Showing 3001 words to 6000 words out of 54969 words

Chapter 2 - ZAMAN TASHA COMPLETE BY UMMY AYSHA.pdf

10 Jul 2025

3384


Bakinciki, yasanya IRFAN dauke Ado da'wani mahaukacin marin, dayasanya Ado, watsawa da
gudu bala'i cikin motar, dayakawo, tare dajan motar aguje, yayi gaba, dan duk daukarshi
mahaukacine yagamu dashi.

IRFAN baison sadda yawatsa, da'gudu ba yana kiran Ado, amma ina Ado ya gigice yayi gaba,
dole tasasu tsayawa suna nishi.

Driver yakara daukar wayarshi dan yakira Ado yana kira saijin wayar yayi kusa da kafarshi,
alamun tsoro yasashi barinta. cikin bacin rai yace yallabai, bamu da wani solution yanzu, abu
daya yarage shine muhau kurkura mutafi gida, dan wanda muke sanya ran zai taimakamana,

yazama mahaukaci, cikin yan mintina.
dan,haka muhau kawae mutafi, yafi tsayuwar, nan damuke mutane duk sunzuba mamu ido
suna kallonmu tin dazu.

Wata r'azananniyar tsawa IRFAN yadakamai, tare dafadin Allah yakiyaye hawan keke napep nii
IRFAN, bazan taba hawan wancen matsiyacin abun, da duk dattin duwawun talakawane akaiba,
badaini IRFAN ba. yafada yana zaro zabgegiyar wayarshi tare da lallatsawa, yakara akunne,
yadan jima kana naji cikin daddadan muryarshi dayakasance mai sauri saurin magana yafara
magana yana fadin Ammar kana ina ?yafada yanasanya wayar speaker dan inya kaita akunne
zata iya baci da dattin fuskarshi, daga cen bangaran Ammar yace "Maza" inanan cikin gari nazo
gaida tsohuwa kuma na iske batanan tayi tafiya.


IRFAN yace kakaraso kadaukeni, ina nan, cikin gari amma bansan sunan unguwarba, ga bala
zai fadama.

Daga inda yake bala yakai bakinshi dan babban kuskuran dazayayi arayuwarshi yatabama
IRFAN abunshi yace muna kofar guga wajen TASHA jibiya.


Basu dade, tsayeba saiga motar Ammar tayi parking dai dai wajen motarsu, yafiddo waya
zaikira IRFAN kenan yaji an bude site din mai zaman banza anzauna.

Cike da bala'i Ammar yajuyo zai magana idonshi yasauka akan fuskar abokinshi datasha penti
cikin yatsina fuska yace kai lfy kuwa "Maza" kaji warin kwatamin dakake kuwa?

IRFAN yazubamai jajayen idanuwanshi, tare dafadin kakaini gida nace.


Ammar yace wlh dama ka koma gidan baya, tsakanina da Allah tsami kake haba, dan bala'i
danka kwasa kowama saiya kwasa waima tsaya faduwa kai ko-ko?


Karaf cikin kunnan driver,jikinshi har rawa yake yace wata yar budurwace tawatsamamu,
kwatamincen! na bakin tasha, wlh nima kaga fuskata yafada yana nuna fuskarshi datakoma
wata kala dan duk kwatamin, yabushe ajikinta saiti secuising.

Ammar yasaki wata mahaukaciyar dariya, tare da fadin mace? macace taima Maza haka ?kuttt
dan Allah tana inah?

Bala driver yace wlh yallabai yar ZAMAN TASHA ce bamuson inda takeba yanzu, da alama
mota takeja dan lodi akamata tazo taimana wanna iskancin .

Dariya kawae Ammar yake, tare da tada motar yace kasamu mai gyara saiku dawo da
wannan.driver yace toshikenan.

