Showing 36001 words to 39000 words out of 53627 words

Chapter 13 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt

Advertisement

09 Aug 2025

2011

saurare shi?

sallam yayi abakin falon ya shiga


ummi na ganin shi ta daure fuska kasa yayi da kansa ya nemi guri ya zauna.

bayan ya gaida daddy be sake cewa kome ba , ummi da daddy hirar su suka ci gaba dayi .


zuwa cen daddy ya kalli agogo yace

" kai bazaka tashi kaje ka kwanta bane?

gyara zama yayi ya zauna akan gwuiwan sa yasa hannun shi daya yana sosa keyan sa.

daddy ya kara daure fuska yace ko akwai wani abu ne?


cikin sanyin murya yace daddy nazo na baka hakuri ne naga jiya fatima bata dawo d'aki ba, wlh daddy ni ban dake ta ba..... daddy ne ya katseshi ai dama baza kasan ka daketa ba tun da kasha ka koshi katashi maza kabani guri.


shiru yayi kuma yana nan a inda yake sai yau yasan fatima ta zama wani bangare na jikin sa domin ji yake yau idan daddy be bashi fatima ba , toh yau bazai iya bacci ba.


hawaye ne suka fara zubo mai daddy ya bishi da kallo take tausayin sa ya kamashi Amman sai ya dake yace wai haydar banace ka fita kabani guri bane.


Saida ya share hawayen sannan yace daddy wlh zan iya rantsewa da Qur,ani ban dake fatima ba.

shiru daddy yayi zuwa can yace jeka ka kiramin fatima.

zuwacen suka shigo yana gaba fatima na baya ummi ko tana zaune ta had'a fuska.

daddy ne yayi mgn cikin kausasassiyar murya fatima haydar yace wai be dake kiba, yace zaiyi rantsuwa ko kema zaki iya rantsuwa cewa ya mare ki?

shiru tayi tana wasa da yatsun hannun ta hankalin ta tashe.

daddy ma kallonta yake yana na zari zuwa cen ya sake cewa mamana yanaji kinyi shiru?

nan ma bata ce komi ba.

daddy ya danyi murmushi sannan yace

ga dukkan alamu mamana bata da gsky.

kuka ta fara duk suka bita da kallo, ahankali daddy yace fatima ki gayamin menene ya faru.

Cikin kuka tace ai shine yaje gurin mama ya kullamin sharri yasata ta dake ni, ta kwashe komai ta fad'a .

dariya daddy yayi sosai San nan yace toh ai baki yi lefi ba kinyi daidai ' san nan yace kai kuma kaSan bakaso me yasa ka bata kayan kace ta saka.

cikin sauri haydar yace daddy aini bance ma mama kome ba, nidai kawai nace ne abata hijjab.

fuskar daddy sake yace toh yanzon dai haydar kayi kuskure Saika kiyaye gaba, ya juya ya kalli ummi yace baki ce kome ba.

toh Alhj me zance aini yanzon haydar yafi karfi na.

nisawa yayi sannan yace nagama duku kutashi Ku tafi.

fatima ce ta fara mikewa tayi gaba tana kuka.

tana fita daga barayin su ummi kafin ta karasa nasu taga wata bakar mage, aguje ta juya tana ihu daidai lokacin haydar yafito , ji yayi kawai an cikuikuye shi duk da haka bata natsuba sai kara kwakume shi take.

rungumeta yayi sosai ajikin shi yana fidin fatima menene?

gani yayi bata da niyar mgn dan haka ya dauketa cek .

kan gadon shi ya ajeta amman sai taki kwanciya tana dad'a kamashi, tuni yanayin jikin shi ya fara cenzawa shima gadon ya hau ya jawota jikin shi sannan yace fatima menene ya baki tsoro ?

ahankali tace mage ce.

murmushi yayi sannan yace yanzo magen ce tasa kk rude haka?

bata ce kome ba ta Kara mannewa ajikin shi tana maida ajiyan zuciya.

ahankali ya fara buga bayanta ji yayi kamar tayi bacci dan haka ya fara shafata.

zabura tayi ta mike sakamakon hannu haydar da taji akirjin ta.

saida takai karshen gadon sannan ta tsaya.

shiru haydar yayi yana maida nunfashi gsky yau banzan iya hakuri ba dan tariga ta motsomin sha,awa ta ,tunanin da yayi kenan azuciyar shi , dan haka ya dauki wani filon shi me laushi ya jefeta dashi.

ihu ta kurma ta daka wini uban tsalle ta dire jikin haydar tana fadin yaya haydar dan Allah ka rakani gurin ummi


πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
[7:59PM, 4/20/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*



76 - 78



Kara menneta yayi ajikin shi sannan yace ki kwanta kawai babu abinda zai same ki.

