Showing 27001 words to 30000 words out of 43151 words
Chapter 10 - KARUWAR GIDA END BOOK COMPLETE Hausa Novels Complete By Mrs Sadauki .pdf
ɗau kama ke kuma kin ɗau farin fata"
Ranar nan su Mu'azam ba su kwana a ko ina ba sai a sabon gidan da Dr Ma'aruf ya basu
wanda ke ADS can wajen masallacin jingile,Hajiya Babba sai zaga gida ta ke ta na kwararawa
Dr Ma'aruf albarka.
***GIDAN ALHAJI
Cike da murnar yau Allah ya azurta shi da samun ƙaruwa ta Ƴa mace ya haɗa ƴar ƙaramar
walima iya ahalin shi,zuwa yanzu duk yaran shi murna suke su ma sun samu little sis dama can
su yawan aure-auren ne ba sa so.
Duk wanda ka gani fuskar shi a sake ta ke ya mai nuni da farin ciki amman banda Ma'aruf da
ya koma gefe ya na tunanin ya rayuwar ƙanwarsa za ta kasance duk da dai ya fara ingantata ta
hanyar canza masu muhalli mai kyau.
Alhaji ya ɗauki baby girl ɗin sannan yayi gyaran murya yace "alhamdullah gida yayi ƙamshi,ya
haskaka,ya girmama da zuwan Raihan"duk taɓi ɗiyan shi suka shiga yi Agaishat ta ɗan
murmusa yayinda sauran matan Alhajin suka cicije.
Hidimar da ake ta shagaltar da mutane hakan yasa Hajiya ta zuba wani garin magani farin fal a
cikin biberon ɗin da ake baiwa Raihan ruwan zam-zam.
Cikin rashin sani kuma Agaishat ta ɗauka ta baiwa Raihan ruwan,ashe duk abinda ke faruwa a
kan idon Ma'aruf
***
Mimi na cika kwana bakwai aka yanka mata ragon sunanta Fadimatu, gagarumin biki aka yi dan
kuwa kusan dama Mu'azam mutumen jama'a ne.
Soyayya ƙauna suka haɗe gu ɗaya suka yiwa zuciyar Mu'azam ƙawanya sosai ya ke son Mimi
fiye da komi na shi,a haka har Mimi ta fara girma ta fara ce mashi Daddy Rahama kuma Mami.
Mimi na cikin shekara ta biyu Allah ya yiwa Daddy wani irin buɗi na arziki,nan fah Mami ta aza
masifa a doli suka tashi suka koma sabon gidan da ya gina yayinda Hajiya Babba kuma ta
zauna wancan.
***Bayan 4years
Daddy ne da Mami zaune gaban Dr Ibrah wanda yanzu ya zama cikaken likita,bayani dai ya
sake yi masu kan dukan su lafiyar su lau kawai su jira lokaci.
Su na shirin miƙewa yace "am tsaya na ɗibi jinin ku sai na kaiwa wani abokina mu ga shi mai
result ɗin shi za ta bada"babu muso kuwa suka tsaya ya ɗiba sannan suka dawo gida.
Washegari tun da safe Daddy zai tafi aiki ya ja hannun Mimi suka fita tare ya biya ya aje ta
gidan Hajiya Babba.
Fitar Daddy babu wuya Dr Ibrah ya shigo gidan,sai da ya shigo falon ya ƙwala sallame.Mami ta
fito daga ita sai kayan barci jigida nayi mata kacau-kacau cak ta tsaya ganin ashe ba Daddy ba
ne,har za ta juya sai taji muryar Dr Ibrah "masha Allah a nan Allah yayi babba ƙaddara wacce
ba ta dace da baƙar fata ba"da sauri ta juyo ta na kallon shi .
Gira ya ɗaga ya ajiye takardun hannun shi ya fara takawa zuwa gare ta,wuyanta ya sunsuna
yace "Hummm komi ma na Gimbiya haɗaɗe ne"lumshe ido Mami tayi ta na jin tsikar jikinta na
tashi.
Wuyanta Dr Ibrah ya fara yiwa kissing kafin ya koma ga lips ɗin ta,cikin ƙanƙanan lokaci ya
birkita mata lissafi.Ɗaukarta yayi cak ya nufi ɗaki da ita,abinda Mami ba ta taɓa tunani ba shine
ya faru wai ita ce tayi zina da wayon ta.
