Showing 30001 words to 33000 words out of 43151 words

Chapter 11 - KARUWAR GIDA END BOOK COMPLETE Hausa Novels Complete By Mrs Sadauki .pdf

01 Jul 2025

4496

saiti da ƙofar ɗakin, murmurshi na sakar
mashi shi kuwa Daddy zuciyarsa ce ta shiga bugawa ganin na shanun Mimi sun yi tsiriri a tsaye
suna zagin sakawai haka yaji haushi ko bra ba ta saka ba za ta fito haka alhalin akwai
mutane falon.

A shagwaɓe na faɗa jikin Daddy daga zuwana "shine ka fara ci ka manta da ni"na faɗi haka ina
mai amshe apple ɗin hannunsa, murmurshi yayi yace "Mimi uwar rigima ai na zata ma kin
kwanta saboda gajiya,yanzu yaya kike ji komi normal ?"Kai na gyaɗa na guntsiri apple ɗin
daidai shatin haƙoran sa sannan nace "Daddy wai sai yaushe Tantie Munawara za ta sauka
daga dokin kafiya? ni dai na matsu na gan ta mijinta na da kirki"Daddy yace "sai ranar da
kasuwar apple ta tashi"ya faɗi haka ya na kimtse dariya,ƙafafu na shiga bugawa ina kukan
shagwaɓa nace "Allah ba santi nayi ba kawai dai na tambaya"


"To Sarkin surutu sai ki sauko ki ci abinci dan na san in an biye ta taki ba za ki ci ba"cewar
Hajiya Babba ta na juye dafafun zabi wanda suka sha jar miya kallon Daddy nayi nace "ni ba
zan ci ba kar na ɓata hannu na"murmurshi yayi dan ya san mi ni ke nufi a duk lokacin da nayi
sha'awar ya ciyar da ni da hannunsa haka ni ke faɗa.

Hajiya Babba ta taɓe baki tace "na ga yaushe za ka barin sangarta ƙatuwa har haka wai fah sai
dai ya bata a baki kamar jaririya "cikin shagwaɓar da ta zame min jiki nace "ni dai ba ƙatuwa ba
wai duka-duka ma nawa ni ke da ake sa min ido?haka fah jiya ta ƙi ban abinci a baki alhalin
Daddy cewa kayi ta je ta kula da ni"duk dariya aka yi Hajiya Babba tace "ah to ni ban iya gantali
ba ƙatuwar budurwar da ko yau sai a ɗaura mata aure zan baiwa abinci a baki dan dai duniya ta
zo ƙarshe can shi da ya sangartar da ke ya baki"

Baki na turo nace "to na ma fasa ci ban so"na faɗa ina shirin tashi Daddy ya mayar da ni na
zauna "miye haka Mimi ki nutsu mana ko ba ki ganin ba mu ɗaya ba ne akwai baƙi?koko so kike

Abba yace na sangartar mashi da yarinya?"Daddy ya raɗa min a kunne,turo baki gaba nayi na
juyo ina facing shi har zan yi magana ya aza min yatsansa a baki.


Cikin plate Hajiya Babba ta zuba min Daddy ya karɓa ya na bani shi ma ya na ci,yayinda su
kuma suka gewaya suna ci su ma.
Ƙurawa Daddy ido nayi ina jin wata irin ƙaunarsa a raina,shi ma jefi-jefi ya ke kallon ƙwayar
idona.Sai da mu ka ci mu ka ƙoshi sannan Daddy ya aje plate ya zuba mana jus,miƙewa nayi
na fita zuwa harabar gidan.
Iskar Ubangiji na shaƙa na lumshe ido,an ɗauki kamar minti goma suka fito Hajiya Babba riƙe
da hijabi a hannunta saka min tayi kafin na tambayeta lafiya naji Daddy na cewa "Mimi sai in na
zo ki kula da kan ki"idona ne suka yi rau-rau na kalli Daddy nace "zuwa ina?"Hajiya Babba tace
"ai kaji sakalci Abban ki za ki bi kuje can gida"wani kukan kura nayi na faɗa jikin Daddy na ririƙe
shi ina kuka tare da girgiza kai.


