Showing 48001 words to 51000 words out of 53627 words
Chapter 17 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
95 - 96
Lokacin da haydar ya shiga dakin fatima samunta yayi tana bacci kuma dagani tanajjin dadin baccin dan haka bazai iya tashinta ba.
Ahankali ya hau gadon daf da ita ya kwanta ya manne da jikinta, zuwa cen yasa hannu ya rugumota jikin shi, yaso ya hakura ya barta tayi baccin ta Amman ina bazai iya ba, hannun shi ya fara wasa dashi ajikin ta.
da sauri tasa ahanun ta tarike nashi ta tura hannun nashi baya sannan tace yaya meye haka?
Hannun shi ya Kara daurawa ajikinta ahankali yace dan Allah fatima kiyi hakuri ki bani hakkina, wlh amatse nake.
da sauri ta tashi ta zauna tace nidai gaskiya kayi hakuri bazan iya ba.
Shima tashi yayi ya zauna yace bazafah ki iyaba kikace , ko bakisan hukuncin matar da mijinta ya nemeta taki amince bane?
da sauri tace nasani aini bani da lfy ne, kuma ni ina ganin kamar ma cikin be fita ba, dan duk abinda nakeji ban daina jiba, har yanzon.
Daure fuskar shi yayi sanna yace ya fita mana toh ya za, ayi ki daina ji, bayan har yazon mgni kike sha, hannun shi ya kara kaiwa jikinta yace fatima kiyi hakuri mana amatse nake kuma inada matsala idan kk hanani cikina zai iyayimin ciwo.
Mikewa tayi ta fara buga kafa, tana fadin nidai gaskiya ka rabu dani bacci nakeji.
Abin da fatima bata sani ba wannan abin da take kara riketa haydar takeyi.
Zuba mata ido yayi kamar me kallon TV
ganin da yayi ya fara shiga yanayin da indai fatima ta hanashi zai iya shiga Matsala, dan haka muryar shi ciki ciki yace toh ya isa haka, na hakura , zoki kwanta.
Cigaba tayi tana fadin toh kazo ka tafi dakin ka mana.
Daure fuska yayi sannan yace anan zan kwana, kuma wlh idan kika batamin rai, dasafe zanje nagayawa baba abin da kk min.
Tanajin ya fadi haka ta tsaya cek kamar me tsonron kar wani abu ya kamata ta fara hayowa gadon nesa dashi ta kwanta, ba dadewa kuwa bacci ya kwasheta.
Cen cikin barcin ta tafarjin nishin haydar wasa wasa taji abin na kara yawa , dan haka ta bude Ido ganin shi tayi cen gefe ya kudundune yana rike da ciki, dasauri ta matsa daf dashi tace yaya menene ?
babu amsa sai wani irin numfashi daya ke fitarwa gawani uban zufah dake karyo mishi, kalmar shice ta fado mata idan kika hanani cikina zai iyamin ciwo.
Kallon shi tayi sosai sannan tace ciyon cikin ne?
Hawaye ta fara gani suna zubo mishi, yana wani irin kamar numfashin shi zai dauke, dan haka itama kuka ya kwace mata, acikin kuka take fadin bari nakira ummi.
Da sauri ya rike hannun ta yana girgiza mata kai, kuka take sosai domin abun ya balakin bata tsoro.
Cikin sauri takai hannun ta kan cikin haydar gurin dataga yana rikewa ta ture hannun shi tanayin kamar yadda taga yanayi, hawayen ta na sauka akan ruwan cikin shi.
Sun dade ahaka daga cen ta fara jin kamar numfashin na sauka ahankali, dan haka ta gyara zamanta sosai ta dauki kanshi ta daura akan ciyar ta, taci gaba da abin da take.
Zuwa can taga bacci ya dauke shi dan haka ta bishi da kallo gani tayi harya fada yayi zuro zuro.
dan haka ta fajin haushin kanta dan ta dau hakkin haydar.
Ahaka fatima ta kwana bata runtsaba dan gani take kamar data cire hannun ta zai tashi, kiran sallan subahi ne ya tadashi, da sauri ya miki ya kalli fatima, da sauri ta dukar dakai, yace fatima bakiyi bacci ba, baki da hankali ne?
Kanta akasa tace banajin baccin ne.
Shiru yayi sannan yace toh tashi kiyi sallah saiki kwanta.
Wanka yayi sannan ya wuce masallaci bayan ya dawo ya samu fatima zaune akan sallaya, wuceta yayi ya isa bakin gadon ya fara gyarawa, da sauri fatima ta miki ta rike zanin gadon.
Haydar yace sake mana zan gyara miki ne saiki kwanta.
Tace kabarshi zan gyara da kaina.
Yace a,a nizan gyara
Sakimai tayi dan yanzun batason yimai musu
Yana gamawa yace toh zoki kwanta.