cikin kuka tad'an ture shi tace nidai gsky kazo karakani bazan iya kwana anan ba.

daure fuska yayi sannan yace ke babu inda zani idan zaki kwanta ki kwanta ni karki dame ni.

bata kara cewa komai ba ta lafe ajikin shi, zuwa cen taji ya ci gaba da taba ta , da sauri tasa hannunta tana tura nashi daga jikin ta.

cikin raunanan niyar muryar yace ki bari mana nifah mijin ki ne.

a,a bawani miji ni gaskiya ka bari bana so.

ahankali ya sake fadin nima ai ba cewa nayi kina so ba nine nake son hakkina.

tashi tayi tsam daga jikin shi tana kokarin sauka agadon.

da sauri ya jawota yace wlh idan baki daina ba zan fita na rufeki ad'akin nan bagen ta kashe ki.

cikin sauri ta tura kanta cikin kirjin shi tana fadin nabari

ai daga nan haydar ya samu abin da yake so domin kuwa kwanciya tayi kamar me bacci haka haydar yayita wasa da ita, jin da fatima tayi yana neman ya wuce iyaka yasa ta fara kuka domin har ya fara raba ta da kayan jikin

koda yaji tana kuka be saurara mata ba illah ma karfi daya fara gwada mata dan yaga kokarin guduwa take.

Nidai danaga haydar da gaske yakeyi tashi nayi suf suf nabar musu d'akin.

ina daga bakin kofah, zuwacen na fara jiyo ihun fatima tana kuka meban tausayi tana ma haydar magiya kayi hakuri dan Allah dan darajan annabi ka kyaleni, waiyo Allah na nashiga uku , haka fatin taita kuka saida aka kira sallahn subahi sannan haydar yabar fatima, idan me karatu be manta ba haydar dama ta wannan fannin ba daga nan ba.

********

wanka ya fito ya tsaya yana karewa fatima kallo kai gaskiya yau ya kwashi garan da be taba jin irin shiba Ashe duk tarin yan matan da yake dashi duk shirme ne, fatima da yake rainawa yake ganinta kamar wata yar kauye ta fisu gard'i kallonta yayi yaga ta kwanta kamar gawa azuciyar shi yace Allah sarki Fatima anya kuwa zaki iya daukan d'awai niya ta, da wannan tunanin ya wuce masallaci,


yana fita fatima ta bude idon ta ahankali hawaye ne ya biyo baya, ahankali ta zame ta sauka akan gadon, da rarrafe ta shiga toilet.

zuwacen ta fito tana bin bango ahankali ta tsuna ta dauki duguwar rigarta dake yashe akasa ta maida jikinta domin babu kayanta ko guda daya adakin haydar , taso ta fita adakin ta koma nata amman bazata iya ba dan haka ta koma kan gadon ta kwanta.


bata dade da kwaciya ba haydar ya dawo, kai tsaye ya nufi bakin gadon yana kallonta ya gane tayi wanka amman idonta har yanzon arufe yake.

saitin kunneta yaje yace zahra shine kk koma kan gadon baki bari na gyara miki ba.

da sauri ta bude idonta dan ji tayi kaman salis ne ya kira sunan ta tana ganin haydar tamai da idonta ta rufe, ta fashe da kuka.


hannun shi yakai ya taba gushinta yace yi hakuri fatima ki daina kuka.

itama hannunta takai ta bige nashi taci gaba da kukanta.

shiru yayi na wasu dakikai yana tunani zuwacen yace


fatima dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan zai iya jawo miki wani ciwon, kinji

batace dashi komai ba haka yayita mgn har ya gaji karfe 8:00 yace fatima zantafi Office kinga lokaci ya kure.

banza tayi dashi har ya fice.

ummi naganin haydar gabanta ya fadi saboda yadda ta ganshi da ganin shi akwai abin da yake damun shi tace haydar yadai me kake yi har yanzon baka wuce office ba?

jikin shi asanyaye yace makara nayi yazon zan wuce, Ina taslim ne ?

da sauri ta fito daga kitchen tana fadin gani.

ko kallonta beyi ba yace fatima na kiran ki.
toh kawai tace a takaice.

koda taslim taje fatima bata daina kuka ba kuma bata ci abinci ba haka ta gaji da tambayan ta meya sameta, amman babu amsa.

ahaka har aka kwashe kwana biyu yadda aka aje abincin fatima haka ake dauka, haydar ko yayi lallashin har ya gaji dan haka abin ya fara bashi tsoro.

ranar da suka cika kwana 3 ahaka da safe haydar yana zaune afalo taslim ta shigo, gaidashi tayi ta nufi dakin fatima.

muryan haydar taji ya kira sunnanta ta dawo ta tsaya ,cikin sanyin murya yace

taslim wai fatima batacin abinci ne kwata kwata ko akwai wani abun da take sone daban.

tace yaya wlh nima ba yadda banyi da ita ba, ta fadamin abin da take so na dafa mata, amman ko mgn bata min.

cikin mamaki yace kina nufin kema bata miki mgn?

kaita daga. yasake cewa ummi ta sani?

eh nagaya mata tace wai babu ruwanta.

