta mutunci da sukayi da bello a jiya.
Tana fitowa harabar gidan ta hango motar saleem a harabar gidan yana jiranta. A ranta sai mita
take sbda dad yace suje gida tare su gaida su mammy

Ta qarasa gaban motan tayi tsaye tana tunanin inda zatabi ta shiga, shi kuma saleem gani
yake duk tsabar iskanci ne da kuma raina shi data gama yi ne yasata kin shiga motan.....kamn
ance taybah ta dago kanta, kawai saita hango faysal tsaye nesa dau kadan idanunshi jawur dan

baqin ciki, lallai taybah da gaske take a furucin data mai shekaran jiya cewa ahe hates him,
tunda gashi harda kwalliya tama saleem dan kawai zasu fita. Tunda yake da ita aii bata taba
mai kwalliya irin wannan ba....(kishi ya rufemai ido ya manta yanda take mai gayu in yaje abj).


Dauke kanta tayi da sauri sannan ta kama murfin gaban motan ta shiga. Kamshin turarenshi ne
ya fara mata sallamah, runtse idanunta tayi yayin da qamshin naci gaba da ratsa ta. A nashi
bangaren ma haka abun yake, shi ma'abocin son kamshi ne, gashi taybah arabian pefs take
using masu kama jiki. A hankali yaja motar suka bar gidan har lokacin kuma idanun faysal na
kansu.....(so kenan


WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

"Taybah, rayuwace haka, kana naka Allah na nashi.....kiyi haquri kamn yanda kika nuna ma
kowa kin haqura, who knows he might b your luck, kiyi haquri swthrt". Hafsah takai karshen
zancen nata in tears itama tareda rungume taybah da tunda tazo ba abunda take banda kuka.

"I hate yaa saleem sis, na tsaneshi ne kamar yanda ya tsane ni...ke fiyema da yanda ya
tsaneni....inba KADDARA ba mezai hadani da wannan likitan.....jiya harda cemun saina dandani
kuka ta inna shiga gidanshi, kaman nina ce ina sonshi...mene abun so a jikin
wannan....mtswww". Taybah ta fada tana jan dogon tsaki. "Yanzu dai koma mene magana ta qare, wani sati by this time kina gidanshi a matsayin
matarshi, ni Allah yasa ma ya barki kici gaba da karatun ki".

"Kutuseeeeee!, aii tunda ya aureni da karatuna dole ya barni inci gaba, aii baima isa ba in gaya
miki". Taybah ta fada cikin masifa.....riqe baki hafsah tayi cikin mamaki tana kallon taybah dake
ta fada..."taybah, yaushe kika zama masifaffiya haka?". Hafsah ta fada tana rufe baki.

Haka suka sha hiran su har zuwa yamma da faysal yazo daukan ta.

Koda suka qarasa gida faysal na zaune a harabar gidan dafe da kuncin shi cikin zurfin tunani.
Taybah ta fito daga motar ba tareda data cema saleem komai ba ta nufi cikin gida. Da sauri
faysal ya tashi daga inda yake zaune ya nufi gurin saleem.

"Bro, inada magana dakai, Dan Allah ka taimakeni kace ma dad ka janye auren taybah, bro i
love her, i love her alot".

*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:55 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG



Written by
*MSS MJAY*



In dedication to
*SEMBYY LUFF*




*28*

A yau asabar da misalin karfe 2:00 na rana muka shaida daurin auren SALEEM DA
TAYBAH......Allah bada zaman lfya.

Taybah na sanye cikin lace pale yellow, dinkin ya mata cas a jikinta, ga kunshi ta sha sai baza
kamshi take.

"Iyyee! Kaga amarya a gidan doctor, kinyi kyau fa yan matan likita". Hafsah ta fada cikin
barkwanci.

Taybah ta dago rinannun idanunta da suka rine dan kukan data sha ta zabga ma hafsah harara
sannan cikin jin haushi tace..."kinga bansan iskanci, ki kama kanki kina jina koh".

Sallamar da yasmeen tayi dakin ne ya hana hafsah tankawa.

"Adda taybah, Abba da mammay na kiranki, kizo kuyi sallama anzo daukan ki".

"Na shiga uku! Har sunzo?". Taybah ta fada tana kama baki cikin baqin ciki. Sannan a hankali
ta miqe ta nufi dakin iyayyen nata. Duk inda ta gifta kamshi ne ke sallama yayin da yanuwa da
abokan arziki ake binta da guda.

Ta karasa dakin tareda yin sallama sannan ta shiga, a zaune ta samu iyayyen nata cikin
kwalliya mai kyau, Mammy sai fara'a take alamun tana cikin farin ciki mabayyani.

"Malam gatanan fa tazo tun dazu naji kuma kayo shiru baka ce komai ba kuma kasan mutanen
nan jira suke a fito da ita".

"Yoo ni me kikeso ince? Banda abun cemata nida na rage mugun iri a gidana. Allah raka taki
gona". Ya kai karshen maganar tareda tashi ya kade babbar rigarshi sannan yayi gaba.

Taybah ta share hawayen da suka zubo mata masu zafi, ta rasa irin mahaifin da Allah ya basu,
A da tana tunanin zai chanja ya rage tsangwamar da yake nuna musu amma kamar komai kara
gaba yake.

"Ina godiya ga Allah daya nuna min wannan ranar, ba wanda ya kaini farin ciki a yanxu. Dan
haka ki riqe auren ki da muhimmanci, yafi komai a wurinki.
Komai wuya komai dadi ki sani dakin mijinki shine gatanki yanzu. Ki riqe shi da yanuwanshi,
yanzu kin zama su, sun zama ke. Ban yarda matsala ta fito daga gareki ba. Allah ya baku
zaman lfya. In shaa Allah ba zakiyi dana sanin wannan auren ba. Kullum zan kasance cikin
maku addu'a".
Rungume mammy tayi ta rushe da kuka mai tsuma rai..."wayyo mammy ki yafe min, ki yafe min
banason tafiya".