Rumtse ido yayi ya na jin abubuwa na mashi yawo a kwanya,na ɗaya saukar dukiyar Fulaninta
a kan ƙirjinsa na biyu sautin kukanta.Dakyal ya aro jarumta ya shiga bubuga bayanta,cikin
murya mai taushi gami da kasala yace "yi shiru Mimina ai zan zo zuwa dare "kafaɗa na maƙe
ina gyara kwanciya kan ƙirjinsa.

"Ku shiga mota ina zuwa"cewar Daddy,wucewa suka yi Hajiya Babba kuma ta koma ciki saboda
karyewa da zuciyarta tayi.
Haɓata ya ɗago ya ƙura min ido,ta saman gashin idona da suka jiƙe da hawaye ni ke kallon
shi.Iska ya fara hura min a fuska na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya, daidai saitin laɓana naji
ya sauke na shi kafin ya janye yace "ina son ki,ki kula da kan ki ke ɗaya ce mace a can ƴan
uwan ki na can na jiran ki saboda bege"idona na a lumshe nace "Daddy mu je tare"murmurshi
yayi mai ɗan sauti ya cire ni daga jikinsa ya ja hannu na zuwa mota ina hawaye ina ji ina gani
Daddy ya buɗe seat ɗin baya ya sanya ni ya rufe.Wani kukan ne ya kubce min ina leƙen Daddy
ta glass Ma'aruf ya yi mata key mai gadi ya buɗe mana gate.





**Cike da tashin hankali Mami ke duba takardar,ihu tayi ta dire daga bisa gado ta fito daga cikin
asibitin.Direct bakin hanya ta nufa ta tari mai adaidaita,ya na sauketa ta shiga ciki a falo ta tarar
da Ameera ita da Twins duk sun dawo daga school.
Ɗakinta ta shiga ta ɗauko kuɗi ta miƙawa Ameera ba tare da tace komi ba ta nuna mata hanyar
waje hakan yasa Ameera fita,Twins kuwa sai sannu da dawowa suke yi mata amman ta ƙi kula
su.
Dr Ibrah ta kira ta shaida masa komi dariya ya shiga ƙyarƙyatawa kafin ya kashe kiran,ba'a fi

minti goma ba ya zo gidan.Da gudu Twins suka rungume shi suna mashi oyoyo,Ameera kuwa yi
tayi kamar ba ta san da zuwan shi ba.
Mami ta fito ta na kuka,Dr Ibrah ya taɓe baki yace "to miye na kuka dan ya sake ki?kuma fah
yaran nan duk kin san ni ne mahaifin su to damuwar ta mi ce?"kai Mami ta girgiza tace "na cutar
da Mu'azam na haifa masa shegu cikin gida ya ciyar da su haɗi da ɗawainiya yanzu kuma har
gidan ya ce ya bar min ba zai iya sake rayuwa cikin sa ba"ta ida maganar cikin fashewa da
kuka.
Ameera ta miƙe tsaye ta na jin abun kamar almara "ni ne sabon Daddyn ku kun ji ko?daga yau
Daddy za ku kira ni kun ji ko?"Dr Ibrah ya faɗa ya na rungume Twins .
Kuka Ameera ta fashe da shi ta fita da gudu da sauri Dr Ibrah ya fito ya na kiran sunanta ganin
haka yasa mai gadi liƙe ƙofa.
Ƙarasawa Dr Ibrah yayi ya ɗauketa da wani gigitacen mari yace "gidan uban wa za ki je?"cikin
kuka da rashin tsoro tace "gidan uban ka zan je shege zakka ɗan asara da ba zai ganin Annabi
ba da yarda Allah mutuwa kare za ka..."waro ido yayi ya sake ɗauke ta da mari kafin ya
fincikota ya shiga bal da ita a ƙarshe ya jata ƙiii zuwa ɗaki. Banda kuka babu abinda Mami ke yi tare da dana sani maras amfani,ganin bugun da Dr Ibrah
ke yiwa ƴarta yasa ta miƙe da sauri Ameera tace "kar ki taɓa ni ban son ki ban ƙaunar duk mai
ƙaunar ki sannan sai na shiga duniya na zama shaƙiƙiyar tantiriya sai na kawo maki shegu kin
raina tunda rainon su kawai kika iya"tayi maganar ta bubuga hannunta da table. Cak Mami ta tsaya ta na jin zuciyar ta na barazanar faɗowa,tabbas ta san Ameera ta aika yin
karuwanci ga ɗiyar *KARUWAR GIDA* ai ƙaramin abu ne amman sam ba za ta lamunta ba.