Shiru yayi zuwa cen yace shike nan jeki.

tana shiga haydar ya mike gurin ummi ya nufah.

tana zaune afalo tana amsa waya kusa da ita yaje ya zauna ya daura kanshi akafadar ta.

tana gama wayar ta waigo ta kalleshi tace yadai na fatima meya same fatiman taka kwana 2 ?

cikin shagwaba yace ummi bayan kinsan halin da muke ciki amman baki kula muba.

d'an murmushi tayi kad'an tace aini baku sakani aciki ba, sai kanwarka ka kira.

murmushi yayi kadan sannan yace

toh ummi ai ta kasa dole sai kinsa mana baki.

tace toh inajin ka menene ya faru?

saida yayi kasa dakai sannan yace ummi laifi na mata kuma na lallasheta taki kulani.

da saurinta tace toh yanzon me kk son ayi?

dagowa yayi suka hada ido da ummi sannan yace ummi hakuri zaki bata.

kallon shi tayi sosai sannan tace ikon Allah ashe akwai lokacin da zanga wannan ranar, haydar ashe taurin kanka na banza ne tunda gashi lokaci 1 mace na shirin susutaka, wai yau kaine ke rokon aba fatima hakuri.

mumurshi yayi sannan yace nimafah bansan yadda akayi na samu kaina ahaka ba, ummi idan fatima na cikin damuwa sainaji duk banajin dadi

itama tana murmushi tace aini tuni na lura da haka, saidai fani gsky yadda fatima take nuna kiyayyar ka haushi take bani.

da sauri yace ummi ki daina jin haushin ta, in Allah ya yarda Wata rana zata bari.

mikewa ummi tayi tace toh shikenan haydar tunda kaji ka gani tashi muje naga ginbiyar taka.

suna cikin tafiya ummi ta kalli haydar tace haydar bari na baka wata shawara kaga wannan kananan kayan kadaina saka su karinka saka manyan kaya kamar yadda salis keyi, d'aga kanta tayi ta kalli gashin kanshi tace haba haydar ai ko nice fatima bazan soka ba jifa inda ka tara gashi saikace bishiya, wannan gashin naka bazai rasa wari ba.

da sauri ya tintsere da dariya ya tura mata kan yace haba ummi shinshina kiji kullum fah sainaje an gyaramin shi.

da sauri ta kauda fuskarta tace bazan shinshina ba, kaje ka askeshi kawai.

yana dariya yace toh shikenan ummi zan aske

da haka ummi ta tura d'akin fatima ta shiga haydar nabinta abaya.

taslim ko na zaune agefen fatima tana danna wayar ta yayin da fatima ke kwance agado tayi ruf da ciki.

ummi ta kalli taslim tace har yanzon dai zaman kuramen kuke?

taslim tace toh ummi taki magana.

karasawa bakin gadon ummi tayi ta zauna sannan ta dafah bayan fatima tace fatima

can ciki ciki ta amsa, ummi ta sake cewa tashi ki zauna.

ahankali ta fara kokarin tashi haydar ko nacen gefe kamar munafi hannuwan shi cikin aljihun shi.

baya ta zauna ummi ta kalleta sosai taga har tadan fad'a tace.

fatima wai meke damunki ne haka me yayi zafi?

nan danan hawaye ya fara zubo mata zuwacen ta fashe da kuka.

da sauri ummi ta jawota jikinta ta rugume tana fadin ya isa.

daker ummi ta shawo kan fatima tayi shiru , shiko haydar tunani yake azuciyar shi wannan wacce irin yariya ce.

ummi ta sake cewa haba 'yata kidaina daukan abu da zafi haka, haydar ya fad'amin shine ya miki laifi , kisan abin da nake so dake daga yau idan ya sake bata miki rai kizo ki gayamin duk hukun daya dace dashi ni zanmai karki kara tada hankalin ki, kinji ?

ahankali ta daga kai.

ummi tace yauwa ko kefah yanzon dai mgnr ta wuce ko?

murya cen ciki tace eh.

toh Sakko kici abinci.
sakkowa tayi ummi da kanta ta zuba mata .

kwana biyu haydar ya dan samu sauki gurin fatima dan yanzon bata harara shi kuma yanaji tana mgn da muta ne


fatima ce zaune adakin ummi suna hira ummi tace fatima yaushe zaki fara girki ko kunfi son kuyita cin namu.

