Showing 3001 words to 6000 words out of 43151 words
Chapter 2 - KARUWAR GIDA END BOOK COMPLETE Hausa Novels Complete By Mrs Sadauki .pdf
za su haɗu har su garwaya"ta na gama faɗar haka ta samu waje can ƙarshen
classe ta zauna ta bar ni da faɗuwar gaba,tabbas na fi kowa sanin wacece Nabee duk namijin
da ya burgeta to tabbas sai ta san yadda ta yi ta same shi.
Nabee kuwa shiru tayi ta na ta tunani ashe maganata ta daketa sosai taji haushinta,ni kuwa a
gaba na zauna na fiddo book ɗina na fara dubawa kafin malami ya shigo.
Students sai zuwa suke a sannu yayinda kowa ke harakar gaban shi wasu kuma na hira,Nabee
na tunani yayinda ni kuma ni ke révision.Babu jimawa duk students suka shigo aji saboda ganin
teacher ya nufo ajin mu,"good morning class"cewar teacher lokacin da ya shigo duk amsawa
mu ka yi. Cours ɗin shi ya fara na koyar da mu halshen English saboda ko da wani patient ya zo mai jin
language ɗin amman a zahiri babu ma anglais cikin programme ɗin karatun likita.
Question ya fara kamar kullum ni ce ke yawan amsawa ya na gamawa mushen science ya
shigo,haka dai mu ka ta yin cours har lokacin récréation yayi.
Fuuu Nabee ta bi ta gabana ta wuce ba tare da tace min komi ba saɓanin yadda mu ke tafiya
kullum,har ƙasan raina naji babu daɗi sai na kwashe Books ɗina na bi bayanta ina kiran
sunanta amman ta share ni sai da nayi ta bata haƙuri sannan ta haƙura saboda muna matuƙar
son junan mu.
***
"Anna wai Abba cewa Nasir yayi sai na gama jami'a sannan za'a yi maganar auren mu"cewar
Fadila ta na mai kallon mahaifiyarta ta wacce ke tatar ƙulun koko,kallonta Anna tayi tace "eh jiya
ma mun yi maganar da shi sai na ga hakan ne ya dace kin ga ki na gamawa sai ayi bikin daga
nan shi Nasir ɗin ba sai ya nemo maki aiki ba tunda baban shine shugaban ɗalibai?"cike da
takaici Fadila ta dubi Anna tace "yanzu ke ma kin yarda Anna?in yi ta zama a har sai nan da
wata shekara biyar alhalin ina cikin shekara ta Ashirin da bakwai a duniya?"tatar kokon Anna ta
aje tace "Fadila kin san ciwon kan ki kuwa?ana son yi maki gata ke kuma ba ki gani?duk faɗin
gidan nan wa kika ga yayi dogon karatu in ba ke ba?ina ce saboda kiyi karatu mu ka sayar da
komi na mu dan inganta rayuwar ki,kishiyoyina najin haushin ba ƴaƴan su ba ne ke kuwa ki na
baƙin cikin ɗan farin cikin da ni ke burin samu"da sauri Fadila tace "subahanallah haba Anna ta
yaya Ƴa za ta yi baƙin cikin mahaifiyarta?"
"Eh ga shi kuwa ke ki na yi min,yanzu in Allah ya sa kun kammala karatun ki kin samu aiki mai
ƙwari ai shikenan sai ki saya mana sabon gida mu samu mu fita daga cikin na laka"sororo
Fadila tayi ta na kallon Anna kafin ta miƙe ta shige ɗan ɗakin su na laka wanda tsabar tsufan shi
har ya fara tsatsagewa.
Nasir ta kira ta shaida mashi yadda suka yi da Anna "Fadila gaskiya ba zan iya zaunawa har
5years ba tare da aure ba,kin fi kowa sanin yadda ni ke son ki"cikin kuka Fadila tace "dan Allah
Nasir kar kace haka wlh mutuwa zan yi in ka rabu da ni"cikin ɗan ƙasa da murya yace "naji zan
jira ki amman da da sharaɗi"da sauri tace "na yarda minene sharaɗin?"Nasir yace "ki bari har
mu haɗu school zan faɗa maki"....
