Showing 24001 words to 27000 words out of 43151 words

Chapter 9 - KARUWAR GIDA END BOOK COMPLETE Hausa Novels Complete By Mrs Sadauki .pdf

01 Jul 2025

4504

a jikin ta ba da har kake rawar jiki a kanta"Ibrah ke magana cikin
tsantsar fushi da kishi.

"To ni dai ina son ta a haka kai ma ya kamata ka so duk abinda ni ke so"Mu'azam ya faɗa cikin
rashin jin daɗin abinda abokin nashi ya faɗa a kan Rahama.

Baki Ibrah ya taɓe yace "can ku ƙarata kai da kaji za ka iya,ni tsohuwar wayar ka na zo karɓa
tun da jiya ka sayi sabuwa" sosai ƙeya Mu'azam yayi yace "ai Rahama na saya ma ita shiyasa
ma ka ga na daɗe ban zo shago ba can na tafi na kai mata"waro ido Ibrah yayi yace "la'ilah

illallah wayar 95.000f ɗin ce ka baiwa wata ƙatuwar banza Mu'azam kan ka ɗaya kuw..."hannu
ya ɗaga mashi yace "Ibrah ya isa haka kar ka ƙara cewa Rahama ƙatuwa saboda duk fafutuka
da neman ni ke yi domin ita ni ke yin su dan haka zan iya mallakawa Rahama duk abinda na
mallaka"cike da fushi Ibrah ya bar gun.

Wunin ranar haka Mu'azam yayi shi a jagule dan sosai ya ke son abokinsa amman ko kaɗan bai
kamo ƙafar Rahama ba, murmurshi yayi tuna manyan breast ɗin ta yammm haka jikinsa yayi
tare da jin son yin aure ya taso mashi.



Sai marice ya koma gida inda ya tarar ana ta shirye-shiryen bikin Munawara wanda ya rage
kwana biyu kacal,ɗakin shi ya buɗe ya aje kayan da ya shigo sannan ya shiga banɗaki yayi
wanka.
A tsanake ya ke shirinsa inda ya saka wasu fararen kaya uwanda suka yi masifar karɓar sa,in
ka ga Mu'azam za ka ɗauka ya kai 25years.
Turare ya saka ya buɗe ledar da ya shigo ita ya fitar da na shi sannan ya ƙulle,ya na ƙoƙarin fita
yaji muryar Hajiya Babba "ina zuwa kuma yanzu daga shigowar ka,?"waigowa yayi ya gaishe ta
sannan yace "zan kaiwa Rahama kayan shigar biki ne"Hajiya Babba ba tace komi ba.



***GIDAN ALHAJI

"Alhaji aure-auren nan ya isa haka,yawan auren nan ba shi zai sa ka samu abinda Allah bai
nufa za ka samu ba"wata ƴar datijuwa ke faɗar haka yayinda shi kuma Alhajin da ta ke yiwa
magana ya rabka uban tagumi.
Can ya ɗago ya dube ta yace "ki bar wannan zancen dan tuni an ɗaura yanzu haka yau bayan
sallah isha'i amarya za ta shigo"ya na gama faɗar haka ya miƙe tsaye ya fito babban falo
yayinda Hajiya ke take masa baya.

Samari ne a ƙalla sun kai ashirin da wani abu,duk rusunawa su ka yi su na gaishe da
mahaifinsu bai amsa ba sai da ya zauna kan wata farar kujera wacce ta banbanta da ta cikin
falon sannan yace "lafiya lau na ke,na sa an tara ku ne a nan dan na shaida maku yau za'a
kawo sabuwar tantin ku ina son ku buɗe kunnuwan ku da kyau duk wanda yayi mata rashin
kunya akan auren uwar sa"duk sunne kai suka yi Ma'aruf wanda shine babban su kuma ba zai
wuce 34years ba yace "auren kuma again?ina roƙon Allah ya sa alkhairi ya sa kuma wannan
shine na ƙarshe ya cika ma burin ka"murmurshi kan fuskar Alhaji yace "amen ɗan arziki"Hajiya
kuwa ji tayi kamar taje ta maƙure Ɗan na ta dan kuwa kaf cikin yaran shi kawai ke son abinda
Alhaji ke so.

Dare na yi kuwa ƴan kan amarya suka zo tun daga Agadez suka kawota,yarinya ce sharaf ƴar
duma-duma mai jini a jiki kallo ɗaya za ka yi mata ka san taji Addini duba da yanayin shigarta
ba irin yadda amaren zamani suke caɓa kwalliya ba,a goshinta kuma ƙaton tabo ne baƙi ƙirin na
sallah.