Kokarin cire hijjab takeyi dan haka haydar ya nufi fita.
Harya fara tafiya fatima takira shi ahakali tace yaya.
Dawowa yayi ya tsaya yana kallon ta kanta akasa tace ya jiki?
Murmushi yayi sannan yace naji sauki.
Yana kallon fuskarta yaga hawaye na zubowa.
Hannu yamika ya kawota jikin shi yace meyasa kike kuka ?
Cikin kuka tace dan Allah kayi hakuri ka yafemin jiya na jawo maka......hannun shi yasa ya rufe bakin ta sannan yace karki damu ai dama cen inayi, kitaya ni rokon Allah, ya yayemin.
tace eh amman dai ai nice sanadi, tunda ka fad'a tun kafin hakan ta faru
dariya yayi sannan yace toh naji ya wuce yanzon kije ki kwata, inason zaje na shirya kinga lokaci na wucewa.
haka fatima ta wuni da tunanin haydar dan gsky ba karamin tausayi ya bata ba zama tayi tai tagume tace a zuciyar ta toh yanzun da haydar ya mutu ya rayuwa ta zata kasance, afili tace Innalillah wa ina ilaihir raju,un.
haka taita tunani daga baya ta wuce dakin ummi acen ta wuni har yanma ita da taslim.
.
shima haydar daya dawo barayin ummi ya shiga sai dare ummi tace su tafi dakin su.
fatima bata jira haydar ba gaba tayi tana shiga ta fada toilet wanka tayi ta gyara jikin ta.
zama tayi tana jiran shigowan haydar amman har kusan 10:30 be shigo ba , zuwa cen taji motsin shi afalo dan haka ta mike, ta dauki karamin hijjab dinta ta saka ta nufi falon .
koda ta fito falo baya nan, dan haka ta nufi dakin shi, sallama tayi ta turo kofar yana kwance akan gado yana danna waya, ya dago ya kalleta ya saki murmushi.
Alama yayi mata da tazo ta zauna a gaban shi, tana zama ya jawota jikin shi ya rungume dan bakaramin dadi yaji ba dayaga ta kawo kanta da kanta.
*******
washegari fatima sai kusan sha biyu na rana ta fitoh dakin haydar, kwana 1 kawai da tayi adakin haydar harta fita hayyacin ta , tun daga wannan ranar fatima bata sake yinkurin hana haydar hakkin sa ba, koda sonawa zai nemeta bata hanashi, saidai idan bayanan ta zauna taita kuka, kuma dataji dawowar shi gabanta ke faduwa.
ahaka har suka kwashe wata 5 fatima sai ramewa take,gashi al,adanta shiru har yanzon, kuma cikinta nata kara kunbura harda wani motsi yake , bata manta lokacin da tacewa haydar har yazun fa al,dan ta be dawo ba kuma gashi cikin ta sai girma yake , kodai cikin be fita bane yana nan, amman sai yace mata ya fita mana ,ai kece bakishan magani akan lokaci shiyasa yake kumbura miki ciki ,nan gaba ma har mutse zai dinga miki.
tagumi tayi tana kallon cikin zuwa cen ta fara tuno lokacin da haydar ke magana saitaga kamar yanayi ne yana boye darigar sa, dan haka ta fara tunanin anya kuwa ba wayo suka shirya mata ba, hanya kuwa ciki yana fita ta fitsari, afili tace koda yake likitan yace sabon magani ne, toh amman meyasa cikina yake girma kamar na me ciki kuma meyasa yaya haydar yake boyewa yana dariya, mikewa tayi tare da fadin nasan abinda zanyi.
barayin ummi ta nufah acen ta samu haydar dan haka ta wuce dakin taslim, ta bar haydar da ummi suna hira .
Tana shiga samu taslim zaune ko zama bata yi ba tace taslim zo na aikeki gurin ummi amman karkice nice na aiko ki.
tace toh anty babba inajinki.
fatima tace dan Allah kije ki tambayo min ummi wai dagaske ne ciki yana fita ta fitsari?
taslim ta zaro 😳 tace ni wlh bazani ba, kina ganin dazon daga Mubarak yazo gurina ummi tace wai tunda aure nake so nace mishi ya turo, yazun kuma sai naje mata da zancen ciki?
shiru fatima tayi zuwa cen ta sake cewan dan Allah taslim kije mana.
Taslim rufe ido tayi tace bafah zani ba, idan kin matsu kitashi muje na raka ki.