Suna tafiya Ammar yacema "IRFAN" Maza ya akai hakan tafaru? mikayimata? Indutsi
na,magana to IRFAN ma yatanka. haka sukatafi bawanda yasake magana .sun nufi hanyar
le-out adakile IRFAN yace kaini gidana na goroba road.Ammar yakarya kwana tare da nufar
hanyar dazata sadasu, da goruba roud, cikin yam mintina suka iso. suna isowa suka fara
kokarin shiga get din gidan IRFAN opposite dagidan aka bude get wata mota tasheko da gudu,
da baya baya jikake kwassss ta daki bayan motarsu IRFAN, atsorace sukajuya amma ga
mamakinsu mai motar ko tsayawa baiba afusace IRFAN yacema Ammar dawo nan, cikin sauri
Ammar yafita daga motar baki daya ma, daga inda IRFAN yake yafada mazaunin driver yayima
motar key tare dabin bayan motar data bige tasu da gudun bala'i sosai suke gudu da motoci
harsuka kawo titin dazai kaika kwado, mammalakin motar daya daki tasu IRFAN taleko dakanta
tare da dagama IRFAN yatsu biyu alamun suci gaba.
Wani irin zaro idanuwa waje irfayn yayi ganin fuskar wadda taleko ta glass din motar yace jar
ubaaa dama....🖊�
25/03/2022, 22:11 - Khadeejaht Salisu Fari: ��💘��💘��💘��💘
ZAMAN TASHA
��💘��💘��💘��💘
Ummy aysha
💘��💘��💘��💘��
🅿�7�⃣&8�⃣


Dama macace tasashi, wannan mahaukacin gudun, aiko sai yaci ubanta, dagudu ya murza
motar dandanan saigaya yacimmata, lokaci daya motorsu suka jera, yasauke glass dinshi, tare
da fadin mahaukaciyar, inaceke wawiya, dabakison aikinkiba zakima mutane 'banna, bazaki
tsaya kibamu hkr ba banza kawae, mahaukacin babanki yabaki mota sai iskanci kike cikin gari
ko?

Afusace taja wani mahaukacin burki jin zagin dayayima mahaifinta, shima yasamu wuri yayi
parking sanye take da atamfa brown mai kwalliyar milk tasanya jikka da takalma milk cikin wata
tafiya dake cike da kasaita wadda sai mace takai takawo, takeyinta cike da natsuwa, takaraso
wajenshi, tare da bude sit din mai zaman banza, taimai kallon ido cikin ido tare dashekewa da
dariya tace au kaine dama? tafada tama nunashi da yatsanta tace bantaba ganin wawan
mutum kazami kamarkaba, kasan aikin danayi acikin awanni ukku dasuka wuce, lallai kacika
babban wawa kazami yanzu haka kake fama da kwatami afuskarka? har yanzu bakasamu
ruwan wankewaba kazami kawae, "Dan karya" baka da ko sisi sai burgar banza mtsss kacika
mota da tsami, ahaka zaka zageni to kaje gidan tsohuwa taima wanka watakil warin jikinka cikin
kashi goma kasamu ukku yafita, tayi tsaki tare da neman fita daga motar.

Cikin tsananin fushi da zallar bacin rai ya fizgota, tare da dankwafar da ita daga sit din datake
kwokarin mikewa, tinda tafara magana zuciyarshi kemai zafi akaro na biyu, takeso taci bulus

kenan,yadaga hannu tare dason dauketa da mari. kamar wasa yaji ancabke hannushi, taware
tafin hannunta, tare da fiddomai duka idanuwanta waje tace kull, karka kuskura wannan
kazamin hannun naka dabai da tsarki yasauka akan kamilalla fuskata, inba hakaba awajennan
wlh zanma kyawawan maruka guda biyar cur, kuma ba shegen daya isa ya hanani dan ninan
dakake gani cikakkiyar yar ZAMAN TASHA ce, wlh tafada tama yarfe hannushi daga nata cikin
sauri yasaki wata yar siririyar kara dan bisa giyar motar tabugamai hannunshi kamin yayi
magana tafita daga motar tare da leko da kanta tace sanholon namiji kawae raggo.

