Showing 9001 words to 12000 words out of 43151 words

Chapter 4 - KARUWAR GIDA END BOOK COMPLETE Hausa Novels Complete By Mrs Sadauki .pdf

01 Jul 2025

4494

shiga hankalin ki wlh in kika yi kuskuren gwada karuwancin ki ga...."sauran maganar ce ta

maƙale min ganin Daddy ya shigo ya na kallona.


Can ɓangaren Nabee ta sheƙe da dariya tace "na nawa kenan?wai an cewa kuturu Allah ya
la'ance ka ai tuni..."ban ida jin abinda tace ba Daddy ya amshi wayar ya kara a kunnen shi
rumtse ido yayi jin abinda Nabee ɗin ke faɗa,"yanzu ita ba ta ko jin kunya Ƴata ta ke gayawa
wannan maganar?"Daddy ke faɗa a zuci kafin ya kashe kiran ya maido hankalin shi gare ni.
Kaina a duƙe tuni idona sun fara ɗigar da ruwan hawaye,ɗago haɓata yayi sai kawai ya jawo ni
zuwa jikin shi dan bai san abinda zai ce ba ta ina ma zai soma?
"Daddy ka kai ni gun Hajiyar mu ina son komawa can da zama"na faɗa cikin muryar kuka
bayana ya bubuga yace "no Mimi ba za ki koma can ba zan dai kai ki sai ki wuni in ya so da
marice sai naje na ɗauko ki kin ji?"kai na ɗaga ina mai barin jikin shi na nufi bedroom.

Daddy kuwa huci ya sauke,ya shigo ne dan ya ga jikin Ameera sai kuma ya tarar da wannan
kayan baƙin cikin na *KARUWAR GIDA* da ta ke tsarawa ƴarsa abinda zai sa zuciyarta ta
buga,dan kuwa ya san ba iya abinda ya faru ba ne kawai Nabee ta gayawa Mimi har da ƙarin ta
kawai dan sawa Mimin tension.
Ƙaton hijab kawai na aza bisa tare da ɗaukar coton(auduga)dan wani sa'in period ɗina ya na
dawowa duk da dai dama kwana ɗaya ne ni ke yi ya tsaya.
Kallona yayi yace "Mimi a haka za ki je?"kallon kaina nayi nace "mi nayi Daddy?"kai ya girgiza
dan ya gane wayon da Mimi tayi na saka bungulin hijab a tunaninta bai hangi ƙafarta ba, ya ga
har yanzu riga da wando ne.


Kai na ɗan sosa sai kuma na fuske na ɗauki Teddyna,gaba ya yi ina bin shi a baya har mu ka
fito a farfajiya.
Seat ɗin mai zaman banza na shiga Daddy zaman drever,ai kuwa ƙamshin turaren Nabee ne ya
cika motar duk sai naji raina ya ɓace tare da jin haushin Daddy "wato a cikin motar ma suka
kasance?miyasa Daddy zai min haka ya bayyana sirrin shi ga sa'ar ƴar cikin shi?duk ƙoƙarin da
Mami ke yi bai gani ne komi?"Teddyna na rungume tare da ɓoye fuskata har mu ka zo gidan
Hajiya Babba.

Mu na shiga falon Twins suka rugo suka rungume ni,cikin dariya nace "to ku sake ni kar na
faɗi,ashe nan kuka zo ?ni shaf na ma manta da ku shiyasa ban ji motsin ku ba"Imane tace "eh
jiya Daddy ya kawo mu yace nan za mu zauna har sai kun samu lafiya"murmurshi nayi na ja
hannunta dan tuni Ihsane ta bar guna ta nufi Daddy .

Fitowa Hajiya Babba tayi daga kitchen gaisheta nayi ta amsa tare da tambayata jikina,nace "da
sauƙi alhamdullah"Daddy ne ya matso suna gaisawa da mahaifiyar ta shi amman duk rabin
hankalin shi na ga Mimi wacce ta rakuɓe ta rungume Teddynta tayi ƙasaƙe alamu tunani ta ke.

