Showing 42001 words to 45000 words out of 53627 words

Chapter 15 - Tsuntsu Mai Wayo Complete Book by Fadila Lamido.txt

Advertisement

09 Aug 2025

2005

da yawa agari ya neme wata


shiru mama tayi ba dan ranta ya so ba, alhj yusuf na zaune agurin ya daga waya ya kira haydar ba,a dau lokaci ba haydar ya iso bayan ya zauna ya mika gaisuwa.

jiki babu kwari suka amsa, shiru sukayi na dan wani lokaci sannan alhj yusuf yace


" haydar kasan dalilin kiran ka?

cikin dasheshshiyar murya yace a,a.

alhj yace akan mgnr ki da fatima ne, kasan daddyn ku ya dauki zafi akan mgnr dan haka nake son na baka shawara , ko da bani bani bane mahaifin ka amman nasan zan baka shawara ka dauka, dan haka inason kayi hakuri ka rubutawa fatima ta karda , dan na kula daddyn ku ya shirya daukan matakin da idan haka ta kasan ce bazakaji dadin rayuwar ka ba, sabo da bakin iyaye da kake gani babban masifa ne.

'kasa yayi dakai ya kasa daguwa , ko motsi bayayi.

shima alhj shiru yayi zuwa cen yace haydar nasan mgn ta zatama tsauri da yawa, amman inason ka daure kayi haka din, idan Allah ya nufah zaman ku be kare ba sai kaga ta koma daga baya, kaje ka nemo ko yar waye ni zan tsaya maka ayi auren.

a hankali haydar ya dago kai, idon shi cike da hawaye yace baba wlh ni babu wata wadda nake so fatima kawai nake so dan Allah baba karka bari daddy ya rabani da ita, nasan kai ka dai ne zaka iya tsaya min, karashe mgnr yayi cikin kuka.

shiru alhj yayi yana sauraran haydar sautin kukan shi kawai kakeji.


mama ko tuni tausayin haydar ya kamata dan haka cikin sauri tabar wajen.

alhj yabita da kallo sannan ya juyar da kallon shi ga haydar yace

" kai haydar ya isa haka, ya kake yin abu saikace ba namiji ba, karna sake ganin ka kana kuka akan fatima, fatiman me, ga yan mata cen birjik agari, ko hadu kake so sai ahada maka.

ahankali haydar ya fara share hawaye zuwa cen ya mike yace na tafi.

shima alhj asanyaye yace toh ka gaida mutan gidan.

har haydar ya isa gida kuka yake yi, kai tsaye ya dakin ummi ya shiga.

ummi na ganin haydar ta dawo da baya ta zauna akan kujera sannan tace haydar dan allah ka kwantar da hankalin ka.

cikin kuka yace ummi bazan iya ba, bazan iya rayuwa babu fatima ba kuma su daddy nema suke su rabani da ita, kuka yake sosai.

hankalin ummi ya tashi ahankali tace haydar yanzon fatima tana ina?

atakaice yace gidan hajiya.

shiru tayi zuwa cen tace tashi muje gidan.




πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
[6:12PM, 4/29/2017] Fadila Lamido: _Β©Exquisite Online Writers_

πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*



85 - 87


*SLM masoya wanna lbrn Tsuntsun me wayo, kunjini shiru kwana 2, haka ya faru ne sanadin ciyon kai da nayi, nasamu sakonnin ku na gaisuwa agereni babu adadi, kuma nagode da nuna kulawar ku agareni, wannan ya nuna min kuna biye dani kuma kunajin dadin wannan lbrn😍😍😍*




Haydar ne kejan motar cikin garaje dan ya balakin kosawa su isa gida.


ummi ta bishi da kallo tace haydar kajamu ahankali garajen me kake.

bece komai ba yaci gaba da tafiya idon nan zuro zuro.

suna isa ummi ta sauka, har ta kusa shiga gidan ta waigo tace haydar kasan menene, ka zauna ka jirani na fara shiga zuwa anjima sai ka shigo.

Haka ya hakura ummi ta shiga badan ranshi yaso ba.

Lokacin da ummi tayi sallama afalon hajiya, ta hango fatima kwance akan cinyar hajiya, kibiya ce ahannun ta tana tsafewa fatima kai.

Ciki ciki hajiya ta amsa sallaman ummi fatima ko tana ganin ummi ta fara kokarin mikewa, hajiya tasa hannunta ta dan danne fatima sannan tace kwanta abin ki.

Bayan ummi ta gaida hajiya, sai shiru ya ziyarci falon.

Zuwa cen ummi taga shirun na hajiya yayi yawa, bayan tasan cewa surukar tata mutun ce me sakin fuska da wasa da dariya, amman yau tazo taga sabanin haka.


Bayan ummi ta gama tunanin ta tayi kundun bala tace


" Hajiya nazo ne akan maganar fatima da haydar"

Kan hajiya na kasa tana kokarin tajewa fatima kai, tace toh inajin ki, yaya akayi?