Kuka ta shiga yi sosai Dr Ibrah na bata haƙuri,ganin ta ƙi barin kukan yasa ya kimtsa ya bar
mata gidan kafin a rutsa shi.
Da marice Daddy ya shigo gidan amman sai yaji shi tsit, ɓangaren Mami ya nufa yaji ƙofar a
ƙage fitowa yayi ya nufi kitchen dan ya ga babu komi a dining nan ma wayam .
Falo ya dawo ya zauna idon shi ya sauka da farar takarda,ya ɗauka ya karanta sai ya miƙe
murmurshi kan fuskar shi ya nufi ɗakin shi wanka yayi sannan ya kira Dr Ibrah amman har ta
gama ringing bai ɗauka ba.
Motsin da ya ji yasa shi waiwayo Mami ce kallonta ya tsaya yi ganin tayi wani irin sanyi"ashe
har ka shigo ?barka da zuwa ina Mimi"
"Yauwa!ta na gun Hajiya Babba yau amarci ni ke son mu sha sosai"ya ɗaga mata gira gabanta
ne ya faɗi sai ta ke ganin tamkar zai gane ne in ya kusanceta.
"Ayya Daddyn Mimi banda lafiya kuma"da sauri ya kai hannun shi kan wuyanta ai kuwa yaji
kamar da alamar zazzaɓi,magani ya bata sannan ya fita ya nemo masu abinda za su ci su da
masu gadi.
Sai da aka kwashe wata ɗaya cur sannan Mami ta fara sakin jikinta ta koma kamar da,Mimi
kuwa na gidan Hajiya Babba zamanin ta.
Tun da safiya ta waye ta ke zabga amai,babu ɓata lokaci Daddy ya kaita asibiti awon farko Dr
Ibrah yace mashi "congratulations kai ma ka kusa zama baba"da murna Daddy ya rungume shi
can kuma ya sake shi yayi sujada shukur.
Gira Dr Ibrah ya ɗagawa Mami ya mata nuni da cikin jikinta sannan ya nuna kan shi ma'ana dai
ciki na shi ne ba na Daddy ba,kawar da kai tayi gefe dan dama tun farko ba tayi wata murna ba.
Murmushi ta saki tare da ambaliya hawayen baƙin ciki na da aurenta za ta haifi shege a zuci
tace "lalle na tabbata *KARUWAR GIDA* tunda har zan haifi ɗan da ba na mijina ba"Daddy
kuwa a tunanin shi kukan murna Mami ta ke a haka ya kwasheta suka wuce gidan Hajiya
Babba..... [05/12 à 14:08] Cham~rose: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI
KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA
TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI♀️ mai
son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*Page 35-36*
Haka Mami tayi rainon cikinta har ta haifi ƴarta mace aka saka mata suna Ameera,sosai Daddy
ke nunawa ƴaƴan nashi so amman ya fi ƙaunar Mimi.
Sam ba za ka ce Mimi ba ƴar su ba ce yadda suke ririta ta da nuna kulawar su fiye da
Ameera,lokaci zuwa lokaci Dr Ibrah ya na kawowa Mami farmaki a duk lokacin da Daddy ya fita
tun ta na kaucewa har suka ɗinke kullum sai sun yi RDV.
Ameera na da 3years Mami ta kuma samun wani cikin,sosai Daddy ya nuna murnar shi.Ita
kuwa Mami masifa ta rinƙa yiwa Dr Ibrah na ya munafinceta bai yi mata allura hana haihuwa
ba,to daga nan ne suka yi baran-baran suka rabu Mami ta tuba.
Cikinta na shiga watan haihuwa ta haifo Twins duk mata aka sa masu Imane da Ihsane to tun
shi ba ta sake haihuwa ba.
***Cigaban labari
Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Daddy,sam bai tsammaci haka ba tunanin shi ma bai taɓa
kawowa da rainon ƴaƴan wani ya ke ba.
