Showing 39001 words to 42000 words out of 53627 words

Chapter 14 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt

Advertisement

09 Aug 2025

2018

wani aljanu ummi yanzun haka be wace mage ta......... wayar shi daya hango agefen fatima shine ya dakatar dashi da sauri yakai hannun shi ya dauki wayar , zamewa yayi akasa ya zauna sannan ya cire hular dake kansa ya fara fifita yana fadin Inna lillahi wa inna ilaihir raju,un.

da sauri ummi ta juya gurin haydar tace toh kaikuma meya same ka.

basu ankara ba sukaga fatima tayi waje aguje, yayin da haydar ke fadin shikenan ummi nashiga uku.

taslim ce tabi bayan fatima da gudu ummi ko tana gun haydar sai fifita take mai zuwacen ta fara girgiza shi tana fadin haydar wai meke faruwa kar ku maidamu mahaukata mana.

itako taslim ko da ta fita kofar gidan babu fatima babu alamarta juyawa tayi tana kuka.

tana shiga tace ummi ban ganta ba.

da sauri haydar ya daki bango.

cikin bacin rai ummi tace taslim wuce muje tunda bazai gaya min abin da ke faruwa ba, Allah ya baku sa,a.

ummi tana komawa barayin su ta kira daddy awaya ta fad'a mishi halin da suke ciki.

ba,a dade ba saiga daddy ya shigo d'akin su haydar ya fara shiga, samun shi yayi ya hada kai da gwaiwa.

kiran sunan shi yayi haydar, da sauri ya dago kai ya kalleshi yace taso muje.

mikewa yayi sumi sumi yabi bayan shi bayan sun shiga motar daddy sun zauna daddy ya kalleshi sosai yace

" me ya hadaka da fatima harta wuce gidana ta tafi gidan mahaifin ta?, babanta yayi min waya cewa gata tazo ko mayafi babu kuma tunda taje ta kasa mgn illah fadin haydar ne, haydar ne, me ka mata dahar ta shiga wannan yanayin ?


kasa mgn yayi ya dukar da kanshi cikin matsanan cin tashin hankali.

daddy yasake yin mgn haydar badakai nake mgn back.

nan ma shiru babu amsa


daddy yace kana nufin bazakayi mgn ba kenan?

kara dukar da kanshi yayi kasa danji yake kamar kasa ta bude ya shiga.

kallon shi daddy yayi cikin takaici sannan yace

nakula baka da gsky tunda gashi ka kasa mgn , ummi ya kira awaya tana dauka yace dauko gyalen ki kizo muje , basu juma ba ummi ta fito.

gidan alhj yusuf suka nufah.

suna shiga cikin falon fatima ta mike da saurinta tace baba gashinan yazo shine macucin dakace idan ka ganshi zaka karban min yanci na , yau gashi agaban ka.

baba ne ya daka mata tsawa sannan yace koma ki zauna .
batayi musuba ta koma ta zauna sannan ta runtse idonta tace wlh baba bana son ganin haydar arayuwata tunda na fara sanin kaina yake cuta ta.

ahankali daddy ya matso inda take yace fatima gayamin wanne irin cutar dake haydar keyi?

kowa afalon ita yake kallo , haydar ne kawai kansa ke kasa.

cikin kuka fatima tace daddy haydar shine mutumin da yayi min fyade tun da kankanin kuruciya ta.

ummi ce ta mike dafe da kirji tace lallai fatima yau na tabbatar baki kaunan haydar ai basai kinmai sharri ba, dan kina son rabuwa dashi , muyar daddy taji yana fadin

ke banson mgnr banza keda kk wannan surutun shi haydar din kinga ya musa ne.

da sauri ummi ta kalli haydar taga ya kasa daga kan shi sai hawayen dake digowa, itama kuka take tace haydar da gaske ne?

bece komai ba illah kukan sa daya karu har mutanen dake falon na iyajin sheshshekan kukan sa.

kuka ummi ta fashe dashi tana fadin nashiga uku Allah ka dauki raina na huta daganin wannan abin takaici.

mama ce ta dafah ummi tace bar kuka dan Allah ai tama kona gidan sauki.

cikin fada daddy yace wanne sauki ai babu wani sauki, Kai haydar maxa katashi kabar wajen nan tun kafin na kwashe maka albarka, kuma aure tsakanin ta dakai babu dan iska me abin kunya kawai ina takaicin ka amatsayin dana tari ya fara babu kaukautawa haydar ya tashi da sauri ya nufeshi, tun kafin ya karaso daddy ya daga mai hannu cikin tsananin tarin yace idan ka sake ka tabani Allah ya isa tsakani na dakai.

kuka ya tsaya yanayi , baba yace kai haydar jeka kawai .

