Showing 51001 words to 53627 words out of 53627 words
Chapter 18 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt
zuwacen ta rike ciki.
Hankalin haydar ya tashi, wayar shi ya daga ya kira ummi ya gaya mata halin da fatima ke ciki, ba a dau lokaci ba saigata ta iso.
Ummi naganin inda fatima keyi tace wa haydar yi maza ka fito da ita muje asibiti.
Arikece haydar ya wawusu fatima yayo waje da ita
ππ
Maman yazeed
πππ
[10:01PM, 5/7/2017] Fadila Lamido: πππ
πππ
πππ
πππ
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πππππ
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
*Na sadaukar da wannan page din ga iyalan πmarigayi*
_Alhj Lamido Bello_
*Godiya ta mussaman ga yan group d'ina Fadila lamido novels ,bansan taya zan nuna farin cikina akan yadda kuke bani goyon baya ba, gasky Ina alfahari daku wannan page din bazai isa nakira sunan ku ba saidai nace Allah ya barmu tare*ππ
Jinjina gareku
Faty Afreen
Cwtjiddah
zeezee
Billy galadanci
Ummi jafar
hussaina ubandiya
zeenasir
Aisha big girl
Yar gatan hudah
Yar mutan yudil
Hamagee
Fatima umar abdallah
Nana zee
Meenat tabacco
Anty sa,adatu
Marubutanπ mu kenan
99 - 100β
Kai tsaye asibiti suka nufa, daka kalli haydar kasan hankalin shi tashe yake, bayan anshiga da fatima dakin haihuwa ummi ta kalli haidar taga duk jikin shi yayi sanyi, dan haka ta matsa ta dafah shi tace ya haka kaida zaka mata addu,a Allah ya rabasu lfy kuma saikabi ka tada hankalin ka.
yace ummi ina tausayin fatima sai nake ganin kamar bazata iya hauhuwan yara har guda 2 ba.
Ummi tace Hmmm haydar kenan in Allah ya yarda lfy zata haihu lokacin dana haifeku nima ai kamar fatima nake .
Shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa.
Zuwacen ummi tace haydar tashi kaje gida ka karbo min sako gurin taslim.
tashi yayi badan ransa yaso ba.
yana kokarin shiga gidan ummi ta kira wayar shi, cikin sauri ya dauka.
Muryan ummi yaji cikin fara,a tana fadin Alhamdulillah fatima ta sauka.
Alhamdulillah ya fara furtawa komawa yayi ya fada mota batare da ya karbi sakon da ummi ta tura shi ya karbo ba.
Yana isa dakin da fatima take ya nufah ya samu ummi da mama zaune adakin.
cike da fara,yake kallon su, mama tayi dariya sannan ta mike ta mikamai jaririn dake hannun ta, sannan ta dauko dayan ta sake mikamai , rugume su yayi ya kuresu da ido ganin yaran sunyi kama dashi sosai, idon shi cike da hawaye yace
Mama ina hasan din yake?
Ummi ce ta mike ta taho gurin ta leka fuskar yaran sannan ta nuna mai hassan din tana fadin kaga yadda yaran nan suke kuma haka kuke sak lokacin da na haife ku, naso ace salis nanan aka haifi yaran nan.
Nan danan haydar ya fara kuka, daidai lokacin da dada ta fito da fatima daga toilet ahankali take tafiya fukarta kumbure da gani taci kuka ta gaji.
Ummi ya mikawa yaran ya karasa gurin fatima ya rike mata hannu ahankali cikin rada yace sannu fatima.
Wani sabon hawayen ne ya sake zubo mata.
Haydar yasake cewa meyasa kk kuka fatima, keda zaki farin ciki kuma saiki na kuka.
cikin kuka tace na tuna da yaya salis ne.
Yace karki damu muyi hakuri kuma ai gawani salis din Allah ya bamu.
********
Washegari suka koma gida cike da farin cike, agidan suka samu yadikko lokacin da haydar yaga yadikko abarayin su daure fuska yayi yace meya kawoki gida na, ko burin kunya kk zoyi.
