Showing 12001 words to 15000 words out of 53627 words
Chapter 5 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt
eh tace ahankali.
Shirye shiryen biki nata kankama acikin wannan family ummi shiri take sosai komai ta gama had'awa da dan ganci na
fatima dan yazun bikin saura sati 2 kuma har wannan lokacin salis be kawa yariyar da zai aura ba dan haka akabar batunsa dama alhj yusuf ne yaso ahad'a amman daddy tuni yabar zancen haydar kamar yadda yace ya cireshi acikin 'ya'yan shi.
haydar ne zaune shida abokin sa anas a harabar gidan su anas sigari kawai yake sha daya shanye wani sai ya kara d'akkowa
anas ne ya lura haydar ya kusa shanye kwalin sigarin dauke ragowar yayi sannan yace big boy waikai meke damun ka?
yana fesar da hayakin dake bakin shi yana fadin fatima.
Hmm daman aikai ya kamata ka aureta sai da fad'a maka kace bahaka ba sai yanzun da lokaci ya kure zakace wani fatima, kana nufin sonta kk?
niba sonta nake ba amman ni banason salis ya aure ta, saboda Ina matukar sha,wan yariyar dan haka nafison wani daban ya aure ta, yanzun fah duk tarin 'yan matan dana ke dasu basa birgeni Dana rufe ido fatima nake gani
tsaki anas yayi cikin takaici yace toh yanzon dai saidai kayi hakuri garama ka cireta aranka dan tafi karfin ka.
tsaki shima yayi yamike yabar wajen tundaga ranar haydar ya zama kamar mara lafiya baya mgn sosai besan me yake damun shiba.
Yau sauran kwana biyu biki dan haka yan baki sun fara isowa fatima da taslim sai shirye shirye sukeyi daddy na cikin farin ciki.
ummi ce ad'aki zaune da kawayenta suna kallon akwati ta zuwa cen saiga salis rike da hannun haydar ummi ce ta kalli haydar tace meya kawoka?
haydar ne yace ummi ninace yazo yaga akwati.
cikin fad'a tace to tunda kai ka kirashi saika shirya amsan da zakaba babanku idan yadawo ya samu haydar agidan na, mikewa tayi tafita adakin ahankali mutane dake dakin suka fita daya bayan daya.
haydar ya tsuguna gaban akwati yana dariya yana duba kayan zuwace yace brother kaya sunyi saidai kacika hijjab dayawa aciki.
murmushi salis yayi sannan yace ra,ayina kenan.
anagobe daurin aure da daddare salis ya shiga har d'akin su fatima fatima ya hango manne jikin gado ta rufe fuskarta gefe ko kawayen su ne zaune suna hira sunna ganin shigowan shi suka bar daki gaban Fatima yaje ya tsuguna dariya yayi sosai sannan yace zahara duk tsoron auren ne haka,
batace kome ba ya sake cewa zahara dan Allah ki kwantar da hankali bana son ganinki cikin wannan halin .
cikin kuka tace yaya kwata kwata banajin dadi, azuciyata taki natsuwa nayi nayi in natsar da ita nakasa gani nake kamar wani abu zai faru.
da sauri yace babu wani abu dazai faru zahara sai alheri kiyi tunani dakau kila akwai abinda yake damunki.
shiru tayi zuwacen tace yaya jiya nayi mafarkin na auri yaya haydar.
dariya yayi sannan yace ni daman nasan akwai abunda yake damunki dan Allah ki cire tsanar haydar azuciyar ki, kuma kidaina wannan tunanin mafarki ne kawai insha Allahu gobe warhaka burin mu ya cika saida muyi fatan cikawa da imani, haka haydar yayi ta rarrashin fatima harta fara dariya.
washe gari aka tashi da shirye shiryen dauren aure tun 12:00 bakin daddy suka fara halara kofar gidan ya ciki makil da jama,a sai hada hada ake salis ne ya fito cikin babban riga farare kal yayi matukar kyau waige ya farayi yana neman haydar amman ko alamar shi begani ba dan haka ya shiga neman no barshi tsaki yaje sabo da layin kwata kwata yaki shiga ya koma cikin abokan sa ya tsaya ranshi bace zucen yaga guri ya kara cika duba agogo yayi yaga karfe 12:43 cikin sauri ya nufi motar shi wani abokin sane yabi bayan sa yana fadin inakuma zaka?
yana kokarin barin wajen yace tahir yanzon zandawo zanje na dauko haydar ne.
gidasu anas ya nufa yana tura kofar anas dakin yaga haydar zaune ya tasa sigari cikin zafin zuciya yace haydar kana nufin bazaka halarci daurin aure na bane?
