Showing 21001 words to 24000 words out of 53627 words
Chapter 8 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt
haharara shi tayi sannan tace hakuri me kayi?
murmushi yayi sannan yace Zahara Kenan kisan fah kina da kyau kuma na kusa najiki jiki na
kawai daurewa nakeyi karne abin kunya, kasa ya yayi da murya ya Kira sunanta sannan yace kifah shirya dan idan mukayi aure akan kirjin ki Zan rinqa kwana.
hannuta tasa ta rufe ido dan be saba mata irin wannan maganganun ba.
murmushi yayi sannan yace zahara idan akace yau andaura mana aure bakaramin farin ciki zanyi ba, bare kuma na ganki ad'akina, Hmmm ranar zan nuna miki irin son da nake miki zan tarairayeki kaman kwai zan nunamiki soyayyar daba kowane namiji bane zai iya nunawa matar sa irin saba.
kwashewa fatima tayi da dariya sannan tace amman dai yaya sambatu kk KO, wannan irin cin buri ne haka.
shima dariya yayi sannan yace aidama nasan bazaki gane ba amman ahankali zan ganar dake, mikewa yayi tare da fadin bari naje gurin haydar.
dasauri tace bayan zon ,muka dawo ba shine har zaka koma, ni wlh natsani haydar d'in nan banason ganin shi.
shima cikin mama ya kalleta yace zahara kinada hankali kuwa d'an uwan nawa, meya miki ?
toh yaya ai shima ya tsane ni dan haka nima bana sonshi wlh ko sunan shi aka kira gaba na faduwa yakeyi.
kallon ta yayi cikin ido yace xahara haydar ba tsanar ki yayi ba haka halinsa yake nima bakiga yana min ba, kuma dan Allah ki yafe masa karki kara kullatan shi aranki kinga d'an uwanki ne , koya miki wani abu kijin haushi toh ki gayamin ni kuma xan faranta miki rai kinji KO ?.
da sauri ta d'aga kai .
yace kin yafe masa?
eh tace ahankali.
Shirye shiryen biki nata kankama acikin wannan family ummi shiri take sosai komai ta gama had'awa da dan ganci na
fatima dan yazun bikin saura sati 2 kuma har wannan lokacin salis be kawa yariyar da zai aura ba dan haka akabar batunsa dama alhj yusuf ne yaso ahad'a amman daddy tuni yabar zancen haydar kamar yadda yace ya cireshi acikin 'ya'yan shi.
haydar ne zaune shida abokin sa anas a harabar gidan su anas sigari kawai yake sha daya shanye wani sai ya kara d'akkowa
anas ne ya lura haydar ya kusa shanye kwalin sigarin dauke ragowar yayi sannan yace big boy waikai meke damun ka?
yana fesar da hayakin dake bakin shi yana fadin fatima.
Hmm daman aikai ya kamata ka aureta sai da fad'a maka kace bahaka ba sai yanzun da lokaci ya kure zakace wani fatima, kana nufin sonta kk?
niba sonta nake ba amman ni banason salis ya aure ta, saboda Ina matukar sha,wan yariyar dan haka nafison wani daban ya aure ta, yanzun fah duk tarin 'yan matan dana ke dasu basa birgeni Dana rufe ido fatima nake gani
tsaki anas yayi cikin takaici yace toh yanzon dai saidai kayi hakuri garama ka cireta aranka dan tafi karfin ka.
tsaki shima yayi yamike yabar wajen tundaga ranar haydar ya zama kamar mara lafiya baya mgn sosai besan me yake damun shiba.
Yau sauran kwana biyu biki dan haka yan baki sun fara isowa fatima da taslim sai shirye shirye sukeyi daddy na cikin farin ciki.
ummi ce ad'aki zaune da kawayenta suna kallon akwati ta zuwa cen saiga salis rike da hannun haydar ummi ce ta kalli haydar tace meya kawoka?
haydar ne yace ummi ninace yazo yaga akwati.
cikin fad'a tace to tunda kai ka kirashi saika shirya amsan da zakaba babanku idan yadawo ya samu haydar agidan na, mikewa tayi tafita adakin ahankali mutane dake dakin suka fita daya bayan daya.
haydar ya tsuguna gaban akwati yana dariya yana duba kayan zuwace yace brother kaya sunyi saidai kacika hijjab dayawa aciki.
murmushi salis yayi sannan yace ra,ayina kenan.
