Showing 24001 words to 27000 words out of 54969 words
kaini yanzu ina gane hanya.
Haka na tafi ina waiwayen Inna da har lokacin take tsaye tana É—a gaman hannu.
Bayan nashiga get din makarantarmu nasamu kowa yashiga aji nima a'guje nayi ajinmu
nazauna .
Ina zama gari ya ƙara ɗin kewa yazamana kamar duhun mangari ba, anan kawata Sadiya
dake kusa dani tace "mufeeda bukar dama munzo da fitila ji yan da gari ya yi, haka taya
zamuga abunda a'karubuta mana.
Ni dai bance matankomiba haka nan naji gabana na'bugawa da mugun ƙarfi!! haka nai zau
ne gari nata sake rinewa zuwa cen a'kafara wasu irin kwala-kwalan yay'yafi, kankace mi ruwa
ya kaule kamar da bakin kwarya, sosai ake zuk'a ruwa da tsawa mai karfi, sosai hankalina ya
tashi Inna kawai nike tinani!" ina tinanin tanacen ita kad'ai dama Ammi wata ce dasaitashiga ta
ta yata zama, Amma nason bazata iyaba, tanacen wajen talla rta dan yan zu tabar tallar fura
saita gwanjo.
Haka naita tinani ga babu malam ko guda acikin ajin, hakanan Inna ta hanani kwanciya ta gida,
gashi nason kaka na masallaci yan zu, dan in yafita karfe goma baya dawowa sai bayan la'asar.
A'takaice ruwa bai daukeba sai kusan a'zahar, suka dan É—auke suma ba duka ba ana
yay-yafi, a'dai-dai lokacin da bugun kirjina ya yawaita bantsaya komiba kawai na hau taga na
dire, sadiya na tambaya ta ina zani?" ko kallonta ban ba fatana in isa ga Inna ta da bani da
kamarta" haka naita tafiya gaba na na tsananta bugawa har na iso wajen get, anan mai gadin
mu ya taso yana faÉ—in ina za ki? ko kallon shi ban ba nabi ta karamar kofa na fara tafiya ta
cikin sauri-sauri har na fara hango kofar shagon baba na, na ganshi a'bude cikin sas'sarfa hade
da gudu-gudu na karasa shagon. Baba na zau ne ya É—aga kanshi sama na fado shagon!!
a'razane ya kalleni tare da fadin Moopy ya dai?miya faru? lfy naganki yanzu ko antashi ?
Nace aa baba Inna nikeson in'gani.
Baba yazaro wayarshi yaga a'shema12:34 ko 1 bata ida ba! yace Moopy gudowa kikai?
Nace eh Baba ba a'yimana komi ba.
Baba yace shikenan .
Nace Baba wallah nan ina fad'uwa yake!! na nunamai kirjina..
Baba yace saikita maimaita Innalillahi wa inna ilaihirraji un, dan nima nawa haka yakeyiman tin
É—a'zu ".
Nace bari inshige gida .
Baba yace bari in rufe shagon in biki, dan nima duk yau ban shi gaba, haka ya rufe muka shiga
soron gidanmu tare mukai sallama shuru!! sai da muka karasa tsakar gida anan naga Ammi
nata wanke kayan gwanjo ta, da a'lama ɓaci sukai. "ko am'samana batai ba wannan bai hanani
duka wa nace Ammi ina wuni ba. Ta É—ago a'fusace tare da dungureman kai tace matsa cen yal banza dawata shegiyar
muryarki kamar an sakamaki radio cikin makwoshi, haka kawai kika sheman dodon kunne."..
Baba yaja hannu na muka fada É—akin Inna tare da sallama mukaji shuru!! muka yaye labulen
É—akin muka fada...
Atare nida Baba na muka saki wani mahaukacin ihun daya janyo hankalin Ammi tayo É—akin
a'guje .
Gabaki dayan ban'gwon É—akin Inna ya faÉ—i kana kallon bayan gidan mu, kasar baki daya
ta ruf'zo har kan gadon Inna ta.
Cikin kuka nafara kiran Inna-Inna!! tare da rugawa waje na bude toilet dinmu ba Inna babu
a'lamunta,na dawo É—akin ina kuka, banson sadda na haye gadon ba, anan naci karo da
hannun Inna nasaki kuka tare da faÉ—in baba ga Inna ta nan, dan Allah Baba a'É—agoman
Inna dan Allah karta mutu tabar ni, bani da kowa sai Inna ta, Inna dan Allah kitashi in kintafi
nima zan biki, sada nace kibar ni mukwanta tare kika ki yarda.."