Itama daure fuska tayi tace tafiya da fatima nazoyi dan aguri na zatayi wanka.
Haydar yace wlh baki isaba babu inda zata ina hauka ne zan baki matata ki tafi da ita.
Dariya sukayi gaba daya dakin.
Da daddare haydar na xaune adakin ummi saiga anas da mahaifiyar shi sunyi sallama adakin ummi.
Bayan sun gaisa da ummi anas yazo ya mikawa haydar hannu suka gaisa sannan anas yayi mishi barka
Kunyace ta kama haydar dan haka ya rike hannun anas sukayo waje, hakuri ya bashi akan abinda yaje har gida ya mishi.
Anas yace aini daman ban rikeka azuciyata ba, amman abinda ya bani mamaki watannin danaga ka share baka nemeni ba, shine yasani tunanin kodai haryanzon kana kullace danine.
Dafashi haydar yayi sannan yace baka ba ne , naki zuwa wajen kane saboda ina tunanin indai naje gurin ka zan iya komawa harka da nakeyi ada , wadda bazanso hakan ya kasance ba, dan ni yanzon bana shan komai kuma natsaya ga matata ce kadai, bana bin mata ayanzo.
Anas yayi murmhshi sannan yace aini ma tuni na daina banayi yanzon bani ma da lokaci yazon tare muke kasuwanci da abban mu duk inda ya saka kafa ina biye dashi, kuma nima ayanzun inada iyali watan na uku da aure.
Haydar ya zaro ido sannan yadan daki anas yace shine kayi aure baka nemeni ba.
yace yazan nemeka bayan ka shareni yanzon badan naji lbr nazoba ai bazaka nemeni ba.
Haka suka cigaba da tattaunawa saigurin karfe 10 suka bargidan.
Ranara suna ta zagayo yaran sukaci sunan salis da haydar, suna sukayi sosai domin nuna farin cikin so da wadan yaran da Allah ya basu, kowa acikin wannan family daya bude baki cewa yake Allah yama wadan yara albarka.
Shiko haydar azuciyar shi cewa yake Allah yasa duk su biyo halin salis.
Itako fatima kirikiri take nuna tafi son salis din dan koda yaushe shi zaka gani ahannuta idan ma nono ne salis din take fara bamawa sannan tabawa haydar.
Yadikko ce ke zaune da Fatima, ita ke kula da ita.
Satin fatima 2 da haihuwa akai bikin taslim , zagewa fatima tayi akayi komai da ita dan idan ka kalli Fatima baxakace mejego bace tayi d'as da ita komai nabikin tare akayi da ita kai amarya ne kawai haidar ya hana fatima zuwa.
Haka zaman su yaci gaba da kasancewa cikin farin ciki da annashuwa gashi yau kwanan fatima 34 , suna zaune ita da yadikko daki haydar ya kira wayar fatima , bayan ta dau suna gama mgn saita miki ta nufi fita.
Hajiya tace ina zaki kuma?
Tace inazuwa hajiya yanzon zan dawo yaya ne yake kira na, bata jira me hajiya zatace ba tayi gaba.
Hajiya taita zaman jiran dawowan fatima shiru har 12:00pm gashi yaran suntashi sai kuka sukeyi , haka hajiya taita lallashin su amman inna kwana sukayi suna kuka haka hajiya ta kwana babu bacci.
Da asuba ummi taji kukan su yayi yawa dan haka ta shigo har dakin fatima, samon hajiya tayi tsaye sai faman jijjigasu takeyi .
Tace hajiya meya same su ina uwar su take.
Hajiya tace tana gurin mijinta cen ta kwana.
ummi batace komai ba tamika hannu ta karbi yaran ta wuce barayin ta dasu.
Sai shidda da rabi na safe ta shigo tana sanye da jallabiyar haydar ta reke kasan da hannun ta saboda ta mata yawa
Hajiya na zaune akasa tana hada kayanta kallonta fatima tayi sosai sannan tace inakwana.