Alhaji cike da zumuɗi ya gabatar da duk abinda Shari'a ta gindiya tambayoyin da yayi mata na
hukunce-hukuncen sallah da sauran su ras ta bashi amsar su.
A slow ya dinga binta har ya mayar da ita cikakkar mace,azaba kam ta sha ta, Alhaji da kan shi
ya gasa ta ita kuma sai noƙewa ta ke yi....



**

Cike da murna Rahama ke buɗa kayan da Mu'azam ya kawo mata har kala uku,farar shadda ta
shigar safe, lèche na shigar rana sai lafaya ta kan amarya.
Ishalle sai yaba kayan ta ke can tace "ya kamata azo kuma ayi bikin ku kafin ƴan baƙin ciki su
kutso kai,kawai ki ce mashi ya turo magabatan shi"dariya Rahama tayi tace "toh ai sai gobe ne
zai gabatar da Ni ga danginsa sannan kuma ai sai mun tafi ƙauye ya gaido su Inna"(Ishalle ba
ta haihuwa shiyasa ta ɗauko ƙanwarta Rahama daga ƙauye wajen iyayenta,kishiyarta ɗaya sai
dai ba gida guda suke ba wannan kenan)


Ranar biki Rahama ta tsantsara ado suka tafi ita da Ishalle,sosai kuwa suka samu tarba mai
kyau gun Hajiya Babba sai nan-nan ta ke yi da su.
Dangin Abban su ma sosai suka yaba da Rahama ita kuwa sai sunne kai ta ke,Gift ɗin da ta
kawowa Munawara sai kowa yayi san Barka dan kuwa sai da ta danne zuciyar ta tayi mata
sayayya irin ta amare.

Da dadare a ka kai amarya gidan surukanta wanda ya ke nan cikin unguwa,Mu'azam kuwa
sosai ya ke murna dan kawu Tanimi yace in shaa Allah shi ma in ya shirya za su je nema masa
auren Rahama.....
[03/12 à 09:18] Cham~rose: *KARUWAR GIDA*


*LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA
MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA
TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta
WhatsApp* +22795045822
*Après chaque prière*

E1 ُرِفْغَتْس
َأ
F Eَ
هَّللا2َّمُهَّللاF َتْن
َأ
،ُمَالَّسلا َكْنِمَو ،ُماَلَّسلا َتْكَراَبَت اَي اَذ ِلاَلَجْلا
ِ
ماَرْك
ِإل
اَو

Je demande pardon à Allah [trois fois]. Ô Seigneur ! Tu es la Paix et la paix vient de Toi. Béni
sois-Tu, ô Digne de glorification et de munificence. »

Muslim 1/414.

*JUMMA'A MUBARAK MES FANS*

*PAGE 31-32*


Cikin ikon Allah an kai lefe gidan su Rahamatullah bayan Mu'azam ya je har ƙauyen su ya
gaishe da iyayen ta.
Ba wani saka dogon lokaci ba wata biyu ne kacal,tuni Mu'azam ya fara shirye-shirye ɗakin
Hajiya Babba aka gyara wanda ya ke cikin da falo ita kuma ta koma ɗakin shi mai ciki ɗaya.


Abotar su Mu'azam kuwa ta ɗan rage ƙarfi shi da Ibrah duk da sun shirya amman tuni ya gane
da Ibrah ya na hassadar shi ne da ƙyashin abun hannun shi.
Munawara babu yadda ba ta yi da Kamal su tsaya har ayi bikin Mu'azam ba amman ya ƙiya a
ƙarshe da ya ga za ta kawo mashi cikas yayi mata gami da Hajiya Babba ita kuwa ta shiga yi
mata faɗa a ƙarshe ta ɗirka mata ɗan karan duka da ciwon jiki da birdin tsamanga Munawara ta
isa Saudiyya tare da ƙudirin ita da zuwa Niger sai kuwa in gawarta za'a kawo tunda ba ƙaunarta
Hajiya Babba ke yi ba



***Bayan wata biyu

Tuni su Rahama an zama amare,zalama gun Mu'azam kuwa ba'a magana ɗaya rana sai ya
nemeta fiye da biyar tun ta na kuka har ta saba sai ya zamana har ta fi mai kora shafawa dan
wani sa'in ya na shago za ta kiran shi ta aza mashi kuka sai ya dawo gida ya yi mata abun