Comment and share Please
Jikar Rabo ce
[17/11 à 15:50] Cham~rose: *KARUWAR GIDA...*♀️
```LOVE and
ROMANTIC STORY```
```MRS SADAUKI```
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Whatsapp OR
Call 08066268951*
*PAGE 5-6*
Sai da ta nutsu sosai tace "Nasir ina jin ka tun ɗazu kace na zo kuma kayi shiru"ɗan jim yayi
kaɗan kafin yayi gyaran murya har zai yi magana sai kuma ya fasa saboda bai san ta ina zai
fara ba.
Fahimtar haka ya sa Fadila miƙewa tako ɗaya tayi taji ya rungumota ta baya,ido ta rumtse ta na
jin zuciyar ta na yi mata raɗaɗi "Nasir miye haka sake ni mana"ta faɗa ta na mai son ƙwace
kanta amman ya riƙeta gam.
Wani huci taji ya na sauke mata nan take jikinta ya fara kyarma,an ɗauki tsawon minti biyu ya
saketa tare da juyota suna facing juna.Kai ta sunkuyar ta na jin wata irin matsananciyar kunya
wai yau ita ce namiji ya rungume? "Ki yi haƙuri Fadila abinda ni ke son sanar da ke kenan
amman laɓana sun kasa furta min,na sani ke ɗin kamila ce abu mai matuƙar wahala ne ki yarda
da buƙatata a gare ki amman ki sani ba zan ɓoye maki ba aure ni ke so dan haƙuri na ya zo
ƙarshe".
Idonta ne ya ciko da ƙwalla tabbas ta san Nasir ya na sonta kuma tsawon shekaru biyun da su
kayi tare bai taɓa yi mata magana banza ba balle har yace ya taɓa jikinta sannan ya yi mata
nasiha a ko da yaushe,abu guda ɗaya ta sani shine da ta tambaye shi yawan azumin da ya ke
ya sanar da ita saboda gujewa zina to amman yanzu miyasa ya ke jan su izuwa gareta alhalin
ya san ita ɗin alfasha ce?.
"Nasir zina kake so mu yi?"da sauri ya girgiza kai ya na shirin riƙe mata hannu ta ja da
baya,"kar ka taɓa ni"ta faɗa ta na mai ficewa daga cikin ajin.
Bakin titi ta nufa ta tsayar da adaidaita ta tafi gida,ta na shiga ta tarar da Anna ta na ƙullin kafa
yayinda gefe ɗaya kuma radiyo ne kunne ta na sauraren wani shiri da ake mai taken Ƙafarka
Mai gida.
Har ta kai ɗaki taji Anna na cewa "ke Fadila fito ki ɗauko min ruwa gidan malam Mussa tunda
shi wannan bai da niyyar dawowa balle ya buɗe mana pampon an taɓa abu kamar na tsiya ka
sa pampo gida amman duk in za ka tafi kasuwa sai ka rufe shi"Anna ke faɗa cikin masifa
saboda hali irin na Abba da ya ke rufe pampon cikin gidan tun safe bai buɗe shi kuma sai in ya
dawo daga kasuwa da marice.
Kukan da Fadila ta ke ne ya hanata fitowa sai yi ta ke kamar ranta zai fita,jin shiru yasa Anna
miƙewa a hasale ta shiga ɗakin.
"Laha'ila mi aka maki kike kuka?"Anna ta faɗa ta na taɓa hannuwa,hawaye Fadila ta goge ta
dubi Anna tace "dan Allah ki samu Abba ki yi mashi magana ya bar Nasir ya kawo lefen nan in
ya so nayi karatun...."kumbutsar da Anna ta kai mata ne a baki yasa yin shiru tare da dafe
bakinta,muciya Anna ta ɗauko ta shiga jibgarta da ita sai faɗi ta ke "ƴar baƙin ciki mai baƙin hali
da ki tusa min baƙin ciki gwara na kashe ki na huta,wato gida da mota da kai ni ɗakin Allah shi
kike ma baƙin cikin yi min"banda kururuwa babu abinda Fadila ke yi.