Amsawa hajiya tayi ba yabo babu fallasa, fatima ta kalli gadon ,ganin shi tayi babu yaran kuma gashi ta kasa tambayan ta ina yaran suke.
Zama tayi tai tagumi .
Zuwacen hajiya ta gama hada kayan ta tamike ta yafah mayafin ta bude kofar zata fita.
Mikewa fatima tayi tabi bayanta tana fadin hajiya ina zaki?
Atakaice tace gida zani tunda naga kiyi arba,in harkin koma gurin miji.
Bata rai tayi kamar zatai kuka tace bacci ne fah ya kwasheni ban sani ba dan Allah kiyi hakuri,
Ko sauraran ta batayi ba ta fita adakin.
Kukun fatima ne ya fito da haydar yana tambayan ta menene yafaru.
Bayan ta gama gayamai yaja tsaki yace toh ai gwara ta tafi daman ta takuramin.
Bin bayan hajiya sukayi suka sameta afalon daddy su ummi na bata hakuri tana fadi wlh gida zani bazan zauna ba, yara basu da kunya mezan zauna nayi.
Haydar ko ganin inda yadikko take fada sai dariya yakeyi, daddy yakalle shi yace kai fita kaba mutane waje.
juyawa yayi ya fita fatima ko sai share hawaye takeyi.
Daddy yamike ya zubawa fatima yaran sannan yace wa hajiya muje na kaiki gida.
Suna fita fatima ta kalli ummi tace wlh ummi yaya ne yahanani......
Ummi ce ta katse fatima da fadin ni ban tambayeki ba ai mijin kine bakiyi laifi ba, hajiya tana guje miki wahala ne tanason yaranki suyi kwari tukuna.
Haka fatima ta wuni sukuku saboda damuwar tafiyan hajiya.
Da daddare ummi ta kira haydar fada tamai akan barin yaran da sukayi gurin gajiya san tace batason ta karajin kukan su dan idan taji kukansu kuma har taga da ganga akabarsu toh fa zata dauke fatima harsai ta yaye yaran Zatw dawo dakin ta.
Wani sabon amarci suka bude wadda ba,ayishi daba, haydar dakansa yana tunanin wai ya kayi ya zama haka akan fatima ji yake kamar ita kadaice mace aduniya.
Lokacin nata tafiya yanzo yan biyu watan su 7 kuma a daidai wannan lokacin ne fatima ta fara rashin lfy duk abinda taci saita amayar dashi ta dade tanajin cenji ajikin ta, dan haka yau data wuni amai abin ya dame ta, haydar na dawowa ta tareshi da zance.
Haydar karame ya dauka yasashi akan ruwan cikin shi sannan yace mekika ce?
Bakinta cike da miyau tace aikaji abin da nace.
Haydar ya daga ya daura mata akan ciyarta sannan ya dauki salis ya rugume yace to kodai ciki ne.
Cikin muryan kuka tace nima abinda nake zargi kenan , dan Allah kazo muje asibiti aciremin.
Haydar yace kina hauka ne kinga karki sakemin mgnr zubar da ciki kisan dai yanzon ba da bane , idan bakina son ranki ya baci bane karki sakemin wannan maganar.
Mikewa tayi ta wurga mai haydar , cikin sauri ya saka hannun shi ya rike shi kuka ya saka saka makon firgita da yayi.
Fatima ko waigowa batayi ba , dan haka haydar ya kule.
Lallashin shi ya shiga yi amman yakiyin shiru, zuwacen salis ma ya fara, haydar ya rasa ya zaiyi dasu, ummi ce taji kukan yayi yawa ta shigo. salis ta gani tsaye ya hada su duk biyun yana jijjigawa.
Ummi ta mika hannu ya saka mata haydar tace ina mamar su?
Idonshi jawur yace ummi ki rabu da ita kawai zanje na sawo musu madara.
Tace akan me wani abune ya faru?
Cikin fada yace kibarta kawai yariyar nan ta riga ta raina ni kwata kwata bata ganin mutun ci na.
ummi ta fara kwalawa fatima kira.