Cikin isa tafara tako d'ai d'ai!! ba tsoro ba shakka take tafiya cike da natsuwa, tashika shagwon
Shaban Super Market dake kusa da inda suke ta amso ruwan roba guda, da ledar omo guda,
tajuye gabaki dayan omon hannunta tare da kiran wani yaro, dake bakin shagon tace zuboman
ruwannan, yaron yakarba yana zubamata tana gamawa tazaro dubu biyu tabashi tare da yarfe
hannuwanta tafara shinshinawa ,saikuma tayamutsa fuska tare dafara tafiya, cike da natsuwa
tafada motarta tafigeta aguje tana tafiya sosai takejinta cikin nishadi, karansu na biyu ita da
"DAN KARYA" acewarta.


Bakin cikin dabaida misali, baida farko baida karshe, wulakancin datinda yake, ba a'tabayimaiba
yau daya yarinya karama tabata, duk wani farinciki da walwalarshi ta yau, afusace yace wlh wlh
karonmu dake na ukku bazaimaki dadiba, daga yau zamu sanya kafar wando daya dake, saina
yagaki, nayaga duk abunda kike takamadashi, alkawarinane saina binciko koke wacece, daga
baya zan wulakantaki, in watsaki, a idon duniya, banza mai fuska biyu. yafada afusace yana
juya kan motarshi yakoma goruba road, Yana zuwa ya iske Ammar tsaye yana waya, sai
zagaye yake kai dagani wayar namai dadi, aguje IRFAN yayo kanshi cikin wani mahaukacin
tsalle Ammar yakoma gefe tare da cewa tsohuwa zankiraki anjima yadatse wayar .

IRFAN yafito afusace ko rufe motar baiba yafara buga get din gidan da mugun karfi, da sauri
maigadinshi yadakko baka yace aiko yau zanci uwar masu kama tsintsayen yallabai, wlh saina
sakarmasu baka ga idanuwa inyaso infara haukan karya daganan inyi kauye, cikin sand'a
yabude kyauren tare da labewa yana ganin ansanyo kafa daya, baima kula da kowayeba
yasakarma IRFAN wani wawan duka adaidai saitin kirjinshi. wata uwar kara IRFAN yasanya
tare da dukewa kasa yana laluben kirjinshi, take idanuwanshi suka koma jajawur dan sosai yaji
naushin da akakaimai, cikin dariya mai gadi yafara kokarin rife kofa, batare daya juyoba yace
kowane shegene yau yaji tafin maza, yajuyo dan duk tinanishi wanda yabuga yaruga mizaigani
maigidanshine duke, kasa tare da rike kirjinshi idanshi yakoma kamar wuta da sauri maigadi
yace innalillahi mai gida waya tulloka tasama munshiga bakwae.

IRFAN yatashi tare da yo wajen dayake,ganin haka yasanya mai gadi faraja baya tare dafadin
haba mai gida katsaya mana, yakake yo wajena?IRFAN yaci gaba dabinshi harsuka jingine da
get, yashake mai gadi tare dafadin ubami naima kaiman wannan dukan? mai gadi dayaji bala i
yace wlh nasanya buzun cen gidanne, cikin maseefa IRFAN yace butar shayine ba buzu ba, kai
wlh kana bakauye jayili dan kauye baka isa karainaman wayoba, sakarai kawae, yafada yana
kwala keyar mai gadi da get,afusace yafada cikin gidan tare da sanya key yabude palon kai

palon yahadu kaidagani kasan bawai palon yakubayi bane dan komi yaji cikin sauri sauri yafara
taka matattakalar dazata sadashi dasaman benen dakin, ashe kallo na sama ba kasaba,palon
yahadu iya haduwa yana shiga yafada toilet yafara dirzar jikinshi duk inya tafa fuskarshi saiyaji
kamar bata fitaba, sosai yake wanka maganganu datayimai nadawomai fes akanshi, saida yayi
wanka goma kana yafito yana fitowa yyi saurin shiryawa yagabatar da Sallah, tare da dannan
number bala driver, bala na dauka IRFAN yace ka bincikoman asalin yarinyarnan dako wacece
ita nan da sati biyu zan baka million daya.