Ba yadda fatima ta iyi Dan haka tace muje.
suna fitowa haydar ya daure fuska kamar baya dariya sabo da ganin taslim.
zama sukayi guri daya kamar munafukai kowa bakin shi na motsi.
ummi ta kallesu tace fatima yaya meya faru?
shiru tayi kamar bazata yi magana ahankali tace ummi wai ciki yana fita ta fitsari?
dasauri haydar ya dago ya kalli fatima sannan ya harari taslim
Cike da mamaki take kallon fatima tace wanne irin ciki ne kuma yake fita ta fitsari ke waye ya gaya miki?
haydar ta kalla sannan tace yaya haydar ne yacemin cikin ya fita ta fitsari.
dariya tayi irin tasu ta manya tace wane cikin ne ya fita bayan wanda yake jikin ki, tsokanan ki yakeyi, ta juya barayin haydar tace kaikuma ya zaka dinga firgita ta ai irin wannan sai kasa jininta ya hau
Daure fuska yayi sannan ya kalli taslim yace ke tashi kibar nan gurin.
Gudu gudu ta mike har tana tuntube ya juya ya kalli ummi yace ummi kisan meye?
🕊🕊
Mmn Yazeed
🕊🕊🕊
[8:12PM, 5/6/2017] Fadila Lamido: 🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
🕊🕊🕊
*_Tsuntsu Me Wayo_*
🕊🕊🕊🕊🕊
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
97 - 98
Ban sani ba saika fad'a, ummi ke fadin haka cike da haushin haydar.
Dariya yayi sannan yace ummi toh ki sallame fatima sai muyi maganar.
Tace bazan sallameta ba idan ma bazakayi mgnr ba ka barshi, ta juya gurin fatima tace ke kuma ki kwantar da hankalin ki karya yake miki, cikin ki na nan lfy kalau, kema ban da shashanci irin naki ina kika taba jin ciki ya fita ta fitsari.
Turo baki tayi tana hararar haydar tana fadin wlh ummi shine yace min wai yanzon haka akeyi.
Juyawa ummi tayi ta rufe haydar da fada, dan haka ya warware mata kome.
Bayan ummi ta gama sauraran haydar komawa tayi kan fatima , daga karshe ta koma nasiha tare da lallashin ta da ta kwantar da hankalin ta.
Hawaye take sharewa, haydar ko ido ya zoba mata.
zuwa cen ummi tace toh kutashi ku tafi dare nayi.
Fatima bata tsaya jiran haydar ba gaba tayi , tana tafe yana binta abaya.
Suna shiga barayin su haydar ya rike fatima, yace
Wai fushi kk yi dani?
Rufe idon ta tayi domin ko ganinshi bata sonyi.
Saidai azuciyar ta koda taji cikin nanan batajin tsanar shi, saima wani sabon so da takeyiwa cikin, abin da kawai yabata haushi rainin wayon da su haydar suka mata.
Muryar haydar ce ta katse mata tunanin dayake fadin , fatima banayi haka da niyar yaudararki bane, naga awannan lokacin bani da kalmar da zan rarrashiki da ita ne idan ba wannan ba. amman kema inda kina da wayo zakisan baxan dauke ki da hannu na nakaiki acire miki cikin ba, ni yanzon abin da nakeso dake ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu nan bada dadewa ba salis karami zai iso.
Murmushi ta saki har zuciyar ta taji dade kanta tasa akasa saiga hawaye yana zubo mata.
Haydar ya kalleta yace toh meye abin kuka kuma, ke babu damar ayi maganar salis saiki kama kuka, kina nufin kin fini sonshi ne?
Cikin kuka tace ban fika son shiba amman nafika kaunar shi.
nan danan fuskar haydar ta cenza, yace toh naji mubar maganan kawai.
Shiru tayi zuwacen ta sake cewa kaima wlh idan har zaka fadi gaskiya kasan har son na shima na fika.
Mikewa yayi cikin daga murya yace nace miki kibar mgnr ko bazakibar ta bane, juyawa yayi har ya fara tafiya ya bude kofar zai fita sai kuma ya dawo idon shi jawur cikin fada yace ai dole ne ki fini sonsa tunda tare aka hayfeku, kuma ni banson kina sonsa ba sai ranar da kika....... kasa karasawa yayi ya dafa kanshi da duk hannuwan shi guda 2 sannan ya girgiza kai ya fita.
Binshi da kallo tayi itama hawaye ciki da idonta azuciyar ta tace kodai haydar kishi yake da yaya salis idan ba haka ba yaya za,ayi daga mgn sai ya dau zafi haka, mikewa tayi tabi bayan sa ta sameshi adakin shi ya hada kai da gado.
Karasawa tayi ta dafa shi ko d'agowa beyi ba, tace yaya dan Allah da gaske kk yi sunnan salis zaka saka min idan nahaihu?
