Showing 36001 words to 39000 words out of 54969 words

Chapter 13 - ZAMAN TASHA COMPLETE BY UMMY AYSHA.pdf

Advertisement

10 Jul 2025

4048

🅿�4�⃣3�⃣&4�⃣4�⃣


""""Baba ya k'usa fad'owa, a'guje Nai kanshi na tallabo shi ina jijjigashi tare da tam'bayarshi
miyake so?

Hannunshi mai lafiya ya dinga nuna man sa'shin da littatafai na da nike a'jiyewa saboda rubuta
waka. cikin mamaki " nace Baba littafi zan b'aka?


Ya d'aga man kanshi tabbacin eh .

Da sauri na tashi na �akko mai!!cikin mamaki yasake nuna wurin, nayi shuru ina nazari'n ko
miyake kuma nufi " nace Baba rubutu za kai in'baka Biro?

Ya sake d'aga man kai a'karo na biyu.

"Natashi da sauri na �akko mai na bashi, tare da samu na jir'kitoshi ta yanda zaiji da�in
rubutun abunda ya keso in mashi .

Ya fara Rubuntu tari ya sake sar'keshi, da sauri na d'auki ruwa na bashi,. ya k'afa kai wani ya
shiga bakin shi wani ya fito, har'yasha ruwan Sosai,bayan ya gama yaci gaba da rubutun shi
a'hankali ya d'auki 40mnt kana ya daka ta tare da kallona ya lumshe Idon shi,.

"Nace Baba in d'auka?ya d'agaman kai alamar eh, "Nasa hannuna na É—auka na fara
karantawa kamar haka.
(Assalamu Alaikum ya �iyata abin Soyiwa aga'reni, ina mai baki hakurin akan rayuwar da zaki
tsinci kanki nan gaba, amma ina'so kisanya ma ranki banine gatanki ba dama Allah ne
gatan'ki,kuma shi zai shige maki gaba a'duk kan lamur'ranki na yau da gobe, kiyi Hakuri da
halin Mahaifiyar ki, 'ki kyaleta ki ke b'ance kanki daga gareta, ko bayan bani ban'yardar maki

komawa gidan ta ki zauna ba, inaso kibar wannan gidan da bata son dashi ba a'matsayin sirri,
akwai sauran bayani zakiji a'wajen Alhaji kiyi hakuri ki yafeman, abu na karshe na roke'ki da
Allah karki zama mai yawan kuka a'kaina, duk abunda rayuwa zata nuna maki ki �aukeshi
a'matsayin kaddara, ina sake jaddadamaki wannan gidan na kine ke d'aya, daga masoyinki na
har a'bada Mahaifinki, ki yawaita yiman Addu'a �iyata, Nagode da kotkarin da kukeman Allah
yasaka maku da Alkhairi Bissalam)
ina gamawa na fashe da kuka tare da fadin haba Baba yazakaman wanan abun dan Allah,
harda doguwar takadda Baba kamar wanda zai barni.

Na d'ago da idona fal hawaye na kalli Baba, take gabana yafadi ganin kanshi a'langa'be,
bans'on sadda na jawo shi duka jikina ba na saki wani mahaukacin ihu da yasanya ina Asibi
shigowa da gudu ba.

""Inna Asibi tai kai na tana duba hannun Baba, take ta saki salati tana mai janyeshi ta mai dashi
akan katifar shi,ta sanya babban bedsheet ta lulu'beshi tana share hawayen ta.

Duk abun da take da ido nike binta, zuwa cen jikina yafara kyarma tinowa da mutuwar Inna data
Kaka," koda ina da kananun shekaru nason mutuwa.
Na dago jaj'jayen idanuwana na. Zubama Inna nace mikenan haka ?

Inna asibi ta share hawayenta tare da fadin" kiyi hakuri mufeeda kullu nafsin za ikatul maut, dan
haka a'wannan lokacin Addu'a yafi bukata ba kuka ba"tafita daga dakin tana latsa wayarta...

Duk maganar da take fad'a ba komi naji ba , nakai minti talatin ni banyi kuka ba bankuma
motsa ba, Zuwa cen sai ga Alhaji a'gigice shida mutane da yawa, na d'ago ido na kalleshi tare
da "fa�in Alhaji kaji a'bunda Inna Asibi tace, daga yau bazan sake kwana da ita ba tinda
batason Baba'na, ka gafa cewa take ya mutu, kenan tana nufin cikin kasa za a'sashi, Na fada
cikin gushewar hankali, Alhaji shima ya fashe da kuka tare da fadin shikenan nayi rashin Aboki
marar Hayani da bai �auki Duniya da zafi ba, dan Allah Sirikina ka tashi yafada cikin kuka
shima yana jijjiga Baba...

