Showing 21001 words to 24000 words out of 43151 words

Chapter 8 - KARUWAR GIDA END BOOK COMPLETE Hausa Novels Complete By Mrs Sadauki .pdf

01 Jul 2025

4505

ceceta,da sauri ta saɓi hijabinta da hannu ta ari na kare "Suraj ka dubi

tantiriyar yarinyar nan wai ta zo har office ɗina neman ra'ayina kwanakin baya ma ta zo na
koreta,ban san inda ta samu lambata ba haka ta ke aiko min hotunan ta da mugunyar
shiga.Amman da yake ƴar iska ce shine ta sake dawowa"haƙuri PA ya shiga baiwa Daddy ya na
mai cewa "uwannan su ne ɓata gari barin su cikin gari ba ƙaramar illa za su yiwa mutane
ba"Daddy yace "shiyasa fah na mayar da Mimi Niamey ka san classe ɗin su ɗaya ban san ko
miyasa ta ke bibiya ta ba"PA yace "sir wannan da ka ganta ai ka ga *KARUWAR GIDA* saboda
idonta a tsatsaye suke"cike da ɓacin rai Daddy ya rufe office ya nufi hanyar gida.

Tun da ya karyo kwanar ya ke jin zuciyar shi na wani matsiyacin bugawa,da mai gadi ya buɗe
mashi get ya shiga yayi parking sai murmurshi mai gadi ya ke wanda Daddy bai san na minene
ba.


Wani irin sarawa kan Daddy yayi ya na maimaita kalmar "yi da ƙarfi Dr na yauwa da
ƙarfi"numfashin shi ne ya tsaya cak na wuccin gadi kafin ya samu zuciyar shi ta fara halbawa da
ƙarfi da ƙarfi.
Zaune yayi a falo dafe da zuciya dan ba zai iya ƙarasawa ciki ba,kar ya tai ya ga abinda zai sa
zuciyar shi yin bindiga.Ya na nan zaune ya ke jin sautin su tun suna yi da ƙarfi har suka
ƙyale,can kamar minti biyar Dr Ibrah ya saɓo Mami zuwa falo babu kaya a jikinsu.
Wani irin sakin Mami Dr Ibrah yayi ya ta faɗi timmm lokacin da idon shi suka sauka kan
Mu'azam babban aminin shi,"my lovely kan ka ɗaya da za ka sak...."ragowar maganar ce ta
tsaya a maƙoshi sakamakon haɗa ido da suka da Daddy ya zuba mata idon shi da suka yi jawur
tsabar ɓacin rai.... [29/11 à 15:22] Cham~rose: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI
KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA
TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI‍♀️ mai
son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 27-28*

Tsananin furgice,tashin hankali,rashin zaton faruwar haka ya haifarwa da Mami zubar jini
tamkar wacce aka buɗewa pampo kafin wani lokaci tuni lumfashinta ya tsaya cak lokacin da tayi
ƙoƙarin tashi tsaye ne juwa ta kayar da ita.
Duk tashin hankalin da Daddy ke ciki ganin Mami cikin wannan halin yasa ya mayar da shi gefe
ya nufota ya na kiran sunanta da wannan damar Dr Ibrah ya koma ɗaki ya saka kayan shi tare
da ficewa daga gidan.


Duk ruwan da Daddy ke malaya mata bai sa ta farfaɗo ba,ɗakinta ya shiga ya ɗauko mata
kayan jikinta bayan ya saka mata ya ciciɓeta zuwa asibiti.

An ɗauki lokaci kafin likita ya fito "masha Allah mun yi nasarar daidaita numfashinta sai da
kamar wuya cikin jikinta ya tsaya duba da irin shock da attaque ɗin da suka kawo mata
farmaki,zuciyarta ma kingin kaɗan ta buga tsabar tsoro"banda ido babu abinda Daddy ya iya
sarrafawa su ma likitan ne ya zubawa wasu,sai da zuciyar shi ta dawo daga suman wucen gadi
sannan ya fara jujuya maganar likita bisa lizamin hankali a fili yace "ciki?ciki ne da ita?"cikin
tausayi Dr yace "kayi haƙuri bawan Allah nima na so ace ya tsaya duba da shekarun da kuka
ɗauka ba ku taɓa samun haihuwa ba,nayi mamaki ma sosai yadda ƙwan halittar ka har iya
zama a cikin mahaifarta dan kuwa a wancan karon da na auna ku na ga kamar ma impossible
ne saboda ƙarfin ƙwayar hallitar ka amman duba da lamarin na Allah ne shiyasa ban yi
décourager ɗin ku ba"


Idon Daddy ne suka rikiɗa suka jawur kamar garwashin wuta,shi sam ya ma manta da ya taɓa
zuwa wannan asibitin tun shekarun baya da suka wuce to wai mi ma ke faruwa?