Baba da yake kuka shida Ammi suka hayo gadon, da sauri sakafara ƙoƙarin jawo kasar
amma ina ta yiwa Inna runfa, aguje na fita waje nafara ihu ina ne man É—auki,yan tsirarun
mutane da basufi ukku ba suka biyoni mukashigo har dakyar suka dinga zaro kasar har Allah
yabasu sa'a suka zaro Inna da jikinta ya yi kaca_kaca da jini, aguje nayi kanta ina kiran sunan
ta tare da neman ta tashi tafadaman miya faru.
Wani acikinsune naji yana fadin sai hakuri da a'lama ya daÉ—e da dan neta dan gaskiya Allah
ya amshi a'bunshi."
Jin furucin bawan Allah nan yasani yan ke jiki na'fad'i!!daga nan ban sake sanin a'bunda ya
faruba sai ranar da Inna tacika kwana shidda da rasuwa!
Agigi ce natashi ina kiran Inna! inna!! wai kinji nayi mafalki kin rasu Inna fito inganki dan Allah,
nafad'a jikina na rawa..
Kaka na dake gefe zau ne da casbaha da baba suka yo kaina suna kallona kowannansu idon
shi cike da hawaye.
Baba yakama hannunan yarike yace "uwata a islamiya nason ansha fad'amaku illar yiwa
mamaci kuka ko ba haka ba? sannan nason an'fadamaku kudunka hak'uri da k'addara mai kyau
ko akasin haka ko ba haka ba?.
Dan haka "Inna Allah yakarb'i ranta ba muda yan da zamuyi sai dai abu d'aya data ke bukata
anan shine mubita da addu'a, dan wata rana muma haka za a'wayi gari ba bumu a'doron duniya
kinji ko uwata?
Nafashe da kuka nace ma Baba to yanzu wazai dingaman kwalliya yana saman kaya baba?.
Baba yabud'e baki zai magana Ammi tafi to daga É—akinta ta duka ta gaida kaka tare da gaida
baba na" abunda bata tabayi ba tin bayan mutuwar auransu.
Baba ya amsa cikin mamaki.
Ammi cikin sanyin murya ta fara bama Baba hak'uri akan a'bunda yafaru kwanaki, tare dasa ke
masu ta a'ziyya tace a'shirye take data rike Moopy a'yanzu.
Bakaramin daÉ—i baba yaji ba shida kaka suka samata albarka!!" takama hannuna tashiga
dani ɗakin ta duk a'tsorace nike da ita, dan ban saba ke ɓewa da itaba .
Munashaiga taban a'binci. "na gilgiza mata kai a'lamun bazanci ba." ta zaroman ido tare da
faÉ—in banason iskanci maza ci kiban kwanan," haka nafara tura abincin ba dan daÉ—i ba,
bayan nagama nayi sallah nadawo wajen kaka nazauna nafara mai magana Inna,'." kaka sai
yaban hakuri yace in bita da addu'a ita tafi bukata.
Bayan kwana arba'in É—in Inna da sati biyu, kaka yatashi da amai da gudawa, bai wani jimaba
ya amsa kiran mahaliccin shi.
"Nan da nan rana tazameman zafi inuwa ƙuna," dan Ammi a'gabansu take lallaɓani bayan
idonsu kuma zagi ne sai duka ke shiga tsakanina da ita.
Bayan anyi sadaka kaka!! Baba ya yi sallama wa Ammi yace ta fito, bayan tafito cikin ladabi ta
gaidashi ya amsa tare dayin shuru.
Azuciyar Ammi fatanta Allah yasanya abunda take tinanine zai wakana.
Ilaiko sai gashi Baba yafara mata magana akan tana da ra'ayin a'maida auransu ko-ko yasamo
wata, dan gaskiya yagaji dazama ba mata, gaya babu iyaye dole yabukaci mai de bemai kewa.
,,Jin a'bunda yace yasa Ammi cikin rawar murya tace ta amince,washe gari aka maida auran su
baba da Ammi, nan suka fara sabuwar rayuwa a'inda a'ka d'ibi dakin inna aka gyaraman baba
yasaman sabuwar katifana ina kwana.
