Showing 42001 words to 43151 words out of 43151 words

Chapter 15 - KARUWAR GIDA END BOOK COMPLETE Hausa Novels Complete By Mrs Sadauki .pdf

01 Jul 2025

4497

kuwa ba za'a kai ka zuwa asibiti ba haihuwar za ta zo tunda tuni kan
É—a ya sawo kai,cikin azaba na fara kiran sunan Daddy wanda tuni ya fice hayyacin sa duk da
manganar da Hajiya Babba ke mashi na ya fita waje amman ya ƙiya.
Cikin ikon Allah na haifo triples duk gan mata,wani irin kuka Daddy ya fashe da shi ya duƙa yayi
sujidah shukur kafin ya fara É—aukar yaran.


Gyara min jiki Hajiya Babba tayi aka gyara gun da na ɓata aka saka turaren wuta, asibiti mu ka
wuce aka duba lafiyar mu da ta babies sannan aka sa min ƙarin ruwa.
Momy,Hajiya Babba, Daddy da kuma Abba sai aka rasa wanda ya fi son yaran kowa sai bajinta
ya ke nunawa.
Washegari aka sallame mu,direct gidana aka kai ni Hajiya Babba ta min wanka dan ita ba ta
É—auke ni a sarakuwa ba matsayin jika ta ke É—aukata.
Sai bayan ta gama min ta yiwa ƴan uku sai kuka suke,ni kuwa na ɓata rai kar a toye min yara😹
Daddy ma da ya shigo sai da ya saka hannunsa cikin ruwan dan jin zafin su Æ´an barka uwanda
suka kasance duk dangi sai dariya suke.


Ranar suna aka saka masu *UMMU SALMA,UMMU HABIBA DA UMMU KULTHUM* sosai na
samu Gift daga ɓangarori daban-daban.
Lokacin da Mami ta zo kasa É—agowa nayi na kalleta dan kunya na aure mijinta har da
haihuwa,Gift ta bani ta na murmurshin da duk wanda ya gani ya san na ƙarfin hali ne.




Bayan arba'in
Tuni yarana sun yi ƙiba sosai zallar kyawun su ya fito,cikin shirin fita na fito na goya ɗaya Daddy
ma ya É—auki É—aya sai na rungume É—aya mu ka nufi mota inda drever ke jiran mu.
Asibiti mu ka je aka yi mana ayo,cikin shagwaɓa nace "please Daddy ka bari na ɗauki ko na
shekara biyu ne"hannu ya aza min a baki yace "shuuut!kar naji kar na gani babu wani magani
da za ki ɗauka,haihuwa duk shekara na ke sonta so na ke ki tara min yara dayawa"buba ƙafafu
na fara ina shirin magana naji muryar da har abada ba zan taɓa manta ta ba.

Cikin kuka da damuwa ta ke cewa "wlh likita ni ban taɓa yin iskanci ba ta yaya zan samu

HIV?ka sake dubawa dai"da sauri na ƙaraso Daddy na bi na daga baya.
Iyani ta goge hawayenta tace "likita ta yaya za ta samu cutar ƙanjamau bayan ka tabbatar min
ta na É—auke da budurcinta har yanzu?koko result É—in wata ce ka É—auko?"Dr ya girgiza yace "ku
yi haƙuri abinda sakamako ya bada kenan ta na ɗauke da cuta mai karya gangar jiki kuma tuni
ta yi tsanani rashin zuwa kan lokaci ta na traitement a gida" "Na shiga uku ni Nabee wacce irin baƙar rana na ke gani?"Iyani tace "Nabeela na zata ciki ne
kika kwaso shiyasa har na kawo ki asibiti a min gwaji amman kika ce sai dai a maki na budurci
ashe ga banza ne,to gidan ubanwa SIDA ta shiga jikin ki?"
"Haba ba haka ya kamata ki yi ba,rarrashi ta cancanta a wannan lokacin dan kuwa har da cutar
Hanta gare ta ga kuma infections wacce duk ana É—auka ne ta hanyar zina ko kuma biye-biyen
maza na soyayyar shan minti "