bece komaiba dan haka yasa hannushi ya fara jawoshi bayan motar ya turashi anas ma ya shiga sun kamo hanya kenan kiran daddy ya shigo wayar salis cikin fada yace kana ina?
yace daddy ganinan zuwa naje dako haydar n.......
salatin dasu anas kiyine ya dakatar da shi yana d'ago kanshi yaga Wata babban mota ta nufosu salis yayi kokarin kaucewa amman Ina tuni motar ta fara watan gaririya akan titi.basu kara sani me ya faru ba
zucen haydar ya bude ido ganin shi yayi kwace cikin jini muryan salis yaji yana kiran sunan shi daker yaja kashi ya kalli gurin kwance yaganshi jini na bulbulowa ta cikin shi jan jiki ya fara har ya isa gaban shi ya kama hannun shi babu abun yake kira banda zahara zuwace yayi kalmar shada be kara motsawa ba haydar ya farajan shi duk da shima ajikace yake.
karan wata mota yaji yana kallon gurin yaga daddy da baba yusuf suna tahowa, gurin salis suka nufa daddy ne ya daga hannun shi yace ya innalillahi wa inna ilaihir raju,un Allah ya karbi abun saππ
πππ
[10:02PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_
πππ
πππ
πππ
πππ
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πππππ
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
*Gaisuwa da fatan alheri gare ku*
*Zainab bobbo adamawa*
*Yahancy gombe*
*bilkisu muhammad*
*xeeshata*
*mmn abdulnasir*
*hajju lokoja*
*Fatyma*
*harda wadan da bankira suna ba inajin dadin yadda kuke nuna sayayyar ku ga wannan lbr*πππ
38 - 39
Tattara su akayi gaba daya aka nufa asibiti har anas.
nan danan wannan mummunan lbr ya isa kofar gidan daddy dake cike da jama,a yan daurin aure.
itako ummi daddy ne yamata waya ya gaya mata amman be gayamata rasuwan salis ba yadaice gasu sun wuce asibiti.
hakalinta ne yayi mummunan tashi dan ta dade tana munanen mafarkai akan salis da haydar
itako fatima tun safe ta kulle kanta ad'aki tana kuka dan haka ummi tace abarta kar agaya mata abari aga abinda allah zaiyi.
haka gidan ya zama jugun kowa da abin da yake sakawa.
zuwacen daddy ya sake kiran ummi.
tana ganin kiran daddy gabanta ya fadi tana dauka tace
" alhj yaya abin da sauki kodai na taho ne kuna wanne asibiti?
" cikin jarinta irin na maza yace basai kinzo ba muma gamunan tahowa kuma nasan ke musulma ce kin yadda da kaddara mekyau da marakyau.
kuka ta fara tace alhj kardai kacemin mutuwa sukayi?
"a,a haydar yanan araye sai dai ya samu karaya acinya"
kara rushewa tayi da kuka sannan tace salis fah ?
cikin shashshekan kuka yace sai dai muyi hakuri hafsat salis ya koma ga mahalicin sa.
ummi jitayi kafafuwan ta bazasu iya daukanta ba take ta yar da wayar ta shiga fadin innalillahi wa inna ilaihir raju,in.
jin salatin da ummi keyi gaba daya hankalin mutane yadawo gurinta ummi tana kuka tana gaya musu salis ya rasu.
fatima dake kule ad'aki kunnen ta ya fara juyo mata koke koke da sauri ta bude kofar ta fito idon ta jajur bisu tayi da kallo daya bayan daya kowa afalon kuka yake.
" cikin tsawa tace menene wani abu ne ya faru?
Wata yayar ummi ce ta jawo ta jikinta nasiha ta shiga yimata sannan ta gaya mata rasuwan salis.
jitayi kamar an buga mata guduma hawaye kuwa kamar an bude fanfu cikin kuka take fadin nashiga uku na lalace meyasa yayimin haka jiya fah yace min yau tare zamu kwana shine kuma zai tafi ya barni kai ban yadda ba be mutu ba,nasan shi me cika alkawari ne.
daidai lokacin daddy ya shigo mutane ne abayan sa dauke da gawar salis d'akin ummi aka shigar dashi da sauri fatima ta kutsa ta cikin mazan ta shige d'akin ,hannu tasa ta bude fukar shi girgizashi tayi tana kuka tana fadin yaya katashi dan Allah.
daddy na tsaye abayan ta ya kasa cewa komai alhj yusuf ne ya d'agota yace fatima salis yariga ya tafi ki daina mai kuka soyayyar da zaki nunamai yanzun shine kibishi da addu,a
wani hawaye ne me dumi ya zubo mata alhj yusuf najanta tana waiwayen gawar salis.