Wata laraba ina zau ne malamin makarantar mu ya aiko kirana, akan in dawo makaranta," Baba
dake É—akin Ammi yaceman in tashi in sanya hijjob infita, haka nafita na isa wajen malam na
zau na, na gaisheshi yaman gaisuwa daga nan muka dasa daga inda muka tsaya.
Bayan sati biyu makaranta islamiya mu aka fara ba da hardar maulidi !!nima a'kabani tawa,
bayan angama malam yari keman littafi nakawo ta cikin sassanyar muryata mai daÉ—in
sauraro, wanda sanadin hakan yasanya har nakai karshe malam baisani ba, sai da nacemai
malam nayi dai-dai? "Malam mubarak ya É—i mauce yace kwaraiko Mufeedah, Allah ya yi ki da zakin murya mai
sama ma a'boci sauraro natsuwa, anya kuwa bake za ki re ramana wakar da zamusanya ba
ranar da zamuyi maulidin.?
Nai dariya ban ce komiba.
Kamar wasa kullum malam sai yaman magana, har wata rana yazo da duguwar farar t akadda
yabani tare da cewa dan Allah mufeeda ki kwatanta raira wakar nan, ina ganin za ki iya cimma
nasara ."
Kamar wasa naji abun yashiga raina! nan nafarayi duk da ba wani kwarewa nai da rai rawar ba,
amma kasancewar na iya hausa sosai sai abun bai-ban wahala sosai ba.
Har wata litinin muntashi daga makaranta," malam Mubarak yaceman yanaso muyi magana in
tsaya shagon baba na zai iskeni anan."
Nace mai to ba matsala" cikin tafiya ta ta natsuwa data zame man jiki, nashiga shagon Baba na,
na iskeshi ya yi tagumi nakarasa wajenshi tare da zare hannunshi nace Baba miyasame ka?
Baba yarungumeni sosai tare da fashewa da kuka, yace narasa mikikayima mahaifiyarki ba tun
yau na fahimci kalar tsanar datakemaki ba mufee, dama bata baki abinci amma baki faÉ—aman
ba sai É—azu dana zo shiga naji tana maki faÉ—an a'kan bazata baki ba?
Nai murmushi tare da zare jikina daga nashi nace" haba Baba bakomi ni bana mason abinci,
kuma inna zo wanke wanke ina samun kanzo inci, kuma in kaban kudi ina sayen wani abu
makaranta inci, ita Ammi sai tace sai naje tallah ba tare daka sani ba, wai in zanje boko kar
inshiga in wuce tallah, nikuma nace aa inason karatu inaso inzama babba likita Baba in'dunga
ma mata allura ko?
Baba yayi murmushi yashare hawayanshi yace "Allah yacikamaki burinki Moopy, sai dai ina so
in'saki islamiya yamma, karki yarda kiyi tallah!! daga yan zu in kindawo boko zamushiga cikin
gidan kiyi bukatar da zakiyi zamu dawo nan shago in koyamaki dinki, in hudu tayi zanyi alwallah
la'asar zamu shiga kisanya ka yanki kitai islamiya, in kindawo ki zau na ta mangari ba abinci
kuma maci nawa ki rabu da ita kinji ko?
"Nadagamai kai dan nima naji daÉ—in hakan sosai."
Muna zau ne muna fira malam mubarak ya yi sallama yashigo, bayan sungaisa da Baba yake
ma Baba bayani, akan dan Allah inba damuwa sunaso a'barni muje STUDIO in rai ramasu wata
waka dazasuyi maulidi da ita.
Baba ya jinkirta zuwa cen yace to wazai tafi da ita? sanna mamana bata iya waka ba
kar'tamaku shirme duba da duka yanxu tacika shekara 11"
Malam ya yi murmushi yace wallahi Malam Bukar na hango baiwa mai tarin yawa game da
moopy, Dan Allah karka hana mu wannan damar data samemu, baka damasaniya ko Yarka
zata iya ko bazata iya ba, fatana dai kawai kasama abun albarka."
Baba yace to shikenan "mama na" za ki iya kuwa?.
Cikin murna na kadamai kai a'lamar eh.
Yace to masha Allah yau she za ayi abun? zan shirya da kaina in kaita?
Malam mubarak ya sake yabawa da tarbiyya da Baba ya
ÆŠorani akai, yace gobe ne bayan azahar.
Baba yace bakomi Allah yakaimu.
