Showing 3001 words to 6000 words out of 53627 words

Chapter 2 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt

Advertisement

09 Aug 2025

2003

karo da alhaji yana shigowa yace kasameshi kuwa?

cikin sauri yace a,a daddy bansame shi ba amman zuwa anjima zankara gwaawa.

4:02pm salis ya dawo gida yana ardu,a azuciyar shi Allah yasa haydar ya dawo.

afalo ya samu taslim da fatima suma kallon wani film a TV, fatima ya gani tasa wasu kaya masu kyau riga da siket na atamfa bakaramin kyau suka mata ba ya dade tsaye yana kare mata kallo suko hankalin su na wajen kallo hannun shi yasa acikin aljihun shi sannan yayi magana ahankali yace sister zahra.

dukkan su suka juyo suka kalleshi murmushi fatima tayi taslim tace yaya yaushe kashigo?

zuwa yayi dafda fatima ya zauna sannan yace zahara kinga yadda kikayi kyau kuwa.

cikin sauri taslim tace nifa yaya?

kema kinyi kyau amman zahara ta fiki kyau, tsaki yaja sannan yace haydar ya dawo kuwa.

nidai bansani ba ammafa kamar be dawowa ba.

mikewa yayi sannan yace kuje Ku shirya na kaiku kuyi gidan alhj

da gudu taslim ta tashi ta shige daki fatima ma mikewa tayi tabi bayan ta sumi sumi dan har yanzon bata gama sabawa da gidan ba.

bayan sungama shiryawa taslim tace nidai fatima ki sameni dakin yaya.

bayan fatima ta saka hijjabinta tace ummi mun tafi murmushi tayi sannan tace adawo lfy fatima.

tana fitowa falo ta hango salis kwance akan kujera idonshi rufe saidai abida ya bata mamaki kananan kayane jikinshi sun matseshi kuma daidai da takalminshi be cireba dashi ya kwanta kara matsowa tayi ta kalli shi sosai wani gashhi ne cike akan sa cibiri cibiri irin na samarin zamani tabe baki tayi sannan tace azuceyar ta toh ina taslim tayi,
gani tayi bata da mafita dole ta tasheshi wata kela ita suke jira gashi yaci uban kwalliya dan hakka ta matsa dafdashi tace yaya katashi muje nagama fah.

ahaukaci ya bude ido yakai mata tokari aciki ,cikin sauri ta duka ta rike cikin


matsowa ya Farayi yana fadin dan kutumar uban ki wacece ke dazaki zo ki tadani ina bacci.

a sittin ta mike rike da ciki tayi dakin



πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•Š
[10:00PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*



12 -14


Ummi na kwace akan gado taga fatima rike da ciki arude ta diro da kafafuwan ta tace

" fatima lfy me ya sameki aciki ?

kasa magana tayi illa kuka da ta keyi.

ummi ce ta kamota ta kwantar da ita jikinta tana rarrashinta ,ta gayamata me yasame ta

daidai lokacin salis da taslim suka shigo dakin, salis yace sister ya haka muna ta jiran ki kuma kinki fitowa,

kallonta yayi sosai yaga ashema kuka take ya sake cewa ummi me ya sameta.

nima abinda nake tambayanta kenan taki magana.

tsugunawa yayi gaban su yace sister gayamin me ya sameki?

cikin mamaki take kallon salis azuciyar ta tace lallai wannan munafiki ne wato har yaje ya cenzo kaya dan tsabar mugun ta ahankali ta dago jajayen idonta ta harare shi sannan tace

bakai bane kasa kafar ka ka naushe ni aciki.

zaro ido yayi sannan yace ni kuma ? gaskiya bani bane ,sister toh me kikamin da zan dake ki?

ummi ta kalli salis tace haydar ya dawo ne?

Ok eh ummi sanda muka fita nida taslim naga shigowan shi.

batace komai ba ta mike ta fita adakin salis ya matsa gabanta ya kamo hannun ta yana wasa da yatsuta yace kiyi hakuri, zahara bani bane kisan mu yan biyu ne kuma muna matukar kama nan gaba kad'an zaki fara banbance mu dan akwai dan banbanci,
kallon idonta yayi sannan yayi murmushi yace ban da abinki ma sister ai shigar mu ba iri daya bace shi bakiga ya tara gashi bane saikace mahaukaci.

taslim ce ta saki dariya tace wlh brother ni yanzon ma tsoro yake bani haka ranar nan daga naje wucewa ta kusa dashi lokacin yana waya saiji nayi ya jifeni da cup wai nazo naji abinda yake cewa ne naje na gayawa ummi.