***GIDAN ALHAJI


Tamkar wata tv haka duk suka sani a gaba su na kallo duk yaran murmurshi kan fuskarsu
yayinda matan suka turniƙe fuska kamar tsohon kashi.
Momy kuwa ta na zaune kusa da ni ta riƙe hannuna gam,Abba na zaune daga gefe ya na
murmurshi Dr Ma'aruf yace "tanti amaya ya kamata a kai little ɗaki ta huta kin sa da gajiya a
jikinta"murmurshi Momy tayi ta ja hannuna zuwa ɗakinta.Lafiyayen gadonta ta nuna min na
kwanta bisan shi, hasken ɗakin ta kashe min na rungume pilow ina jin wasu hawaye na ziraro
min kewar Daddyna ni ke yi murmushi nayi tuna ba shine biologique parent ɗina ba.....
[08/12 à 16:05] Cham~rose: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI
KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA
TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI‍♀️ mai
son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 39-40*

Kamar yadda Daddy yayi alƙawali da dadare sai gashi kuwa,kowa na gidan ya hallara banda
Mimi wacce rashin sabo ya sa tayi zamanninta a ɗaki.

```gani a cikin gidan ku amman ban gan ki ba``` shine text ɗin da na karanta wanda ya fito kuma
daga Daddyna,zumbur na miƙe ko kallabi ban saka ba balle wani hijab da ɗan guduna haɗi da
murna na nufe shi na faɗa jikinsa duk da kuwa ƙoƙarin hana ni da ya so yi.


"Daddy ka zo ka tafi da ni ne?dama ni na gaji ni ɗaya babu su Twins kuma Teddyna ya na can
gun Hajiya Babba"na faɗa ina mai kwantar da kaina bisa kafaɗarsa,sumar kaina ya shafa yace
"Mimi ai kin zo gida kuma ke da can sai in kin zo ganin mu"da sauri na girgiza kai nace "a'a
Daddy dan Allah kar ka bar ni nan wlh ban san kowa ba kuma fah su nan babu mace ƴar
yarinya to da wa zan yi hira?"dariya kusan rabin mutanen suka yi kafin Dr Ma'aruf yace "ai
shiyasa Abba ke son ki dawo nan ɗin amman kar ki damu zan cewa Fatima (cewa da Ɗiyar
shi)ta dawo nan da zama"kafaɗa na maƙe na jimƙe hannun Daddy.


Mutanen falon duk Alhaji ya sallama ya bar Momy da Ma'aruf kawai wanda tun ɗazu suka yanke
shawara duk da ba su san ko Mu'azam zai karɓeta ba ni kuwa ina jikin Daddy na lafe kamar
mage.
Gyaran murya Abba yayi yace "Mu'azam banda bakin gode maka sai dai in ce Allah saka maka
da alkhairi ya biya maka buƙatunka duniya da lahira,sannan a ƙarshe ina neman wata alfarma
dan Allah amman sai ka min alƙawari za ka amince"ɗagowa Daddy yayi kalli Abba murmurshi
kan fuskar shi yace "to Abba ina jin ka in shaa Allah "
Sai da Abba ya sake nutsuwa sannan yace "ina son ka cigaba da riƙe min Fadimatu a gun ka
na san za ka fi kula da ita sai dai wannan karon ba'a matsayin Ƴa za ka riƙe ta ba a matsayin
mata"da sauri Daddy ya zabura yace "Mata?mata dai?aure? Mimi? Abba..."hannu Abba ya
ɗaga yace "kar ka manta ka min alƙawali"Daddy yace "ita fah Mimi yarinya ce har yanzu kuma
kamar an cuce ta an gama ta da tsoho"dariya Ma'aruf yayi yace "haba Mu'azam duka-duka
nawa kake ba fa za ka wuce 45years ba amman bari mu tambayi Mimin Daddy ko ta amince"ya
ida maganar cikin barkwanci.


Ƙara ɓoye fuskata nayi cikin ƙirjin Daddy dan duk abinda su ke ina jin su magana ce kawai ban