Malam yace Ameen yakama gabanshi.
Washe gari ina kwance Ammi tashigo ta zabgaman mari, tare da faÉ—in tashi kisanya kayan
makarantarki, ki É—auki kaya kitai tallah, ai bazakiman zau ne cikin gida ba kina zubaman
wannan shegun idanuwan naki kamar goruba ba".
Na tashi a'gigice ina matsawa ina bata hak'uri tare da cewa dan Allah Ammi kiyi hakuri ni karatu
nikeso.?
Tayo kaina gadan-gadan "Baba yashigo É—akin ya yadakama ta tsawa" tare da furta duk ranar
da hannunki yasake kuskuran kaiwa jikin uwata wlh tallahi sai ranki ya ɓaci wadda batason
ciwon kanta ba.
A'fusace Ammi tace wlh bazan aje wannan zabge'giyar yarinyar a'gidan nan ba bata neman
man kudi ba, haka kawai to ni k'ake so inje ko-ko? bayan Allah yasanya da ranta da lafiyar ta.
Baba yace ai bawani yasaki talla ba ke kika sa kanki, dan haka sai ki É—auka kitafi tinda ke
baki da ma'faÉ—i, yayi tsaye kaina na shirya mukaje shagonshi yabani tia da bread nasha na
tafi school, bayan nadawo na iske Baba shago muka shiga gida yayi tsaye kaina nai wanka
nashir ya cikin jar a'tamfar da Yaman sabuwa mai ratsin baki, yaban sabuwar hijob baka
nasanya nafito.
Baba yace Masha Allah uwata tafi ta kowa kinyi kyau sosai .
Nai dariya tare da cewa Baba nida bana kwalliya ban'ma iyaba, wanka kawai na iya sai shafa
mai, Inna ke man kwalliya yanzu kuma batanan.
Baba yace ki mata addu'a nan gaba zaki iya, ke kyankima ai ajini yake uwata ko bakiyi wanka
ba.
Haka mukaita labari har na fito muka dawo shagon shi, Baba yabani abinci naci muna fira
malam mubarak yashigo shagon .
Bayan sun gaisa da Baba muka taso muka hau a'daidaita mukayi wani Studio bayan munje aka
tarbemu a'inda malam yafara masu magana akan yanaso in masu wakar maulidi.
Mai Studio yayi dariya yace malam ga yam matanan sai wannan yar yarinyar taya zata iya?
Malam ya ɓata fuska tare dacewa ok shikenan bari mucanza wani wurin.
.
"cikin sauri mutumin yace aa malam kayi hakuri ba haka nike nufi ba tazo mugani.
Haka a'kashiga dani wani dan É—aki !!muna shiga naga ina hango Baba na da malam ta cikin
glass hankalina yakwanta, anan mutumin yabani takardar tare da saman wani gin'gimemen abu
a'kunne yace in fara karanta rubun takardar amma cikin waka.
"Sosai abun yaman nawi a'kunne haka na daddage nafara karanta wakar cikin takarda, har
nakai karshe mutumin baiceman komiba saida nagama na kalleshi shikuma tacikin glass din ya
kalli wani mutum dake zazzaune yana lallatsa computer wajenshi na wajen ya É—agamai
hannu alamun komi dai-dai...
Yacireman a'bubuwan tare da cewa gaskiya kinada murya, Allah yabaki basira cutt akwai dai
zakin murya, to yanzu tinda naga zaki iya zan koya maki yanda zaki lankwasa halshenki da jan
bakin abun yanda zai bada ma'ana, sai musamaki kiÉ—a dai-dai da wakar.
Nace mai to.
"Haka yafara koyaman nai tsaye ina kallon shi dan har na har dace abunda yaceman..
Bayan yagama a'kasake saman a'bun saman a'bunan ga kunne, nafara raira wakata mai
masifar daÉ—i data bada ma'ana sosai,babu kuskure ko É—aya. bayan nagama mutumin
yashiga tafaman tare da cireman a'bun muka fito.
Bayan mun fito suka kunna wakar saiga muryata cakwai acikin computer, sosai Baba yayi
mamaki wai nice da wannan wakar malam mubarak kau sai murmushi yake tare da cema
wanda yakoyaman Rafel kace bazata iyaba?
Rafel ya sosa kai tare da fadin afuwan USTAZ nadauka bazata iya bane wlh, gaskiya Baban ta
ya haifi hazuka, dan wannan komu wlh inza a'bamu munaso dan akwai masu son mata su
masu am'shi.