Cikin ruɗani yace "Dr wannan shine ciki na wajen huɗu da ta samu amman uwancan duk da ta
haife su"ido Dr ya zaro yace "kuma da kai?"kallon ban gane ba Daddy yayi masjid sai yayi
saurin cewa "ina nufin kuma kai ne uban cikin na gaske?"

"Daram!dam!dimmm"haka zuciyar Daddy ta buga,yayinda yawun bakin shi suka kafe
ƙwaƙwalwar shi ta daina tunani kafin wani lokaci zuciyar shi ta tsaya cak samakon hasaso
abinda ya ke fatan ko a mafarki ne ba zai so ace hakan ta faru ba.



*Wasu shekarun baya da suka shuɗe...*


CEG3 makaranta ce da ke jamhuriyar Niger a garin Maradi,makarantar ta kasance ta ɗaya
fannin ƙoƙari da hazaƙa a duk makarantun gwamnati da ke Maradi.
Ɗalibai ne zaune matasa ƴan 4em duk kowanensu sanye ya ke da uniforme,a tsarin classe ɗin
4em mafi akasari matasa ne sabbin balaga saboda a ƙiyasi ƴan 13 zuwa 15years ne.
Gungun students kawai kake gani kowa da abinda ya dame shi,wasu na cin abinci wasu na
danna wayar hannu yayinda wasu ke hira.


"Yauwa yanzu abinda za'a yi kowa ya zo ya faɗa mana ra'ayinsa idan ya girma aikin mi zai
yi"cewar wani ɗan matashin yaro mai suna Hafiz,nan fah kowa ya shiga faɗin ra'ayinsa haɗi da
hujja wasu sun zaɓi koyarwa,wasu aikin soja,masu son kuɗi sun zaɓi aikin ɗan sanda dan
karɓar cin hanci.
Hafiz ya dubi Mu'azam yace "ku biyu ya rage ku faɗi ra'ayin ku kai mi kake son
zama?"murmurshi Mu'azam yayi yace "ina son na zama ɗan kasuwa nayi kuɗi na gina manyan

gidaje,na sayi motoci dayawa ta yadda zan auri mata huɗu tsalatsala masu kyau "dukansu
dariya suka yi dan kuwa kusan kowa ya san yadda Mu'azam ke son yin aure tun da ƙananun
shekarunsa saboda ya na da yawan sha'awa.
Ibrahim shine kawai bai faɗi ra'ayinsa ba hakan yasa yace "ku tsaya-ku tsaya dariyar ta isa
haka nan a bari na faɗi nawa nima"duk ƙyalewa suka yi suka zuba mashi ido.


Sai da ya gyara zama sannan yace "ni kuma likitan mata ni ke son zama,saboda na rinƙa kallon
mata yadda ni ke so in yau na ga baƙa gobe fara zan gani daga nan nima sai nayi profiter eh
yane"ihu suka kwashe da shi wasu na sake zuzuta shi yayinda Mu'azam ya kai mashi dukan
wasa dan sun fi kusa duk a cikin délégation ɗin.

"Ɗan iska in mutane suka gane ai sai a kore ka"cewar Mu'azam, Ibrahim yayi dariya yace "ai shi
Dr Ibrah ya na da ilimi da wayo ba zai yi yadda za'a gano shi ba ƴan ƙauye kawai zan rinƙa eh
yane" Mu'azam yace "ku na ji fah wai Dr Ibrah hhh shi har ya ga ya zama likitan hhh"nan aka
shiga yiwa Ibrahim dariya ana ce mashi Dr Ibrah ashe wannan abu yayi mashi ciwo sai ya ga
kamar da gayya Mu'azam ɗin yasa yin haka collègues sun dare shi.