Saigata ta fito sanye da hijjabi , ummi ta bita da kallo tace fatima yazaki bar yara kinaji suna kuka, idan ma wani abu ne ya faru tsakanin ki da haydar aisu babu ruwan su , dan Allah karki kara hucewa akan su, zoki karbe shi kibashi nono.
Mikewa tayi ta wuce ummi taje gaban haydar tace kawo shi.
Daure fuska yayi sannan yace bazan bayar ba kije ki fara bawa haydar shine yake kuka.
Itama cikin fada tace ai yafishi jin yunwa kawai dan dai yana da hukuri ne kabani shi, waccen dama rigimar tsiya gareshi.
Ummi tace wai meyasa kuke irin wannan ne, ke rabo dashi kizo ki karba haydar din.
Tana kuka take shayar da haydar karami, haydar ya bita da kallo yace ummi kinga arin abin da fatima takemin ko, wlh banbanci take nunawa atsakanin su wai ita tafison haydar danayi magana saitace wai ai yana da hakuri ne, ummi metake nufi da wannan mgnr Zagina takeyi kenan, ita har yanzun akwai wani abu azuciyar ta, wlh....
Ummi tace ya isa haka haydar kubar mgnr ni banason fitana ta juya gurin fatima tace waike fatima me yasa kike haka, wadan nan yaran dukka fah yaran ki ne, kefah kikayi yunkuri kk haifesu meye naki na nuna banbanci atsakanin su, kinason su taso da rabowar kaine, yazun kamar wannan dan yaron har kin fara mai shedan rashin hakuri, nasiha ummi ta mata meshiga jikisa
sannan tace tabawa haydar hakuri.
Ahankali ta fura kayi hakuri.
Be amsa ba ya juya yace ummi, yanzon ma ciki gareta shiyasa take fushi .
Zaro ido tayi tace ciki, toh fah, ai shikenan Allah ya rabasu lfy
Haydar ne ya amsa da ameen.
Washegari ummi ta shirya kai fatima asibiti haydar ne kejan motar, bayan sunje suna kan hanyar su ta dawowa Fatima taga wata me gasa masara tace
Ummi kalli me masara ummi tace zakici ne?
Tun kafin ta bada amsa haydar ya tsaya agurin da kanshi ya sauka.
Zuwacen ya dawo ya mikawa fatima masarar sannan ya shiga motar ya zauna yace ummi kin gane yariyar cen.
Kallon yariyar tayi cike da mamaki ta bude murfin mutar ta fita,
Tana zuwa gurin tace ke ina yaron da kk hayfa?.
Cikin firgici ta mike tace hajiya dan Allah kiyi hakuri wlh daman cen bani da ciki kawai nayi haka ne dan haydar ya aure ni dan allah ki gafar ceni.
Tsaki ummi taja sannan ta koma motar suka kama hanyar gida.
Haka rayuwa taci gaba da kasancewa agidan daddy cikin kwanciyar hankali shekaran yan biyu daya suka fara yawo ko ina lokacin fatima cikinta wata shidda, kuma adaidai wannan lokacin ne taslim ta haifi yarta mece wacce akasawa sunan Aisha, wantan Aisha 4 fatima ta sake haihuwan yan biyu mace da namiji.
Murna ce ta kama haydar har ya fara cika bakin wai shekara me zuwa yan uku fatima zata haifar mai.
Alhj yusuf da daddy kuwa ji suke kaamar sunfi kowa farin ciki, bare kuma hajiya yadikko me fatan tara uguwa guda,
Ayanzun salis karami yana gun ummi shiko haydar yana gurin mama, dan haka fatima daga ita sai yan biyun ta .
Ranar da fatima tayi arba,in haydar ya biyo ta har daki da bukatar shi, ke meme taki amincewa domin tsoran karta dau ciki,amman saida haydar yasan yadda yayi ya mata dubara suka lula.β
Alhamdulilah
Sai mun hadu a sabon novel din na nagaba
~*_Ta mishi illah_*~
Maman yazeed
07014197556
πππππππ