salis yace ai yana da matsala haka dai zakuita hakuri dashi.

ji sukayi anturo kofar ummi na gaba haydar na bin ta abaya zuwa yayi ya tsuguna agaban fatima kamar yadda yaga salis yayi kamar me ciwon baki yayi mgn ahankali sister kiyi hakuri na manta acemin kina gidan nan na dauka wata ce daban.

shiru tayi ko kallon shi batayi ba sai dai ko ahaka ta gane banbancin murya atsakkanin su domin kuwa muryar salis tafi na haydar sanyi.

jinda yayi tayi shiru yasa ya waiga ya kalli salis yace brother katayani bata hakuri

salis yace bakumai haydar ya wuce sai dai akiyaye gaba.

sai alokacin haydar ya kalli fatima daniyar yayi mata godiya amman yana kallon fuskarta ya kasa cewa komai sakamokon muguwar kama da tayi masa da wata yariya da yake marmarin sake kasan cewa da ita

mikewa yayi cikin sauri ya nufi kofa dukkansu binshi sukayi da kallo ummi ce tace ikon allah, Allah ka shirya wannan bawa naka

salia ko mikewa yayi daga gaban fatima yana fadin toh yanzo dai shikenan haydar ya hanamu fita.


Haydar na fita ya nufi dakin mahaifin shi kamar yadda ummi ta umarceshi ahankali ya tura kofar ya shiga neman guri yayi ya zauna sannan ya daga kai ya dubi mahaifin shi dake zaune yana karatun jarida, ahankali yace


" daddy ina yuni?

baza yayi dashi kamar ma besan da shigowar shiba zuwa cen yace a inakakwana?

kanshi akasa yace daddy mun je zaria ne muna kan hanyar mu ta dawowa motar ta lalace amman dan Allah kayi hakuri bazan....

tsawa ya daka mishi wanda yasa dole yayi shiru sannan yace Karka maidani mutumin banza haydar guda nawa kake, nine ubanka babu wani dubara da zakamin, batun yauba na kula kai mutumin banza ne, toh bari kaji daga yau kar magriba ta sake maka awaje kuma daga office ban amince ka wuce ko Ina ba kanajina ?

eh kawai ya iya furtawa domin hukuncin yayi masa tsauri.

da daddare salis ne zaune adakin su yana karatun Qur,ani yayin da haydar ke kwance akan gado sai juyi ya keyi.

zuwacen salis ya rufe Qur,anin ya iso bakin gadon ya zauna sannan yace

" brother meke damun ka ne naga sai juyi kake?

tashi yayi ya zauna sannan yace kasan matsalata brother bana iya bacci ni d'aya.

murmushin takaice salis yayi sannan yace haydar al,amarin ka yana bani mamaki kai wai bakajin tsoron Allah ne, ga hanya mafi sauki kabi kaki sai anyi amma mgn kacei Allah ne ya daura maka toh naji Allah ne ya daura maka kayi aure mana, ko mata hudu ne kana iya hadawa.

hannu haydar ya dagawa salis haba wai kai sai ka rinka cewa nayi aure duka duka guda nawa nake ko 30 years ban hadaba fah.

kulewa salis yayi cikin fada yace kananufin sai mutun yakai 30 sannan zaiyi aure wani malamin ne ya fada maka?

nidai kawai ka rufamin asiri na dan fita da suba zandawo.

cikin fada salis yace wlh bazan rufama ba kana fita zan fadawa daddy

tsaki haydar yaja ya tura kanshi cikin bargo yana fadin muna fuki kawai

naji ni munafuki ne kaikuma dan iska me lalata yaran muta ne.

hankade bargon yaye ya duro ya cefkke wuyar rigar salis nan danan dabe ya kyaure atsakanin su.

ummi da yan matanta suna falo suna kallon wani film suka farajiyu hayaniyar su aguje suka nufi dakin.

salis naganin su ya tsaya cek amman haydar be daina kaimai doka ba.

ummi ce ta fara kokarin jan haydar tana cewa haydar duk yadda akayi kana shan kayan maye ka rasa dawa zakayi fada saida dan uwanka innalillahi wa ina ilaihir raju, un.

salis ne yazo ya rike ummi yana fadin ummi jeki abinki ya wuce taslim zahra kuje ku kwanta.

ummi kuka takeyi dan haka su fatima suka fara kuka.

shiko haydar sai maida numfashi yake yana hararar salis ya koma bakin gado ya zauna.