cikin matsanan cin tashin hankali ya fita waje, wani haushin anas yaji yana taso mai, wai wace ma ya dauki hoton, duk shine yaja mai wannan tashin hankalin dana ke ciki, cikin zafin zuciya ya nufi mota yau anas saiya ci uban shi,zai gayamin uban waye yasashi ya dauki hoton


πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•Š
[8:33PM, 4/22/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*



79 - 81


Kai tsaye gidan su anas ya nufah yana isa ya fito daga motar ko rufeta beyi ba, d'akin anas ya tura.

anas naganin haydar abirke ce ya mike da sauri kafin ya bude baki haydar ya kaimai duka abaki, tuni bakin ya fara jini amman duk da haka bebari ba duka kawai yake aika mai , shiko anas yana dafe da bakin shi yake fadin haydar ka bari mana menene haka baka da hankali ko, mena maka, ganin da yayi haydar besan yanayi ba yasa ya fara ramawa.

mahaifiya anas ce ta fito da gudu tsakiyan su ta shiga tana fadin kai kai ku bari menene haka kuma, kai haydar anas kubari, bazaku bari ba ko saina kira maza, basuma san tanayi ba gashi gidan babu kowa me gadin ma ta aikeshi dan haka ta fashe da kuka.

ganin mahaifiyar anas na kuka yasa suka saki juna , da sauri haydar ya juya ya fita momy nakira kai haydar zo nan , ina harya tada mota.


yana shiga gida dakin ummi ya shiga ya sameta zaune kanta babu dan kwali ta kwanta akan kujera ta daga kanta sama tana girgiza kafah ga kuma hawaye nabin fuskar ta.

jikin shi asanyaye yaje gabanta ya tsuguna ya rike kafar ta yace

" ummi dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, ummi kidaina zubar da hawaye akaina"


cikin kuka tace haydar ka tashi kabani guri bana son ganin ka , dan ka bani mamaki kuma kabani kunya idan banyi kuka ba me kake son nayi, haydar ashe ka dad'e kana shiga kyauye kyauye kana lalata yaran mutane.

cikin kuka yace ummi wlh ba haka bane itama wannan tsautsayi ne, momyn su ansa ce ta aikeshi gurin yayanta , shine yace narakashi, wlh ummi muna kokarin shiga wauyen ne muka hadu da ita.

da sauri ummi tace kaikuma dayake bunsuru ne baka gani ka bari KO, ashe shiyasa lokacin da salis yanuna yana sonta kaita tsoro da tsurfa kala kala, wlh haydar bakayi ba kayi asara wlh, ni kuma kasani takaici ka shayar dani bakin ciki , inama kai aka dauke aka barmin salis


kuka haydar ya fashe dashi sosai sannan yace kiyi hakuri ummi in Allah ya yarda zan zama kamar shi.

cikin kuka ummi ke girgiza kai tana fadin bazaka taba zama kamar shi ba salis mutumin kirki ne , kwata kwata ba halin ku daya ba har yabar duniya bazan ce ga abinda yamin ba kai kuwa fah, tun kana karami kake batamin rai .

yana kuka yana rokon ummi ta yafe mai amman ina daga karshe ma tashi tayi tabarshi agurin.

tashi yayi ya koma barayin su yaci kukan shi ya koshi gashi besan wanne hali daddy yake ciki ba.

haka ya kwashe kwana biyu adaki dan ko sallah agida yakeyin ta babu ci babu sha duk yayi baki ya rame.


ummi ma zuwa wannan lokacin tayi kuka harta gaji.


daddy ne kwance a turakar sa yayin da alhj yusuf ke zaune agefen shi yana mai yajiki.

ahankali daddy yace naji sauki yusuf, Ina fatima fah?

fatima tana nan lfy tace agaida ka.

dan murmushi yayi kadan sannan yace nagode.

zuwacen ya sake cewa kaga abinda haydar yayi KO, ashe duk surutun da mukeyi kallon mu kawai yakeyi , ya maida mu shashatai.

dan dukar dakai alhj yusuf yayi kad'an sannan yace toh ya za,ayi sai hakuri kawai, itama fatiman tana cen tana cigaba da haukanta wai ita sai dai ya sake ta, nace zama tayi tabari ne.

cikin zafi daddy, yace ai indai ina raye mamana baza dawo dakin haydar ba, me zatayi da dan iska.

alhj yusuf da sauri yace yaya dan Allah ka dunga gyara kalaman ka akan haydar kai fah uba ne, kuma ai wannan abun daya faru da ne yanzon ya natsu.

Hmmm haka kake gani.