Cikin zumɓurar baki Rahama ta shiga tuƙa tuwon ta na gunguni tare da zagin Hajiya Babba
ƙasa-ƙasa ita da ta sa a yi tuwon laushi,cikin yanayin rashin jin daɗin rashin kunyar da Rahama
ta tsiro Hajiya Babba ta dube ta tace "Rahamu yanzu haka ake tuƙa tuwo garin ku?duk kin bi kin
ɓata madafa da gari kuma tuwon ki na ganin ya na ƙulalai shine kike zuba gari dayawa?to bani
in yi kaya na tun farko sai da nace ku yi girkin ku in yi nawa"


Miƙewa Rahama tayi ta baiwa Hajiya Babba wuri,bakin pampo taje ta wanke hannunta ta shige

ɗaki zaunawa tayi ta kalli baƙuwarta wato ƙawarta Rahama mai irin sunanta tace "wlh na gaji
waccan baƙar tsohuwar ta sa ni yi mata ƙaddararen tuwo kiji fah da rana tsaka a saka ni girgizar
jiki"
"Innalillahi yanzu takwara uwar mijin ta ki ce tsohuwar banza?"to kiyi saurin tuba ga Allah domin
duk wacce ta haifa maka miji ta gama maka komi a duniya "wani uban tsuki ta ja tace "dallah
kar ki kawo min ƙabli da ba'adi ke a ko ina sai kin nuna ke ustaziya ce tai can ki zauna ke uwar
mijin na ki tayi ta juya ki,shi kuma mijin ki riƙa goya shi iyakar biyayya wai na ga kwanaki har
wani duƙawa kike dan za ki miƙa mashi makuli mota kawai salon ya raina ki"


Ita dai ba ta ce komi ba dan ta riga da ta san namsake ɗinta babu abinda ta saka a gaba sai
duniya,sallama tayi mata ta yi tafiyarta.

Dare nayi Mu'azam ya dawo,kunkume fuska Rahama tayi shi kuwa bawan Allah duk ya susuce
ya shiga tambayarta lafiya buɗar bakinta sai cewa tayi "ai Hajiyar ka ce ta zage ni wai ƴar ƙauye
ban iya girki ba,kuma fah ina tsaka da girki ta karɓe wai ai Ɗanta ya yo cefanen shiyasa ma ban
yi girkin dare ba kuma ni yanzu yunwa ni ke ji"

Shiru Mu'azam yayi ya na ta juya zancen can dai yace "ina zuwa"ya faɗa tare da fita ya ja
babur.
Gasasun kaji da frite ya sawo,sai da ya kaiwa Hajiya Babba na ta sannan ya wuce part ɗin su.
Cike da murna Rahama ta fara cin kajin a zuci kuma ta na kitsa yadda za'a yi ta haɗa tugun da
zai sa su bar gidan.



***2years later



Arzikin Mu'azam ya buƙansa sosai dan har yayi na shi jarin yanzu kan ƙafafun shi ya ke tsaye
daram,matsalar shi ɗaya ita ce rigimar Rahama kullum da sabuwar fitinar da ta ke kawo mashi
yanzu ita kuma Hajiya Babba ta matsa doli sai ya ƙara aure saboda har yanzu Rahama ko
ɓatan wata ba tayi ba.
Ɓangaren karatu kuma BEPC kawai Mu'azam ya ke da daga nan kuma ya tattara su ya maida
gefe,yayinda Ibrah tuni ya fara karantar karatun likitanci yanzu haka ya na cikin shekara ta biyu.



Kuka Rahama ke yi wiwi kamar ranta zai fita jin wai kishiya za a yi mata,cikin ɗaukar shawarar
da takwararta ta bata ta dubi Mu'azam tace "kafin kayi auren sai ka shirya mu fara zuwa asibiti

tukunna a san daga ina ne matsalar ta ke"bai wani damu ba ya amince.


Da zuwan su aka gwada su likita ya tabbatar da duka lafiyar su lau matsala ɗaya ce shine
kamar ƙwan haihuwar Mu'azam ya fi ƙarfin ƙwan hallitar Rahama maimakon in sun gamu suyi
fécondé sai ya ƙona shi.Cikin dubaru na likitoci ya shiga kwantar masu da hankali sannan yace
su dage da addu'a duk da su na da 1% na chance amman lamarin Allah sai shi.