Wani sabon haushi ne ya kamashi domin da ace fatima tasan zafin dayake ji azuciyar shi idan tayi maganar salis da bazatayi ba, badan yanajin kunyan kar ummi tace yana kishi da d'an uwan shiba dasai ya fasa mata baki wata kila daga lokacin zata kiyaye shi, dagowa yayi da jajayen idonshi ya kalli fatima sannan yace
Ai badan ke zansa sunan ba dan kaina zan saka dan d'an uwa nane tare muka kwanta acikin mahaifiyar mu aka kuma hayfemu tare kuma mukasha nono tare muka girma ,dan haka duk wata kyauna dazaki nuna kina mai a bayan nine, dan ku su ummi da sukai sular zuwan mu duniya bazasu fini kaunar shi ba, bare ke.
Cikin fatima cike da dariya tace meda wukar, yaya daga wasa saika dauki abu da zafi aini wasa nake maka ni son da nake mishi ma ai dane, Allah ya huci zuciyar ka.
Fuskar shi adaure yace ke kika sani, fita kibani guri.
Kalon shi fatima tayi damamaki azuciyarta tace wannan wani irin kishi gareshi dan tunda suka shirya baya taba bari su raba shinfida amman shine yau harda koran ta.
Mikewa tayi da niyar ta fita adakin amman saitaji batason yin hakan saboda tafi kowa sanin halil haydar idai ko har ta fita adakin yau bazaiyi bacci ba wata kila ma sai yayi ciwon ciki, dan haka ta fara kokarin hawa gadon, gefen shi ta kwanta ta daura kanta ajiki shi.
Ahankali yace wai banace ki fita bane?
Itama daure fuska tayi sannan tace nifa bazan fita ba, kwanciya zanyi, kuma ai nace maka kayi hakuri.
Baza yayi da ita ya rufe ido dan haka fatima ta zuba hannunta duk 2 cikin rigar shi tana mai cakulkuli tun yana fadin meye haka bari mana, har ya fara dariya, daga karshe ya shiga ramawa.
Tun daga wannan rana suka kara kullewa kamar sa ahad'iye juna sabo da yadda suke nunawa junan su so, tun da fatima ta gane haydar baya son tana mgnr haydar ta daina yi agaban shi, saidai data tuna salis zata shiga daki tai kuka dan son da takeyiwa salis ajininta yake.
Ayanzun haka dai cikin fatima ya isa hayhuwa girma yayi sosai dan yanzo fatima zama da ker dashima haka, wani zubin idan fatima ta kalli cikin tsoro yake bata, daidai wannan lokacin ne aka tsaida bakin taslim ita da mubarak dane agun kawar ummi , kuma mahaifin shi hamshakin me kudi ne, ba,asa rana me tsayi ba sati 2 kawai akasa
Fatima bataji dadin saranar da akayi a wannan lokacin ba dako tafiya daker takeyin ta, dan haka lokacin da daddy yake sanar musu ta fara kuka.
Daddy ne ya lura da ita dan haka yace mamana yayadai?
Goge hawayen ta fara sannan tace daddy da anbari bayanzun ba, kagani fah bana iya tashi
Dariya sukayi sannan haydar yace ton idan kina iya tafiyar me zakiyi?
Bata kulashi ba ta sake cewa daddy dan Allah abari sainan da wata 1.
Fukar daddy cike da dariya yace mamana ki cire mgnr biki azuciyar ki mu fatan mu Allah ya rabaku lfy, wata kila ma kafin bikin ,kiga kin haihu, ina fatan dai duk kunsaya kayan haihuwa?
Kan fatima akasa tace nima ban sani ba.
Daddy ya waiga ya kalli ummi sannan yace kuna nufin ba,asai komai ba har yanzun?
Murmushi tayi sannan tace alhj komai yana hannu itace dai bata sani ba.
yace toh yayi kyau ina fatan dai komai 2 kuka saya?
ummi ce ta bashi amsa eh , daddy yace to ai yakamata ku nuna mata ko akwai wani abun da take so ba,a saya ba.
Ummi tace toh mijinta ne yace kar anuna mata.
Fada daddy ya farawa haydar akan me zaice kar anuna mata, daga karshe yace maza aje anuna mata.
Dakin ummi suka shiga ummi ce ke nuna wa fatima kayan haydar na zaune agefe.
Gani tayi komai 2 ake daukowa, daidai da bahon wanka ma guda 2 ne, dan haka tace ummi meyasa naga kayan komai 2?
Haydar ne yayi sauri yace, sabo da idan wani ya lalace ad'ako wani.
Harara fatima ta galla mai sannan tace ni bakai nake tambaya ba.
Ummi ta kallesu tayi murmushi sannan tace fatima haydar boye miki yake, likita yace yan 2 ne acikin ki, dan haka ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu lfy lau zaki hayhu.
Watsi tayi da kayan dake hannun ta tafara kuka.
Ummi ta bita da kallo nan danan hankalin ta ya tashi ,zuwacen ta mike tayi daki, saboda tsoro amai ta dinga kwarawa, haydar na biye da ita,