Tashi Hajiya Babba ta yi ta koma kitchen zuwa can suka fito ita da mai aikinta wacce ke riƙe da
ƙaton tray,hijab ɗina na cire na zo na zauna ƙasan Capet na fara haɗa abun breakfast ɗin.


Doya ce aka soya da ƙwai tare da yin wata ƴar sauce ta mayonnaise sai kayan tea,a cikin ƙaton
plate n'a zuba duk suka gewaya suna ci har da Hajiya Babba ni kuma tea ni ke sha ina satar
kallon Daddy yadda ya ke ci a nutse sajen fuskar shi na ɗan motsawa a hankali hakan ba
ƙaramin tafiyar min da hankali ya yi na.
Ina kurɓar tea ina kallon shi tare da sakin murmurshi,kofin tea ɗin na aje na kwanta bisa salon
mai zaman mutum uku Teddyna rungume a hannuna.
A hankali na fara rera waƙa wacce taƙamaima ban san ya ake yin ta ba kawai in na wuce a
hanya wani sa'in ina jin ta a gari,to kawai yanzu sai na samu bakina da rerata ```Yaushe ne
buƙatar za ta biya yau ne ko gobe?da ina da hali janyo shi zan yi mu yi zobeda siyasa ce
tabbas da nai yi zaɓe``` da sauri nayi shiru jin Hajiya Babba na cewa "iyeee!takwara ta aure
ta ke so"da sauri na miƙe zan ruga sai aka yi rashin sa'a Daddy ma da ya miƙe ya na dariya zai
wanke hannun shi sai mu ka yi karo dafe goshi nayi zan faɗi sai kawai ya taro ni na faɗa jikin
shi.


"Subahanallah Mimi kiyi a hankali mana,ga shi kin sa na shafa maki maiƙon mai a kaya"cewar
Daddy ya na mai daidaita min tsayuwa,baki na turo gaba ina kallon inda yayi tâche ɗin.
Su Twins dariya suka shiga yi min ganin ina gunguni tare da buga ƙafafu a ƙasa, murmurshi
Daddy yayi yace "ayya ki yi haƙuri ai gobe ma zan saya maki wasu tunda na ga so kike ki zama
kamar ƴar ƙwllo kullum cikin kayan gudu"Hajiya Babba ta karɓe zancen da cewa "ai kuwa dai
yau na ga sakalci goɗai-goɗai da ita ka tsaya ka na sangarta ta a haka ai ba gata kake mata ba
dan kuwa babu namijin da zai ɗauki sakarcin takwara komi kuka sai kace pampon an taɓa ido
ba su tsayawa sai zubar da hawaye"baki na kwaɓe nace "Daddy kaji ko Allah yanzu Hajiyar mu
ta bar ji da Ni kawai ka mayar da ni gida "na ƙarashe maganai ina yin kukan wasa.


Kai Daddy ya girgiza ya shiga kitchen ya wanke hannun shi,ko da ya fito bai tarar da Mimi ba
dan tuni ta wuce ƙurya ɗakin Hajiya Babba.
Sallama yayi masu ai kuwa Twins suka laƙe mashi doli ya tafi da su gida,Hajiya Babba ta miƙe
ta shigo ɗaki "binciken miye ake min a ɗaki?"ban ko juyo ba na shiga duba kayan da ta ke tara
min na ciro wasu baƙaƙen riguna guda biyu,da sauri ta karɓe su ta na cewa "ba fah zan baki su
ba sai kin yi aure dan haka kar ki yi wahala"na turo baki gaba nace "dan Allah Hajiya Babba ki
bani Allah ina son yin kwalliya da su ne"dariya tayi irin ta su ta tsofi tace "ai kam ba zan bayar
ba ko Amadu dakyar na bashi turaren da ya kai maki jiya shi ma dan ya nace ne".

"Wane turare Hajiya Babba?"na tambayeta ta bani amsa da "turaren da dai na saba saya maki

tun ki na ƙarama amman dan shegantaka shine kika canza wani kala kika bar saka shi shiyasa
ni ke tara maki shi a nan in kin yi aure sai ki cigaba da amfani da shi,na san mijin ki zai so
ƙamshi saboda ko a can Saudiyya matan su shi suke shafawa"shiru nayi ina tunani "to ko dai
Daddy bai tafi gun Nabee ba?dan ban mancewa da Nabee ta ji ƙamshin turarena ne tayi
ƙwaƙuwa na bata ɗaya sai kuma ta cigaba da sayen irin shi yayinda ni kuma na canza wani iri
daban.To amman in haka ne miyasa Nabee za ta gayi maganar ɓatanci a kan Daddyna har tace
sugar ɗin ta ne?".