Cikin fushi ya miƙe ya fice ya bar class ɗin,da sauri Mu'azam ya bi bayansa ya na kiran sunan
shi amman ya ƙi ko da juyowa ne balle ya tsaya.Da gudu ya sha gaban shi tunkuɗe shi Ibrahim
yayi ya wuce ya bar Mu'azam da mamaki.


Washegari da suka dawo école sai students suke kiran Ibrahim da Dr Ibrah to fah shikenan
sunan ya bi shi tun ya na faɗa da jin haushi har ya haƙura amman har yanzu ba su shirya da
Mu'azam ba.

A gajiye ya shiga gidan ya na dab da shiga ɗakin shi ya ji muryar Hajiya Babba na cewa "yau
kuma lafiya na ga sai ɓata fuska kake kuma ko gaishe ni ba za'a yi ba?"ƙeya ya ɗan sosa yace
"a gajiye ni ke wlh ina sauri naje na kwanta ne"cewar Mu'azam Hajiya Babba ba ta ce komi ba
sai kayan Munawara da ta ke kwashewa kan igiyar shanya.
Mu'azam na shiga ɗaki ya haye ƴar sofar shi,tunanin canzawar Ibrahim ya ke son yi tare da
nemo mafita amman abu ya sauya salo sakamakon ƙugi da marar shi ta ke.
Dafe marar yayi ya furta "ya Allah!"a zuci kuwa cewa ya ke "ƙila wannan shine silar mutuwata ta
yaya zan jure wannan muguwar sha'awar a ƴan ƙanƙanan shekaruna?banda kuɗi balle in ce
zan yi aure,to wace ce ma za ta aure ni ?"huci ya furzar tare yunƙurawa ya tashi.


Dala biyar ya lalabo a aljihu tare da fita waje ya leƙa ya aiki wani yaro ya sawo mashi
ƙanƙara,yaron na miƙo mashi ya buga ƙanƙarar ga bango sannan ya shige ɗaki.

Cikin wani ƙyale ya saka ƙanƙarar ya fara dannawa ga mararsa,a hankali ya ke fitar da
numfashin wahala a sannu ciwon ya ke ragewa can barci ya ɗauke shi.



Sai wuraren ƙarfe biyun rana ya farka wandon shi duk ya ɓace da sperm saboda mafarkin da
yayi,bokiti ya cika ya je yayi wankan tsarki haɗi da yin na sabulu a ƙarshe ya wanke wandon.

Doguwar riga ya saka ya fito daga banɗaki,alwala ya ɗaura kafin ya wuce masallaci.
Ya na dawowa ya tarar da Munawara zaune a ɗakin shi ta na jiran sa,cikin sangarta tace "ya
Mu'az tun ɗazu ni ke jiran ka kazo mu ci abinci"bai ce komi ba ya zauna haɗi da buɗe abincin
da ta kawo masu.
Bismillah yayi ya fara ci ita ma sai ta saka hannunta,"Ya Mu'az albishirin ka"ɗagowa yayi kalleta
ganin sai murmurshi ta ke zubawa "ya aka yi ne?"sai da ta ɓoye fuskarta tace "dama ɗan gidan
Alhaji Abubakar ne yace ya na sona zai aure ni sai mu tafi Makka "shiru yayi ya na kallonta
yarinyar duka ba za ta wuce 12year ba amman murna ta ke za ta yi aure.

"Yaushe ya gaya maki haka?kuma kin tabbata dagaske ya ke?"cewar Mu'azam kafin Munawara
tayi magana suka jiyo muryar Alhaji Abubakar da sauri Mu'azam ya fita ya na amsa sallamar
saboda duk unguwar Alhaji Abubakar ya fi su kuɗi sannan mutumen kirki ne tun rasuwar
mahaifin su shi ya ke aiko masu da abinci duk wata.

Cikin girmamawa ya gaishe shi haɗi da yi mashi iso gun Hajiya Babba,har Mu'azam zai fita
Alhaji yace "dawo ka zauna yaron kirki "zaunawa Mu'azam yayi.


Nan Alhaji yayi gyaran murya tare da gaya masu abinda ya ke tafe da shi dangane da auren
Munawara da yaron wajen shi Kamal ke so, Hajiya Babba tayi murmurshi tace "ai Alhaji duk
ƴaƴan ka ne duk yadda kayi daidai ne,ko yau kace za'a ɗaura ni ban ga wata matsala ba tunda
da kai da kaya duk mallakar wuya ne".

