Showing 1 words to 3000 words out of 54969 words
💘
ZAMAN TASHA
��💘��💘��💘��💘
BY YMMY AYSHA
��💘��💘��💘��💘
🅿�1�⃣&2�⃣
BISSIMILLAH RAHMANI RAHIM yanda nafara littafinnan lfy da raina da lfy ta ya Allah
kagwadaman karshenshi daraina da lfy ta inasonku masoyana so mai tsananin girma, fatan
alkhairi ga dukkan masoyan ummy aysha 💅
Zaune take abakin TASHA hannunta rike dawata katuwar rake saisha take hankalinta kwance
sanye take da riga da wando na Pakistan wandon fari sol riga orange sai wata hijjob mai
saukin kudi fara sol yar karama mai hula data dace da kyakyawar fuskarta dabazata wuce yadi
d'ayaba tsakiyar kanta tayi acuci bawata kwalliya taiba bayan kwalli dake idonta amma saboda
farinta bazaka ce batashafa powder ba kafarta sanye dawasu orange din takalma dabazasufi
dari ukkuba cikin daga sauti irinna yan TASHA tace yane
BIG har yanzu baka kammalaba? wani dan tulaki na hango yayo wajenta dadan gudunshi yace
yar Cara's wlh mutum daya yayi saura tace ok zankarasa shanye rake nah inban samuba zan
wulla da wayanda suka samu tafada tana lumshe idonta BIG yace angama yanda kikace haka
za'ayi tana zaune taga wata hadadiyar mota mai maseefar kyau tayanko da gudu tagefen
datake zaune akan wani dan karamin table cikin daga sauti take fadi wait wait!!!
Ganin motar bazai tsayaba cike da kwarewa tasaita raken hannunta tajefi bayan motar dasauri
aka parker motar wani yafito dasauri da alama driver ne ,
Cikin wata tafiya mai cike da kasaita kasancewarta doguwa mai jikin kiba amma basosaiba sai
tafiyar tamata mugun kyau tafara tafiya tare da jefa hannuwanta acikin ajjihunta takaraso wajen
da driver yake tacemai bakason aikinkaba ko?
Indai kason aikina ai yakamata inkana tuki kaji wani canji amotarka katsaya kakula wannan
taurin ran naka zai iya jamaka matsala watarana..
Afusace driver yace baza akulanba ke harkin isa kigayaman aikina shekara goma ina tuka mota
ko keke bantaba bigewaba shikenan yau zaki koyaman aikina mtss
Ta lumshe idonta dana lura dabi'artace tace ok tare da dukawa kason motar saiga zungureriyar
'kusa ajikin tayar da gab take da fashewa tace wannan yakake ganin zaku kaya aduk sadda
tafashe? .
Cikin rashin gaskiya da kame kame driver yafara kallon cikin motar yace to to!! Naji jeki.
Tamikomai hannu tare da fadin bani zan wuce .
Driver yace mizanbaki tace kudi nasanya nasai rake inasha ganin zakuyi accident yasani
jefamaka raketa ka,kauga bazanyi asaraba tafada tana juya ido
Cikin takaici yace to ubanwa yasaki kika jefa? kikaki barina inma mutuwace in ....
Baikarasaba yaji an daukeshi da mahaukacin mari tadago idonta da,cikin "kankanin" lokaci suka
koma jajawur tacemai mafi girman kuskuran dazakai shine kazagi mahaifina duk ranar da
tsautsayi yasaka sake zagin mahaifina wlh anan zan gwadama ni cikakkiyar yar ZAMAN TASHA
ce wlh banza kawae kaban kudina inwuce nacema
Sosai yarike kuncinshi yana kallon yarinyar dabazata wuce shekara ashirin da biyarba
tadaukeshi da marin daya nemi gigita tinaninshi yace nikika mara?
Tace eh karama mana yadaga hannu zai kifamata mari aka zuge glass din motar tare dacemai
kull cikin wata tattausar murya.
Bahaka yasoba yaso yanunamata shima yayi ZAMAN TASHA bawai ita kadaiba.
Bude motar akai tare daziro wata kyakyawar farar kafa dake sanye cikin bakaken cover sai
kyalli suke ahankali jikinshi ya ida fitowa bansan sadda nace masha Allah tubarakhallah lallai
Allah yayi halitta kyakyawan namijine farine kyakyawan gaske ajin farko yasha wata danyar
gizna fara sol yasanya hular zanna mai ratsin fari da'baki sajenshi kwance lub lub
bakikirin,bakinshi pink color yan kananu dasuka dace da fuskarshi hancinshi dogo sosai har
baka yanada yalwar gira da manyan idanuwa da kallo guda saiya ladaftar da mai laifi.