yi,yadda Daddy ke shafa gashin kaina yasa barci ɗauke ni ban ma san abinda suka yanke ba
akai.



Washegari da asubah Momy ta tashe ni nayi sallah,ina gamawa na zumɓuro baki ganin ashe
wayo Daddy ya yi min bai tafi da ni ba.

Momy da ke daga gefe ta na lura da Mimi kai kawai ta girgiza ta na jin son ƴarta har
ƙasanƙasan zuciyarta,zuma ta miƙo min wacce ta sha haɗi ni kuwa Uwar son zaƙi na shiga sha.
Wayata na ɗauka na danna kiran Daddy sai turo baki ni ke yi ina tsara yadda zance mashi
amman har ta gama ruri bai ɗauka ba.
Daddy kuwa da ke can kwance cikin ɗakin shi tun na farko kafin su tashi daga gidan Hajiya
Babba kwanci ya gyara ya na mai cigaba da kallon hotunan Mimi,sam ya kasa daina kallon
ƙirjinta tunda aka bashi ita aurenta ya samu kan shi da kalle surar jikinta.


Kiran ya maida mata,ni kuwa ganin appel ɗin shi yasa na ɗauka cikin sanyin murya nace
"Daddyna ina kwana?shine jiya ka tafi ka bar ni a nan haba dai"na ida maganar cikin shagwaɓa.

Numfashi ya fesar kafin yace "Mimina?"a yadda yayi maganar yasa ni yin shiru ina jin zuciyata
na bugawa "Mimina?"ya sake faɗa "uhum!"murmurshi yayi mai sauti yace "rigima ko?"ido na
rufe na turo baki gaba nace "ba kai ne ka bar ni ba"Daddy yace "yaushe kike son dawowa nan
ɗin ?"cikin zaƙuwa nace "yau ni ko yanzu ma"Daddy yace "kenan na faɗawa Abba a ɗaura
auren yau?"kai na girgiza kamar ya na gani na dan wani tsoro ne ya zo shige ni nan take.



"Kin yi shiru ko ba ki shirya zuwa gidan ba?"ya tambaye ni,a sanyaye nace "na shirya mana
amman gun Hajiya Babba zan zauna"dariya Daddy yayi yace "naji kar a kawo ki guna
kenan?"da sauri nace "eh" "tsorona kike Mimi?"yayi tambayar cikin kalar tausayi nace "a'a
Daddyna"ya sauke ajiyar zuciya yace "kin ci abinci ne ?"na bashi amsa da "a'a Momy dai ta
bani zuma ga kuma madara ta kawo min jira ni ke ta wuce in sha"shiru Daddy yayi ya na jin
tausayinta a ran shi dan kuwa tuni ya gane an fara gyaran amarya ne.



"Ok to ɗauki ki sha da zafin ta sannan in kin yi wanka ki saka kayan da na kawo maki jiya
Please kar kice ba za ki saka bra ɗin ba"Daddy ya faɗa ya na yanke kiran.
Ajiyar zuciya na sauke na ɗauki madarar da Momy ta aje na fara sha ina yamutsa fuska saboda
goût ɗin hulba da naji.




***Bayan 1week

Tuni aka kawo lefena akwatina dozin kowane cike da kaya,tuni kuma Momy ke ta min gyaran
jiki da na km.Cikin ƙanƙanan lokaci na canja na ciko sai sheƙi ni ke yayinda kuma ko muryar
Daddy naji sai na wanke pant ban san dalili ba,sosai mu ka shaƙu da Daddy na ɓangaren
soyayya sam bai nuna wata kunya dan zai aure ni balle ni da dama na mutu cikin ƙaunarsa da

son shi.
In muna waya da Daddy za ka ɗauka da wani ƙaramin yaro ne ɗan 27years yadda ya ke
tsayawa ya saurare ni ya biye min wajen shirme da sangarta haɗi da shagwaɓa.


A yanzu na saba da gidan mu ga kuma Fatima da ta dawo gidan mu wacce kusan sa'ata ce sai
dai na girme ta,duk da ta na zaman ɗiyata amman ni a abokiya na ɗauketa.Ita ke min rakiya in
