Showing 33001 words to 36000 words out of 54969 words

Chapter 12 - ZAMAN TASHA COMPLETE BY UMMY AYSHA.pdf

Advertisement

10 Jul 2025

4056


Moopy zata fara magana sukaji ana buga kofar da mugun karfi, tare da fad'in abude! abude!!
abude!!! Ba lafiya Tsohuwa ga yan wuta sun bayyana, wayyo Allah nah kun shiga ukku , nidai
nayi nan zasu balbakaku Modibbo ya fad'a da mahaukacin ihu..

Da gudun bala'i Tsohuwa ta tashi tana fad'in na shiga ukku Modibbo miyafaru?
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘��💘��💘��💘��
ZAMAN TASHA
💘��💘��💘��💘��
NA UMMY AYSHA
��💘��💘��💘����
4�⃣1�⃣&4�⃣2�⃣

""" Modibbo "yace inkin bud'e da wuri kya'gani, dan Hurawa zanyi sama Wallahi".

Tsohuwa duka jikinta yad'auki rawa ta fara la'luben Aljuhun data jefa key din kofar, da kyal ta
ganshi rawar da hannunta keyi yasa takasa bude kofar, kawai ta saki kuka tare da dawo'wa
wajen Ammar da kanshi na kasa har lokacin hawaye yake," tace Ammaru."
Da sauri yatashi tsaye zai magana! Tsohuwa ta sanya iya karfinta ta kai mai naushi a kirji, tare
da fadin kai kam akwai dan banza sai kai man zaune kana kuka, kamai da idonka kamar bututu
gidan mai sai zuba yake, kanajin an'ce yan wuta a'gidana baza ka iya tashi ka bud'emamu
muga a'bunda ke faruwa ba, in sukaja mana bala'i fa? kafa sani sarai bamu da nisa da
Makabarta..

Ammar ya dafe saitin data naushe shi ya karbi key din ya bude kofar, zai dawo ciki ya zauna
Tsohuwa taja hannunshi da karfi tare da fadin mai jego ma taci ubanta, shikenan bazaka fitaba
sai ni ka keso in'fita, da zaka lallabo kadawo ka zauna?

Ammar "yace haba Tsohuwa kin'son haukan Modibbo sarai, yanzu haka bawani abu bane kawai
za'izo ya d'agama mutane hankali.

Timm!!! Sukaji an'fado dakin!!da sauri Tsohuwar ta tashi zata ruga modibbo yace
garkame-garkame Ammar yan wutane Wallahi sai turiri suke..

Ammar ya da kamai tsawa tare da fad'in wai su waye yan wuta ne?..

Tsohuwa daga bakin kofarta "tace ka leka mana kagani, katon banza kai, ka tsaya palo kaki
fita...

Ammar ya zura takalmanshi Moopy ma ta bishi a'baya, daga nesa Tsohuwa taga Moopy ta bishi
aguje ta fito tana "fadin Wallahi baki isa ba, saikin karasaman, dama rabo na da kuka na dad'e
ina bukatar in'tsiyayyar da duk wasu hawayen da suka taran ma sukai datti,sabbi nike so su
taran'man. takamo hannu Moopy ta rike gam har suka karasa harabar gidan, inda suka ga ba
mai Gadi sai kofa a wangale.

Ammar ya kwalama Modibbo kira tare da "fadin kai Modibbo fito banga kowa ba".

Jin anyi magana yasanya Modibbo daya shige cikin la bule fitowa har harabar gidan,"yace
Wallahi Amiru Yan wuta ne miye riba ta in nai maku KARYA.

Ammar zai magana sukaga wasu Samudawa su biyu suna shigowa, sunsha uniform dinsu
jajjaye suka doso wajensu," Tsohuwa ta rike kugu tana fadin AA dama kune yan jahanama ne
ko yan lazza ..

Daya daga cikinsu "yace Auzu billahi" haba Inna, ya daga shigowarmu zaki ai'bantamu mu yan
gyaran wuta,ne..

Modibbo "yace karya kuke ceman kukai yan wuta ne ku".

Daya daga cikin su "yace kam bala'i muzakace ma Yan wuta? lallai baka da hankali,da bakina
da naka nacema yan gyran wuta ne, Alh Khabir ya ai'komu zamu kara maku Waya guda wadda
bazaku taba rasa wuta ba, kullum zaku kasance cikin haske, shine zakace nace ma Yan wuta .

Tsohuwa 'tace au Yan wutan dai kenan, da gaskiyar Modibbo ..