Wata rose ɗin riga da Hajiya Babba ta yaɓa min a fuska ya sa ni dawowa daga duniyar
tunani,ihu nayi na rungume Kakata nace "thank You my granny,ya aka yi kika san ina son launin
rose?"na tambayeta ina mai sake ɗaga rigar.
"Ko uban ki ai na san launin da ya fi so balle ke da aka haifa jiya"cewar Hajiya Babba ta na mai
maida kayan yadda suke,"kai Hajiya shine har da saka Daddyna?to ni dai kar ki rufe kayan ki
bani mayafin da zan haɗa rigai"ba ta tanka ni ba ta jawo min wani farin adiko fari sol wanda aka
yi ma adon duwatsu.

Bisa gado na ajiye kayan tare da kwantawa ina rungume da Teddyna ,sai a yanzu na tuna
wayata na ga hannun Daddy bai bani ba.
Tunanin shi na fara moments ɗin ɗazu na tuna inda ya tallabe ni na faɗa jikin shi,lumshe ido
nayi jin tamkar yanzu ne ƴan yatsun shi suka luma bisa fatar cikina.
Rigata na sunsuna ai kuwa naji ɗan ƙamshin mayatacen turaren shi,a haka har barci ya ɗauke
ni mai cike da famarkin Daddyna.



Sai wuraren sha biyu da rabi na rana na farka,zanen Hajiya Babba na ɗauka na shige toilet.
Tâche ɗin jini kaɗan na gani a pant ga kuma liquide ɗin da ya fita yayin mafarki.
Shiru nayi ina tunanin "to wane wanka zan yi?na janaba ko na haila?"
Tuna malamin mu na islamiyya yace ```«Mazhaba Malikiyya sun ce idan wanka biyu ya haɗu
waje ɗaya na Haila da na Janaba to a nan wanka biyu za ka yi a rarrabe,kayi na abinda ya fara
samuwa a gare ka misali kamar mace wadda miji ya sadu da ita kafin ta yi wankan janaba sai
kuma haila ta risketa to a nan za ta fara yin wanka janaba ne sannan ta kawo na haila daga
ba.Yayinda sauran Mazhabobin ke cewa a'a wanka ɗaya za ta yi da niyya biyu kenan niyyar
wankan janaba da kuma na Haila»``` shiru nayi ina tunanin "to ni wane ya fara zo min jinin
Hailar ko kuwa wancan?kawai bari na ɗauki misali na biyu na ɗauki niyya biyu" na faɗa a zuci
tare ```da yin Bismillah,na wanke hannuwana sau uku,nayi tsarki,sannan na wanke gashin kaina
ina cuɗa shi ta yadda ruwa zai shiga duk ƙofofin mahudar gashin,sannan na game dukan jikina
da ruwa ina cucuɗawa tare da gaggautawa,ruwa na ɗebo a tafin hannu na kuskure baki sau
ɗaya na shaƙa a hanci sau ɗaya tare fyacewa``` ajiyar zuciya na sauke jin tamkar an sauke min
wasu kayan nauyi saboda na tsarkaka.