salis ko ganin ummi tana kuka hankalin shi ya tashi, yayi daya sanin biyewa haydar yace ummi dan Allah kije ki kwanta babu abinda zai sake faruwa.
suna fita haydar ya mike ya koma kujera ya zauna hannu yasa a aljihunshi ya dauko sigari ya kunna ya fara zuka yana fesar da da hayakin



πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•Š

Comment 07014197556
[10:00PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
( ta wuya ake kamashi)
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*


15 - 16


Salis tsaya wa yayi yabishi da kallo cikin mamaki yasan haydar yana shen sigari tunda yasha gani amotar shi amman betaba sha agaban shiba sai yau ,

filo ya dauka ya nufi falo dan baxai iya shakan wannnan warin ba.

washegari

salis yakai fatima makaranta secondary akasata jss 1
itako taslim tuni ta kare secondary ayanzo haka tana cigaba da karatu, dan haka kullum salis kekai fatima makaran ta drive kuma ya dakota saboda lokacin salis yana gurin aiki.

shakuwa ce tashiga tsakanin salis da fatima me karfi dan ayanzon har fatima ta saki jikin ta dashi sosai.


shiko haydar tun ranar da su kai hayaniya da salis kwata kwata baya mai maga gashi har an hada one week amman daddy yake cire takunkumin shi saima kara samai ido da yake haka kullum zaita juyin shi akan gado sai dai salis yayi tsaki ya juyamai baya dan haka abin ya fara damun shi.

yauma kamar kullum haydar ne kwance agado rike da ciki yana murkusu ya hada uban zufa.

salis ne ya taro kofar ya shigo kallon haydar yayi cikin sauri ya karasa bakin gadon yace make damunka.

daker ya iya bude baki yace cikina ne.

mikewa yayi ya nufi kofa ahankali haydar ya kirashi bayan ya dawo yace Ina zaka.

zan fadawa daddy ne.

zaro ido haydar yayi yace dan Allah karka gayamai nasha magani zuwa anjima zai sauka.

shiru salis yayi ya zauna abakin gadon ganin inda haydar yake hada zufa ya sake mikewa ya kunna mai A.C amman duk da haka zufa yake zuwa cen hawaye ya fara zubowa a idon shi hannun shi kuwa yana kasan cikin shi yana dan matsawa
zuwa cen bacci ya kwashe shi.

ajiyan zuciya salis yayi sannan ya gyara kwanciyar shi .

washegari

sunfito cikin shirin su na tafiya Office salis ya kalli haydar yace au me ciwon ciki ya cikin naka?

tsaki haydar yayi sannan yace sai yanzon zaka tambaye ni.

fashewa yayi da dariya sannan yace

" wlh brother mamaki kake mani jibeka one week kawai dobi inda kayi zuro zuro, kasan Allah kamata yayi ahada maka mata hadu dan daya ta maka kadan.

tsaki haydar yayi ya shege motar shi yabar wajen.

yana isa Office yayi amfani da wayar shi ya kira babban aminin shi anas,

ba ajima ba anas ya shigo, wata budurwa nabinshi abaya.

haydar naganin su ya miki yariyar ya rungumo yana kissing dinta itama yariyar yar duniya ce dan tuni ta fara aika mai da makata nan suka lalace.

jin nurfarfashin da haydar keyi yasa anas barin office din dan yasan idan ya zauna zasu tasomai da tsumin sa.

saida ya kwashi awa 3 yana zaune abakin office din sannan yamike ya tura kofar ya shiga ganin yariyar yayi kwance tana barci akan kujeran dake cikin office din tayi matashi da cinyar haidar shima bacci yakeyi hannun shi acikin rigarta..

hannun shi ya hada yayi tafi nan danan suka mike anas yace toh waikai yau baka da aiki ne, tsaki yaja sannan yace bar aikin nan gobe nayi, juyawa yayi ya kalli yariya yace

babyna naga alamar kin
gaji da yawa yau nabaki wahala am sorry nayi missing dinki ne dawa.

cikin shagwa tace zani gida nayi wanka na kwanta.