Wani babban mutum da yasha manyan kaya da Cas'baha a'hannunshi "yace haba yallabai
yakamata fa kadaina kukan nan kana k'ara rikita yarinya, gag'gawar sutur'tashi a'kaishi
makwancinshi yakamata ayi."

Tinda naji wannan magana tashi bansake tina komi ba har saida nakwashi kwanikka, ni ba
matatta ba ni ba mai lafiya ba, ni dai naga wata Tsohuwa ba Baba Asubi ba tana jin'yata, amma
bazan iya cewa ko ya take ba saida Alhaji yasa aka dungaman rubutu kana na fara dawowa
hayyacina,bayan navdawo dai-dai na zauna naci kuka na gode Allah, ba mai rarrashina na
hakura na daina, ban son kuma a'dadin kwana nawa Mahaifina garai ba, saida na tambayi mai
kula da Baba dan nabar ganin tsohuwar nan, yau watan Mahaifina nawa? Yaceman yakai kuson
biyu kana na'sani.

Haka rayuwa tai ta tafiya bana um bana um-um, kullum daga gidan Alhaji ake kawoman abinci
duk da bawani na kirki nike ciba, su Rafel kullum na zagaye dani suna ban baki, ban'kara ganin
imiran ba ban kuma damu da in'son inda yake ba, saboda nayi rashin Mahaifi na hyakura banga
wanda zanrasa ba in kasa hakuri.
Na samu wata ukku cur cikin kunci daga baya na fawwala ma Allah komi na dawo naci gaba da
abubuwan rayuwata, inda nazama hamshakiyar mawakiyar da duniya keji dani, har na kara yin
Wak'a wa wani mutum yaban mota Babba, haka na had'asu biyu kud'ad'ena kuma na tambayi
Alhaji nan daya zama Mahaifina duk sati yana leko ni ya tafi, nace'mai ina bukatar gina Filina
zanyi Studio na kai'na." yace man ba matsala shi yataima kaman aka hada komi a wannan
karon'ma yasake man gwaninta dan wasu abubuwan duk shi yasaman" har lokacin mutane
murya ta suka sani basu son ni a'fuska ba, dan banda bukatar hakan, kasance wata mai
ZAMAN TASHA abun zai zama tso'gwami.

Bayan ankammala ginaman gidan gonata da Studio na fara zuba abubuwa kaji dasu kifaye
Alhaji yace man ga mutumin daya kula da Bab'ana da yana jinya zai din'gaman gadi, in yaso
y'ay'anshi dake gidanshi zai barman'shi ya dawo gida na yanaman gadi, na yarda da hakan dan
nason Alhaji bazai man abunda bai dace ba, haka na hada Buzaye biyu Yaya da k'ane d'aya
a'gidana d'aya a'gidan gonata.

Fahad shiya zameman garkuwa Studio na komi shi keyi,yayinda Rafel yasamu wani yasanya
Allah yasama sabon wuri na Al'barka cikin yan watanni manyan mutane suka fahimci wajen,
take na dinga kwasar ciniki naita am'fani da ribar ina kara habbaka wajen harya zama yanda ni
kes, nasamu manyan kud'ad'e agidan Gona ta, hakan yasa a'sace naje unguwarmu nasamu
kusa da masallaci na bada aka'faraman bohol dan inaso yazama sadakhatul jariya ga Baba
na,ina fatan Allah ya sanya ladar takai a makwancinsu shida iyayenshi, bayan an'gama
mutanan unguwa sukai tasa Al'barka dan basu son wayayi ba dan ban'ba ma aikatan wannan
damar ba, nashiga Unguwar dan Sallamar masu aiki,na fito kenan a'mota kamar daga sama
naji an'saki salati tare da "fadin ba shakka, ashe tir'bar daya d'oraki kenan kamin yabar duniya .

Da sauri na waiga naga Ammi ce da kaya a'kanta hannunta jaye da Aminu, "Na durkusa zan
gai'data tace saboda bani na kawoki duniya ba ai'kwara kiman gaisuwa haka, maza to ki biyoni
gida kamin in d'agamaki no-no.

Nace subhanallahi ta sakar man harara tare "da f'adin wannan motar ubanwa yabaki?
Nace wajen sana'atane a'kabani..