Indo ce ta shigo ta ceceta ta na mai baiwa Anna haƙuri amman kamar zugata ma ta ke sai
balbali ta ke ta na ƙara nanata mata kalmar baƙin ciki,ita dai Indo ta na mamakin hali na
Anna domin kuwa Fadila ce kawai ƴarta mace duk ɗiyanta maza ne amman babu wanda ta
azawa burinta sai Fadilar ƙila kuma dan ta fi su duk ilimi ne,dan su mazan babu wanda yayi
boko mai tsayi duk sun kama sana'ar hannu sannan ɗawainiyar iyalinsu kawai suka sani.
"Innalillahi to ɗiyan asara kiyon asara Allah sa duk ku mace da yardar Allah wannan ƙullun kafar
tawa da kuka zubar shi zai sanadiyar shigar ku huta da ku da wanda ya sawo ku"cewar Anna ta
na mai korar awakin kishiyarta Lami wacce ta kwance su dan zuwa kiyo.
"Wlh can dai ta faltsar maki wacce ba ta ganin Annabi, jarababa mai farar ƙafa tunda kika shigo
gidan nan Malam ya talauce"cewar Lami dan ita ma ba baya ba wajen iya masifa, Indo baiwar
Allah duk cikin su ita ce babu ruwanta ƙila ko dan ita ce ƙarama kuma ba ta da wasu ɗiya da
yawa.
Ta na nan kwance har aka kira sallah Asar ta na ganin appel ɗin Nasir na ta shigowa wayarta
tare da saƙonni uwanda rabinsu na ban haƙuri ne da kuma nuna mata zallar soyayyarta gare
shi.
Wani murmurshi Fadila tayi mai ciwo lokacin da ta turawa Nasir saƙo kamar haka ```na amince
da buƙatar ka sai dai kayi min alƙawari duk runtsi ba za ka guje ni ba sannan sex sai bayan
aure```
***
Ina tsaka da kurɓar tea Daddy ya dube ni yace "Mimi ɗazu wata ƙawar ki taje office ɗina"wani
irin tari ne ya zo min ban san lokacin da na saki kofin tea ɗin ba ya zuba a cinyata.
Ban damu da zafin da naji ba dan maganar Daddy ta fi min raɗaɗi fiye da zubar
shayin,"subahanallah! Mimi lafiyar ki kuwa?ba ki ji ciwo ba?"Daddy ya faɗa ya na mai sa wani
ɗan hankicip ya na goge min inda tea ɗin ya zuba tsananin zafin shi har tururi bujen nawa ya
ke.
Tarin da ni ke sam ya ƙi lafawa kamar ma asama ɗina ke son tashi ,ruwa ya bani a kofi na sha
yayinda Twins duk suka kewaye ni.Ƙirjina na ɗan bubuga da hannu saboda ko naji sauƙin
abunda ya tokare min shi,"Daddy mi sunanta ne?"na faɗa ina mai danne tarin,ƙin faɗa min yayi
ko dan ya ga Mami ta fito ne oho sai ma sannu da ya shiga jero min.
"Minene ya sameta daga in shiga ɗaki in fito?"cewar Mami da alamun damuwa a fuskarta "babu
komi tea ɗin ne ya ƙware ni"na faɗa cikin kawar da zancen ƙawata da tafi office ɗin
Daddy.Magani Mami ta ɓalle min ta bani na sha nan ta sake haɗa min wani tean,babu yadda na
iya haka na rinƙa shan shi amman a zahirin gaskiya sam ya fita raina. Miƙewa nayi na koma ɗaki,yau ma kamar jiya a kwance na tarar da Ameera ta sa
écouteurs(abun sauraro na kunne)ta na kallon wani abu a wayarta wanda ko rantsuwa nayi ba
zan yi kaffara ba Film ɗin batsa ta ke kallo.