Cikin kasaitacciyar muryarshi yacema driver bukar bakada hankali ko?
Kai wawan inane danmi zaka biyo dani tacikin gari bayan kason duk yan TASHA ne kezazzaune
suna ZAMAN banza suna jiran azo abasu dagangan zasu sama motarnan wani abu dan
sunganni aciki ke ubanmi za abaki harkina daga,hannu kina marin wanda yagirmeki banza yar
ZAMAN TASHA kawae.
Cikin bacin rai tace ubanka nike zaman jira kasake zagarman uba wlh zansanya amaka dan
banzan duka awajannan dawata banzar fuskarka kamar kosai mtss dallah bani hamsin dina
inwuce.
Cike da mamaki yake kallonta tinda yake baitaba ganin macen data tsinkashiba arayuwarshiba
kamar yarinyar nan wato batama tsoranshi bata shakkarshi bata ganin shidin ko wayeba
kenan?
Yace aikuwa zakison kintabo IRFAN KHABIR HAIFAN ,yafada yana cije bakinshi .
Cikin zaromai idonta tace kai dallah cen dawani shegen sunanka kamar atini niban kudina
inwuce kaji ganin,zata taramai mutane yaxaro makudan kudade yajefamata tace kai harkana da
kudin dazakaban wlh baka dasu kuma bak ajeba ta duka tadauki dubu daya tasiyo rakenta ta
nera hamsin takawomai canjin tare da watsamai su afuska .
Azabure driver yace laaa kai wannan akwae yar banzar yarinya datsayi kamar daran tsalla mai
gida jibi tsohuwar goma talike ahancinka yafada yana nuna naira gomar datai tsaye bisa zufar
dake zuboma IRFAN ahanci suna tsaye kunya duk tacika IRFAN ganin yanda mutane suka
zagayesu suna,kallo basu ankaraba saiga yar Cara's tadawo da wata katuwar kusa mai
maseefar tsini tadagata tacakama tayar motar jikake suttt duk iskan yafita.
Takalli irfan tace jan kosai hukuncin duk wanda yazagi mahaifina kenan tana cikin magana BIG
yace yar Cara's ansamu cikon daya, cikin sauri takarasa cikin tashar nan akafara fadin Cara's
Cara's ko kallonsu bataiba tashiga wata jar mota kirar gowp tayi addu'a tare da daukar wani
bakin glass tasama fuskarta wani mahaukacin kyau yamata dukda fuskar tata adaure take
tamau babu alamun annuri afusace taja motar tafita daga cikin TASHA tana zuwa dai dai inda
IRFAN yake tsaye har lokacin kamar andasashi yakasa komi ga naira goma ahancinshi
baidaujkeba bata kuma fadiba. Wasu ruwan dake kwance bakin inda yake tsaye tamurza tayar
motar cike da kwarewa ruwannan sukai tsalle suka watso jikin farar shaddar IRFAN da driver
dake tsaye yanata magana azabure IRFAN yadago jajayen idanuwanshi yazubama motar
dataimai wannan aika aikar tasauke glass tare da cemai hukuncin duk wanda yaraina mahaifina
kenan mtsss taja motar damahaukacin gudu kamar ba maceba tadauki hanyar jibiya sai gudu
take shararawa wata tsohuwa dake xaune gaba tace haba yar nan kibimu ahankali mana
inbanda lalacewa zamani kina mace kina tukin mota. Tafiya mai nisa irin wannan wlh danason
maca xata kaini gidan balele da bazan shigaba yar Cara's tai parking gefen titi tare da fitowa
tasamu sit belt tadaure tsohuwar nan tare da fadin kisanya wannan kawae gudun karki watsar
da hakoran gaba kinyi expired amma har gobe son duniya kike .
Cikin sauke numfashi tsohuwa tace ke dan ubanki kicereman igiyar nan tinda ba goro bace ni
saiki daureman ciki dan kinsan safara'u matar balele tayankaman kaji bakin ciki kike inci ko?
Tinda kinsan babaki zanba .
Sosai tai murmushin daya fiddo da zankadediyar wushiryarta dake tsakankanun fararen jerarrun
kananun hakoranta masu maseefar kyau ga mamakina hadda hakorin makka gareta dan asali
mai maseefar kyau sosai yakarama hakoranta kyau tace karki damu mama bama TASHA
zankaikiba har kofar gidan dakikeso insha Allah.