D'an Nepa ya gilgiza kai tare da cewa Bulama mufara a'bunda ya kawo mu, wancen
Mahaukacin zai b'ataman rai, kason kiwon kauye ne .

Wanda a'kacema Bulama yayi dariya suka fita suka d'akko dogon Tsani suka shigo dashi,
Tsohuwa ba tace komi ba, hakama Ammar idonshi a kasa yake Moopy kuma hawaye kawai
take,hannunta na cikin na Tsohuwa tai mata mugun ruko..

Sun kai tusani wurin daya dace su had'a wayar bulama da yafi tsawo da kwari, ya haye cen
sama, ya yinda abokin ai'kinshi ya rike tsanin sosai dan gudun samun matsala .

Daga sama Bulama "yace Basho sai ka kawo'man flower zan d'aure wata waya nan.

Wanda aka kira da Basho "yace to sakko ko lafiya lau zaka iya tsayawa..

Bulama yayi dariya yace haba kamar wanda ya fara aiki yau, miu ai sai dai mu gwadama wani
ai'kin nepa Wallahi.

Basho "yace to ai shikenan" ya saki Tsanin ya fita da sauri.

Wata irin dariya ta kama Modibbo dan wani abu ya tino, da sauri yabi Basho ya rufe get din,duk
su Tsohuwa suna cen duniyar tinani basu lura ba.

Modibbo ya zagayo ta cen bayan gidan harya isa wajen tsanin, Bulama bai lura ba yana ta yan
wake-waken shi tare da kod'a kanshi,na su gwanaye'ne. Modibbo ya lalla ba ya dinga hawan
Tsanin a'hankali har ya rage saura step biyu ya cimma Bulama, Modibbo yayi wani murmushi
tare da d'aure fuskarshi a'hankali" yace kai Bulakus ka taka man yara'na da Matata na ba y'arta
no-no, kabi tasaman ta yau zan cirema no-no uwa kam tinda kai mahaukashi ne, ya 'karasa
cikin maganar su ta Fulani..

"Jikake kurrrr cikin Bulama yawani irin juya, dan bakaramin furgi ta yayi ba, yafara k'ok'arin
juyowa

Modibbo "yace juyowar ka dai-dai take da makanshewar ka dan buhun ubanka.

Jikin Bulama ya fara rawa dan ya tabbatar Aljannun ne ba mutum ba, saboda ko kad'an baiji
haurowar Modibbo ba, saboda Modibbo baida nawie

Bulama" yace wattaba'una ma tu-tula shayad'iya ala mulku sulaiman....

Modibbo "yace kana kara magana zanyi majajjawa da kai in she'ka ka da k'asa, wato kazo
gidan mu shine harda cema 'Dan gidan mahaukashi makaryaci ko? bakai kace yan wuta bane?

Bukama "yace Wallahi hakane Ifritu" amma kayi hakuri bazan kara ba.

Modibbo "yace to ya labarin no6no matata daga Ratattaka Rabi da tsani..?

Bulama yace wallahi bansani ba Ifritu, amma zan sawo mata kindirmo kasuwa sai a'sanya ciki
in'kaita asibiti a'juye sai a'd'inke....


Wata mahaukaciyar dariya Modibbo yasanya, tare da fadin au dan banda kishi sai in'bari
a'taɓata ko?yanzu ni keso ka biya ta in'ba hakaba zan je gidan ka in ciro na matarka
in'dasamata yanzu.

Bulama ya kece da kuka yace haba Ifritu Minal Jinnu dami zanji? da rashin haihuwar da batayi
koda kayan a'latun da zaka cire? dan Allah kayi hakuri bari in sauka nabar ma aikin WALLAHi.

Modibbo ya daka mai tsawa "yace WALLAHI ka juyo saina makanta ka har a'bada, kashi gaba
da ai'kinka d'an banza,da wani É—uwawunka kaaua kasa kamar na kura, ubanmi yasa kake
ɗaure Dan ƙugunka? Saboda kai ga kwarto ko...

Bulama "yace Wallahi dokar ai'kice sai muntura rigunan mu cikin wando, munsanya belt É—in
nan mun ɗaure ƙugun mu...

Modibbo" yace to kwance dan ubanka tinda ba dokar Allah bace, maza kwance." da sauri
Bulama hannunshi na kyarma ya fara jawo rigarshi da mugun karfi,yama manta da sama yake,"
jikake rugugum Tsauni ya zame ya faÉ—o, wani irin ihu Modibbo ya saki daya jawo hankalin
duk wani wanda ke gidan, dan kuf towar da sukai shiya fara yo kasa Bulama ya biyo sh,i take
ya sume, dan suma ba tama Modibbo wahala.

