Showing 21001 words to 24000 words out of 54969 words

Chapter 8 - ZAMAN TASHA COMPLETE BY UMMY AYSHA.pdf

10 Jul 2025

4008

shima ya gadane a'wajen mahaifi shi malam ummaru mai sallah,
mahaifina shika dai iyayenshi suka haifa tindaga shi basu sake haihuwar kowaba, Allah
yarayamasu shi dasana'ar dinki malam ummaru yabiyama mahaifina kudi yayi karatun boko da
isalama Amma bai waniyi zurfiba iyakarshi secondary School yatsaya, yayin da karfin malam
ummaru yafara ja, dole mahaifina yafara hawan keken malam ummaru yana É—inkin suna
samun abunda zasuci kuma Alhamdulillah basu taba kwan basu samu ba .
Watarana mahaifina nacikin É—inkin kayan yara na yan makaranta sai ga wata kyakkyawar
bafulatana budurwa ta hadu kamar ita tayi kanta fara sol tashigo shagon, da maganarta irinta
fulani tacema mahaifina ina wuni ko zaka sai fura da nono?

Mahaifina yazubamata ido dan baitaba ganinta ba yace eh amma daga ina kike kawo furar ne?
kasancewar shi mutum mai kyankyami.

Tace gaskiya ni ba yar nan bace munyo gudun hijira daga yankin jiubiya duk narasa a'halina,
daga ni sai mahaifina muke rayuwa sai shanuwar mu guda daya damuka tsira da ita, shiyasa
na zaɓi fara sana'ar siyar da fura ina ta tsar nono ina sayarwa dan insamu abunda zanci nida
mahaifina da yake kwance a'halin jiyya.
Mahaifina yatausayamata tare da faÉ—in to aina kuke anan da zama?

Da hannunta tanunamai wani kango da suke" tace acen nike rayuwa nida baffana...

Mahaifina yasake tausayamata" inda yace ta damomai furar hamsin nono na talatin sai sugar
na a'shirin.

Cikin farin ciki tafara ciniki ta dama mai fura tayi kyau sosai tami ƙamai"
Sosai baba na yaji daÉ—in furar nan" anan yasake sayen fura yashiga yakaima iyayenshi..
a'takaice shakuwa mai karfi tashiga tsakanin mahaifina da yar fillo, dan daga bayama anan
bakin shagon take zamanta da yar kwaryarta tana siyar da nono ta da fura, "Bayan shekara
biyu maciji yasari baffanta yan unguwa suka hadu a'kaimai sitira mahaifina shine kan gaba
wajen komi inda yar fillo tasha kuka ta gode Allah mahaifina yashiga yanemi alfarmar tadawo
wajen iyayenshi da kwana, anan suka amince tinda ya macace baikamata ta zauna kango ba .

Bayan shekara daya da rasuwar mahaifinta baba na yanunama iyayenshi yana sha"awar auran
yar fillo, iyayenshi basu wani ja maganar ba suka amince mai,anan aka tambayeta itama ta
amince aka daura masu aure aka basu sashe guda daga cikin gidan kasancewar ginin d'ane da
auransu da wata �aya yar fillo tafara tsiro abubuwa kala_kala kullum mahaifina tsaye yake
bakin kokarin shi amma bata gani, anan tacemai sana'arta ta fura da nono zata dawo yi,, "yace
ya amince amma bai yarda ta tafi talla ba "tace bata amince ba gsky sai dai in ya yarda tadinga

zaman shagonshi kamar da .
Shima yace bai yar daba amma zai iya lamunce mata tayi furar takai bakin shagonshi yasaida,
Ammi" tace ita som dan macace marar yarda" haka sukaita samun saɓani daga baya iyayenshi
suka shiga maganar inda suka bata hkr akan tayi umarni da abunda mijinta keso," nan tai
tamasu rashin kunya akan sunfi son É—ansu a'kanta dan sunga ita marainiyace.. Babu wanda ya kulata dan sunga a'lamar fitina take nema "washe gari da sadakinta dake
a'boye dubu biyar ta tafi ta siyo abunda xata siya washe gari tati furar ta tare da zuwa
ma�acin yan nono tasiyo nono ta mai kyau, kasancewar ta siyar da shanuwarta ta ɓoye
kud'in ta tahad'a furarta, "mahaifina na zau ne shago sai ganinta ya yi ta É—ora kwarya akai
tana asai fura. "Ranshi ya matukar ɓaci yace takoma gida kan ya zubar da fura" tace bazata
komaba saboda ba shi yabata jarinba," ganin zata batamai rai ta ta ramai mutane yakoma
shagonshi yakyaleta a'takaice haka sukaita rayuwa babu Dad'i..