ta bude baki kenan zatayi mgn haydar ya yayi sallama ya shigo.

tana daga kai ta kalleshi,tsaye yake cikin manyan kaya wad'an da suyi matukar karban shi ta zabura aguje ta nufeshi kamshi turaran da taji shi ya tabbatar mata dawa cewa ba salis bane dan bada wannan turaren yake amfani ba tsugunawa tayi ta fashe da kuka.

ummi ma hawaye ne ke zuba a donta, shima kansa haydar d'in fatima ta bashi tausayi

juyawa yayi ya koma barayin su cikin tashin hankali yana zama ya fashe da kuka.

fatima ko bataso haydar ya fita ba ji tayi tana balakin son ta hada ido dashi dan idan ta kalleshi ji take kamar taga salis dan haka cikin sauri ta mike ta nufi dakin su.

tana shiga ta samu haydar zaune afalo idon shi jawur.

zama tayi akujeran dake kallon nasa ta kure shi da ido tana hawaye.

mikewa yayi yazo gabanta ya tsuguna ya fara share mata hawayen yana fad'in baxan kara saka irin wannan kayan ba fatima, da nasan cewa zaku shiga wannan yanayin har kuna zubar da hawaye ke da ummi da banyi ba, cire hular dake kansa yayi aje agefe.

da sauri fatima takai hannunta ta dauka ta daura mai akai tana fadin karka daina yaya wad'an nan kayan sunfi maka kyau.

ya bude baki zaiyi mgn wayar shi tayi kara, ciro wayar yayi a aljihun sa ya duba sannan ya aje agefen fatima, mikewa yayi ya fita da sauri yana fadin Ina zuwa fatima.

harya kule fatima na kallon shi , yana fita ta juyar da kallon ta gawar da ya bari da sauri ta dauki wayar tana share hawaye, ta shiga dannawa.


*Toh masu karatu gadai fatima ta dauki wayar haydar KO me zai faru ?*



πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
[8:59PM, 4/21/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*



79 -80



Tsinta kanta tayi dason kallon hoton dake wayar dan haka ta fara dubawa.

dayawa daga cikin hotonan haydar ne shi da salis wani suna dariya wani kuma kaga sun ware kamar zasuyi danbe, kallo take tana hawaye tana tuna soyayyar da salis ya nuna mata, kai da ace har yanzun salis na nan tohni yar gata ce, da wannan tunanin ta fita daga gurin .

wani gurin ta sake bud'awa innalillahi wa inna ilaihir raju,un shine kallaman daya fara zuwa bakin ta domin kuwa hotunan haydar ne birjik tare da yanmata kala kala cikin shigar lalacewa da nuna tsaraici domin kayan dake jikin su dashi gara babu, kwata kwata babu kyan gani.


take taji wani haushi ya taso mata wani bacin rai taji wadda rabon da taji irin shi tunda akace za,a had'ata aure da haydar.


hawaye taji suna zubu mata, da sauri tasa hannunta ta shafo ta kallah, menene wannan ? tabayar da tayiwa zuciyar ta kenan, kardai ace son haydar nake, dakuwa naci amana, naso wa kuma dan bani da hankali sai naso kani.

mike wa tayi ta aje wayar har ta juya sai kuma ta dawo ta sake daukan wayar wani bangaren ta sake shiga hotun haydar ne shida anas zuwacen ta ?fara cin karo da wasu hotuna da suke neman dauke numfashin ta. bakinta bude ido bude duk sun firfito waje take kallon hotun tabas wannan itace lokacin da take amsa sunan daniju, wanda ko ke kanta haydar ne gashi nan danne da ita akan kujerar motar yana kokari yage mata riga take sunan da anas ya kira haydar dashi kwanaki ya fado mata BIG BOY

take ta kwallara wani kara saida gidan gaba daya ya amsa, jitayi kafafuwan ta bazasu iya daukan ta ba dan haka ta fadi kasa timm.
,
aguje su ummi suka shigo ita da taslim haydar nabin su abaya.

a gaban fatima suka tsuguna suna kokarin dagata suna tambayan ta menene.

shi ko haydar fadi yake ummi yanzon haka mage ta gani kisan matsoraciya ce.

fatima KO hannu ta daga tana kuka take nuna haydar tana fadin shine wlh haydar ne shine wanda ya cuceni , wlh shine ummi, shine gashi nan agaban ki Allah ya tonamai asiri.

haydar sakin baki yayi yana kallon fatima


ummi ko gani take kamar fatima aljanu gareta.

dan haka tacewa taslim kiramin daddyn ku ya samo mana malami amata rukiya.

Matsowa haydar yayi yana fadin babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login