Tare Ammar dasu Tsohuwa harda Moopy suka ƙaraso wajen da tsauri, suka iske Bulama
kwance ya rintse ido dan shi yatabbatar ma da shikenan tashi ta kare, Yafado busa katifar
Al'jannu," Ammar yayi kanshi yana f6adin innalillahi wa inna ilaihirraji un, faduwa kai ne? Ina
abokin aikin naka.?

Bulama yayi shuru dan yason yan uwan Ifritu ne ke mai tambaya .
Ammar ya k'araso wajenshi tare da dan marin kuncinshi amma Bulama bai motsa ba.

" Ammar ya lura kamar busa kafar mutum Bulama yake, yasa karfi ya turashi, tare da fadin kai
tashi ka dan ne a'bokin ai'kinka, ya sake tura Bulama da karfi,tare da kamo fuskar na K'asan.
Amnar ya zaro ido yana fadin Modibbo yaushe kazo nan ne?

Modibbo bai mason kasar da ya keba" aguje Ammar ya É—akko tiyo na ruwa ya kunna yafara
ma Modibbo da Bulama wanka, take Bulama ya mike tsaye yana rike kanshi yana fadin
Alhamdulillah yan agaji sunzo..

Modibbo jin ana mai wanka kota ina da ruwa ya fasa gigitacen ihu tare da fadin ai'shikena abun
yazo, gani tsirara ana man wanka
Gawa, Nashiga ukku ni Modibbo, yanzu a'haka za'atadani a'cikin Kabari, Malam Dan Barno,
yaceman duk abunda ka mutu kanayi dashi za'atadaka, gashi nazo ƙeta na mace, wayyo
Allah nah..

Jin yanata sambatu yasa Ammar dakamai tsawa tare da fadin wai miye haka,kake ma mutane
hauka, bazaka buÉ—e idon kaba?

Modibbo "yace taya zanbude idona bayan na zama Gawa.

Tsohuwa da tin É—azu tai tsaye batace komiba, ta karasa wajen butocin dake kusa na masu
gadi,ta dauko lamba ukku tana zuwa ta kwalama Modibbo busa kai,tare da faÉ—in ubanka!
kasa a'nata asarar man da ruwa..

Modibbo yayi Saurin bude idonshi tare da rufewa dan ruwa kawai ke shigarshi, Ammar nacen
na kallon Moopy dake duke har lokacin tana kuka, yama manta da Tiyo a'hannunshi yana
fesama Modibbo ruwa.

Da kyal Modibbo ya ruga gefe tare da faÉ—in Amma Amiru bakada mutunci, kamar kasamu
Gobara sai fesaman ruwa kake, jibi yanda cikina yakoma kamar kududufin garinmu, kayiman
tatil yau dole na inje asaman robar fitsari ko nasamu saukin bala' in nan na yawan Bawali...

Bulama dake gefe yana maida numfashi, yasamu da kyal yatashi zai tafi.
Tsohuwa "tace kai Huhulahu dama baka iya ai'kinba kahau Tsanin?

Bulama "yace aa ba haka bane Wallahi, na hau ban kula ba ashe ramin turwa na taka, shine nai
masu ɓanna suka jehoni..

Tsohuwa ta zaro ido tare da fadin kaji Kazubi Dan Kazzabu, ai'na nike da Turwa iye? Dan
Yarinya?ina naga Turwa? agidan nawa?

Bulama zai magana modibbo yace"
Nine nan na jefo shege, É—azu ba makaryace yaceman ba gaban ki.

Ammar yayi tsaki tare da cema Moopy muje anyi Sallah..

Tsohuwa "tace ma Modibbo ai'ko gayanan ka gane kai Azzalimine, dan gabaki É—ayan fuskar
ka ta wulakance ta koma kamar ta kurciya Wallahi, dama ai'ni nason da walaki goro a'miya,
kai-kai Modibbo kana ban wahala Wallahi shege gashi ka'ki tafiya sai kace d'ana, kullum fama
nike dakai..
Tinda Tsohuwa tafara magana Modibbo ke kallonta yana kallon sama, dariya ta kufce mai
yafara nuna Tsohuwa yana nuna sama..
Tsohuwar ta kai kallon ta saman dayake nuna wa bata ga komiba sai Yar Moli-Moli
Tsohuwa" tace kai dan ubanka mikake gani wanda mu bama gani?