Bayan shekara biyu ammi tafara kwaikwai mai masifar wahala, wanda yahanata neman
kuÉ—inta duk yanda taso ta daure kasawa tayi daga karshe haka ta kwanta jinya cikin
tausayawa mahaifina yakaita asibiti aka gano ciki ke jikinta dan wata hudu, sosai mahaifina ya
yi murna inda yana zuwa yashedama iyenshi suma sukaji daɗi sun kusa ƙara yawa..
"Yana dawowa yafita yasiyoma mahaifiyata balango mai zafi da wainar shinkafa da miyar kanu,
yakawomata yana zuwa yayi turus ganin ta a'durkushe tana yarfe hannu ga jini na malala ta
kasanta, cikin sauri ya wurgar da ledar tare da tallabo ta yace ke lfy miyasameki? kan yace komi
inna mahaifiyarshi ta faÉ—o É—akin dan taji salatinshi tana zuwa suka kama Ammi zasu fita,
idon inna yafada akan da kakken bedin dake aje da ledar gishiri tadauki a'bin ta jujjuya tare da
sakin salati tace minike gani haka hauwa'u da hankalinki zaki zubar da cikin ki saikace ba dan
halak ba..

Ammi da azabar ciwo ya ishe ta tace natsani cikin yahanani neman kuÉ—ina, ga wahala ina
sha wlh saina fiddashi a'takaice haka sukaje a'sibiti a'kacemata ciki yafita amma tayi hkr zataga
tana wahala kuma yana kumbura, har sai tayi wata ukku, a'bunka da yar karkara bata gane ba,
haka tadawo taci gaba da jinyarta sai dai abunda ke bata mamaki cikinta na kunburi kuma yana
motsi, amma datama inna magana sai inna tace yan cikin kine ke komawa mahallinsu dama
likita yafaÉ—a, haka sukaitayi har cikin yakai wata tara kasancewar bata da jiki bai waniyi girma
sosai ba, wata litinin Ammi tat ashi da mahaukacin ciwon ciki kankace mi tafita hayyacinta sai
ihu take," inna tai tsaye kanta dan tason haihuwace tazo mata "Ammi sai saukati take tana
faÉ—in mutuwa zatai, bata wani jimawa sai ga kan jariri ya turo" ita da ke zukunne batason
sadda ta kwantaba jin abu ya dan nomata inna tai saurin karasa wa wajenta tare da hankaÉ—ar
da zanan dake jikinta, saiga yar kyakyawar jaririya ta sintilo tare da kyankyara kuka, ko uwa
bata biya ba "Ammi jin kukan jariri yasata saurin tashi tana kallon inna tana kallon jaririn
fuskarta ciki da zallar tsana da bacin rai.....��
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari: ��💘��💘��💘��💘
ZAMAN TASHA
��💘��💘��💘��💘
NA UMMY AYSHA

💘��💘��💘��💘��
3�⃣1�⃣&3�⃣2�⃣

""Take jikin Inna ya É—auki rawa, taga irin kallon da Ammi ke mata cikin rawar murya "inna ta
fara faÉ—in dan Allah Hauwa kiyi hakuri wallahi likit.....

"Ammi tadakama inna tsawa tare da faÉ—in iman shuru kina babba kina karya, wato kunyi
a'mfani da duhun kaina kuka rainaman hankali ko, to kisani banyi niyyaba kuma bazan karba
ba, yarinya kuma bazan bata no-no naba, kema kina dashi zaki iya bata" takarasa tana sanya
hannu ta tura jaririyar da inna ta aje gefe cikin zane, sulbin ruwan faya da na ledar dakin
yasanya jinjirar yin suluka daga cikin zane har bakin kofa," ta kyankyara wani mugun kuka" Inna
tai kanta aguje tana É—ago yarinyar tasake yan yara kuka.
Ko ajikin Ammi saima kwanciya da tayi tana maida numfashi.

Inna" takarasa wajen Ammi da jaririyar dake wani irin kuka" tace haba dan Allah hauwa wannan
laifin mumukayi maki bawai yarin yar datazo yanzuba, kijifa a'bunda kika mata ita'da bata son
hawa batason saukaba, "likita yabamu shawarar mu ɓoyemaki dan yaga kinason cire cikin da
yayi kwari jikinki, kuma hakan hatsari ne ga lafiyaki, shiyasanya mukai maki haka.."
Agalabaice "Ammi tace kema no-no ki dakika boye saiki fiddoshi ki bata tasha, dan nikam
yanda natsani mutuwata haka natsani yarin yar nan wlh, saboda tadakusheman hanyar
arzikina, da yanzu Allah ne ƙadai yason abunda zan tara.."