anagobe daurin aure da daddare salis ya shiga har d'akin su fatima fatima ya hango manne jikin gado ta rufe fuskarta gefe ko kawayen su ne zaune suna hira sunna ganin shigowan shi suka bar daki gaban Fatima yaje ya tsuguna dariya yayi sosai sannan yace zahara duk tsoron auren ne haka,
batace kome ba ya sake cewa zahara dan Allah ki kwantar da hankali bana son ganinki cikin wannan halin .
cikin kuka tace yaya kwata kwata banajin dadi, azuciyata taki natsuwa nayi nayi in natsar da ita nakasa gani nake kamar wani abu zai faru.
da sauri yace babu wani abu dazai faru zahara sai alheri kiyi tunani dakau kila akwai abinda yake damunki.
shiru tayi zuwacen tace yaya jiya nayi mafarkin na auri yaya haydar.
dariya yayi sannan yace ni daman nasan akwai abunda yake damunki dan Allah ki cire tsanar haydar azuciyar ki, kuma kidaina wannan tunanin mafarki ne kawai insha Allahu gobe warhaka burin mu ya cika saida muyi fatan cikawa da imani, haka haydar yayi ta rarrashin fatima harta fara dariya.
washe gari aka tashi da shirye shiryen dauren aure tun 12:00 bakin daddy suka fara halara kofar gidan ya ciki makil da jama,a sai hada hada ake salis ne ya fito cikin babban riga farare kal yayi matukar kyau waige ya farayi yana neman haydar amman ko alamar shi begani ba dan haka ya shiga neman no barshi tsaki yaje sabo da layin kwata kwata yaki shiga ya koma cikin abokan sa ya tsaya ranshi bace zucen yaga guri ya kara cika duba agogo yayi yaga karfe 12:43 cikin sauri ya nufi motar shi wani abokin sane yabi bayan sa yana fadin inakuma zaka?
yana kokarin barin wajen yace tahir yanzon zandawo zanje na dauko haydar ne.
gidasu anas ya nufa yana tura kofar anas dakin yaga haydar zaune ya tasa sigari cikin zafin zuciya yace haydar kana nufin bazaka halarci daurin aure na bane?
bece komaiba dan haka yasa hannushi ya fara jawoshi bayan motar ya turashi anas ma ya shiga sun kamo hanya kenan kiran daddy ya shigo wayar salis cikin fada yace kana ina?
yace daddy ganinan zuwa naje dako haydar n.......
salatin dasu anas kiyine ya dakatar da shi yana d'ago kanshi yaga Wata babban mota ta nufosu salis yayi kokarin kaucewa amman Ina tuni motar ta fara watan gaririya akan titi.basu kara sani me ya faru ba
zucen haydar ya bude ido ganin shi yayi kwace cikin jini muryan salis yaji yana kiran sunan shi daker yaja kashi ya kalli gurin kwance yaganshi jini na bulbulowa ta cikin shi jan jiki ya fara har ya isa gaban shi ya kama hannun shi babu abun yake kira banda zahara zuwace yayi kalmar shada be kara motsawa ba haydar ya farajan shi duk da shima ajikace yake.
karan wata mota yaji yana kallon gurin yaga daddy da baba yusuf suna tahowa, gurin salis suka nufa daddy ne ya daga hannun shi yace ya innalillahi wa inna ilaihir raju,un Allah ya karbi abun saππ
πππ
[9:04PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_
πππ
πππ
πππ
πππ
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πππππ
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
*Gaisuwa da fatan alheri gare ku*
*Zainab bobbo adamawa*
*Yahancy gombe*
*bilkisu muhammad*
*xeeshata*
*mmn abdulnasir*
*hajju lokoja*
*Fatyma*
*harda wadan da bankira suna ba inajin dadin yadda kuke nuna sayayyar ku ga wannan lbr*πππ
38 - 39
Tattara su akayi gaba daya aka nufa asibiti har anas.
nan danan wannan mummunan lbr ya isa kofar gidan daddy dake cike da jama,a yan daurin aure.
itako ummi daddy ne yamata waya ya gaya mata amman be gayamata rasuwan salis ba yadaice gasu sun wuce asibiti.
hakalinta ne yayi mummunan tashi dan ta dade tana munanen mafarkai akan salis da haydar
itako fatima tun safe ta kulle kanta ad'aki tana kuka dan haka ummi tace abarta kar agaya mata abari aga abinda allah zaiyi.
haka gidan ya zama jugun kowa da abin da yake sakawa.
zuwacen daddy ya sake kiran ummi.
tana ganin kiran daddy gabanta ya fadi tana dauka tace
" alhj yaya abin da sauki kodai na taho ne kuna wanne asibiti?