Teddyna da ke kan gado na je zan ɗauka da sauri ta kife screen ɗin wayar wai dan kar na
gani,a falo na koma dan bata liberté saɓawa Ubangijinta yadda ta ga dama dan dai kuwa duk
wanda yayi daidai a duk inda ya ke ya sani haka ma akasin haka.
Kira Nabee nayi sai dai tayi ta sonné ba ta ɗauka ba har sau biyu,wasu hawayen baƙin ciki ne
suka silalo min "ta yaya ma zan bari *KARUWAR GIDA* tauraruwa mai wutsiya ta kafawa uba
mahaifina tarko na ƙyaleta?to wai yanzu minene mafita koko na roƙi Daddy akan ya aureta
tunda ya fi dai ace ƙawata ta san sirrin mahaifina ta hanyar zina?"na faɗa a zuci tare da
ƙanƙame Teddyna gam kamar zan shige cikin shi.
Turo ƙofa aka yi,Mami ce ta shigo kawo min chocolat ɗin da na sa a sawo min.Tsayawa tayi ta
na nazarina bayan na karɓi robar, "Mimi ko sai mun je asibiti sai na ga kamar ma kin ɗan rame
lokaci ɗaya"cewar Mami ta na shirin zama kusa da ni mu ka jiyo ihun Ameera.
Zuciyata ce ta bada dam ganin Mami ta nufi ƙofar kamar na riƙe ta na hanata zuwa sai dai
bakina ya yi min nauyi,ko second ɗaya ba tayi da shiga ba naji ta na salalami da sauri na tashi
na mara mata baya.
Tsaye cak Mami tayi ta na kallon Ameera wacce ta haye pilow ta na....ga kuma video ta na
kallo,har mu ka ƙarasa kusa da ita ba ta san mun zo ba sai ihunta ta ke saboda ta ƙure ƙarshen
volume ɗin.
Kujerar dressing mirror Mami ta ɗauka ta buga mata ita a tsakar baya babu shiri tayi watsi da
wayar tare da cire écouteurs ɗin ta na mai fasa uwar ƙara.
Da kujerar Mami ta shiga jibgarta har sai da ta kare,Ameera na ta kuka a ƙarshe Mami ta mayar
da ita kujera ta ɗale sai kishi take ta na buga kanta da ƙasa.
Ganin abun ya yi yawa na ruga aguje dan kirawo Daddy kar Mami tayi kisan kai,a yadda na ga
Mami ta haɗa mata jini da majina ba ƙaramin tayar min da hankali yayi ba ina zuwa na faɗa jikin
Daddy a sume......
Comment and share Please
Jikar Rabo ce
[18/11 à 15:29] Cham~rose: *KARUWAR GIDA...*♀️
```LOVE and
ROMANTIC STORY```
```MRS SADAUKI```
☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Whatsapp OR
Call 08066268951*
*PAGE 7-8*
Frigo Daddy ya nufa ya ɗauko ruwan sanyi ya malala mani,ajiyar zuciya na sauke tare da yi
mashi nuni da ɗakina.
Shi sai yanzu ma ya tuna a firgice na fito ashe,bisa moquette ya shimfiɗe ni ya nufin ɗakin
wanda tuni Mami ta sumar da Ameera ta koma gefe ta na rusa wani irin kuka mai taɓa zuciya.
"Innalillahi wa'inna iley raji'un"cewar Daddy ya na mai nufar inda Ameera ta ke a sheme babu
numfashi,bai samu damar tambayar Mami abinda ke faruwa ba ya ciciɓeta ya nufi waje da ita
tuni mai gadi ya wangale mashi get.
Tun a hanya ya yiwa Dr Ibrah magana wanda shi ma tun a waya ya nuna tashin hankalin
shi,suna zuwa tuni nures sun fito da gado aka ɗauke ta aka aza bisa tare da turata zuwa
emergency.
Idanun Dr Ibrah sun yi jawur saboda tashin hankali da ɓacin rai,sam ya kasa tambayar yadda
aka yi wannan lamari ya faru ko kuma akan minene.