Modibbo yakara kwashewa da dariya "yace Wallahi kanki nike gani kamar na namijin Moli-Moli
cen ,ashe haka kike in'baki da d'an kwali hahahahahah...

Tsohuwa ta zaro ido tare da nuna kanta, tasaki kuka tajuyo taima Ammar magana taga wayam
babushi babu Moopy, take ta manta da maganr Modibbo ta watsa da gudu waje danta ga ko fita
sukai, tana buÉ—e get Basho ya kunno kai yana faÉ—in wannan wane uryin iskanci ne,kunbar
mutane nata buga gida.
Tsohuwa "tace ubanka, wayaji ka matsa kaban waje da cikinka kamar tukunyar rodi,nace kaga
wasu sun fita..?


Basho "yace ina fa wani yafita da tini banshigoba, ai wallahi baccin yan canji nnan da tini
nakama gabana.

Tsohuwa batace komiba ta koma
Palo, taga Moopy harta sallame sallayh tana ta kwararo Addu'oi hannunta sama idonta na
zubda hawaye

Tsohuwa ta sauke ajiyar zuciya tare da fad'awa toilet tai wanka dan jikinta tsami yakemata, tana
fitowa tasa rigarta ta dauki hijjob tai Sallah.

Acen wajekam Bulama naganin shigarsu yatashi ya shake modibbo yamai Dan banzan
duka,kana ya sakeshi.

Basho yakaraso wajen zai fara fada Bulama yafadamai komi Basho yace kayi dai-dai.

Nan suka hada abunda zasu hada cikin sauri sukabar gidan, sukabar Modibbo zube kamar

kayan wanki kasa yana kuka.


Bayan sungama sallah Ammar yashigo palon tare da robar ice cream yaba Moopy ta karɓa
tamai godiya tare da bude ledar tafarasha shima yasha nashi


Tsohuwa ta fito wajen tare dafadin duk mungama ci gaba..

Moopy ta rife robar da bata wani sha sosai ba ta fara daga inda ta tsaya.

Faduwar da Baba yayi taj awomai matsala babba dan take dukkan sashen jikinshi ya mutu.
Bakinshima ya jirkice haka naita kuka ina salati ganin yanda mahaifina abin sona yadawo
lokaci guda, shikanshi Baba yanataso yaman magana Amma ina halsheshi yakare saidai
hawaye yay tayi .

Na É—auki wayata nakira Imran cikin kuka na shedamai halin da ake ciki.
Bai wani jimaba yazo shima iya rudewa ya rude, yasanya duka karfin shi zai É—auki Baba
amma Baba yayi nawie sosai na ban mamaki, nakama kafar baoba yakama hannun haka muka
fita dashi waje muka sanyashi motar Imran muka nifi Asibiti, muna zuwa a'kafito da gadon
marasa lafiya aka É—ora Baba aka shiga dashi É—akin da za abashi taimakwon gaggawa,
sunjima sosai cikin É—akin kana likitocin suka fito, É—aya yace ma Imran É—anshi ne kai..
Imran yace eh muduka yay'an shine.

Likitan yace ku biyoni office yayi gaba.

Haka muka bishi inata kuka Imran na rarrashina
Muka shiga muka zauna, munajiran muji abunda zaice..

likitan yashare gumin dake tsattsafowa daga fuskarshi ya kallemu tare da fadin kunson ita
kaddara ba a'tayanda bata zuwa, kuma duk wanda yayi Hakuri sai Allah ya masanya ma da
Al'khairi, gaskiya Mahaifinku nada matsala dama ta Hawan jini, dan jinin shi ya hau sosai
mafarin faÉ—uwar da yayi ta zomai da tsosai, a'yanzu haka maganar da nike maku gaskiya
yasamu matsalar shanyewar ɓarin jiki, amma zamu barshi yaɗauki kwana biyu muna kula
dashi zuwa sati biyu, zamu dan faramai gashin kashi mugani.
Sosai nike kuka jin abunda yasamu Mahaifina,naita tinowa da ko É—azu zaune muke muna fira
cikin jirgi, da ƙafarshi ya sakko da kafarshi yashiga gidanshi amma cikin awa biyu sai gashi
tsautsayi ya af'kamai, Allah kenan mai yanda yaso aduk sadda yaso.