" cikin jarinta irin na maza yace basai kinzo ba muma gamunan tahowa kuma nasan ke musulma ce kin yadda da kaddara mekyau da marakyau.
kuka ta fara tace alhj kardai kacemin mutuwa sukayi?
"a,a haydar yanan araye sai dai ya samu karaya acinya"
kara rushewa tayi da kuka sannan tace salis fah ?
cikin shashshekan kuka yace sai dai muyi hakuri hafsat salis ya koma ga mahalicin sa.
ummi jitayi kafafuwan ta bazasu iya daukanta ba take ta yar da wayar ta shiga fadin innalillahi wa inna ilaihir raju,in.
jin salatin da ummi keyi gaba daya hankalin mutane yadawo gurinta ummi tana kuka tana gaya musu salis ya rasu.
fatima dake kule ad'aki kunnen ta ya fara juyo mata koke koke da sauri ta bude kofar ta fito idon ta jajur bisu tayi da kallo daya bayan daya kowa afalon kuka yake.
" cikin tsawa tace menene wani abu ne ya faru?
Wata yayar ummi ce ta jawo ta jikinta nasiha ta shiga yimata sannan ta gaya mata rasuwan salis.
jitayi kamar an buga mata guduma hawaye kuwa kamar an bude fanfu cikin kuka take fadin nashiga uku na lalace meyasa yayimin haka jiya fah yace min yau tare zamu kwana shine kuma zai tafi ya barni kai ban yadda ba be mutu ba,nasan shi me cika alkawari ne.
daidai lokacin daddy ya shigo mutane ne abayan sa dauke da gawar salis d'akin ummi aka shigar dashi da sauri fatima ta kutsa ta cikin mazan ta shige d'akin ,hannu tasa ta bude fukar shi girgizashi tayi tana kuka tana fadin yaya katashi dan Allah.
daddy na tsaye abayan ta ya kasa cewa komai alhj yusuf ne ya d'agota yace fatima salis yariga ya tafi ki daina mai kuka soyayyar da zaki nunamai yanzun shine kibishi da addu,a
wani hawaye ne me dumi ya zubo mata alhj yusuf najanta tana waiwayen gawar salis.
bayan angama gyara salis aka kira ummi tamai addu,a cikin kuka tamai addu,a albarka ko tasamai babu adadi, daddy ne yace akira fatima suyi sallama.
kamota akayi dan ayanZon bata iya tafiya saitin kunen shi taje babu meji metake cewa.
daddy ne yoga abin nata bana kare bane dan haka yace afita da ita
haka sunaji suna gani aka tafi da salis gidan sa na gaskiya
fatima ko mawa d'akin su tayi ta fashe da kuka kallon hannuta tayi taga zanen fulawa wani haushine ya kamata tunani yadda zatayi ta goge lallen ta fara
dan haka ta fara buga hannun ta ajikin bango tuni kyawawan warwaro dake hannun ta suka lanlan kwashi.
dada ce tahigo taga halin da Fatima take ciki da sauri ta riketa tana fadin meye haka fatima saikace ba musulma ba, dan Allah dan darajan annabi ki dainawa bawan Allah nan kuka.
suna cikin haka salamatu mahaifiyar fatima ta shigo, fatima ta daga kai tace mama kin ga haydar ya kashe salis KO ?
cikin tsawa mama tace waye yace miki haka, kifah dai na irin wannan surutun ki kama bakin ki, haydar d'in da kike mgn shima yana cen akwance bemasa inda yake ba.
cikin kuka tace
" ai dama bazai san inda yake ba kuma da ikon Allah shima mutuwa zaiyi"
cikin zafin zuciya mama ta nufi gurin ta gadan gadan
ππ
Mmn Yazeed
πππ
[9:32PM, 3/30/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_
πππ
πππ
πππ
πππ
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πππππ
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
40 - 41
Dada ce tace haba salamatu ki rabu da yariyar nan, kisan yazon hankalinta ba jikinta yake ba dole abita ahankali.
fita mama tayi adakin dan bazata iya sauraran irin kalamen dasuke fitowa daga bakin fatima ba.
bayan sati biyu
fatima ce ita kadai agidan su ummi sun tafi duba jikin haydar dan haka ta wuce dakin su salis gurin kayan shi ta nufa gasunan jere kamar meshi yana raye tana kamshin turaren shi ke dukan hancin ta dan kaha tasaki kuka meban tausayi da sauri ta juya barayin da takalman sa suke nata kallo tana kuka
zuwacen ta farajin muryan ummi tana kiranta tashi tayi da sauri ta fito tana share hawaye
ummi da daddy ta gani tsaye afalo taslim nagefe tana share hawaye daddy ya kalli fatima yace
" me yakai ki d'akin su haydar me kike zuwa yi d'akin ?