Ana cikin haka wayar shi ta ɗauki ringing *Dr Ma'aruf* ya gani cike da mamakin kiran Daddy ya
ke kallon screen ɗin wayar dan an fi shekarar da tafi goma rabon shi da Dr Ma'aruf ɗin,zai iya
cewa ma tun tashin su daga gidan da ya basu saboda ya sha gwada lambar amman ba ta
shiga.
Sai da ta tsinke Daddy bai ɗaga ba,wani kiran ya shigo danne zuciya yayi ya ɗaga kiran ba tare
da yace komi ba "Assalamu alaikum Alhaji na zo gida ne sai na gan shi a rufe"
"Ina Clinic Agaji ne Madam babu lafiya"ba'a ƙara cewa komi ba daga ɗayan ɓangaren aka
kashe wayar.
Can kamar minti ashirin sai ga wata dalleliyar mota tayi parking a harabar asibitin,su uku ne duk
sukafito Alhaji ne,sai Agaishat da kuma Ma'aruf wanda shi ya tuƙo motar.
Dialing number Daddy yayi ya na ɗagawa yace "am ka fito mu na harabar asibitin"da
"toh"Daddy ya amsa ya miƙe a kasalance ya fito.
Gaban shi ne ya faɗi lokacin da yayi tozali da Agaishat wacce ta ƙurawa hanya ido,ƙarasowa
yayi amman ya kasa ɗauke idon shi kanta saboda tsantsar kama da Mimin shi da ya ga ta na yi.
Hannu ya basu suka yi musabaha yayinda suka fara tambayar shi mai jiki,jin murya Agaishat
kuma ya sa zuciyar shi yin rauni tabbas ko makawo ya laluba ya san wannan jinin Mimi ce.
Murmushi Dr Ma'aruf yayi haɗi da sosa ƙeya yace "in ba za ka damu ba ina son mu ɗan zauna
za mu yi magana"ya faɗa ya na mai ɗan waige-waige.
Murmushi Daddy yayi yace "maganar mi kuma Dr ?bayan tun kafin ka faɗa na san kun zo nan
ne dan ku raba ni da Mimina"ya yi maganar cikin tausayi yayinda idon shi da suka yi ja tun ɗazu
suka cika da ƙwalla.
Alhaji yace "Ma'aruf kenan dai dagaske ɗin ne Allahu Akbar"ya faɗa ya na mai zubewa ƙasa ya
na sujidah shukur kafin ya ɗago ya fashe da kuka kuma Agaishat ma kukan ta taya shi.
Waje suka samu can ƙarƙashin innuwar mangwaro suka zauna Dr Ma'aruf ya shiga baiwa
Daddy labarin komi dangane da haihuwar ƴaƴa Mazan da Allah ke azurta Abban shi sai Mimi ce
kaɗai mace.
Ajiyar zuciya Daddy ya sauke yace "to miyasa ba ka barta cikin gantan ta ba?"Dr Ma'aruf yace
"saboda kar a cutar da ita,na san in na barta za'a kasheta ne saboda su sauran matan ba sa so
ace an fifita ƴar kishiyar su fiye da nasu ƴaƴan kuma maganar da ni ke yi maka yarinyar da na
masayan tuni suka kasheta duk da ƙoƙarin kariyar da nayi ta bata"
Cikin son kawar da zancen tashin hankali nan Daddy yace "yanzu dai Mimi ta na Niamey in
shaa Allah gobe zan sa su dawo"
Mimiƙewa suka yi sun so shiga duba Mami amman Daddy ya hana ta hanyar ce masu barci ta
ke,su na tafiya Daddy ya kira Alhaji Kamal yace ya yiwa su Hajiya Babba réservation ta dawowa
gobe ya na gama faɗa ya kashe wayar shi kwata-kwata.
Takarda ya samu gun Dr ya yi rubutu ya aje ta kusan kan Mami kafin ya fice,bai zarce ko ina ba
sai gidan Hajiya Babba .
Toilet ya shige ya sakarwa kan shi shower,a sannu ruwan ke dukan fatar jikin shi lumshe ido
yayi ya na tunanin rayuwa hawaye idon shi suka shiga fitarwa.