Bayan na shafa mai na tsane kashina wani zanen Hajiya Babba na fiddo tare da irin rigar nan ta
tsofi munafata na saka,dariya na yiwa kaina ganin na dawo tamkar wata ƴar ƙauye sai na shafa
madarar turare na fita falo.
A kwance na tarar da Hajiya Babba mai aikinta na yi mata tausar ƙafafu, kitchen na shiga ne
ɗebo dafa dukar shinkafa da su kayi wace taji ɗayen kifi.
Sai da naci na ƙoshi na sha ruwa na miƙe a kujera nace "Washhh Allah na gaji"Hajiya Babba ta
ɗago kai ta kalle ni tace "bayan kin share plate ɗaya na abincin?"na turo baki nace "ke ma ai kin
ci to minene na min dariya sabida Allah?"mai aikinta tayi dariya tace "Hajiya Babba ana
takurawa ƴata fah ai ba ma wani ci tayi sosai ba"Hajiya Babba ta taɓe baki tace "ƴar ta ki ma da
ko gaishe ki ba ta yi ba?"buɗe baki nayi da mamaki jin Hajiya Babba za ta watsa ni,"a'a ba ki dai
ji ba ta kau gaishe ni"cewar Lami kunya ce ta kama ni hankan yasa na fice na fita zuwa
farfajiyar gidan daidai nan kuma motar Daddy ta shigo harabar gidan.....


*Kar ku manta book ɗin kuɗi ki yi ƙoƙari ki biya 200 kacal ki sha karatun ki cikin nutsuwa ,wacce
ta shirya saya ta yi min magana ta WhatsApp* +22795045822
[21/11 à 19:48] Cham~rose: *KARUWAR GIDA...*‍♀️
```LOVE and
ROMANTIC STORY```

```MRS SADAUKI```

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*

*Whatsapp OR
Call 08066268951*

*Last free page mai son shiga paid group sai ya yi min magana ta WhatsApp* +22795045822

*PAGE 13-14*

Tsayawa yayi ya ƙare mata kallo tsaf,a yadda ta ke cikin zane simple sai ya fiddo manya hips
ɗin ta tare da shap ɗin su.
"A'u'zu billahi mina shaitani rajim"Daddy ya faɗa jin shaiɗan na kwaɗaita mashi surar ƴar cikin
shi.A jikina naji kamar a na kallona hakan ya sa na juyo caraf mu ka haɗa ido da Daddy
murmurshi na sakar mashi tare da nufowa inda ya ke jingine jikin mota,duk takonta ɗaya haka
zuciyar Daddy ke halbawa saboda yadda ƙirjinta ke motsawa saboda ba ta sa bra ba. Saurin kawar da kai Daddy yayi daga kallonta ya na ɗumin zuci "Mimi ki na da matsala wlh
yanzu haka kika fito babu breziya duk jikin ki na motsawa ga kuma masu gadi a gidan,kenan
bra ɗin da na sawo maki sun zama na banza"ji yayi zuciyar shi na suya dan har ga Allah ya na
son ganin ƴaƴan shi cikin shiga ta kamala gudun faɗawa tarkon sheɗan,dan dayawan maza sun
ɓaya ƴaƴan cikin su wanda dalilin shigar banza da wasu ƴan mata ke yi tsakar gida ya ke sa
uba yayi sha'awar ƴar sa.


A shagwaɓe nace "Daddy shine ka kawar da fuskar ka?"juyowa yayi ya kalle ni yace "no Mimi
akwai dai tunanin da nike yi ne"ya faɗa ya na mai jan hannuna mu ka nufi falo.


Bayan mun zauna ne Daddy yayi wata magana da ta sa zuciyata bugawa,"Hajiya Babba ki
fahimce ni ba wai ina son nisanta Mimi daga nan ba ne kawai a'a akwai ƙwaƙwaren dalili,kuma
makarantar can ta fi ta nan bada horo sannan duk bayan wata uku za ta dinga zowa ganin
gida".
Sharrr haka hawaye suka shiga ambaliya a fuskata "ta yaya ma har Daddy ya ke tunanin zan
iya barin shi na tafi wani gari karatu?miyasa tun farko bai kai ni ba sai yanzu da ruhina da
gangar jikina ke muradin shi?".


Tasowa yayi ya dawo kusa da ni ya na mai kamo hannuwana "Mimina kiyi haƙuri Daddy ba zai
taɓa yin abinda zai cutar da ke ba kin ji?"kai na ɗaga amman ba dan na so ba.