Tace bawani abu bane hajiya daman hakuri nazo nabaki dan Allah kiyi hakuri komai ya wuce.

Dariya hjy tayi sannan tace ashe baki da kunya haka ban sani ba, ai banzaci zakizo ki tareni da mgnr haydar da fatima ba, kokin manta lokacin da kikecewa rufawa fatima asiri haydar zaiyi, saboda kawai tsautsayi ya fada mata, yazun badan Allah ya tona mai asiri ba, nan da shekara ishirin saikin goranta mata, kuma babu abin da yafi bani mamaki duk abinda haydar yake yi baki gani, wai har kece kike bude baki kina fadin duk abun da namiji yayi ado ne, toh yaje ya karaci adon acen munan bamu bukata.


Ummi jitayi kamar kasa ta bude ta shige sai yanzon ta gane be kamata ta biyewa haydar akan duk abin da yake so ba, cikin kuka tace

" Hajiya tabbas nayi kuskure amman ina neman gafara dan Allah ki tayani bawa fatima hakuri ta yi haru ta yafemin.

Fatima dake kwance jikin hajiya ta kara matse idonta kamar me bacci.

Haydar ne yayi sallama ya shigo, be ko kqlli inda ummi take ba, kai tsaye ya wuce gaban hajiya ya tsuguna yana leka fuskar fatima, hajiya bata ce komai ba, illa binshi da kallo da take.

zuwacen ya daga hannu zaikai jikin fatima, muryar hajiya yaji tana fadin wlh ka taba yariyar nan saina barka kwance.

Ko ajikin shi hancinta ya kama yadan matsa kadan

. zabura tayi da sauri ta mike tsaye cikin dakin hajiya ta nufa tana fadin Allah ya isa.

tashi yayi zaibi bayanta sai alokacin ummi tayi magana cikin muryar da taci kuka ta koshi tace karka bita haydar , kayi wa fatima lefi yanzon neman gafarar ta ya dace kayi.

daidailo kacin hajiya yadidko ta fitoh daga kitchen rike da wata yar karamar muciya tana fadin barshi ya bita idan ka fasa ka raina uwarka mara kunya kawai fitsararre.

Juyawa yayi ya kalli fuskar ummi yasan lallai tayi kuka wani haushi ne ya taso masa ya juya ya kalli hajiya yace towai ke da kike wani shishshigewa yarkice.....
ummi ce ta daka mai tsawa sannan ta mike tace muje

Haydar na gaba ummi na binshi abaya suna kokarin fita ummi tace muntafi.

ta bude baki zatayi mgn haydar yace kuma wlh zan dawo idai baki bani Fatima ba bazan taba daina zuwa ba
na dinga sintiri kenan.


har suka koma gida haydar cike yake da haushin hjy

ummi kuwa kalaman hajiya ne suka tsaya mata amakoshi, babu abin da yafi bata mamaki wai yau fatima ce taki gaisheta har tana wani bacci dan dai kawai karta gaida ta, taslim ce ta katse mata tunanin da fadin ummi kun dawo?

Ajiyan zuciya ta sauke sannan tace mundawo taslim.

taslim ta sake cewa ina fatima ai na dauka tare zaku dawo.

Saida ummi ta share hawaye sannan tace ai fatima inaga saidai muyi hakuri domin fatima ta hada kai da hjy suna neman ganawa haydar azaba, saboda sun fahimci haydar ya kamu da son fatima, nima kaina bakiga yadda hajiya ta rufe ido tacimin mutunci ba, fatima ko,ko kallo ban isheta ba, bare nasa ran zata gaidani.

Tuni taslim ta dafah kirji tace ummi fatiman ce tamiki haka, toh ai ba dole bane saita dawo, shima yaya haydar dinne ya cika naci ya rabu da ita mana.

ummi tace ai haydar bazai iya ba yariga ya zama kamar wani wawa akan fatima, wlh tunda nake bantaba tunanin akwai yariyar da zata juya haydar haka ba, yaunzo fah ko mgnr fatima yakeyi babu wuya kiga hawayen shi.

mikewa taslim tayi tace ummi aikuwa yanzun dai dole ne ya rabu da ita .

suna cikin haka haydar shigo jiki asanyaye bayan ya zauna yace ummi wai yaushe alhaji babba zai dawo.

cikin daure fuska ummi tace

" Ni ina zan sani ai wannan saidai ka tambaye daddyn ku ko kuma alhj yusuf dan nasan ko hjy yadikko batasan sanda zai dawo ba.


Shiru yayi zuwacen yayi kwalkwal da ido yace toh ni yanzon ummi ya zanyi hakuri nafah ya fara karewa narasa ya zanyi, ummi dan Allah ki taimakeni mana.

taslim ce ta bude baki ahankali tace

" toh yaya kaima dai kayi hakuri mana ka rabu da ita, tunda tace bataso ga yanmata nan ka neme wata mana.

yadda taga haydar na kallonta ya sa tayi shiru tayi kasa dakai , mikewa yayi azuciye ya fara takowa kusa da ita, ummi ta mike da sauri ta shiga tsakiyar su, dan haka haydar ya fara fadin dan ubanki ina wasa dakene ni sa,an wasanki ne, daker ummi ta samu ta fitar dashi adakin.