Da kyar mammy ta banbareta tace..."taybah yanzu dakinki shine gidanki, ki kasance mai tsoron
Allah, kullum shi zai yaye miki baqin ciki ya sanya farin ciki, kuma banda wasa da sallah".

Da kyar su hafsah suka samu suka banbare taybah daga jikin mammy, tana rusa kuka mammy
nayi....su yasmeen ma na taya su......awwwnn..so pathetic.

Saida aka kara komawa gida wurinsu dad suma suka daura nasu fadan sannan aka dauki
hanyar abuja da amarya da misalin karfe 5:00 na yamma.



*SALEEM*

Sake sauke ajiyar zuciya mai nauyi yayi cikin baqin ciki da rashin madafa. Yanzu shyknn ya
tabbata taybah ta zama matar shi. Yarinyar daya tsana deep inside to the core.....Dammit!.... Na
tsaneki taybah!!.

Mukhtar ne ya sake dafa shi cikin damuwa yace..."aboki, wannan tunanin da kuncin da kake
won't solve anything, ka rungumi auren nan hannu biyu. Allah kadai yasan dalilin da haka ya
faru".

Furzar da huci mai zafi yayi sannan yace....."bazaka gane bane, na tsani yarinyar, i just hate
her....ni me zanyi da baqar mace dan Allah, ka dubeni da kyau, nayi kamada mijin baqar mace

balle ita lauje". Saleem ya fada cikin fushi.

"Hmmn, saleem kenan, kabi rayuwar nan a hankali, who knows gobe ko you'll be head over
hills for her? Ka dena cika baki my man". Cewar mukhtar.

"Allah ya sauwaqe, me zanyi da ita, abeeg spare me that riddle, abunda kawai na sani shine
saita gwammaci kida da karatu.

Nikam dai nace maji ma gani....namu ido muga abunda zai faru!!!.




*FAYSAL*

A hankali ya zame wayar daga kunnenshi yayin da wasu hawaye masu tsananin zafi suka zubo
mai, yes shyknn yanxu ya rasa taybah for sure....his happiness, his pretty face, his priceless
jewel to someone who doesn't even know her worth!.
Kuka yake wiwi yana fadin...."taybah na rasa ki, Allah ya bani ikon juriyar rashinki, har a yau da
kike matar wani ban daina sonki ba kuma banji ranar dazan daina ba taybah.....i love you and i
still do". Ya fada cikin kuka nima ina tayashi.......yaxo kawai ga doctor sumayyah durln na bashi
ya manta taybah.




Sai ana kiran isha'i suka shigo garin abuja, gidan nanan yanda yake sai sabon fenti daya sha,
daga gani ansan wannan gidan amarya ne.

Allah bada zaman lfya amaryar likita!.... Nida seeyermerh mun kwashi shoki wurin biki...lol.







*©MSS MJAY*
[12/17/2016, 5:55 AM] Mss Mjay: WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG
*KUNDIN KADDARA*
WWW.HAUSAEBOOKS.COM.NG

Written by
*MSS MJAY*



In dedication to
*SEMBYY LUFF*





*29*

Sai ran sunday yan kawo amarya suka koma, taybah da hafsah sunsha kukan rabuwa thou
bawai suna gari daya bane tun months back.


That same sunday misalin 2:30 na rana, taybah na zaune parlor ta dafe kuncin ta deep in
thoughts na abubuwan da suka faru lately.

Saleem yayi sallama ya shigo, shi duk tunaninshi ba kowa a falon tunda yasan duk sun tafi,
kuma beyi tunanin ganin taybah zaune a falon ba.

Yana shigowa ya hangota zaune a kan kujera tana aikin tunani, kallonta yayi daga sama har
qasa baiga meta sa ba, saboda tana sanye ne ta katon hijabi wanda da alama ta sashi ne tun
lokacin da zatayi rakiya.
"Wai wannan bagidajiyar yarinyar aka bani a matsayin matar aure". Kalaman dake kai kawo
kenan cikin zuciyarshi. "To inyi me da ita?" Ya sake yiwa kanshi tambayar. Cikin sauri yaji
zuciyarshi tana kokarin tattaro mishi shekarunta....17-18yrs....kuma a rasa abun bashi sai lauje
irin wannan, the worst part ma wai baqa....yanda ya hade dinnan ace taybah matarshi ce aii an
gama dashi.

Wani dogon tsaki yaja wanda yayi dalilin dawo da taybah daga kogon tunanin data fada. Cikin
tsoro ta miqe tana fadin......"Sa..san..sannu da zu..wa yaa saleem". Ta fada muryar ta na rawa
tsabar tsoro.

"Keh, uban me kikeyi a parlorn nan? Bari in gaya miki wani abu kiji, karki kuskura ki bari in qara
zuwa in sameki a parlorn nan zaune, keh duk inda kika san zamu hadu karki yadda ki bari haka
ya faru, kuma duk aikin gidan nan ke zaki dinga yi, komai da komai kuwa. Aii tunda kika yarda

aka daura auren nan sunanki sorry....bloody fool! Get the hell out of my sight". Ya fada a
tsawace.

Taybah da tunda ya fara magana ba abunda take banda kuka, da gudu ta nufi dakinta har tana
tuntube da hijabinta saboda tsawonshi.

Kan gado ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login