"To sai dai in tare za mu je dan ba zan bari ta tafi ita ɗaya ba Niamey can cikin gwarawa babu
dangin Iya balle na Abba"cewar Hajiya Babba, murmurshi Daddy yayi yace "wlh Hajiya Babba
tamkar kin shiga raina, dama yanzu yadda duniya ta lalace wa zai sakin ƴar sa budurwa ta tafi
wani gun inda babu mai tsawatarwa?"Hajiya Babba tace "ah to na zata kai ma sakalcin ƴan
Boko za ka yi saboda bariki ka kai Univasaty ta ke ko mi?"dariya abun ya bani nace "kai Hajiya
Babba yanzu Université ɗin ce ba ki iya faɗa ba?inda sunan goro ne ai ke ce a gaba"

"Kin yiwa Rahamu da kika baro gida "cewar Hajiya Babba ta na mai miƙewa,ni dai dariya nayi
Daddy yace "Hajiya Babba ban fah gama maganar ba " tace "akwatin da zan tafi da shi zan
kimtsa ko ba cikin satin nan za mu tafi ba?"kai ya jinjina yace "eh in shaa Allah in an kammala
komi ina sa ran zuwa jibi za ku tafi" "to kuma a bar ni na shirya kayana cikin hankali kwance
"Hajiya Babba ta faɗa tare da yin gaba.


Duban shi ya kai ga Mimi wacce ta tsunduma cikin tunani,yatsun hannuna ya fara ja suna fidda
sautin ƙwas.
"Washhh "na faɗa da ya ja ɗan ƙaramin amman yaƙi yin ƙara sai ya ja da ƙarfi,dariya ya yi min
ni kuma na turo baki kafin na tsurawa gemun shi ido.


Abun ka da abinda zuciya ke so haka na kai hannuna na shafi gefen fuskar shi nace "Daddy wai
miyasa maza ke barin saje ko sun san ya na yi masu kyau ne?"shiru yayi ya na kallona kafin
yace "tambayi surukina"na turo baki gaba nace "miye kuma haka nan?"duk da na san nufin
shi,"mijin da zan aura maki kafin ki tafi Niamey"na turo baki nace "ban so, Daddy jiya ina ka tafi
na ga kayi shiri irin na ƴan gayu wanda rabon da in ga kayi shi an kai wata biyu?"bai bani amsa
ta ba ganin na ƙure shi da ido sai kawai yace min "tashi ki kimtsa ina son mu biya shopping
kafin mu wuce gida "ba dan na so ba na miƙe ina gunguni tare da jin haushin ƙin bani amsa ta.


Tuntsrewa da dariya nayi ina cewa "Hajiya Babba duk ina za ki je da uwannan uban kaya sai
kace dai wacce za ta yi hijira?"ba ta kula ni ba ta cigaba da jera kayanta a trolly yayinda nima
na shiga sabgar gabana na shirya cikin doguwar rigar da Hajiya Babba ta bani da safe tare da
yane kaina da mayafi.

"Masha Allah takwas kin tsaf tubarkallah,yau dai kam da ace fita za kiyi na tabbata da sai kin
samo mijin aure kin ga kuwa sai nayi zamana"cewar Hajiya Babba ta na ƙare min kallo tare da
yaba kwalliyata.


Madarar turare na murza a hannu kafin in fice ina mai cewa Hajiya Babba "a wanke min
sous-vêtement ɗina kafin gobe" "a'a mi zai hana ki tafi da kayan ki?"cewar Hajiya Babba wacce
ta biyo bayana.


Sallama mu ka yi mata kafin mu bar gidan,cikin zuciyata ni ke mamakin yadda Daddy ya kauda
kan shi daga gare ni ba tare da kuma ya yabi kwalliyata ba.
Hakan da yayi duk sai naji babu daɗi,Kalla Mall mu ka je da shigar mu wani buzu da ke zaune
bisa kujera inda comptable ke zama yace "masha Allah ka ga wata tsadaddar flower"murmurshi

na sakar mashi ganin ya ƙure ni da ido kuma da ɗan sauti yayi maganar ta yadda kusan duk
wanda ke wajen ya ji.


Ji nayi Daddy ya riƙo hannuna cikin nashi,wani irin shock naji haɗi da wani abu ya tsikare ni.
Hararata yayi sannan yayi ƙasa da murya ya na cewa "ki zama mace mai kamewa a duk inda
kika je kar ki nuna ke mai arha farashi ce ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login