Wannan batu sam bai kwantawa Hajiya Babba ba hakan yasa ta fara neman masu maganin
gargajiya a ƙarshe dai sai ta gayyato wani malami kwanan shi bakwai a gidan su ya na aikin shi.
Jungum suka yi suna sauraren malam wanda ya ke ta yin murmushi can yace "tabbas akwai
arzikin ƴaƴa amman da alamu duk mata sannan hakan za ta faru ne in kun dage da roƙon Allah
ku yawaita yin saraka sannan mabuɗin arzikin ku shine ɗaukar Maraya ku ingata rayuwar shi"


"Maraya?ina za mu samu Maraya kuma malam?"cewar Mu'azam "gidan marayu za ku je ku yi
adopter ɗin sabuwar haihuwa saboda ita ɗin haske ce tamkar tauraruwa yayin ɗaukar ta za ta
canyara kuka ne tamkar lokacin ne aka fiddota daga cikin cikin mahaifiyar ta"malam ya faɗa ya
na murmurshi "malam kuma doli sai mace?"Mu'azam ya faɗa dan ya fara ganin abun kamar an
kaucewa hanya.


Tsawa Hajiya Babba ta daka mashi tace "ka fi shi sanin aikin shi ne?" Malam yace "istakhara
nayi in kuma ka na so kai ma za ka iya yi,tabbas a mafarkina mace na gani haske ya luluɓeta"

Da sauri Mu'azam yace "malam bani karatun istahara ɗin"

Malam yace to ga addu'ar kamar haka:
َّمُهَّللا يِّنِإ َكُرـيِخَتْس
َأ
،َكَمْلِعِب َكُرِدْقَتْسأَو ،َكِتَرْدُقِب َكُل
َأْس
َأ
َو ْنِم َكِلْضَف ،
ِ
ميِظَعْلا َكَّنِإ
َف ُرِدْقَت اَلَو ،ُرِدْق
َأ
ُمَلْعَتَو اَلَو ،ُمَلْع
َأ
َتْن
َأ
َو ُمَّالَع ،ِبوُيُغْلا
َّمُهَّللا ْنِإ َتْنُك ُمَلْعَت َّن
َأ
اَذَه َرْمأَلا يِّمَسُيَوE Fهَتَجاَح ٌرْيَخ
يِل يِف يِنيِد يِشاَعَمَو ِةَبِقاَعَو ،ي
ِ
رْم
َأ
ُهْرُدْقاَف يِل ُهْرِّسَيَو يِل َّمُث ْك
ِ
راَب يِل ،ِهيِف ْنِإَو َتْنُك ُمَلْعَت َّن
َأ
اَذَه َرْم
َأل
ا ٌّرَش يِل يِف يِنيِد يِشاَعَمَو ِةَبِقاَعَو
،ي
ِ
رْم
َأ
ُهْف
ِ
رْصاَف يِّنَع يِنْف
ِ
رْصاَو ُهْنَع ْرُدْقاَو َيِل َرْيَخْلا ُثْيَح َناَك َّمُث يِنِضْر
َأ
ِهِب

Godiya Mu'azam yayi sannan Hajiya Babba ta sallami malam.
Dare na yi Mu'azam yayi raka'a biyu sannan ya karanto addu'a da malam ya bashi yayi tawasli
da Allah tare da miƙa dukan yarda shi.



***GIDAN ALHAJI

Dr Ma'aruf ne sanye da kayan likitoci,idon shi manne da farin glass hankali tashe ya shigo
gidan.
Kallon Abban nasa yayi yace "Abba doli sai an tafi asibiti ka yarda da ni dan Allah wlh ba za'a
samu matsalar komi ba"cikin yarda da Ɗan na shi ya tallabo Agaishat wacce ta jigata saboda
zafin naƙuda mota ya sakata tare da ɗaukar kayan haihuwa suka wuce asibiti.

Allurar naƙuda Dr Ma'aruf yayi mata sai addu'a ya ke yi Allah sa matan biyu su haifu lokaci
ɗaya,waccan ɗayar ta fara nishi da sauri ya tafi ya karɓi haihuwar ta cikin ikon Allah ko minti
biyu ba'a yi Agaishat ma ta haihu.
Bisa gado ya ɗora jariran wanda suka kasance duk mata ne,sai da ya rumtse ido sosai sannan
yayi masaye wato ya canza su ya baiwa Agaishat ƴar wacan matar ita kuma ya bata ta
Agaishat.



Cike da murna Alhaji ya ɗauki baby girl ɗin ya na mata huɗuba,tuni kuwa alhalin shi suka cika
asibitin amman ƙememe ya hana kowa ya taɓa yarinyar.