"Tace da kyau!! tayi gaba dole na fito na biyota muka shiga har gidan mu naita kallon gidan
kamar zanga Baba, banson sadda hawaye ya sakkoman ba.
Tsawa da Ammi ta dakaman yasanya na furgita na fada d'akinta jikina na rawa, nazauna kasa
ina gaisheta bata am'saba tace yawwa kikace motar kice ko? kuma kin iya kenan.?

"Nace eh Ammi nike janta.

Tayi murmushi" tace to ai shikenan kinga faduwa tazo dai-dai dazama, yanzu tashi muje nan
gidan Magaji mai gyaran radio.

Naji da�in yanda Ammi taman hakan yasa na bita har gidan muka gaisa dasu tace dan Allah
Big na nan ?

Maman shi "tace bayanan Yar Fillo"da yake haka suke cemata, muka fito har munzo soron
gidan Ammi" tace man jirani inzo" nace to nai tsaye ina mamakin canjin danasamu yau awajen
Ammi, harna fara tinanin kila ta barni in dawo gidan, inci gaba da zama gabanta, kila tana
tausaya man ne ganin Babana ya rasu.
Ammi" tace muje ki kaini TASHA nan ta kofar Guga.
"Nace to Ammi"

Muka karasa wajen mota na budema ta baya ta hakimce, tare da zaunar da Aminu a'kanta ta
namai wasa cikin farin ciki" sosai abun nasu ya burgini nace Allah yajikan Baba na.

Na tada motar muka tafi har TASHA, muna zuwa Ammi ta sauka tare da ceman biyoni.
Nabi bayanta mukaje tayi kwatancen wanda take nema, nan take suka had'ata da wani luteten
mutum, yak'araso yana aa Yar Fillo akwai no-no.

Ammi ta �aure fuska tare da cewa tai'mako nikeso kaman, yarinya ce gatanan mota gareta,
ina so tazama yar ZAMAN TASHA saboda ta nemo man abunda zanci nida Yaro na.
Big yayi dariya ta yan duniya "yace an'gama ai ita har kar kuÉ—i ba mace ba namiji,dan haka in
yanzu ki keso a'fara zamu fasa da ita kawai.

Ammi tace ta kwana gidan sauki, sai dai kuÉ—in halak nikeso bana haram ba, bada motar nan
ta taba da taku zaku bata, saiku dinga fitar wa.

Big "yace ba damuwa, take ya juya ya jawo wata gof yayi parking d'inta wajena,"Yace shige
akwai full lodi zamu aje taki anan in'kin dawo kya É—auka, zaki biyoni a'baya.

Ammi ta kallan ta daure fuska tare da cewa maza ki bishi yanzu nikeso ki nemo ki
kawoman,dan nagama wahala nari ga nasaida komi nawa banda wani jarin kirki,maza kibishi
kamin in tsinemaki, wato kin'ban wahala da cikinki yanzu kuma kin kud"ance ki nata faman
shakatawar ki da kudin haram ko..?
"Na fashe da kuka nace yanzu Ammi ni zaki kawo kice inyi ZAMAN TASHA
? kawai dan in nemo maki, Wallahi na maki Al'kawarin zan dinga kawomaki komi na rayuwa
batare da na zauna a'nanba,saboda duk wanda ya ganni anan mutuncina da darajata zai zube..

Ammi tayi salati tare da faÉ—in shige kuje na cemaki kamin in maki Allah ya isa.

Haka na shige mota ina kuka rai a'bace na figi motar nan batare da na tsaya jiran kowaba,ita
kanta Ammi saida ta tsorata balle mutanan dake ciki, take TASHA ta dauki ihu suna "fadin Falau
Yar Cara's, ba tasu nikeba haka na dauki hanyar Jibiya duk da banta ba zuwa ba, Amma nason
hanyar da take. sosai nike gudu yan motar duk suka rude wasu harda kuka saida naje
magamar Jibiya kana na sauk'aka, na juyo da jajayen idanuwana na tambayi wani saurayi ya
gwadaman hanya, na yanka da su aguje har TASHA, ina zuwa TASHA wani yataso yace yawwa
kece Big ya yima lodi ko? Nai banza dashi na fita na juya, mutanan nan suka filfito suna godiyar
Allah, "nayi kasa da kaina tare da faÉ—in kuyi hakuri dan Allah, bawanda yaceman komi nafara
ƙoƙarin shiga motar, mutumin yakawoman wasu mutane suna gama shiga ya mikoman
kudi na karba nayi Katsina, anan na samu Ammi tsaye nayi parking din motar tare da fitowa na
bata kudin zan shiga motana "tace idan baki dawo gobe ba Allah ya isa tsakanina dake no-no
na da kika sha ban yafemaki ba.