zan je wani gun sai Daddy ya zo ya kai mu in mun gama abinda muke ya je ya ɗauko mu.


Abu guda ne ya tsaya min a rai yadda kwata-kwata Daddy bai son nayi mashi maganar Ameera
balle uwa uba Mami,yanzu ma mu na zaune a mota mu na hira bayan ya maido ni daga gyaran
gashi.
Wayar shi na karɓa ina kallon hotuna cikin gallerie yayinda shi kuma ya ke kallona lokaci zuwa
lokaci ya na sauke ajiyar zuciya wacce tuni na gane ta bege na ce dan ni ba yarinya ba ce na
san da Daddy ya na fama da sha'awa haƙuri kawai ya ke yi.


Hoton wata mage na gani na ɗago ina cewa "ina son irin wannan magen Daddy please ka sa a
nemo min"laɓana ya tsurawa ido,babu zato babu tsammani naji saukar bakin shi kan lips ɗina
da sauri na rumtse ido ina jin zuciyata na bugawa yayinda jikina ya ɗauki kyarma.


An ɗauki tsawon min biyar kafin ya janye daga jikina,sunkuyar da kai nayi ina jin wata kunya.
Kan shi ya ɗora saman volant ya rumtse ido ya na sauke ajiyar zuciya "bani gorar ruwa "ya faɗa
cikin kasala duƙawa nayi kusan ƙafafuna na zaro ɗaya na miƙa mashi ya ɓalle murfin ya fara
shan ruwan.


"Mimi dan Allah ki fara shirin tarbata tun ranar farko kin dai ga halin da ni ke ciki"Daddy ya faɗa
ya na mai jingina da kujerar mota, rau-rau idona ya kawo ruwa dan tsoro da jajayen idon shi ya
tsare ni.....
[10/12 à 16:05] Cham~rose: *LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI
KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA
TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI‍♀️ mai
son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp* +22795045822

*Page 41-42*



"Ni dai a'a sai na gama karatu"na faɗa ina matsar ƙwalla,shiru Daddy yayi ya na kallona can ya

nisa yace "sam hakan ba zai yiyu ba Mimi kuma maganar karatu ki mayar da shi gefe sai wata
shekara kuma,yanzu time ɗin kula da ni ne"ɗagowa nayi ina kallon shi jin abinda ya ke faɗa kai
na girgiza nace "please Daddy"kawar da kai yayi gefe dan kuwa sam bai ji zai iya cutar da kan
shi ba alhalin Mimi ta isa ɗaukar nauyin namiji.

Jiki na min rawa na kamo tafin hannun shi wanda ya ke masifar sanyi ba kamar nawa ba da ya
ke rau da zafi,dan kuwa kullumin jikina cikin ɗumi ya ke.
"Daddyna please ko yi za kayi ka bari har mu saba"cike da mamaki ya juyo yace "Mimi wane
sabo kuma bayan wanda mu ka yi?"na turo baki nace "ni dai ban saba da kai ba"lips ɗin ta ya
ƙurawa ido kafin kuma ya kawar da kai gefe dan ya na tabbacin in ya cigaba da kallonta to
tabbas sai ya sake kai bakin shi ga laɓanta.

"Ki shiga ciki Mimi in na isa gida zan kira ki"Daddy ya faɗa ya na kunna mota,cikin ƙin jin daɗin
rabuwar da za mu yi na fita bayan nayi mashi kiss ga kumatu.
Wajen da sanyin laɓanta ya sauka ya shafa ya na murmurshi kafin ya fara tuƙa motar mai gadi
ya buɗe mashi gate.



***

"Wayyo Allah Anna zan mutu,wai wai Allah Innalillahi Allah na tuba ka yafe min wayyo na shiga
uku na lalace"Fadila ke faɗa ta durƙushe tsakar ɗaki farin ruwa gami da jini na zuba ta ƙasanta
yayinda Anna ke gefe ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login