Jin abunda yace yasa bala cewa angama yallabai bazanma kaiba wlh, yafada cikin zumudi
IRFAN yadatse wayar tare da sakkowa kasa anan ya iske Ammar nata kallonshi hankali
kwance, IRFAN yazauna kusa dashi tare da fadin nifa yunwa nikeji wlh muje muci abinci gidan
tsohuwa mana, Allah yasanya tayi abunnan .
Ammar yadaure fuska tare da kauda kanshi gefe, yace karka sakeman magana tinda kai inkayi
fushi baka iya control din kanka, jibifa dazu daka bugeni abanza, naitajin ihun mai gadi ashe
kashi kabashi dayamaka mi?
IRFAN yace kai share kawae kaji tashi muje gidanta insata yiman dan wakenan. Ammar yace
audaxu da inagayama daga gidanta nike batanan bakajiba kenan?

To batanan taje gidan kawu balele..🖊�
25/03/2022, 22:12 - Khadeejaht Salisu Fari: ��💘��💘��💘��💘
ZAMAN TASHA
��💘��💘💘💘��💘
UMMY AYSHA
��💘��💘��💘��💘
🅿�9�⃣&1�⃣0�⃣


FREE NOVEL


Cikin mamaki yace wlh tsohuwa tayi nema ma kanta masifa,amma ba laifinta bane laifin driver
daya kaitane,sai naci ubanshi yanzu ko wlh tinda nafadamai duk inzata fita yatabbatar
yafadaman.

Ammar yace aiko daka dauki alhakinshi dan shima yana bacci tabude gidan tafita, saida ta isa
kana takirashi tana dariya wai ansashi tsaranta tamai wayo taitafiyarta, ina dalili a ajemata bakin
driver kullum fuskarshi na maiko kamar sabon quli,bazata kara yarda yafita da itaba.

Irfan yace aikaji matsalata iyayi, ina ruwanta da ba'kinshi? Allah yakyauta ai danta ziddamana
da mutuncine, amma jibi zanshiga wasa CHAMA
PARK dole inbiya indawo da ita, dan banson wazai dingaman girkiba kamin taga dama dawowa.

Ammar yace duk dai zafin kanka kasan tsohuwa tadameka ta shanye wlh, inkuma kace
zakaimata fin karfi kasanta sarai, har kwara kabi da ita ta lalama sai kasamu abunda kakeso
cikin kwanciyar hankali.


"Irfan'yace kai kyaleta kaji tashi muje gida.


Washe gari tinda safe yar Cara's" tadauki wanka na mutunci cikin dakeken lace dinta read and
black, komi najikinta yakasance black tindaga takalminta harzuwa glass din idonta, cike da
yanga ta dakko key din black din motarta kirar benz tayi mata key tare da fita daga gidan,
kamar jiya hanyar kwaÉ—o tabi Saida tayi tafiya mai tsayi ta parker daidai wani makeken get,
daga samanshi ansamai suna MOOPY STUDIO& ZOO PARK tadanna hon, cikin sauri wani
buzun mutum ya leko ta karama ƙofa, ganin motar uwar ɗakin shine yasashi komawa da
sauri tare da wangalemata get din Baki daya,

"Yar Cara's tadanna hancin motarta cikin yalwataccen wurin daya gaji da haduwa tayi parking
wajen da akayi dan adana motoci,tare da zuro fararan ƙafafuwan ta da suke cikin Black din
takalma dasuka sake fiddo asalin kyan fatar kafarta,ahankali takwaso takaddunta dake sit din
Mai zaman banza tare da jikkata tafito,cikin fara'a dabantaba ganinta afuskartaba takaraso
wajen mai gadi tare da duƙawa har ƙasa tace baba habu Ina wuni, ya aiki fatan kana lfy.