Wani kuka ne ya kubce min ban san lokacin da na furta "Innalillahi wa'inna iley raji'un Nabee ke
ce a haka?ke ce kika yi baƙi kika rame kika yakuce haka?Nabee kin ga illar zama *KARUWAR
GIDA* ko?mi kuÉ—aÉ—en da kika tara suka amfana maki?minene amfanin budurcin da kika yi ta
tattali ki na cin duniyar ki da tsinke?" "Mimi ki yafe min na san ƙarshe na ya zo,na so cutar da ke da mahaifin ki amman Allah bai so
ba.Yau gani a wulaƙance babu daraja babu kyawun surar da ke ruɗar maza suna biyata..."
"Na yafe maki duniya da lahira Allah baki lafiya,dan Allah Nabeela kiyi traitement yadda likita
yace da sannu za ki samu sauƙi"banda gyaɗa kai babu abinda Nabee ta ke ta rairafo za ta zo
wajen Daddy yayi saurin cewa ya yafe mata ya na mai jan hannuna mu ka koma can cikin room
É—in da triples suke mu ka É—auko su mu ka dawo gida.

Wuni ranar nan haka nayi shi babu daɗi,sosai na ƙara tsorata da lamarin duniya yadda ya ke
juyawa kamar juyin waina.Daddy kasa fita yayi doli ya zauna kusa da ni ya na min nasiha
sannan ya ƙara da cewa "ki kula min da yara na ki basu tarbiyya ta ƙwarai ta yadda Ubangiji zai
yi alfahari da mu na tsare amanar da ya ba mu"rungumesa nayi nace "in shaa Allah mijina kuma
ka yafe min zargin da nayi ma na ka kasance da Nabee"ƙirjina ya shafo yace "bai komi my
Life"ya faÉ—a ya na mai kai bakinsa kan nawa.



***Bayan wasu shekaru
Abubuwa dayawa sun faru,ciki kuwa har da samun lafiyar Fauziya na yoyon fitsari tuni tayi aure
,Fadila ma masha Allah ta jerawa Nasir yara sannan tuni ta fara aikin gwamnati mai tsoka ta
canza rayuwar Anna wacce ta aza buri akan ta Nabeela ma ana ta ɗaukar magani a ƙarshe
kuma ta auri Alhaji Tanimu wanda yayi sanadiyar laƙa mata ƙanjamau cike da baƙin ciki ta
baiwa tsohon kyautar budurcin da samari da dama sun so karɓar sa ta hana.Iyani kuwa tuni tayi
saranda daga shegen kwaÉ—ayi na son kuÉ—i tare da nadamar rayuwa.

Ameera ma ta na zaune ƙalau da mijinta Abu Maleek,haihuwar su biyu duk maza.

Twins kuwa sosai suka girma ana ta karatu,Mami da Dr Ibrah ma an buÉ—e babin soyayya zahiri
bayan ta ɓoye da aka yi.

A ɓangaren Daddy kuwa tuni na cika mashi gida da ƴan mata har shidda bayan haihuwar ƴan
uku na haifi Agaishat mu na kiranta da Ummi sai Twins Nabeela da Nadeera sosai mu ke
gudanar da soyayyar mu ni da Æ´aÆ´ana da mijina.
Har yanzu Daddy na ke kiransa duk da yayi bakin ƙoƙarin sa na ganin ya hana ni, wannan yasa
yarana ma suke kiran sa da Daddy.


Ina zaune ina koyar da yarana karatu alƙur'ani Daddy ya shigo,duk suka fara yi mashi sannu da
zuwa murmurshi kan fuskata na ke kallon su yadda ya ke rarraba masu abinda ya shigo da shi
duk wanda aka ba sai yayi ihu koma gefe ya na murna.
Kusa da ni ya ƙaraso bayan ya gama da yaran ya jawo ni jikin sa ya zura min zoben gold da
yatsana ya na mai furta "i love You so mush my farin cikin rayuwa"ƙanƙamesa nayi ina mai ɗora
hannuna saman ƙirjinsa nace "na gode miji na gari"maganga ya raɗa min a kunne nayi
murmushi na saci inda yara suke sai na hankalinsu bai kan mu,hannun shi na ja mu ka fara
taka step.....



*ALHAMDULLAH !!!!*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login