***
Arerewa haɗi da shewa Lami tayi tace "wuuu *KARUWAR GIDA* an kusa saukewa,a toh dama
ƴan jami'a ai duk ƴan iska sun fi yawa yanzu ba sai ayi mu gani ba in tusa ta hura wuta sai mu
ga yadda za'a yi karatun hhh"ta ɓaɓake da wata dariya mugunta.
Shiru Anna tayi ta na nazartar kalaman Lami kafin ta maido duban ta ga Fadila wacce tayi fari
fyarau ta ƙara ƙiba,kallon da Anna ke yi mata ne yasa ta tsargu kawai sai ta miƙe ta nufi ɗaki.
Tafiyarta Anna ta bi da kallo ta na sake tantance ta,ko minti ɗaya Fadila ba ta yi ba Anna ta
shigo.Da sauri ta juyo ta na kallon mahaifiyarta ta haɗi da zare ido kamar wacce ta yiwa sarki
ƙarya.
"Cire min hijabin jikin ki baƙar munafuka"cewar Anna ta na harar Fadila,kasa cire hijab ɗin tayi
hakan yasa Anna ta ja hijabin da ƙarfi ta cire.
Taɓa hannuwa ta shiga yi ta na salalami sakamakon cikin Fadila da ta gani kamar ƴar ƙwarya
ya fito yayi mata wani cercle ai Anna ba ta san lokacin da ta ɗauke ta da mari ba ta shiga
dukanta haɗi da tambayarta uban wa yayi mata ciki amman ta ƙi faɗa.
Sai da taji wuya sosai sannan tace "Nasir ne Anna"wata uwar gwabza ta kaiwa bakinta nan take
jini ya ɓalle,ƙetare ta Anna tayi ta shiga ɗakinta ta ɗauki hijabi ba ta zarce ko ina ba sai gidan su
Nasir .
"Uban da ya ɗaura auren uwarka da uban ka Allah ɗebe masu albarka,asarare haihuwar asara
da yarda Allah ba za ka gama da duniya lafiya ba"wannan shine abinda Anna ta faɗa lokacin da
ta shigo gidan su Nasir madadin sallama.
Duk fitowa suka yi suna kallon ikon Allah, Iyani ta fito daga banɗaki kallon kwabo saura takwas
ta yiwa Anna kafin tace "baiwar Allah daga gidan mahaukata kika gudo da za ki shigo mana
gida ki na zage-zage?"
"Kutumar uban can!ba ki ma gane ni ba?to uwar Fadila ce wanda tanbaɗaɗen yaron ki ya
ɗirkawa ciki"dariya Iyani ta fashe da shi tace "to sai mi dan yayi mata cikin?ai haka duniya ta ke
dama abinda aka yiwa naka wata rana na ka ɗin ne zai yi ma wata dubi can ƴata ce nima wanin
ne ya mayar da ita haka"ta ida maganar ta na mai nuna mata Fauziya wacce ke tsaye da ƙaton
cikinta duk ya mayar da ita wata kala.
"Ina ruwana da ƴar ki ni tawa na sani dan haka ki shaida mashi da zarar ya dawo,gobe kotu za
ta raba mu"ta na gama faɗa ta fice,tsuki Nabee tayi ta koma ɗaki a zuciyarta ta na mamakin
yadda har ƴan mata suke sakacin baiwa namiji kansu kamar shashashu koko dan ba su ƙwarai
a barikin ba ne ?oho
***
Cike da masifa Hajiya Babba ta shiga balbale Alhaji Kamal da faɗa sai kace ba sirikin ta ba,a
haka dai ta tattare kayan su ni kuwa sai murna ni ke zan koma gida gun Daddy.
Washegari 16h tuni motar mu ta dira a Maradi, drever Daddy ya aiko ya ɗauke mu.
Gidan Hajiya Babba aka kai mu,da murnata na buɗe mota na fito na shiga da gudu ina
"Daddynaaa "cak na tsaya gani baƙin fuska duk miƙewa suka yi suna kallona nima haka sai dai
na tsayar da dubana ne ga mai irin fuskata.
Murmushin da yafi kuka ciwo Daddy yayi yace "Mimina "a Shagwaɓe na je na faɗa jikinsa ina
turo baki nace "i miss You Daddyna shine ka ƙi tafiya ka tarbo ni ai da kai na so idona su fara
gani sai kawai ka turo min drever"laƙace min hanci yayi yace "ba ki ga baƙi ba ne?"juyawa nayi
gun su sai na ga ashe mu su ke kallo.