bayan angama gyara salis aka kira ummi tamai addu,a cikin kuka tamai addu,a albarka ko tasamai babu adadi, daddy ne yace akira fatima suyi sallama.
kamota akayi dan ayanZon bata iya tafiya saitin kunen shi taje babu meji metake cewa.
daddy ne yoga abin nata bana kare bane dan haka yace afita da ita
haka sunaji suna gani aka tafi da salis gidan sa na gaskiya
fatima ko mawa d'akin su tayi ta fashe da kuka kallon hannuta tayi taga zanen fulawa wani haushine ya kamata tunani yadda zatayi ta goge lallen ta fara
dan haka ta fara buga hannun ta ajikin bango tuni kyawawan warwaro dake hannun ta suka lanlan kwashi.
dada ce tahigo taga halin da Fatima take ciki da sauri ta riketa tana fadin meye haka fatima saikace ba musulma ba, dan Allah dan darajan annabi ki dainawa bawan Allah nan kuka.
suna cikin haka salamatu mahaifiyar fatima ta shigo, fatima ta daga kai tace mama kin ga haydar ya kashe salis KO ?
cikin tsawa mama tace waye yace miki haka, kifah dai na irin wannan surutun ki kama bakin ki, haydar d'in da kike mgn shima yana cen akwance bemasa inda yake ba.
cikin kuka tace
" ai dama bazai san inda yake ba kuma da ikon Allah shima mutuwa zaiyi"
cikin zafin zuciya mama ta nufi gurin ta gadan gadan
ππ
Mmn Yazeed
πππ
[10:36AM, 3/31/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_
πππ
πππ
πππ
πππ
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
πππππ
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
17-20
Taslim ce ta zaro ido dan tunda suke da haydar betaba kaita unguwa ba fatima ko idonta ne ya cika da hawaye dan ko muryar haydar taji sai cikinta ya murd'a
salis ya lura da halin da suka shiga ci dan haka yace haydar ai inaga kubar tafiyar nan sai gobe dan nalura zahara batajin dadi sosai
ysaki haydar yayi ya bar wajen.
da dadare anas ya kawowa haydar ziyara har dakin ummi yaje ya gaisheta domin shi ba bako bane agidan adakin ya samu salis dan haka ya dan zauna suna hira bayan sundan taba hira anas ya nufi dakin su haydar
hira suka barke acikin hiran tasune haydar yake cewa anas akwai wata yariyar kanin daddy da ta dawo gidan nan tana min kama da yariyar nan da na huta da ita a wannan kauyen.
dariya anas yayi sannan yace kace dai yariyar nan tasamu matsayi tunda gashi har gizo take maka
yatsuna fuska yayi sannan yace bahaka bane anas kaima nasan idan ka ganta zaka gane tsananin kamar su.
suna cikin haka taslim tashigo da kula ahanun ta ta ajiye agaban anas tace gashi injji ummi.
hayadar yace ke ina wannan yariyar ?
wacece fatima?
tsawa ya daka mata dan ubanki ina tambayanki kina tambaya na, koni sa,an wasanki ne
yamusha fuska tayi sannan tace toh ai ban gane wacce kake mgn bane idan fatima ce tana dakin ummi.
atakai ce yace jeki kirata
zuwa cen saigata ta shigo tare da sallama tsugunawa tayi akasa dan balakin tsoron haydar take ta bude baki ahankali tace yaya haydar taslim tace kana kirana.
be dago ya kalleta ba cigaba yayi da danna wayar shi cikin kasaita ya bude baki yace ke baki ganin bakone bazaki gaida shiba nifa ba salis bane wlh saina zaneki dan ni bana daukan raini.
shikuwa anas har yanzon be kalle fatima ba illa cin abincin da yake dan haka lokacin data gaida shi ya dago kai ya kalleta.
sakin abincin yayi ya fadi kasa ya mike da sauri
ganin inda anas ya rude yasa shi yace ke tafi kiba ni guri
tana fita anas yace wlh itace kai anya kuwa yariyar nan ba aljana bace.
musu suka fara haydar na fadin kamace yayin da anas yace itace.
ganin da anas yayi musun yaki karewa sai ya bude wayar shi ya bude hoton da ya dauki yariyar lokacin tana kwace amotar haydar zuwa yayi daf da haydar yanuna mai photo.
karban wayar yayi ya shiga kallon hoton, wayar shi ya jawo ya tura sannan yayi delete na wayar anas cikin tashin hakali yace zanyi bincike akanta.
shiru sukayi gaba dayan su kowa da abinda yake sakawa.