kasa tayi dakai sannan tace bakomai tana cikin fad'a ta fashe da kuka.
daddy yace fatima dan Allah ki kwantar da hankalin ki wannan koke koken zai iya jawo miki matsala kiyi hakuri kidaina masa kuka, kuka bashi da amfani agurin mamaci addu,a yafi bukata ayanzon, fatima idan har kin cika masoyiyar shi toh karki sake mai kuka, yanzun nagama ma haydar fad'a tun da ya farfad'o bashi da aiki sai kuka yana kiran salis sai kace ba musulmi ba.
ummi tace wlh alhj ya kara tayar min da hankali sai mutuwan ta dawo min sabowa.
" ahankali fatima tace wlh ummi kukan munafunci yakeyi, bayan duk abin da ya faru shi ya jawo"
gaba dayan su binta sukayi da kallo baki sake, zuwacen ummi tace
" fatima ashe zargin haydar kk shi yasa tunda ake zuwa dubashi baki taba cewa zaki ba"
kallon ummi daddy yayi sannan yace kubar wannan maganar, ke Fatima tashi ki wuce d'aki
haka acigaba da tafiya babu wani kwanciyar hankali agidan alhj kasim fatima ta rame tayi baki duk wanda yasan ta da ya ganta yanzun bazai gane taba.
duk bayan kwana buyu ummi da taslim suke zuwa doba jikin salis kuma duk randa zasutafi sai suncewa fatima tazo su tafi amman sai tace bazata ba dan haka ummi ta farajin haushin fatima.
yauma kamar kullum su ummi sun fito cikin shirin tafiya, lokacin fatima na zaune afalo tana karatun Qur,ani taslim tace
sister dan Allah yau kizo muje ki gaida yaya haydar jiya fa sai da ya tambaye ki har yana cewa yasan kina cikin damu....
ummice ta d'akawa taslim duka abaya tace wuce muje kada Allah yasa taje ke da yake d'anwan ki ne yazama dole kije amman ita be zaman mata dole ba, sabo da makiyin tane, tana fadan haka suka fita adakin.
fatima na zaune tun bayan fitansu tana kuka domin kalaman ummi sun bata haushi woto haydar har tambayan ta yake yaji wani hali take cuci saboda yasan yasata cikin tashin hankali afili tace shega dan iska kawai.
wayarta taji tayi kara ta juya ta kalli wayar no baba ta gani da sauri ta dauka, daga cen cikin wayar baba yace maza ki fito drive ya kawoki asibiti.
dasaurin ta tace baba kaina ke ciwo bazan ...
bana son musu fatima koma me yake damunki ki fito kawai .
tana kuka ta mike tasaka hijjabin ta tayo waje
*kuyi hakuri da wannan*
ππ
Mmn Yazeed
πππ
[6:52PM, 3/31/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_
πππ
πππ
πππ
πππ
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πππππ
_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*
42 -45
Suna tafe tana kuka har suka Iso asibitin drive ne yayi mata jagora har cikin dakin da haydar yake.
daurewa kawai tayi ta shiga dan babu inda zata yi.
mutane ne cike ad'akin wasu ma bata san su ba har kakar su yadidko batace wa kowa kome ba ta tsaya cen gefe.
dadace tace Oh ikon Allah KO sallama bazaki mana ba kenan.
ahankali tace nayi fah.
yace ke bamu son shashanci wane irin tunani ne wannan ace ke har yanzo bazaki yadda da kandara ba.
ai lefin ku ne alhj da bakuci ubanta ba, wawiya kawai mara wayau mama
ce take wannan fad'a
daddy ya matsa gaban godon da haydar yake yace
" haydar ga kanwar ka tazo gaishe ka"
cikin muryar dake nuna mutun yana jigata yace wacece?
"fatima ce daddy ya fada atakai ce"
hannun shi ya fara mikowa yana fadin ina take?
mama ta jawo fatima ta kaita jikin gadon, d'agowa yayi ya kalli fuskar fatima yace
fatima kinga salis yatafi ya barmu bamu shirya ba ,a lokacin da muke tsananin bokatar sa.
idon ta akasa yake amman yana kallon hawayenta na sauka akan hijjabin ta.
shima cikin kuka ya sake cewa fatima ki daina kuka salis bazai so kukan ki ba, lokacin da abin ya faru sunan ki ne abakin shi gashi ya jigata amman sunan ki radau abakin shi yana fadi zahra zahra sai lokacin da Allah zai karbi numfashi sa sannan