Cikin fara'a baba habu yace Alhamdulillah É—iyata yagida ya rayuwa ina É—an uwana
Haruna?

Tasadda kanta ƙasa tare dafadin baba Alhamdulillah yana nan lfy Lau shima, yanacen yana
dafa shiyi kamar kai, tafada tana nuna butar shayin dake kan garwashi sai tafasa yake ga
kamshi sai tashi yake.yace ai É—iyata mu buzaye bamayi Saida shayi, Zaki zagane wajen
dabbobin ko Sai anjima? dan sosai ansamu ƙaruwar abubuwa Hajiya ko yau na fidda
ƙwai yakai dari biyu a'wajen kaji nan, kifaye kam mu bada kwali biyar gidan ALH KHABIR
HAIFAN kudin na wajen Alh Fahad.

Tace Masha Allah baba haka akeso Allah yataimaka, amma yau bazan zagaba dan badewa
zanba zanje TASHA.

Cikin tausaya mata yarinya da rufin asirin ta amma hatsabibiyar uwarta tamaidata yar ZAMAN
TASHA, ina amfani wasu iyayen dake amfani da girman matsayin da Allah yabasu su
ƙuntatama yaransu.

Tace bakomi baba bara inshiga ciki,saina fito insha Allah.

Tana shiga saiga Alh Fahad Yana fadin sannu dazuwa haj MOOPY.
Tace yawwa yallabai. bayan sungaisa ta turamai taƙaddun gabanta tare dafadin wannan

wakar Nike bukataryi anjima in Allah yamaidoni lfy, so Aman clearing din komi asaita kiÉ—an
dazai hau da ita, inyaso danazo zamuyi muwuce wurin,abu na biyu kuma akwae bikin gidan
HON.HASHIM YARIMA zamuyi wasa a'wajen da Aliyu nata.

Fahad yace angama gimbiya MOOPY mai maƙwogaran zinari.

Tayi dariya tare dafadin zan wuce sai nadawo.
Fahad yace Allah yakiyaye ya tsare hanya ga wannan dubu É—ari ne mun bada kwali biyar na
kifaye.

Tace bamatsala ka ajesu wajenka kadauki 30k kaba baba 20k ka ajeman 50k sosai yamata gdy
dafatan alkhairi dan duk wanda ke ƙasa MOOPY yasan bata da baƙin ciki abunta na
kowane.


Tana fitowa zata fita saiga baba da gudunshi, yayi mata manyan lodoji da kayan lambu sai
ƙwai dasu kaji da yayi saurin gyarawa yace haj kema kitafi da wannan gida ko?

Tace to baba ngd Allah yasaka da alkhairi.
Yace ameen haj.hadda gdy keda abunki amma bakya É—iba saidai anbaki.

Tace haba baba dan yana nawa saikuma inta fadin adibarman, Ni banima da lokacin dafasu
amma zansamu mai aiki insha Allah, tai Mai sallama ta wuce.


Bata zame ko inaba sai unguwar tudun-wada, inda ta aje motarta kamar jiya kasan bishiyar
bedi, Takifi kanta da sitiyarin motar, tare da fadin ya rabbi kajiyar Dani alkhairi, Allah kakaraman
juriya akan abinda zantaras a gidan nan.

Takira wani yaro da yazo wucewa tace dan Allah daukar man kayayyakin nan kashiga dasu
gidan cen, tanunamai gidansu da hannu.

Yaran yadauka itama ta rufe motar tare da daukar wasu ledoji tabishi suka shiga tare.