OK baby badamuwa anas zai maidake gida amdai gobe zaki dawo KO, saboda kar mukuma samun irin matsalar yau.

cikin shagwaba ta mike tana buga kafa kamar zatai kuka take mgn ciki ciki

haydar kara rudewa yayi dan yana balakin son yaga mace na irin wannan shagwabar bare wannan yariyar da komai dake jikinta rawa yake besan lokacin daya isa gareta ba ya zura bakinshi cikin nata saida yayi son ransa sannan yabarta.

karfe 4:00 hayadar ya baro office cike da farin da walwala domin yau ya samu abinda zuciyar shi take muradi yana shiga gida ya samu salis da fatima suta hira suna dariya.


bebi ta kansuba ya shige daki bayan yayi wanka ya biya basussukan sallah da ake binshi ya fito falo .

suna nan yadda ya barsu saidai ayanzon harda taslim, zama yayi agefe ya kure fatima da ido shi dai yana ganin kamar yasan yariyar nan, idan ma ba itabace toh sunada dankantaka tv ya kurawa ido amman lokaci zuwa lokaci yana satar kallon fatima.

zuwacen taslim tace fatima kitashi muje gidan yadidko.

salis yayi karaf yace ke bazata ba ni banason yawace yawace.

cikin sanyin murya taslin tace haba yaya gidan yadidkon ne yawace yawace kuma fa bajimawa zamuyi ba.

kalon fatima salis yayi cikin ido yace zahra kinason zuwane?

cikin sauri fatima ta dukar dakai dumin duk lokacin data kalli cikin idon salis saitaji gabanta ya fadi.

riko hannunta yayi tabi hannun shi da kallo yana wasa da yatsun yake fadin idan kinason zuwa ki tashi kuje amman karki irin shigar taslim, kisa hijjab ne kuma karku dade.

da mamaki taslim take kallon salis shima haydar shi yake kallo .

suna fita haydar yadawo dafda salis ya zauna yace

" brother kardai son yariyar nan kake?

a,a haba meka gani, kodan nace tasa hijjab dama shiyasa naga kana kallo na.

hannu haydar ya daga mai kaga malam bawani kwana kwana da zakamin ka fito fili kace sonta kake.

dariya sosai salis yayi sannan yace ni dai bance maka inasonta ba nidai kawai nasan yariyar tana birgeni kuma idan muna tare ina samun kaina cikin nishadi har inji manason mu rabu.

shine zakace bason ta kake ba wlh sonta kakeyi kuma wlh bazaka aureta ba.

murmushi yayi sannan yace tunda kaine ubana ba

mikewa haydar yayi sannan yace
sai kawai friends din na suga wannan yariyar amatsayin amaryar ka aisai sumin dariya idan bazaka iya fita ka nemo mata ba ka bari ni zannemo maka.

dariya salis yayi sannan yace ni kuma narasa wanda zai nemomin mata sai wanda ya kauce hanya

azuciye haydar ya miki daidai lokacin su fatima suka fito cikin shirin tafiya dan haka yadan tsaya.

kallon su yayi ya yamutsa baki saboda ganin su sanyi da hajjab har taslim shiko salis sai mumushi yake yace gaski kunyi kyau takawa yayi zuwa gaban fatima ya daga hannu shi daidai fuskar ta yana kokarin cire mata wani dan zare daga jikin hijjabin bayan ya cire zaran yakai bakin sa daidai kunnen ta yana mata mgn acikin taslim da haydar babu mejin me yake cemata saidai fuskarshi tana dauke da murmushi yayin da fatima ta kamo hijjab dinta ta rufe fuskarta tana dariya.

haydar ya kara kulewa kuma lallai yanason yasan me salis ya fadawa yariyar nan har take dariya, tana nufin itama tasan love ne yar kauye da ita wani dubara ne ya fado masa cikin sauri ya nufi kofa yana fadin kuzo muje nakaiku


πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
[10:00PM, 3/29/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*


*Gaisuwa ta musamman ga duk wanda yake cikin wannan group *Farfazaz novels* _kunfi ko wani group comment da nuna soyayyar ku akan wannan lbr Tsuntsu me wayo inajin dadin kasan cewa daku_ πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ˜˜


21 - 23


Zama yayi nesa da salis kanshi akasa dan duk abin shi yana tsoron daddy shi ahankali yace gani.

daddy ya dago ya kalleshi yasa hannu ya cire gilas din dake idon shi sannan yace me ya had'a ku ?

d'ago kai yayi ya kalli salis ya sake mayar da kanshi kasa yayi shiru.

ummi tace wai ba dakai ake mgn ba ne

bece komai ba kuma har yanzo kansa na kasa.

daddy yace kyale su tun da bazasu fada ba ai sunfi kusa, amman nasan haydar ne baidan gsky wata kila ka kule shi ne amman ni araina banason kuraba daki nafiso sai kunyi aure kowa ya samu abokiyar zama ko ya kuka gani?

haydar ne ya fara magana daddy ai ko munyi aure gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login