"Yau na ga ragguwa yarinya dan rashin tausayi kika bar ni da dakon ƙaton aljanin ki,ina dalili
yarinya kamar wata..."maganar ce ta maƙalewa Hajiya Babba ganin ashe da mutane falon
gaisheta suka shiga yi ta na amsawa tare da yi masu kallon ko ina ta san su.
Teddyna ta jefo min ta na hararena nayi dariya ina kakaɓe shi dan ya faɗi, Hajiya Babba na
zaunawa Daddy yayi gyaran murya ya fara bada labari tiryan-tiryan tun daga ranar da aka
ɗauko ni daga gidan marayu.
Hawaye shararaaa haka suke zuba a idona na ƙurawa Daddy su ƙyaftawa ban yi,hutu na
wucen gadi kwanyata ta tafi ba ta dawo ba sai da naji Daddy na cewa "Mimi ga biologique
parents ɗin ki nan".....
[07/12 à 07:45] Cham~rose: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI
KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA
TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI♀️ mai
son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822
*Page 37-38*
Banda kallo babu abinda nayi saboda sam zuciyata ta kasa yin aikinta daidai ya da ya kamata,
Agaishat ta taso daga inda ta ke ta zo ta rungume ni wani yammm naji da sauri na sauke ajiyar
zuciya ita kuwa kuka ta ke.
Samun bakina nayi da furta "Momyyy"cire ni tayi daga jikinta ta ƙurawa fuskata ido ta na
murmurshi tace "dauther ina son ki sosai na godewa Allah da gwada min wannan rana,ta so ki
je gun Abban ki saura kaɗan zuciyarsa ta buga saboda ke"ta faɗi haka ta na mai miƙar da ni
tsaye mu ka nufi gun dattijon arziki wanda ya ƙura min ido tun shigowa ta.
Duƙawa nayi zan gaishe da sauri ya jawo ni na faɗa jikinsa,wasu sanyayun hawaye suka shiga
malala a idon shi "Fadimatu na? Allah raya ki a kan sunnah ya tsare min ke daga sharrin ƴan
hassada da baƙin ciki..."kuka ne yaci ƙarfinsa sai ya ƙyale.
Hajiya Babba wacce tayi suman zaune tace "oh Allah duniya babu kyau an raba tsoka da jini
gudun mugayen ɓoye,ina ta Rahamun ta ke ta san da maganar ?baiwar Allah ta so Mimi kamar
ranta"ɗagowa Daddy yayi da jajayen idonsa yace "na saketa ai"da sauri duk mu ka kalle shi
dafe zuciyar shi yayi sannan yace "laifi ta yi min mafi muni wanda duk mai ƙaunata ba zai bari
na cigaba da zama da ita ba,Rahama ta cuce ni Hajir mu ta rasa da wanda za ta ci amanata sai
da babban abokina"
"Mine?cin amana kuma?"cewar Hajiya Babba shiru Daddy yayi dan sai yanzu ya gane da bai
kamata ya faɗi haka ba "Mimi tashi kije ki yi wanka"cewar Hajiya Babba ,jiki ba ƙwari na miƙe
tare da nufar part ɗin ta.
Sai bayan Mimi ta tafi ne sannan Daddy ya fayyace masu komi Hajiya Babba kuka ta saka
Momy na bata haƙuri,Abba kuwa nasiha ya shiga yiwa Daddy dan ya ɗauke shi tamkar ɗan
cikinsa.
Dr Ma'aruf ya gyara zama yace "gobe ka same ni a asibitin mu zan duba na hauda ka kan
magani, sannan ka kawo min result ɗin da sauran suka yi ma gwaji" Daddy yace "in shaa Allah
na gode".
Dakyar suka daidaita nutsuwar su suka fara shan fruits,ni kuwa ko da na gama wanka na shafa
mai da turare kayan da Hajiya Babba ke tara min na ciro riga t-shirt fara da buje blue na jeans.
Tunda na fito mu ka haɗa ido da Daddy wanda ke