Tsohuwar tace wlh yar karama zan yanmaki kazar inbakibar guduba yar Cara's tace aini burina
inkaimu inkwaso wasu inkuma kara komawa dan 'ka idata so biyu nike jigila wannan hanya duk
kuma inda shidda tayi na yamma ZAMAN TASHA yakare sai Allah yakaimu kanan.
Tsohuwa tacema wasu samari biyu dake baya kai anshinan kasha wata shegiyar hularka har
bisa ido kamar kakifa po kiraman dana ingayamai ankusa kasheni.
Wanda taima magana cikin muryar yan daba yace waiya tsohuwa wlh karkija bara tadawo bana
wannn hular sata sirrine dan bansaba sawabane amma inkika sake magana zancireta saiki son
dawa kike magana atakaice dai sunana makashi...🖊�😳�
25/03/2022, 22:06 - Khadeejaht Salisu Fari: ��💘��💘��💘��💘
ZAMAN TASHA
��💘��💘��💘��💘
UMMY AYSHA
��💘��💘��💘��💘
🅿� 3�⃣&4�⃣
FREE NOVEL
gabaki daya tsohuwa tafiddo idanuwanta waje tare da fadin yallabai dama kaine? aimundade
munajin labarunku kullum sainaima addu'a Allah yahadamu ko bisa hanyane, inacikin
masoyanka tafada jikinta na rawa baki daya.
Cikin muryar yan daba yace to gdy nike kakus.
Tace karkaji komi masoyina bari mukarasa gidan d'ana in sammaka kaji da safara'u tadafaman
kaji ko?
Yace yawwa kakus dama sai nasha wahala kamin inkarasa inda zani dan haka sai mufasa
kawae muje mushanshareta aha.
Kasa kasa tsohuwa tace jibarshi shege b'akinshi kamar zunibi ya ajiye wani gemen banza
kamar tabarmar kaba.
Makashi yayi ka sake yanajinta yace kikace me tsohe?
Cikin rawar murya tace gafarar Allah nike nemamaka nason dole walakiri ya cima uwa tinda kai
hamshakin dan dabane ka kauga haduwarku babu kyau ko dan jikallena mai kan kwakwa.
Yace wlh tsohuwa kika sakeman sharri saina kifar da motarnan kowa yagane kuranshi yafada
yana zaromata jajayen idonshi. jijinta na rawa tajuya tare da fara lazimi.
Yar Cara's tuki take cike da kwarewa bata um bata um um amma bakinta yana motsawa
ahankali itakadai tason mitake fada suna karasawa bakin gadar jibiya taja wani wawan burki
tsohuwa da tasha dauri saida tai gaba tadawo baya jikake kumm.
Tasaki wani mahaukacin kuka tama fadin Allah ya isa tsakanina dake yar cakwal kike ko yar
firit?
Yar Cara's tafita daga motar tare dakama hannun wani dattijo da tagani zai tsallaka titi, mafari
tsaida motar kenan saida ta tsallakar dashi tana kokarin juyowa, yace yanda kika taimakeni
Allah ya ya'yemaki duk damuwar dake ranki yata ngd da kokari.
Yar Cara's tabishi da kallo tare da fadin bakomi baba karba wannan kasai ruwa. tafada tana
mikamai naira dari biyu bata jira cewarshiba ta tsallaka tabude motarta takara gaba sosai
tsohon nan yabita da kallo har ta baccema ganinshi.
Suna cikin tafiya tsohuwa tace dan ubanki "yar Cakwal" ga kwanar gidan d'ana balele cen kin
zalinceni kin cireman hakoran danikema jikokina dariya,tafada tana bude katon wawulo din ta.
"Yar Cara's" tace kai tsohuwa wannan dasashin naki aibana yau bane kijifa babu alamun jini
awurin amma in ni namaki kiyi hkr kakata kinji?
Tsohuwa tace nayi amma bazan baki ko sisiba dan balele nah bamai kudi bane kashin talauci
garai duk abunda yataba baya albarka. yauma nazo inbashi shawara yafara sana'ar
kidmashins dan duk yayi maganin wani dan iska dawani tsohon dan ta adda dayake ganin
yakai wani shege da masu hula bisa geme tafada tana satar kallon makashi.
Makashi yace idan kika sake kallona inba sai na ciremaki hanciba dan kwal uba nike haba kaji
maseefa.