Sosai Alhaji yayi godiya ya dubi Mu'azam yace "ya karatun har yanzu ka na nan kan bakar ka
na son karantar business ko yaya ?"kai Mu'azam ya ɗaga yace "eh in shaa Allah" "ok babu
matsala gobe ka zo ka same ni tun da ba'a makaranta sai mu tattauna ka ga za ka iya farawa
tun yanzu ta yadda a gaba ba za ka ji wahalar shi ba"godiya Mu'azam yayi.



***Bayan 1week

Hajiya Babba ta gayyato dangin mahaifin su Mu'azam suka tarbi lefen Munawara,dukan su sun
yaba inda kuma a nan take aka ɗaura aure biki kuma sai zuwa gaba.
Ɓangaren Mu'azam kuwa tuni ya fara kasuwanci wanda Alhaji ya ɗora shi a kai,a kullum in ya
taso daga school shago ya ke wucewa yayinda kuma weekend ya ke zuwa da safe tuni cikin
ƙanƙanan lokaci Mu'azam ya fara canzawa yayinda shagon da Alhaji ya bashi ya ƙara bunƙasa.


Ganin Mu'azam ya sayi babur shine yasa Ibrahim saukowa daga dokin gaba,nan fah suka
shirya inda a kullum Mu'azam sai ya je gidan su Ibrahim ɗaukar shi sannan su wuce school.


Tafe ta ke ta na yauƙi irin na ƴan matan zamani sai wani karairaya take ta na juya ƙugu,cak
Mu'azam ya tsaya daga tuƙin da ya ke ya ƙura mata ido ta miror har ta kawo daf da su.

"Am ƴan mata sannu"ya samu bakin shi da furtawa,tsayawa Rahama tayi tare da dafe ƙugu tayi
wani fari da ido wanda ya sa zuciyar Mu'azam da gangar jikinsa amsawa.

"Ka tsayar da ni malam ina sauri ne"ta faɗa cikin dadaɗar murya wacce Mu'azam yaji duk
duniya babu muryar da ta kai ta ta daɗi "dan Allah in ba za ki damu ba ina son ki ban lambar
wayar ki"wani kallo tayi mashi irin na tara saura kwabo.

Dr Ibrah yace "please ƴan mata ki taimakawa abokina mana ganin ki kawai ya sa duk ya fita
hayyacin shi,in kin ƙi ba shi ƙila ya some min nan"ya ida maganar cikin raha wanda hakan yasa
ta yin murmushi haɗi da zayyano mashi numberta.

"Sunan jaruma?"cewar Mu'azam "Rahamatullah"ta bashi amsa.....
[02/12 à 12:29] Cham~rose: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI
KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA
TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI‍♀️ mai
son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*29-30*

Tunda Mu'azam ya gamu da Rahma ya ɗauki son duniya ya ɗora mata,gabaɗaya hankalin shi
na kanta komi ya samu Rahma dai tsabar son da ya ke yi mata ya sa duk wani abu da ya shafi
harafi mai *R* ya ke son shi.


Tuni sunanta ya je gun Hajiya Babba babu kunya haka zai zauna yayi ta bata labarin
Rahama,Munawara kuwa kullum cikin tsokanar shi ta ke ta kan ce duk ranar da Rahama tace
ba ta son shi daga ranar gidan mahaukata za su kai shi.

Ɓangaren Rahama kuwa ba wani sosai ta ke son Mu'azam ba dan ita tafi son namiji kalar fatar
ta wato fari,sai irin yadda ya ke yi mata hidima yasa ta bashi wani gurbi a zuciyar ta .


Cikin masifa Ishalle ta ɗaga labulen ɗakin tace "ke Rahamu uwar mi kike yi da har yanzu ba ki
fito ba?ko ba ki ji tun ɗazu aka aiko Mu'azu na waje ya na kiran ki ba?"