aranan haydar yaje gurin kakar su yadidko tsayawa yayi ahanya yasai mata lemo dan yasan idan tana shan Orange saitai zuba zance.
murna tayi sosai daganin haydar da kansa ya yanka mata lemon ta fara sha tana zubo masa wani lbrn daban .
yana ganin haka ya fara saita mata hanya niba wannan ba hajiya nifa gaskiya fatima na bani tausayi ace yariya kamarta tana jss1 waisu toh garin su ba asa yara makaranta ne?
cikin takaici tace ai bari kawai haydar baban ta ma yana bakin cikin wannan abu amma ai uwarta ce sula haka kawai ta dauki yariya ta kaita kauyen kayayau ko mota bata iya shiga.
daukan wani lomon yayi yamika mata sannan yace kina nufin kauyen babu mota.
saidata matsa ruwan lemon abakin ta sannan tace inafah suka ganta ai wanda ma ya keta mata mutuncin ta badan garin bane dan ita saima allokacin tasan sunan mota nandai ta kwashe komai ta gayawa haydar.
haka haydar ya baro gidan cike da tashin hankali, yana fadi azuciyar shi lallai nayi abin kuya yazon wani hali
iyayen mu zasu shiga idan sukaji nine na aikata Wannan abun gashi yaji kakar tasu sai fadan mugayan kalamai take ga Wanda ya aikata ma jikarta wannan aika aika
gidan su anas ya nufa ya labarta masa cin matsanan cin tashin hankali ya mike yace
" toh yanzon sai ka aureta kawai haka shine abinda ya dace saida nace maka karka taba ta amman kakiji kaga da duk haka bata faru ba"
cikin zafin zuciya haydar yace dallah gafara ina neman mafita kuma zakawo min wata magana daban banason irin wannan.
toh shi kenan tonda bakason agayam gaskiya amman ni bazan kara zuwa gidan ku ba dan idan daddyn ku yasamu wannan lbr harni saina shiga ciki.
aniyarka ta bika in Allah ya yadda daddy bazaiji wannan maganar ba kuma kai nifa bazanma bari taci gaba da zama agidan muba saina san haryar da zanbi tabar gindan nan wlh dama tunda naganta agidan mu naji natsaneta gashi naga salis kaman sonta yake yi amman nasan abinda zanyi.
shiko anas kallo yabi haydar dashi yanason yaba abokin nashi shawara amman yasan yanzon sai su kwashi yan kallo dan haka yayi gum.
*********
bayan haydar ya koma gida dakin su ya nufa ya cire kayan dake jikinshi sannan ya dauki jallah biyar salis ya saka ya haye gado ya kunna sigari yana sha
zuwacen salis ya shigo yakali hayadar yayi tsaki cikin takaici ya fara magana wato dan iskanci ma yanzon har adakin ma shan sigari kake toh wlh abun ya isa haka bazan iyaba zan fadawa daddy.
kashe sigarin yayi ya mike yaje har gaban salis sannan yace baka isa ka hanani shan sigari adakin nan ba kai Ina hanaka kayi wani abu dakin nan ne ? , abin da kaga dama kakeyi dan haka baka isaba wlh.
toh naji ban isaba amman me yasa
ka saka min daya daga cikin rigar da nake sallah da ita bayan kasan ni bashan sigari nake ba kuma ina kyamar me Shanta
Kara matsowa yayi dafda shi yace
" nasa din kayi abinda zakayi "
ran salis ya bacci idon shi yayi jawur kallon haydar kawai yake zuwa cen yayi kwafa sannan yace wlh darajan ummi kake ci dan banason na tayar mata da hankali amman ba komai wata rana zanyi maganin kka
yana fadin haka haydar ya kamo wuyar rigar shi yahada ya matse yace
" dan Allah idan kacika kai jarumi ne kayi maganina yau basai wata ranba"
rufe ido salis yayi zuwacen yace sakeni.
cikin daga murya yace bazan sakeka ba
salis gani yayi haydar na neman kure shi dan haka yasa hannun shi ya hankad'a shi ya fadi kasa cikin sauri ya bar dakin.
falon daddy ya nufa ranshi bace, aciki ya samu ummi bayan ya zauna ummi tace
lfy kuwa yanzon ka fita kana dariya kuma naga kadawo ranka bace wani abu ya faru ne?
a,a babu abinda ya faru ummi amman dai inason dan Allah araba mana daki nida haydar
daddy ya dago da sauri ya kalli shi, sannan yace kunyi fada ne?
kanshi akasa yace bahaka bane kawai dai nafison ne na zauna ni daya
murmushi