Tsohuwa tace wlh karkaga laifina kama ka keman da shanuwa da akai layya bana makwaftana
gidansu irfanu ga hula kakifa kamar kasamu bokitin roba amma namaka alkawari bazan sake
kallonkaba tafada tana maida hankalinta ga titi suna zuwa kwanar gidan balele tace asauketa.
Yar Cara's tace bari inkaiki kofar gida kinji inna?
Tsohuwa tace ke kinsan dalilin daya hananine ne? haba banso saukeni mana yar cara'f.
Yar Cara's tace bafa haka akecemanba inbazaki iyaba kikirani da mufeeda kawae.
Tsohuwa tace ai dama ba zakara aka yankamakiba kikasa akasamaki yar cakwal ? Gasunanki
na mutunci ganin za awuce da ita yasata cewa ke saukeni yayi nan.
Yar Cara's tai parking tasauketa tare da sauka ta,daukarma tsohuwa jikkata ta ajemata tace
inna yaushe zaki koma in,mayar da kene?
Tsohuwa tace ke yar nan inkinganni lahira maza suka kaini ba mataba kinji tsaya inkawomaki
ruwa tinda kinada kirki.
Tafada wani tafkeken gida tare da rufe kofar.
Yar Cara's natsaye tana juya hannuwanta sai jitayi anbude kofar anfito wani zanka deden
sojane tsohuwa nagaba yana bayanta tana zuwa tabude bayan motar da karfi inda makashi ya
jingina da kyaure yana kwasar bacci sai jinshi yayi kasa sharaf agigice yatashi yana fadin
la'ilaha illallahu muhammadu rasulillahi (S.A.W) dan duk tinaninshi accident sukayi .
Tsohuwa takwashe da dariya tare da fadin shege ashe kason Allah to kwantar da hankalinka
nakawoka amaka hukuncij daya dace a musulunci ga dana nan zai cima uwa dai dai
gwargwado tafada tana nunama sojannan dayayi tsaye yana karema yar Cara's kallo.
Tsohuwa ta dage takaimai bugu ga kirjinshi tare dafadin kai dan ubanka bacema nai kacimai
uwa ba kayi tsaye kamar gunki.
Yace innamu bazaifa yiyuba inkamashi hakanan amma kibarshi inkere na yawo zabo nayawo
watarana zamu hade.
Tsohuwa tasanya kuka tace shikenan balele. tadauki wata yar karamar tsoka tacema yar Cara's
anshi ga alkawarin danaimaki .
Yar Caras tai murmushi tare da dukawa har kasa tace ngd inna Allah ya amfana tafada tana
fadawa cikin mota, dasauri makashi yashiga ciki dan hakanan tsohuwa naneman tajamai bala'i
daga wasa Allah yarufamai asiri sojan nan baikamashiba suna hawan bakin titi suka sauka suka
biyata tajuyo katsina aguje cikin kankanin lokaci tashigo cikin tashar KSTA tana shiga ta ajiye
mota su BIG sai sannu sukemata ta amsa tare da cemasu batajin dadi zataje gida sai gobe
insha Allah yau fita daya zatayi kowa yasha mamakinta dan shekara ukku da,fara aiki amma ko
bata lfy saitayi jigila so biyu .
Tana barin TASHA ta hau napep tare da sauka wani karamin gida sosai dayake a'matse sosai
tana shiga ta iske mahaifiyarta da kannanta su biyu zazzaune sunyi uba uban tagumi da alama
yunwa kekaimasu karo tana shigowa kannanta biyu mace da namiji suka mike suna faddin
oyoyo adda sannu da xuwa mikika samomana ne?
Yar Caras tace ga kudin dana samo yau banajin dadi gasu saikusai wani abu ko ? Tafada tana
juyemasu baki dayan kudaden hannunta, takalli ammy su dake zaune gefe ta kauda kanta cen
gefe tace ammy nadawo ga kudin nan nasamo amma bayawa.
Ko kallonta wadda akakira da ammy bataiba. ko kadan yar Cara's batadamuba dan inda sabo
yakamata tasaba tana zaune suka samo taliyar muri dafaffa suka zauna sukaci babu wanda
yacemata komi har suka gama ta dauki bokiti ta debo masu ruwa makwafta ta ajiye tare
dacema kannanta nawuce sai allah yakaimu, ammy natafi kamar yanda tayi tsammani bazata
amsaba hakance tafaru ko kallonta bataiba.