*****

ranar da haydar ya cika kwana 4 adaki hankalin ummi ya tashi dan ko motsin shi bata ji


kasa hakuri tayi taje ta samu daddy domin ta sanar dashi halin da ake ciki.

tana shiga tace alhj haydar fah bana ganin wucewan shi kuma na tambayi me gadi yace shima ya dade be ganshi ba.

da sauri ya daka mata tsawa bana son na sake jin kin kiramin sunnan haydar a gidan nan idai kina son zaman lfy, hannushi ya kad'a sannan yace fita ki bani guri.

tana kokarin fita daddy ya fara kwalawa taslim kira.

lokacin da ummi ta zauna afalo taga wucewan taslim aguje zata gurin kiran daddy, zama tayi ta dafe kai.

zuwa cen sai ga daddy ya fito taslim na binshi abaya ko sallama bema ummi ba ya fita abin shi, taslim ko zama tayi kusa da ummi.

ummi juyowa tayi ta kalli taslim tace taslim tashi kije dakin haydar ki gani lfy yake.

wasa taslim ta fara yi da yatsun ta sannan tace ummi daddy fah yace idan naje gurin yaya haydar be yafemin ba.

da sauri ummi ta dafa kirji wato alhj abin har yakai haka afili tace au haka ya fad'a miki zumunci zai raba kenan toh bazai yiyuba ainima ina da hakki akan ki, maza kije ki duba dan uwanki.

kuka taslim ta fara tana buga kafa asa tana fadin dan Allah ummi karku sani acikin wannan mgnr.

mikewa ummi tayi tana fadin kada Allah yasa kije ,fita tayi ta shiga dakin su haydar.

makure ta sameshi akan gadon shi ya rufah da bargo, tana zuwa ta yaye bargon , kallonta yayi da jajayen idon shi, ya fara kokarin tashi.

ahankali tace baka da lfy ne?

wasu safbin hawaye ne suka zubo masa sannan yace.

hakalina ne yaki natsuwa ummi damuwa yamin yawa saiyau nasan nayi rashi, ummi wlh nasan da ace salis na nan bazai gujeni ba kuma ko ya guje ne bazai wuce kwana daya ba, ummi dan Allah karki gujeni kizaman min kamar salis.

da sauri ummi ta toshe mai baki tace ya isa ya wuce haydar
tashi kaje kayi wanka.

itako fatima yau tun safe take kuka tun da mahaifinta ya shaida mata ta shirya yau haydar zaizu su tafi gida.

dan haka ta wuni tana kuka.

4:15pm mama ce ta fito daga d'aki ta kalli Fatima tace

" wai har yanzon kukan kike, menene naki na tada hankali tunda kema kisan abinda kk so ba faruwa zaiyi ba.

cikin kuka tace mama tohni wai meyasa baki sona ne ,daga ke har baba naga baku damu da abinda haydar yamin ba bayan da har cewa kukayi idan kuka samu wadda yamin haka sai inda karfin ku ya kare.

shiru mama tayi zuwa cen tace fatima dama wulakanci muke guje miki amman kinga tunda Allah yasa shine ya aikata babu wani wulakancin da zaiyi miki.

mama bata rufe baki ba fatima tace mama ai an mun wulakancin tun yaushe ummi ke fadin dan nasamu za,arufamin asiri ba dama nace bana son haydar saita gayamin irin wannan mgnr kuma duk ranar da naga ummi saina gaya mata mgnr da har ta mutu bazata manta ba.

cikin fada mama tace karki fara fatima ni bana son fitsara, ai ko baki ce mata komaiba ta daiji kunya, kitashi maza ki shirya anjima zaizo ku tafi.

muryan hjy yadikko sukaji tana fadin babu inda zata indai ina raye bazata koma gidan haydar ba me ake da dan iska, ke Fatima taso muje.

tuni murna ya kama fatima da sauri ta dauki gyalenta tayi waje

mama ce ta biyo bayan su tan a fadin hajiya dan Allah kiyi hakuri babanta ya riga yayiwa haydar waya anjima zai zo ya dauketa.

hajiya na kokarin shiga mota take fadin waye baban nata, shima zaizo ya sameni.

da daddare haydar ya nufi gidan alhj yusuf ciki da farin ciki saidai yana isa mama ta shaida mai abinda ke faruwa.

be firgita ba domin shi aganin shi kakar tasu kayan sauki ce batare da bata lokaci yayi sallama da mama ya wuce gidan.

yana sallama yaga hajiya zaune afalo, da sauri ta mike tana fadin waye nan, me ya kawo ka?

ahakali yace hajiya nine fah.

