Showing 54001 words to 54969 words out of 54969 words
Chapter 19 - ZAMAN TASHA COMPLETE BY UMMY AYSHA.pdf
rakasu yadawo tarel da bata umarnin taje tayi Alwallah .
Bata musaba taje tayo wanka da Alwallah ta dawo ta iskeshi zaune bakin gado.
Sallah suka gabatar kamar yanda Shari'a ta wajabta, Bayan ya ciyar da ita taciyar dashi suka
koshi sukayi hamdala. kowannen su yayi shuru bakajin komi sai bugun zuciyar su dake hau
hauwa .
Irfan yayi k'arfin halin cewa kije ki kwanta Baby nima zanje D'akina kar in matasamiki nasan kin
gaji ko.
Da sauri Moopy ta kad'a kai . Bankwana yamata yatafi Tare da sakin Murmushi.
Tana ganin fitar shi ta zare kayanta ta sanya na bacci masu mugun taushi, Tare da fesa turare
lungu da sako tayi Addu'a ta kwanta.
Can cikin dare Mufeeda taji bakon al'amari ,kamin kace mene ta cika gidan da ihu.
Washe gari da safe Moopy keta zabga kuka kamar yarinya .
Irfan ma da zazzabi ya rufeshi yanata aikin lallashi da bata baki amma ko kallonshi batayi sai
kuka .
Dakyal ta amincemi shi ya taimakama ta yamata wanka ,ya shiryata shima yayi ,kasa fita
masallaci yayi saboda zafin da jikinshi , Sallah shi yayi gida yana gamawa ya had'omata Tea
mai kauri Bayan tasha ta rage ya shanye tare da b'allar magani yabata,shima yasha ,yajata
jikinshi sai bacci.
Rayuwa mai dadi sukeyi cike da burgewa.
Abangare su Ammi kuwa abun ba acewa kimi, So da k'auna kawai take nunama yaran ta.
Irfan na kula dasu! inda ya maida su Amina makaranta yasama ma Ammi yar aiki suna zama
tare.
Bayan wata goma.
Irfan ne da gudu da Moopy a'hannunshi ya sakko da ita daga saman bene yana nishi da
raf'keken cikinta sai kuka take, Tana fa�in mutuwa zanyi Honey ka yafemun.
Kuka Irfan yasa ya'ce" bazaki.mutuba Matata, in kintafi kibarmawa ni? kingama.ma haihuwar
kinji ko, bazan sake miki ciki ba har Abada.
Aguje yasake yin.sama ya d'akko mata hijjob inta yasamata ya sungumeta yasanya a'mota
sukayi Asibiti da take Awo .
Cikin gaggawa aka karb'eta! inda Irfan ya sanya kanshi shima ciki yahana kowa zuwa wurinta ,
Dan yace babu shegen da zai kalle
mai.mata.
Moopy tasha wahala kamin Allah ya taimaketa haihuwar ta taso.
Tsaye Irfan yake a'gigice wurin kafarta ya samata.ido kamar yasamu tv.
Alhamdulillah ya furta ganin kan Baby ya fara fitowa.
Cike da kwarewa da sanin.makamar aiki ya karb'i haihuwar matar shi, inda santalelan d'ansu ya
fa�a hannun uban shi.
Da sauri ya yan ke cibi tare da fitowa yaba wata nursing Baby yace ta shiryashi.
Da sauri ta karb'a tana fadin Masha Allah.
Irfan baiko kalletaba yakoma wurin Moopy ya gyarata.sosai kana ya canzamata gado ya
gangaro da ita dan kaita d'akin.hutu.
Jaririn aka.mikamai sukuma suka karbi gadon suka kaita dakin daya dace.
Waya ya zaro ya fara bugama yan uwa da abokan arziki dan danan Asibiti ta cika.
Mamy ta kama yaro tarike sosai tanajin soyayyar yaran har cikin ranta, Take taji soyayyar
Moopy mai girma tana ratsa ko ina najikin ta
Tsohuwa sai murna take tayi DA.
Ammi na gefe batace komiba sai murmushi take.
Kwanan su d'aya aka sallameta ,Mai jego da Baby na cikin koshin lafiya.
Gidan ta akawuto da ita dan tasamu kulawa daga mahaifiyar ta.
Tsohuwa tama Ammi magana da hudu ba akan ta cire kunya ta kula da yar ta tinda dai babu
mai tsayawa wurin.
Ammi tace mata bamatsala insha alylah.
Irfam ranshi ya b'aci sosai da aka rabashi da matarshi, Washe gari yazo gidan Ammi ya isketa
tanama yaro wanka.
Bayan sungaisa ya shige d'akin Moopy ya isketa tana d'aura towel za ai'mata wanka .
Rungumeta yayi" yace shine kika bari akarabamu ko?
Tace aa muna tare har abada.
Wake maki wanka yasake jefe mata tambaya?
Moopy tace inna Asibi ce.
Ido ya Zaro yace aikuwa bata isaba daga yau zandinga miki.
Tintana ganin abun kamar wasa har daga baya ta gane dagaske yake, DA kanshi yakamata
yamata wanka yagasata sosai kana ya fiddota.
Haka suketa rayuwa harta iya da kanta.
Ranar suna Baby yaci sunan mahaifin Moopy inda suka samishi suna(ABUL KHAIRI)littafina na
gaba insha allah.
Anci ansha inda yam.uwan irfam suka musu kara sosai .
Ammi ta sha kukan tinowa da danginta da batason inda sukeba. Da yanzu dasu za asha
hidima.
Bayan taro ya watse Amaryar jego tasamu kyaututuka da dama daga dangin mijinta.
Ammi ta zage tana bama yarinyar ta kulawa, Mamy ma ba abarta abayaba tana basu
guduncmuwa tinda tason basu da kowa
Aranar dasuka gama wanka Irfan yakwashesu sai gida.
Inda suka bude sabuwar rayuwa mai cike da in'ganci.
Bayam shekara biyar.
Aka sanya bikin Ammar da Amina, inda su Moopy suka taka rawar gani sosai komi sune kan
gaba.
Shekara na zagayowa meenah ta haifo yarta.mai kyau inda taci suna Ummul KHAIRI suna
cemata.khairi
Kullum rigimar ABUL KHAIRI akaishi wurin KHAIRI ya ganta.
Irafan yace miyasa ka keso a'kaika wurin ta.?
Cike da yarinta yace b6aby nace.
Dariya sukasanya suduka Moopy" tace abunda kake cewa shine yace shima".
Dariya sukayi suka shirya suka tafi gidan Amina su duka.
Acen suka wuni da zasu taho Abul khairi kuka yasan ya sai an'barshi wurin Baby shi.
Dole suka barshi suka musu Sallama suka tafi...
Suna shigowa Irfan yace Baby nah muje sama musamo wani Baby tinda wannan ya gujemu.
Harara shi Moopy tayi tace bazanjeba ,Bakace nagama haihuwa ba.
Kanta an'kare yasureta sukayi sama suna dariya.....
TAMMAT BI HAMDULILLAH.....
I miss you mutanena 🥰🥰