Inna" zatai magana saiga mahaifina yashigo!! yana shigowa yaji kuka jaririyar, da sauri
yakaraso É—akin yana faÉ—in kai Masha Allah," shine Inna ko a'kirani" yakaraso da murnarshi
yana washe baki .
"Inna taÉ—ago idon ta Daya kan'kance tace ga a'bunda a'kasamu" Ta mika mai jin-jirar
yakarɓa!!Yama jaririyar rikon da ba dai-dai ba na take ɗiyar ta kwalla ƙara, daga nan bata
sake motsiba." cikin tashin hankali baba yamikama Inna yarinyar yana fadin Inna kallarta kamar
fa bata lumfashi? ko nono takeso ?
"Inna takarbe'ta da sauri!!anan taga kafadar yarinyar tayi wani irin mugun kunburi tabbacin
turatan da akai tasamu rauni" inna tazaro ido tana faÉ—in raunine jikinta ayi sauri a'kaita asibiti.

Baba yajuyo ya kalli Ammi data rintse idonta kamar mai bacci!!yace sannu hauwa tashi mutafi
a'sibiti kema sai adubaki kinga jinjirama bata lfy.."danshi baison miyafaru ba"

"Inna tace kyaleta ta gaji muje in kaita!! haka ta saɓi diyar dabata numfashi ta ɓoye a hijjob
suka fita, suka nufi general inda suka kaita dakin yara, Allah yasanya babban likita na nan" nan
da nan aka karɓe ta a'kafara bata taimakon gaggawa".

Bayan awa biyu "likitan yafito ranshi a'ɓace yacema baba kubiyoni office " haka suka bishi
jikinsu a'sanyaye dan sunga kallon da yakemasu bana mutunci bane.."

Suna shiga ko zama basuyiba yafara maseefa!! tare da kallon inna yace haba dan Allah
tsohuwa, taya kin girma haihuwa ta kamaki bazaki zo asibiti da wuri ba, duba da jikinki karfi
yafara yin kasa?

"Inna ta fashe da kuka tace haba likita ina ni ina haihuwa yarin yar nan" ni kaka;tace.

Likitan" yace to miyasanya mahifiya ta ba ta zoba?

Inna tai shuru" sai cen kuma tabasu labarin a'bunda yafaru .

Sosai ran baba na dana likitan yabaci!!inda likitan yace aiko sai yakai ƙara Ammi an
kwatarma jariri yar hakkinta .

Baba'na yabashi hakuri tare da cewa Ammi ba cikakkiyar mai lafiya bace, tana da matsala iska
Ammi yason inta falfado komi zai daidaita.
Dakyal suka shawo kanshi ya hakura! tare da basu do'ko-ki kar ama yarin-yar wanka sai dai
agoge jikinta, kar a'kuskura a'goyata sai dai adinga kwantar da ita," daganan yabasu
magungunan yafita yadakkomasu yarin-yar yamikama inna. "inna tace likita yanzu duk sanyin
nan haka za abarta baza asamata kayaba? "Likitan yace tabbas muddum lfy akeso tasamu" kuma tinda kinga uwarta mahaukaciyace dole
kidinga sanya ido dan zata iya sake karya ta wlh.
Baba yamashi godiya suka tafi.

Suna shiga napep baba yacema inna Wallahi tallahi Hauwa batada hankali kawai dan munga
zatayi banna mun takamata burki shikenan saikuma ta dauki tsanar yarin yar da bataji bata gani
ba.

"Inna tace sai hakuri tinda mu muka mata laifi.

Suna isa baba ya sallami mai napep suka shiga gida! ko wannansu turus yayi ganin Ammi tsaye
tana surfe, tayi wankanta tsaf kamar ba itaba..

Baba ya d'anne bacin ranshi!"yace sannu Hauwa, kinji diyar karaya ta samu a'kafada, gatanan
dan Allah bata abincinta sai kibata magunguna.