Imran yamai godiya tare da biyan duk a'binda aka kashe, ya bukaci yanason amaida Baba
Aminity dan matarshi tai jinyarshi hankali kwance..

Likitan "yace ba damuwa indai zaku iya biya.

Imran yace ba matsala washe gari aka maida Baba Aminity inda na koma giufa na faÉ—ama
Ammi abunda yafaru,ita kanta tasha jinin jikinta taceman bakomi zataje an'jima, da yamma ta
shirya tare da kwasar kayanta tantafi asibitin ta kwana, da safe bata tsaya komi ba ta dawo gida
nakoma cen na yini Ammi tazo ta kwana haka nike zaman jinyarshi, Baba baya iya komi sai
an'mai ko wata bukata zaiyyi anan yakeyinta sai nadawo gida nafadama Ammi akan Baba yayifi
fitsari ko kashi. bataceman komi zata tashi ta tafi ta gyrashi tai dawowar ta
Har saida muka samu sati biyu Imran da Alhajin shi keta hidima da Baba, an'mai gashin kashi
saidai muce Alhamdulillah, bad'an laifi Ammi tazo ta daina kwana dan tace zata fita ta dinga
nemo na abincin dazataci ita da É—anta, bazata zauna waje dayaba dan tsautsayi ne.

Aranar da akabamu sallama Imran ya mai domu gida nai ma Baba shimfid'a É—akinshi aka
kwantar dashi,
Na biyo Imran na mai godiya" yaceman ba komi yiwa kaine sai munyi waya.

Ina shigowa gida Ammi tayi man wata shakar wulakanci tare da cewa ta sake ganina da
wannan kwarton yaron saita kasheni ,nacemata ba kwarto bane wallahi taimakona yake, taja
kunne na tare da fadin" kin daiji na fadamaki in kika kara bani bake "nace mata to "

Bayan sati biyu abubuwa sun damu rayuwata na farko dai amymi ta kori Imran dan dakanta
tafita ta wulakantashi, yaman waya tare da fadin inyi hakuri in'kula da Baba zaibar zuwa .nasha
kuka na nagode Allah tare da fadin yanzu Imran wazai dinga kaishi Asibitin duk sati?

Imran yace Insha Allah zata sassaf ko, zandinga kashi ko wasu su Fiddoshi sai in'kaishi .
Haka mukaita rayuwa yau da dadi gobe a'kasin haka, har wata rana muna waya da Imran na
nunamai gaskiya gidana zan koma da zama, dan Ammi tana matsaman kuma inaso in koyi
mota tinda ina da ita..

Imran ya goyi bayana da daddare ammyi ta tafi yawonta Imran yazo yatayani kwasar Baba,
nima na had'a kayana nakwashe komi nawa harda keku nan É—unkuna na, na É—orama
a'daidaita sahu sukabi bayanmu har goruba, nayiwa Baba shimfida É—akin kasa, Imran ya
ajeshi muka zauna muka fara magana nidashi akan inaso in iya mota gaskiya, kuma inaso in
samu wanda zai dinga kulaman da mahaifina tsakani da allauh zan biyashi kudi...

Imran yace ba matsala zai ma Daddy shi magana.

Washe gari saiga Daddy Imran dawani babban mutum sukazo suka duba Baba'na suka
kawomana kayan bukata, Daddy ya yaba da shawarata tare daceman shima zai dinga zuwa
akai-akai, ga wannan Baba labbo kanan mai gadin sune- zai dinga zuwa yana jinyashi,nikuma
zai sanya akawoman Tsohuwa acikin masu aikin gidanshi muna zama da ita, nai mai godiya
suka tafi a'kabarni nida Imran da wannan mutumin ,dayashiga É—akin Baba yagyara mai
jikinshi yacanzamai kaya yafita da nashi ya wanke.

Baba nada wata biyu nakware da iya mota har lokacin bankara waiwayar su Ammi ba,dan
d'unkuna na kawai nike inata tara kudina, wani lokacin kuma inje Studio inyi wakata in dawo
dan lokacin nakware sosai banda burin daya wuce in Tara kuÉ—i mai yawa in fidda Baba'na
ƙasar waje.
Baba nada wata biyar cur da fara jinya, ina zaune da Inna
Asibi Dake tayamu zama taceman kamar fa tari Babanki keyi. Da gudu Nashiga É—akin zaro
ido nayi ganin Baba ya...🥴��
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘����💘��💘��💘
ZAMAN TASHA
��💘��💘��💘��💘
NA UMMY AYSHA
💘��💘��💘��💘💘

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login