Zuciyata ta kafe banajin komi banko kalleta ba, nafada motana nayi gida, haka nasamu Fahad
tsaye yanata zagaye ya
Taso a'gigice ya tambayeni ina naje ?"ban b'oye mai komi ba na fadamai," sosai ya tausayaman
tare da faÉ—in inyi haykuri da halin Ammi wata rana sai labari.

Haka rayuwa tai ta juyawa nazama mai ZAMAN TASHA karfi da yaji, Ammi ta samu wani
Tsohon mashayi ta aura, tare da sai da gidanmu batare da sanina ba," tace gadon Aminu ne
zata juya;mai, ta tare gidan wanan mashayin banso hakaba amma banda yanda zanyi,mijin
Ammi yawareta ita kadai wata unguwa wata rana yabi dare ya kwashe duk kuÉ—aÉ—en Aminu
yakama gabanshi, tashin hankalin da Ammi ta shiga yakusa sata hauka, nidai kam ban ma son
yazan cema ta ba nashareta naci gaba da kawomata kuÉ—i yanda take so, daga baya ta
Dangana ta Hakura, tasaman dokar duk in zani in biya gidanta wani tsohon É—akin ta wareman
taceman ga kayanan in'dinga sawa rayuwar gwanjo tane kar a'ganni da masu kyau aki shiga
motar.." hakan takasance duk in'zani zan biya in aje motana in sanya tsaffin kaya, ahaka har
ammi ta haifi cikin da mutumin yabar ta dashi ya gudu nayi nayi in'bata kuÉ—in hidimar ta kiya,
sai tamaidaman jigila so ukku arana a'haka har ta haifi Amina aka yan'kamata ÆŠan a'kuya,
yanzu maganar da nikema Amina shekara biyar Aminu nada goma sha biyu, kaji labarina yah
Ammar.

Ammar yace tabbas labarinki akwai ban tausai, dakuma ban mamaki, to yanzu ina Imran yake?

Moopy ta daga ka faÉ—a" tace taya zan sani har yau ban taba tambayar Daddy shiba, dan
gaskiya yanzu ya kan daÉ—e bai zo wajena ba saboda yanayin ai'kinshi.

Ammar yayi murmushi tare da cewa ina zuwa..

Tsohuwa ta fasa kuka tare da fadin wallahi tallahi kece kece . ..��
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: 💘��💘��💘����💘
ZAMAN TASHA

💘��💘��💘💘����
NA UMMY AYSHA
��💘��💘��💘��💘
🅿�4�⃣5�⃣&4�⃣6�⃣

""""" Moopy Ta'ce"nice mi?
Tsohuwa ta share hawayen ta ta'ce ina zuwa bani Wayata la'tsoman Alh.khabir.
Moopy ta karb'a ta gano Number ta kira. yana fara ring taba Tsohuwa ta'ce ya shiga.

Tsohuwa ta'ce" barshi zai kirani baya D'auka in yaga nakira kan'tama rufe baki wayarta ta fara
Ring ta tashi tashige D'akin ta tare da banko kofar tace Halo Khabir kana jina kuwa?
Daga cen bangaran yace ina jinki Hajiyamu ina wuni?

Tsohuwa tace kai tureman wunin nan yah banyishi lafiya ba kaganni nan nasha kuka daza
atarashi sai yacika palon nan dan tinda nagama asuba nike kuka har yanzu bai tsayaba..

Alh yayi Dariya yace ikon allah Hajiya mi yafaru haka ko yan NEPA dana turo suka maki wani
abun?

Tsohuwa ta'ce" su D'in banza kai yaro ina yarin yar nan danayi jinya sadda babanta ya rasu ta
kusa da gidan Irfanuuu...

Alhaji ya'ce"eh nagane wannan satinma zanje ganinta tana nan lafiya lau.

Tsohuwa ta'ce" nizan fadama kau tana lafiya ya zancen maganar ta irfanu yakamata fa ka
fadamata gaskiya lamari tin kamin kazama dattijon banza a idonta...

Alhajin yayi shuru yace Hajiyarmu wani abu ya farune?