"Ammi tasakarmai wata shegiyar harara" tare da cewa lallai kam ka isa, ko yanzuma wayon
zaka sakeman, to wlh yanzu ba lokacin wannan bane, lokacine na sana'a tinda kasamu na
haifemaka, no-no kuma mahaifiyarka da kuka hada baki da ita sai tabata tinda itama naga
akwai like ajikinta.."
Baba yadauketa da mari!"yace lallai hauwa kincika tsintacciyar magen da bata mage"
mahaifiyar tawa kike fadama haka, wadda ta d'aukeki diya bata ban-banta ni dake ba,

nakawomata maganar zan aureki bata wani kawo kushenkiba, kasancewar bamuson asalinki
ba, haka ta amince na aureki na zauna dake babu ruwanta da shiga sha 'aninmu shine yau
kuma zakiyi tsaye kina gayamata magana, mike damunki?

"Hauwa tace eh naje nafada dan ni yanzu batada mutunci ko kadan a'kwayar idona," tinda tayi
tsaye ta shekoman karya to wlh duk wani kimarta yazube a idona..

Baba yasake dauketa da mari! yace toshikenan dama darajata kikeci kikoma kangon dakika fito
na sakeki saki daya..

Sosai jikin Ammi yayi la'asar kasancewar tason batada inda zata ta raɓa, amma bata nuna ba
saima cewa tai shikenan na huta wlh dan tafi nono fari, wannan yar Aljana diyar taka dai bazata
kwanta akirjinaba, tashige daki ta dakko kwarya ta juye surfenta ta koma ta zauna bakin gado ta
raf'ka tagumi.
Inna tai salati tace haba "ÆŠan nan" miyayi zafi haka? abu harda saki kamar wanda baida
addini, ai dakabarta da halinta duniyace.

Baba zayyi magana mahaifin shi yashigo yatambayesu lafiya yagansu a'tsai-tsaiye" anan inna
takoramai bayani shima jikinshi yayi sanyi baice komiba sai sallama dayayi bakin kofar dakin
Ammi, ko amsawa bataiba shima baidamuba tinda yason takan zancen, haka yatura kai
yashiga yaga Ammi zaune tazuba tagumi". "Kaka yace barka hauwa ansamu karuwa Allah yaraya ta akan sunna, najin wani labari banji
daÉ—i ba, amma a'matsayina na mahaifi awajenki ina mai haÉ—aki da Allah kiyi Hakuri basu
kyautamakiba amma dan Allah kiyi hakuri ki shayar da yarki.

Ammi namasifar jin nawin baba batace komiba!! saida baba ya daÉ—e yana lallashinta kana
tace na amince, amma da sharaÉ—in za adinga ban É—ari-biyar duk sati.?
Baba yace babu damuwa insha Allah za abaki.
Tace na amince.

Baba yamata godiya yafita yama su inna magana suma suka amince da haka nan" inna tashiga
É—akin ta mikama Ammi jinjira.
Ammi ta figi diyar har saida tasanya kuka.
Inna tace ayi hakuri abita sannu.

Ammi tawatsa mata harara! tare da fiddo nono ta dan nama jinjirar har akan hanci, da sauri inna
ta mike tana fadin waike hauwa baki da hankali ne? karfa ki manta kudi za abaki.

Jim haka yasanya ammi saita kanta taba yarinyar takama a'yunwace, ko 5mnt bataiba Ammi ta
kwace abunta tare da bankama inna ita tace kuma so ukku zan dingabata arana in kun
yarda..��
25/03/2022, 22:29 - Khadeejaht Salisu Fari:

��💘����💘��💘��
ZAMAN TASHA
💘��💘��💘����💘
NA UMMY AYSHA
💘��💘����💘��💘

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da
fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=
mo

*⚜�©J.A.W📚🖌�*

🅿�3�⃣3�⃣&3�⃣4�⃣


"" Inna tace "bakomi Allah yasanya hakan yazame mata "
Alkhairi." ta É—auki jaririyar na kuka ta tafi da ita É—akinta tabata zam-zam tasha, bacci
yaÉ—auke ta tana sauke ajiyar zuciya, haka a'kaita rayuwar har sati yazagayo baba na ya
yanka katon ragon suna a'kasama jaririya suna mufeedah" Inna bata iya kiran sunan dan sunan
tane sai taceman mufee, haka rayuwa taita tagiya har a'kayi arba'in, "Inna keta fama zaryar
asibiti har na warke" har lokacin kuma baba bai maida Ammi ba, ita ma bata bukaci hakanba,
su Baba ma basucemasu komi ba, ga sana'arta ta fura tanayi ta d'auki abunta taje tasiyar
tadawo takwashi jinjirar ta bata nono shape-shape takama gabanta."