Tagumi Daddy yayi ya rasa mi ke mashi daɗi, Allah na gani ya na son ƴaƴan shi fiye da komi da
na duniya da ya mallaka,wayar shi ya zaro daga aljihu ya danna kiran Mimi bugu biyu na ɗauka
cikin sanyi murya nace "Daddy..."ajiyar zuciya ya sauke yace "Mimina ya jikin naki?"nace "na
warke Daddy ina Ameerai?" "Ta na can likitoci na kula da ita"cewar Daddy,"ok Daddy ga mu nan zuwa ita kanta Mamin ba ta
ji daɗin abinda ta yi ba kuma kamar ciwon ta na son tashi" Daddy ya tambaye ni "Mimi minene
ya faru?laifin mi Ameera tayi da har Mamin ku tayi mata wannan dukan?"shiru nayi na kasa
cewa komi dan tuni Mami ta fita ta shiga motar da drever zai kai mu asibitin,jin na ƙyale yasa
Daddy kashewa.
Twins na ja mu ka nufi mota,a baya mu ka shiga dukan mu drever ya ja mu zuwa babbar
asibitin Dr Ibrah abokin Daddy,duk in ba mu lafiya can ake kai mu ko kuma shi ya zo har gida ya
duba mu.
Da taimakona Mami ta shiga cikin asibitin,ba tare da wani ɓata lokaci ba aka bata gado tare da
saka mata ƙarin ruwa duk da na lura ba da son ran Dr Ibrah ba dan sai wani hararen Mami ya
ke kamar zai doke ta.
Mu na nan jungum har aka fito da Ameera an wanke mata fuska tayi fyau yayinda aka naɗe
wuraren da taji ciwo da bandeji,sai a lokacin naji hankalina ya ɗan kwanta dan tuni ta na ta
barcinta.
Ina nan zaune kusa da Daddy yayinda na sa su Mami da Ameera ina kallon yadda kowa ke
sauke numfashi,shi kuwa Daddy ina lura da shi sai satar kallona ya ke ya na danna wayar
hannun shi.
Kamar an ce in juyo nan idona suka yi tozali da hoton Nabee bisa screen ɗin wayar Daddy,ta
sha riga da wando baƙaƙe yayinda ta baza sumar kanta irin ta Bugajen asali a kafaɗunta
,laɓanta sun sha man leɓe sai ƙyalli suke yayinda ƙwala-ƙwalan idonta fara ta ranbaɗa masu
kwalli sai ya fito da tsantsar kyawunta.
Zuciyata ce ta fara tafasa ta na halbawa da ƙarfi lokacin da na ƙara ƙarewa hoton kallo ta
wutsiyar ijiya,a gaban rigar kusan a buɗe ya ke wanda hakan ya baiwa dukiyar Fulaninta fitowa
kusan rabi ga wata irin gantsarowa da tayi irin dai na ƴan duniya.
Hawayen da suka cika min ido ne suka samu damar silalo min,tabbas zuciyata ta yarda kan
Daddy ya faɗa tarkon Nabee tunda har ya kasa ɓadda hoton ta ya tsaya ya na ƙare mashi kallo.
Fita nayi waje nan na tarar da twins suna cin biscuits da chocolat ɗin da na san bai wuce Dr
Ibrah ya saya masu,suna ganina suka taso su na gwada min abubuwan da ke cikin ledar.
Ban iya ce masu komi ba sai bajewa da nayi a kan tabarmar da ke shimfiɗe ina sauke
numfashi,saƙo ni ke son turawa Nabee to amman mi ma zance mata alhalin tuni wuri ya ƙure
min har ta turawa Daddyna karuwan hotunan ta uwanda hatta mace ƴar uwarta ta gan su sai ta
yaba da kyawun hallitarta balle namiji?.
Numfashina ne ya fara kokowar ɗaukewa tsabar tashin hankali,da sauri Dr Ibrah ya ƙaraso ya
na tambayata lafiya?ganin ina dafe ƙirji.Ban iya bashi amsa ba dan kuwa ba zan iya furta komi
ba,hannuna ya ja ya tada