Tsohuwa ta'ce" yo abubuwa mana kai dai kaji abunda nacema inkuma kakiya alhaki na akanka
tom..
Alhajin yace ash'sha Hajiya karki yi fushi yanzu haka ina abuja wani aiki yakawoni nafadama
Irfam ya fadamaki dan nata kiranki baki dagaba.

Tsohuwa tace ina wani abune shiyasa Allah yatsare sai kadawo ta kashe wayarta ta fito palo
tana fadin yar Cakwal ba'inda zaki yau anan zaki kwana in mak....

Kantakarasa taga wayam ba Moopy ba a'lamun ta aguje Tsohuwa tashige D'akin irfan ta iske
Ammar nata gogema irfan jikinshi da towel dan zazzabi yake.

Taohuwa tace Ammar ya haka katafi ka mayar da itane?

Ammar yace wace kenan?

Tsohuwa tace uwaka yarinyar daka barmu afalo mana yar Cakwal.

Azabure ya'ce wai kina nufin Bata gidan nan ne?

Tsohuwa tace Wallahi bata nan! daga shiga in amsa waya na fito naga bata nan.

Ammar ya'ce" ya ilahi dama neman hanyar guduwa take, bari in'bita mugani ko zan sameta
gidan ta, ya fara k'ok'arin mikewa" IRFAN dake kwance magashiyan ya rike mai k'afa tare da
fad'in kamani in'tashi

Tsohuwa ta ya mutse fuska ta'ce" a'yaufa maza na jinya, an'sha dukan Aljannu jiki yayi tsami,
kai Irfanu turai ta lalataka wallahi,da maza na haihuwa da banson uban da zakaiba ranar da
zaka haihu, katon banza mai kashin wando."

Irfan bai ce komi Ammar ma ya kamashi ya mikar dashi ya jinginar dashi akan gado yace bari
in'dawo Bloody .
Akaro na biyu Irfan yasake ruk'oshi tare da gilgiza mai kai idonshi fal hawaye yace zanje.

Ammar ya zaro ido ya'ce ina? kason inda zani ne?..

IRFAN ya'ce" nacema zanje dan Allah ka kamani in mike tsaye...

Tsohuwa ta'ce" oni yasu k'udirar sama liman da wawan zama, yau kuma lalacewar da tasameka
kenan.kai Amiru kamashi ku tafi tare, da kabarshi nan kashi zaiman dan yabani aiki.

Ammar yazo ya kamashi a'hankali suke tafiya dan jikin IRFAN kota ina ciwo yake,haka har
sukaje parking lot Ammar ya jawo motarshi tare da sanya Irfan ciki,suka hau hanya Ammar
ya'ce" gidanka zan kai ka dan ni zanshiga gidan Mufeeda ne.
Irfan ya'ce" nima ka kaini in nemi ya fiyarta" na fahimci abunda nike mata bai kamata ba zan
bata hakuri...

Ammar ya gwalo ido yace Hmm saboda kaji Tarihinta ko, fahimci ko wacece ita ko?

Irfan ya'ce" Wallahi Billahi ko D'aya ban sani ba, kuma bana bukatar in sani, zanyi dan Allah ne
banga am'fanin wannan kiyayyar danike nuna mata ba. ka gafa ko son ganina batayi,in Na mutu
a'wannan halin nason tana da hakki mai girma kaina, tinda har karyata na sakeyi. yafada
hawaye na gangaro mai a'fusaka.

Ammar ya jinjina maganar IRFAN suka dauki hanyar gidan Moopy, suna isa mai gadin ta ya'ce"
masu ba kowa a'gidan ko Inna ma bata nan.."

Ammar yayi mamaki sosai yace to ina Moopy ta fita?..

Mai gadin yace wallahi bansani ba, tinda rana naga wucewar ta har yanzu bata dawo ba.

Ammar ya'ce" to shikenan!! ya tada motar suka tafi, a'tak'aice duk inda Ammar ya son zaiga
Moopy a'ranar ya nema ya rasa,Hankalin Irfan yafi na Ammar tashi, dan sosai yake kwadayin
ya ganshi gabanta yabata hakuri akan abunda ya kemata, amma ina ya makaro dan Moopy tayi
nisan kiwo.
CIKIN sati d'aya Irfan ya zabge ya lalace ga suma duk tamai yawa,ya nemi komawa
mahaukacin karfi da yaji, yauma kwance yake a'd'akinshi na gidansu yana zane zane a paper,
Mamy ta shigo tace Son wai kuwa lafiya kake kwana biyu baka fita ko ina, ko d'an Studio din
kabar zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login