Suna zuwa gidan ammi nazaune gaban murhu tana hura wuta da bakinta, idanuwanta sunyi
jajir ga uban hayaƙi ya turnike gidan.

Da sauri tazaro dari biyar tacema yaron karba ngd jeka, ya aje tare da amsa yayi gdy yafita.

Yana fita da sauri Yar Cara's takarasa wajenta tare da fadin ammi kawo in huramaki wutar.

Cikin daka tsawa ammi tace kauce daga nan dan uban ki, da wannan tanba daddan baƙin,
zaki huraman wuta? so kike takara macewa kenan? wuce kiban wuri kije kisamo man kudin

halas inma yarana sanwa nafadamaki.

Cikin kuka Yar Cara's tace wlh ammi kudina na halal ne ,narokeki da Allah kibani dama inmaki
bayanin dazai gamsar dakei,wlh ammi rayuwata bataman daÉ—i duk uwa da tausayi É—anta
aka santa,kibani dama Ammi indauki nawinku dana ƙannena ta hanyar amfani da abinda
Allah yabani bawai sai nayi ZAMAN TASHA ba.
Ammi taimata wani kallon banza tare da furta kikasakeman magana saina tsinemaki wlh.

Jin abinda tace yasanya Yar Cara's yin gum da bakinta, tare dafadin Ammi kiyi hkr ga wannan
tafaÉ—a tana nunamata ledojin data zodasu.


Cike da isa ammi tazo tabude ledojin tare da warware dukkaninsu ta bude kwalin da kifi keciki,
nan take yawunta yatsinke tadago idon ta tare dafadin yaukuma tanan kika biyo?

To bazan taba cin abinda ya fito daga hannunkiba, saboda bansaniba ko da jinina za'kiman
abinda zanci, maza wuce TASHA kinemoman na halak ga L.B najiranki.


Cikin kuka jin furucin da mahaifiyarta kemata tashiga wani tsohon É—akin su tare da neman
kayanta nada, tadauka wata atamfa tasanya tare da karamar hijjob tafito zata wuce.

Ammi tace ubanwa zakibarma kayan nan ?maza kwashesu kitafi dasu kamin intsinemaki.

Da sauri tafara kwasar kayan tana zuwa zata fita ƙofa, ƙannanta suna ƙoƙarin
shigowa Amina tace adda inazaki?

Cikin kuka tace nakawomaku kayan marmari da kaji dasu kifi, Ammi tace intafi dasu. da sauri
Aminu yabuda ledar tare tare da kwasar kaji sosai yace wlh bazaki koma dasuba, haka kawai
kwana mu nawa bamu ciba,sabo da bakin halin Ammi tahanamu amsa, basaimamu kuma
zataiba, itama tanaso,mu bamu ita kartaci, yafaÉ—a yana daukar kaza ukku da kayan marmari.
cikin raÉ—a yace mata dan Allah ban dubu daya in kai agasaman bakin hanya, cikin sauri tabar
kofar gidan tare dafaÉ—in muje mota inbaku kuÉ—in.sukabita mota tabasu,dubu É—ai É—ai
tare da karama su da kifi mai yawa takaramasu kayan marmari, dagudu suka karya kwana
itakuma ta adana kayanta data cire cikin mota tare dasanya ledojinta bayan but tazauna tana
tinanin komawarta gida kai kayan duk cikin cin lokacine, tana wannan tinani wata mata tataho
ajigaca da tsohon ciki tana waya tare dafadin wlh since banima da jini ajikina nidai kawae zan
hakura in Allah yatadani Alhamdulillah inkuma yadauki Raina Allah yasanya mucika da imani
takarashe cikin hawaye.

Da sauri Yar Cara's tabude motarta tafito tare da isowa wajen matar nan tacemata baiwar Allah
kibar kuka kowace ƙaddara da Allah zai jarabci bawa shi yayi hkr wata rana sai lbr.

Matar tace hakane kawata kinganni cikine dani na farine, Muna zaune cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login