Eh ai nasan kaine mara kunya fitsararre, maza ka fitamin agida tun kafin nama uhu barawo.

dan murmushi yayi kadan ya zauna akujera.

tana ganin ya zauna ta fara kira me gadi zoka taimake ni barawo ne ya shigo min.

aguje me gadin ya shigo yana fadin ina yake.

haydar na kokarin kwanciya akujeran yana fadin baba jeka abinka rudun tsufa ke damunta.

cikin fada tace uwarka ce mahaukaciya mara mutunci kawai.

dasauri haydar ya tashi ya zauna yace karki kara.

idan nakara fah dukana zakayi?

nadai cemiki karki kara.

cikin fada tace dan ubanka kai ba sa an yina na bane kaje ka turomin uwar ka dama ina da cikin ta.

baza yayi da ita taita mgn ta gaji yaki kula ta dan yaga nema take tamai sharri.

itako hajiya jinda tayi yayi banza yasa ta dauki wayarta no mahaifin haydar ta kira yana dauka ta fashe da kuka tana fadin kazo ka fitan min da d'anka daga gida gashinan yana neman duka na



πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
[6:38PM, 4/24/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*



82 - 84



Mikewa haydar yayi yana fadin lallai hajiya abin kuma harda sharri.

yana kokarin shiga dakin hajiya yana fadin kuma baki isa ki hanani ganin fatima ba.

bayan shi tabi da sauri tana kai kai karka shigar min daki .

yana sakai dakin yaga wayam babu fatima ya waiga gurin hjy yace Ina take?

da saurinta tace tana gidan uwarka


Yana kokarin bata amsa alhj yusuf shigo.

da sauri haydar ya fara gaida shi hajiya ko tuni ta fara babatun tana fadin yauwa gara da Allah ya kawoka ka ganshi nan tun d'azon yake min rashin kunya kamar zai gogi kafada dani.

Shiru alhj yayi zuwa cen yace kai haydar tashi ka tafi .

mikewa haydar yayi cike da takaicin tsohuwar kakar su ya so ace ta bari ko ganin fatima ne yayi haka ya wuce yanata hararan hajiya.

hajiya ta kalle shi ta juya tana cewa alhj yusuf kana ganin Inda yake gallamin harara ko?

dan murmushi yayi sannan yace hajiya ai ba me shiga tsakanin ki da haydar zaku shirya ne.

tana kokarin zama tace aini mun riga mun raba jaha, auren dama tuni tace banyi , itama fatima tace batayi sai akai kasuwa.

shima zama yayi sannan yace hajiya hakuri za,ayi bawan da baya kuskure, kuma kinga yayi nadama.

ina sam bazai yuwuba haka kawai yariya yar karama da ita yaje ya dauko cutar zamani ya manna mata, babanshi da kansa ya gayamin kwanaki har gida aka biyo shi da cikin shege, dan haka idan ku baku damu da lfyr yarku ba, ni kubarmin inaso.

daidai lokacin daddy yayi sallama ya shigo, bayan ya zauna yace ina haydar din.

alhaji yusuf yace ai ya tafi tuni.

cizon lebe yayi sannan yace ai naso nazo na sameshi agidan nan , dana nuna mishi karyan iskanci yake, dan beda mutunci sai yaje yayi shaye shayen sa beje ya sauke akan mahaifiyar shiba saiya nufu tawa mahaifiyar.

alhj yusuf ya bata rai sannan yace babu abinda yasha ai nazo na sameshi , shi neman matar sa yazo, dan ninamai waya yazo ya dauketa toh kafin yazo kuma ashe hajiya taje tafi da ita.

da sauri daddy yace da izinin wa zaka bashi matar tasa?

shiru yayi zuwa cen yace nidai nafi son ta koma dakinta dan zaman beda wani amfani.

daddy yana huci yace toh bazata koma ba, ko kanason ka nunamin karfin ikonka ne akanta, toh baka isa ba dole ne nayi iko da fatima kamar yadda zanyi da taslim, dan haka ninace bazata koma ba.


cikin fara,a hajiya tace Allah yama albarka.

shiko alhaji yusuf shiru yayi ranshi bace zuwa cen yace nidai alfarma nake nema dan Allah ayi hakuri abashi mat...... cikin fada daddy yace baza abashi ba idan kana iyawa kazo ka dauketa ka bashi.

da sauri alhj yusuf ya mike ya fita fuuuuu.

duk suka bishi da kallo hajiya yadikko tace au fushin banza kai tayi komawa ne dai bazata yi ba.

shima daddy be dade ba yayi sallama ya tafi.

washegari

alhj yusuf na zaune afalon gidan sa, yana labartawa mama abinda ya faru, bayan ya gama mata bayani, tayi shiru tana nazari.

zuwa cen tace alhj ajima zanje na ruki hajiya nasan data amsa daddyn su fatima shima zai sakko.

da sauri yace a,a karkije yanzon kinayin mgn zasu fassara ta da wata munufa ninayi alkawarin bazan sake cewa ta koma ba, kuma shima haydar din zanbashi hakuri ga yanmata nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login