Malam mubarak yace ga mahaifinta nan saika tambaya kaji.
Rafel yatambayi Baba akan zai barni in an'samu su kirani in amsamasu?.
Baba yace zamuje gida muyi shawara tukunna!!! haka mukai masu sallama muka fito, muna ta
howa malam mubarak ya dakko dubu ukku yaban, nace aa bazan karɓaba.Baba ma yace aa
baza ta am'saba." malam mubarak yace aiko malam bukar sai kai hakuri ta karɓa dan dama
sauran reshen makarantun suka haÉ—a baniba.
Babu yanda Baba ya iya haka ya amsa mukatafi gida cike da farin ciki
Muna shiga mukaga Ammi zaune bakin rijiya tana jajjagen kayan miya..
Baba yakarasa wajenta tare da cewa hauwa kinji ikon Allah yau uwata tashiga studio harda
raira waka...
Afusace Ammi ta ɗaga kai tace mikakace bukar tela ..........��
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: ��💘��💘💘��💘��
ZAMAN TASHA
��💘��💘��💘��💘
NA UMMY AYSHA
💘��💘��💘��💘💘
🅿�3�⃣5�⃣&3�⃣6�⃣
"""Baba ya zaro ido jin a'bunda ta ce "Ya ce ni kike kira haka ga tsau babu lada bi Hauwa..?
Ammi tace nacemaka, Wallahi da akwai sunan da yafi wannan zama ga'tsau da saina fadama,
haka a'keyi har washe baki k'ake dan kaza ma Uban banza zaka zo kana fad'a man wai d'iyar
ka tashiga tsiririo...
"Ban san sadda na kwashe da dariya ba jin furucin Ammi."
A'kufule ta yo kai na taha'yeni ta fara jib'gata, tare da cizgo Kai na Ta ce saita gurje bakina da
k'asa sai taga da Uban da zanyi wakar, da kyal Baba ya samu ya kwace ni daga hannun Ammi.
"Ammi ta d'ago a'fusace Ta ce" Wallahi na tsaneki! na tsaneki!! tsana mafi muni, duk wani jin
dad'ina kin da kushe-shi a'kanki kin shiga tsakani na da Mijina, komi sai Yace sai ke kin ki
zuwar man tallah bayan gaki zaune ba kya komi," ta rushe da kuka kamar wadda aka zalunta".
"Baba ya da kama ta tsawa!!!Ya ce" ke in barcin ma kina mahaukaciya taya zaki tsani a'bunda
kika haifa, har kina fur tawa da bakin ki, Moopy kuma waka yanzu ta fara bazan tab'a da kushe
ta ba Wallahi, dan ban son a'bunda gaba zata haifar ba.
Nan fa Ammi ta rikice ta fara zage-zage,Baba yakama hannuna muka tafi shagonshi muka
cigaba da labarin mu, yasiyo mana abinci mukaci muka koshi, nan yafara ko yaman yankan
É—'inkin cikin lokaci na fahimta har nafara daukar kyalle ina kwatan tawa....
.Agurguje.
Bayan shekara bakwai
"""Abubuwa da dama sunfaru na farin ciki da a'ƙasin haka, ta ɓan'garan Ammi babu
a'bunda ya canza nagame, da tsanar da takeman, kuma bata sake haihuwa ba har lokacin ba
dan tana tsari ko wani abu ba, amma hakan bai dame taba saboda tana ganin ya'yan matsalane
kotama haife su Uban su bazai bari taci gajiyarsu ba, "acewarta tinda baya bari suje tallah."
Ta ɓan'garan d'inki kuwa sai dai in koya ma wasu, dan ɗ'un kunan nike na mata sosai masu
maseefar kyau, dan da nan nafara Tara costumers, ganin haka Baba yasai man sabon keken
d'inki na fara yi dashi, in kaganni gidan mu to wanka zanyi ko wata buk'ata ina mawa zan fita in
koma shago, a'takaice dai rayuwata da mahaifina na santa, shine Uwar shine Uban, ko sadda
girma yazoman Baba yakaini wajen Ammi akan ta gwadaman yanda zan gyara jikina, saita ko
rani akan shi aikin mi yake, haka ya zauna ya kwatan'taman duk yanda zanyi, cikin ikon Allah
na fahimta dan ina da wannan