"Kimtsawa ne ni ke yi tashina daga barci kenan,amman tsabar jaraba har ya ƙumo sammako ya
zo mtsw"ta ja tsaki "to zauna nan dan ubanki garin kallon ruwa kwaɗo yayi maki ƙafa kaf
samarin ki akwai tamkar shi?ina ce katifar da ta ke sa ki ranar barci shi ya saya maki ita
ko?"Rahama ta turo baki tace "kai anty abun kuma har da gori dan ya saya min katifa?"tsuki
Ishalle tayi ta saki labulen direct ƙofar gida ta leƙa ta cewa Mu'azam "Bismillah shigo mana ka
tsaya waje kamar wani baƙo"kai Mu'azam ya sosa yace "antyn mu ina kwana?"tace "lafiya lau
wuce mana ta na cikin ɗaki"babu muso Mu'azam ya nufi ɗakin Rahama.


Ta na ƙoƙarin saka riga ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,da sauri Rahama ta wawuri hijab ta
saka a birkice ma ya ke.
Murmushi Mu'azam yayi ya na kokowa da numfashin shi saboda rabin breast ɗin ta da ya gani
ta sama farar bra ɗin jikin ta.

Cikin masifa tace "Mu'az miye haka sabida Allah in fah ka tarar da ni ciki mugun hali?amman ai
ka ma riga ka gani"ta faɗa ta na turo baki haɗi da juya mashi baya.

"Kiyi haƙuri babyna anty tace na shigo ai"ya faɗa cikin kalar tausayi,"shine dan tace ka shigo sai
ka biye mata ko?"ta faɗa tare da juyowa ta watsa mashi harara.


Murmushi yayi yace "baby ni kike harare kuma?" Ta bashi amsa da "eh ɗin ai kai ne minene na
zowa tun da safe ?"

"Baby sabuwar waya na saya maki shiyasa nace bari na biyo na kawo maki tun jiya na saye ta
amman nace bari har na gani in ba ta dawata matsala sai na kawo maki"Mu'azam ya faɗa tare
da miƙo mata waya sabuwa dal a kwali.


Har ƙasan zuciyar ta taji daɗin haka sai dai ta ƙi nunawa a fuska sai ma kumbure-kumbure da ta
ke yi,cikin rashin jin daɗin sauyin na ta yace "dan Allah baby kiyi haƙuri Allah ba zan sake
ba,karɓi ki duba ki gani Allah sa za ta burge ki"ya ida maganar da ɗan murmurshi.

Karɓa tayi ta fiddo ta,tecno ce Spark 5,tsabar daɗi ba ta san lokacin da murmurshi ya suɓuce
mata ba.
Mu'azam kuwa bawan Allah wata irin ajiyar zuciya ya sauke ganin murmurshi kan fuskar
Rahama.

Tsayawa tayi ta na kallon shi "mi kake ma murmurshi?"amsa ya bata "saboda ganin ki cikin
walwala"wani tausayin shi ne ta ji yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da ɗan ƙarfi "tabbas
Mu'azam shine masoyin gaskiya"ta faɗa a zuci idonta na cika da ƙwalla.


"Ina son ka Mu'az"ta faɗa hawaye na zubowa a kumcinta,wani girrrr ya ji haɗi da yarrr a take
kuma tsikar jikinsa ta miƙe yau ne karon farko da ta taɓa faɗa mashi kalmar so.


Shi ma bai san lokacin da hawayen suka zubo mashi ba,ya duƙa yayi sujada shukur ita kuwa
dariyar shi ta shiga yi ganin yadda ya ke ta yiwa Allah godiya da ya gwada mashi wannan rana.


Ishalle da ke bakin ƙofa laɓe duk ta na jin komi ta murmursa ta na mai barin gun,sallama
Mu'azam yayi mata ya wuce shago.


Ya na zuwa ya tarar da Dr Ibrah zaune shi da wani yaron da suke gudanar da sana'ar tare "sai
yanzu ka tawo?"cewar Ibrah ya na mai kallon Mu'azam wanda ke tangale babur.

"Eh wlh ka ga na daɗe ko?gidan su baby na biya ya ne da fatan ka tashi lafiya?"cewar
Mu'azam ya na mai baiwa Ibrah hannu wanda yayi kicin-kicin da fuska jin ya ambaci sunan
Rahama.

"Lafiya kake wani cin magani?"Mu'azam ya tambaye shi "ban sani ba,kai shikenan wannan
yarinyar ta maida ka ɗan ƙaramin mahaukaci komi Rahama sai kace wata autar mata mtws ni
ban ga ma abinda ka gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login