"Mufeeda nada shekara É—aya ta yaye kanta" dan mugun tsoron Ammi take, ganin yan da take
bata nono tana zaro mata daka dakan idanunta, dalilin da yasanya tsoron Ammi mai tsanani
cikin zuciyar yarinyar" .

Inna na fahimtar Moopy ta yaye kanta itama taji daÉ—in hakan! haka taita kula da yarinyar tai
fess tai maseefar kyau, gata fara sol ga gashi irin na fulani dan daka ganta kaga mahaifiyarta,
kowa a'layin nasu sonta yake hakanan sai azo ace anzo ganin balarabiya Inna" itakuma moopy
tai ta washemasu dan bakinta tana dariya tana kallonsu, har sugaji sutafi, ko kad'an bata zuwa
É—akin Ammi itama Ammi babu ruwanta dasu."

Bayan shekara biyar.
Yakama Moopy nada shekara shidda a'kofar gidansu akwae islamiya da a'keyi tsakanin
mangariba da isha'i.
"Inna tafita da kanta taima malamin magana!! ta roki alfarmar ta nason moopy tadinga zuwa,
malamin yace bakomi sai tazo.
Haka Moopy tafara zuwa kasancewar bata tashi da hayaniya ba ga tsoro yasa babu ruwanta da

kowa, haka tamaida hankalinta sosai wajen koyan abunda yakaita cikin ikon Allah kuma tana ga
newa".

Baba ya É—auketa yakaita primary ta gwamnati a'kasa ta aji É—aya."da ta tashi inna zata
shiryamata zata fiddo ta waje shikuma baba yamata rakiya har bakin get din makaranta su

Moopy nacika shekara goma takara girma kamar yar shekara 15 dan akwaita da jikin girma
gata da tsaf'ta kullum cikin sututa take dan baba na maseefar ko ƙari, duk wai kyalle da ya yi
dinki a'kace an'barmai sai yahaÉ—ashi yan da zai bada style na daban ya É—in kama moopy,
yara har kwatance suke da É—unkunan da moopy kesawa" .
"Wata laraba da bazan mantata ba a'rayuwata"

Gari yayi luf_luf ya yi ba'ki ƙirin da hadari! na sanya kayan makaranta na nashafa mai nafito
waje in shafa powder," aguje na ruga É—akin inna n'ahau tadata" ta kallan taman wani
murmushin da narasa gane na miye!! nace Inna lfy kika tashi da murmushi haka ne?
Ta kallan tace bakomi "takwarata" kina da bukatar wani a'bune?

Nace" aa Inna ba'zanje makaranta ba, bakiga garin ba akwai hadari, kwara muyi kwanciyarmu
muyi bacci kema baccin ki keji ko?

Inna tai murmushi tace bana fatan ki zau na gida moopy, saboda kina jarabawa kuma damuna
ta nisa kina iya ganin hadarin bai sakkoba saidai yasaki iska, dan haka sanya rigar sanyinki
kiwuce kitafi kinjiko yar albarka, Allah yamaki albarka yabaki hakurin juriya da mahaifiyarki
yasanya kizama abun da Al'umma zasuyi a'lfahari dake ".
Na kalleta cike da mamaki!! nace "Ameen inna miyafaru ki ketaman wannan addu'a ne?

"Inna ta saki dariya tace yo sai wani abu yafarune yar nan" fatan nike maki, fatan Al'khairi
arayuwarki!! ta tashi zau ne ta d'auki wata sarkar wuyan ta, ta a'zurfa tasak'alaman awuya!! tare
dacewa kema ki sanya kamar yanda mahaifiyata ta sanyaman."

Na ansa jiki a'sanyaye ina kallon inna.

Inna ta tashi tare da kamo hannuna ta sanyaman naira ashirin tace gashi kisayi aya sai kicin
ko?

Nace ba Baba zaiban ba?

Tace "kedai karba wannan na inna ne bana Baba ba, Allah ya dafamaki ya haska rayuwarki
moopy na".

Nace Ameen uwata abun alfaharina .

Inna"tayi dariya tace wato kin kwaikwayi Baban ki ko?
Nai dariya nace eh mana.

"Inna takamo hannuna tayoman rakiya har soron kofar gida tana É—a gaman hannu, tace ki
ruga moopy kila ayi ruwa kinji ko.
"Nace to Inna" nashiga shagon Baba na na iskeshi yana dinki!!anan yaban hamsin yace in ruga
makarata dan yadai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login