A hankali Dr Ma'aruf ke shafa kan ƴar ƙanwar ta sa lokacin da Marâtre uwar marayun ta karɓe
ta daga hannun shi "a kula da ita sosai ita ɗin marainiya ce mahaifiyata ta mutu wajen haihuwar
ta sannan dama ta ce ko ta haife ta jefar da ita za tayi saboda ba ta hanyar aure aka haife ta
ba"Dr Ma'aruf ke faɗar haka kafin ya tafi ya na jin son yarinyar cikin ɓargon zuciyar shi.

***

Cike da murna Rahama ta shirya saboda mafarkin da Mu'azam yace yayi,cikin ƴar ƙaramar
motar shi suka shiga su dukan su har da Hajiya Babba ba su zarce ko ina ba sai gidan marayu.

Babu ɓata lokaci shugan gidan marayun ya kai su ɗakin da ake aje sabin haihuwa,marâtre ita ta
rinƙa ɗauko jariran ta na miƙawa Mu'azam da ɗaya-ɗaya duk in an bashi sai ya aje.
"Inyaaa !inyaaa"haka jaririyar ke cancara kuka murmurshi dukansu ukun suka yi Mu'azam yace
"alhamdullah na ɗauki wannan"marâtre tayi murmurshi tace "Allah sarki ko minti goma ba'a yi
ba da wani likita ya kawo mana ita mahaifiyar yarinya rasuwa tayi"nan da suka cika takardu
komi da komi Mu'azam yayi mata huɗuba ya juyo ya kalli Hajiya Babba yace "wane suna za'a
saka mata?" "Fadimatu"ta bashi amsa ta na murmurshi shi ma murmurshin yayi yace "takwara
kika yiwa kan ki kenan?to ni kuma zan rinƙa kiranta da *Mimi*".....

```JUMMA'A RANAR HUTUNA CE BAN POSTING```
[04/12 à 14:10] Cham~rose: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI
KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA
TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI‍♀️ mai
son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822


*Page 33-34*

Kiran Dr Ma'aruf marâtre tayi kamar yadda ya buƙata cewa duk ranar da aka samu wanda zai
ɗaukar jaririyar ayi mashi magana.
Babu ɓata lokaci kuwa ya zo adresse ɗin Mu'azam ya karɓa sannan ya bi su har gidan su ya ga
muhallin su kafin ya koma.
Wanka Hajiya Babba ta yiwa takwarar ta na ruwan zafi sai kuka ta ke canyarawa,mai ta shafa
mata ta saka mata kaya masu kyau cikin wanda Mu'azam ya sawo mata.


Karɓar ta Rahama tayi ta shiga bata madara cikin biberon ai kuwa ta fara sha, Mu'azam ya
shigo cike da murna yace "Hajiya Babba albishirin ki?"tace "goro"takardun gida ya ajiye a
gabanta sannan ya zauna bisa tabarmar ya tanƙwashe ƙafafun shi yace "Dr nan ne ya bani
kyautar gida mai kyau ɗan madaidaici sannan kuma har da kaya ya zuba cikin su,babban abun
farin ciki da ya tambaye ni nayi karatu ko yaya ne nace mashi eh kawai sai ya bani
shuwagabancin compagnie ɗin shi yanzu haka gobe zan fara aiki"wata irin buɗa Hajiya Babba
tayi tace "madallah dama malam yace ita ɗin rahama ce gare mu ga shi kuwa tun ba'a yi nisa
ba mun fara samun canjin ratuwa,kai masha Allah bari mu tashi mu fara shirin komawa can in
ya so nan ɗin sai mu saka ƴan haya"ta na gama faɗar haka ta miƙe tare da shigewa ɗaki ta fara
haɗa kayanta


Mu'azam ya kalli Rahama yace "ya na ga ba kya farin ciki?"murmurshin ƙarfin hali tayi dan ita
sam ba ta so Hajiya Babba ta bi su can sabon gida�
Kwanci ta gyarawa Mimi sannan tace "ai abun murna ne sosai ga Ɗiyar nan sai kace kai ka
haifeta dan har kama kuke yi"hannu ya sa ya ɗauki Mimi yace "kai haba bari na gani"Rahama
tace "Allah kuwa kawai dai dan ta fi ka hasken fata ne"murmurshi yayi yace "farin mahaifiyarta
ne tayi,kin ga an raba biyu ni na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login