Tana fitowa ta,tsallaka gefen titin gidansu ta doshi wata bishiyar bedi dake gefe inda wata
zabgegiyar motar mai maseefar kyau kirar zamani take tafada cikin motar tare da sauke
numfashi mai karfi tace ya rabbi ka warwareman matsalata Allah kasan dai dai Allah
kabayyanar da gaskiya lamarinka akan baiwarka tafada hawaye nazubomata. ta kunna motar
tare dabata wuta tahau titi sosai take gudu da motar cikin kankanan lokaci ta iso goruba rood,
wani tafkeken gida da duk yafi sauran gidajen unguwar baki dayanta kyau naga tayi hon da
gudu wani buzun mutum dayasha rawani yarugo yabudemata tare da fadin haj sannu da zuwa
ya aiki Allah yatsareki yakaremanake yabaki lfy sannu hajjaju yafada cikin muryarsu ta buzaye.
Yar Caras tace yawwa baba sannu ya aikin fatan banyi bakiba ko?
Yace eh amma alh fahad yashigo dazu bansan miyayiba yafita.
Tace ok badamuwa tafada tana karasawa wajen parking lot inda wasu mahaukatan motoci
sunkai hudu suke lullube cikin tampal tana gama parking tafito tare da cilla key dinta, ta chabe
tai hanyar cikin gidan masha Allah nace dan wani mahaukacin gidane mai maseefar kyau
(tsayawa tsara kyan gidan zai iya cinye baki daya littafinnan amma ku hararo abun)
Tana shiga tafada saman makaken gadonta tare dafafin wash. Tatashi tacire hijjob dinta nan
wani yalwataccen gashin ta ma aboci tsawo da sheki bakikirin dashi yazubomata har bisa
gadon baya tacire gabaki dayan kayanta tai tsaye bakin mirro ta,fashe da wani irin mahaukacin
kuka tare da fadin ni ni niiiii.......🖊� 25/03/2022, 22:11 - Khadeejaht Salisu Fari:
��💘����💘��💘��
*ZAMAN TASHA*
��💘��💘��💘��💘
WRITER UMMY AYSHA
��💘��💘��💘��💘
🅿�-5�⃣&6�⃣
*Elegant online writers*
Niii rayuwa, zataima haka.
Wace irin mahaifiya, Allah, ya bani da bata, É—aukar kaddara.
Dan ummy, zata kasa É—aukar kaddara da Allah ya É—ora?, bayan komi yafaru dani sana din
tane.
Duk duniya bata da abunda ta tsana a rayuwarta sama dani, ta faÉ—a tana fashewa da wani
mahaukacin kuka mai cin rai.
Saida tai kuka mai isarta bata da wanda zai rarrasheta, kana ta faÉ—a haÉ—aÉ—É—an toilet
ɗinta, da keta ƙamshi, komi nacikinshi fari sol ne.
Sosai gabanshi ke wani irin mugun faÉ—uwa, ga wata matsananciyar kunya data rufeshi, yau
shine wata yar ZAMAN TASHA, zata wulakanta a gaban bainar nasi innalillahi wa inna ilaihirraji
un!
Driver da fuskarshi tacika da kwatamin, da "YAR CARA'S" tawatsamai, yakalli ,IRFAN dako
idonshi baka gani dan baki daya fuskarshi, da jikinshi ya lalace da kwatami.
Kayi hkr yallabai, muje gida kadan dauraye kayan naka saimuje inda zaka ko?
"IRFAN" da bakin ciki ya hanashi motsi, yadago jajayen idonshi, dasaida sukasanya driver ya
daka tsalle, yakoma gefe, yace yallabai wlh wuta ke haramar tashi, daga idonka, dan allah kayi
hkr bari inkira ado yayi maza yakawomaka, sabuwar mota yanzu, yafada yana laluben wayar
shi.
Bayan yakira, yacema ado kakawomana mota, gamunan dai dai TASHA kofar guga kayi sauri
yallabai najiranka.
Baifi 20mint ba saiga wata zabgegiyar mota, tayi parkin gabansu, "Ado yafito dasauri tare da
kalle kallen inda zai gansu.
"IRFAN" nakallanshi amma bazai iya cemai komiba, kamar ancema driver yajuya, yana juyawa
sai yaga Ado, cikin daka tsawa yace gamunan gabanka shine kaketa kalle kallen iskanci, kamar
bajiranka akeba.
Ado yazaro ido yakara kallon driver tare da fashewa da wata mahaukaciyar dariya yace yau
gyaran 'kwata kayi? ko-ko gyaran rijiya? yafada yana dukawa saboda dariya.