Kwanci tashi babu wuya yau fatima satin ta 5 agidan hajiya yadikko haydar yayi sintiri har yagaji dan haka haydar ya koma ruwa dan yanzon hargida yake kawo yan mata, ummi tayi mgn harta gaji kuma tayi tayi dashi ya nemo wata yaki gashi duk yayi wani iri yayi baki ya rame, dan haka ta yake shawaran zatamai aure ko yana so ko baya so.


Fatima ce kwance kan gadon hajiya yadikko sai sharara bacci take, hajiya ta bita da kallo tace

" ke wai baccin nan naki na lfy ne kuwa"

mika tayi sannan tace hajiya gajiya fah nayi .

da sauri hjy tace aikin me kikayi, zakice wani kingaji, toh kitashi ga iyayenki cen sunzo.

fatima na kokarin tashi hajiya yadikko ta bita da kallo sannan tace.

fatima anya baciki gareki ba kuwa, yaushe yabon ki da al,ada?

cikin fatima ne ya bada wani tsurrrrrr saboda tsaban tsoro.

hjy ta sake cewa bada ke nake mgn ba, budemin tafin hannun ki nagani.

kara damke hannun ta tayi sannan tace hajiya dan Allah kibari, karki jamin bala,i ni bani da kome dan ko yanzon ma al,ada nakeyi




πŸ•ŠπŸ•Š
Mmn Yazeed
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
[8:25PM, 4/30/2017] Fadila Lamido: πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š
*_Tsuntsu Me Wayo_*
πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š


_Storry & written_
By
*_Fadeela Lamido_*



88 - 90



Kallon ta hjy tayi shekeke sannan tace ke karki kawomin iskanci, bafa yau aka haifeni ba, batun yau na lura ba ciki gareki.

hawaye ne ya fara zubowa fatima cikin kukan tace nifa bani da ciki haka kawai sai ki kalleni kicemin ina da ciki, ke likita ce, toh ko likita sai ya duba yake fad', karashe mgnr tayi cikin turo baki, sanan ta mike tayi falo.

daddy ta gani tare da baban ta, daddy na ganin ta ya washe baki, yace mamana yayadai ko baki da lfy ne duk sanda naxo sai hjy tace kina bacci.

yar dariya tayi sannan ta zauna tace lfy lau nagaji ne daddy, daganan ta shiga gaishe su daddy ne kadai ya amsa, amman alhj Yusuf yiyayi kamar bejita ba tare da kallon wani gefe.

hajiya ta bishi da kallo, tace waikai kana nufin fushi kake da fatima, toh ai nima saika daina mgn dani tunda nina hata komawa.

cikin sanyin murya yace toh hajiya ai wannan be kamata ba, tunda da haydar da fatima duk daya suke awajen ki, gashi nan yanzon duk kusa shi yazama wani iri duk ya bi yarame.


da sauri hajiya tace yazama tsinken sakuce ma ni babu abinda ya dame ni, aishi ya daura wa kansa fita.

daddy shiru ya musu bece kome ba zuwacen ya juya barayin fatima yace ke tashi ki kawo min ruwa.

shiru yaji kanta na bisa hannun kujera kwace.

ya sake cewa fatima dake fah nake.

nan ma shiru, hajiya ta juyar da kallonta ga fatima sannan ta mike tana fadin bari na kawo maka, ita fatima yanzon inda kasan kasa haka takoma.

zuwa cen ta dawo dauke da ruwan tana cigaba da fadin kunga wannan baccin tun asuba takeyin sa, yanzon haka ko sallar azahar batayi ba, data bude ido zata sake mayarwa.

cikin ta kaice alhj ya mike ya nufi fatima yana fadin kuma kika barta ai wannan iskanci ne ga la,asar na tahowa, daidai lokacin daya zafga mata rankwashi.

da sauri ta mike tana rike da kai take kallon su, cikin fad'a yace maza kije kiyi alwala kizo nan kiyi sallah.

wucewa tayi sumi sumi zuwacen ta fito sanye da hijjab, gefen hajiya ta shinfida sallaya, tana idarwa kuwa ta shige cikin hijjab din taci gaba da baccin ta.

wannan karon daddy ne yayi mgn yace hajiya wai waccen yariyar baccin nan nata na lfy ne kuwa, jifah saikace wata yar maye.

alhj yusuf yace kashhh kayi shiru kawai jira nake na tashi na bugata da bango.

cikin sauri hajiya tace a,a a,a karka fara, kana son kajawo mana bala,i kenan, kubarta tayi baccin ta wannan baccin nata me daliline dan ko tatama banayi ciki gareta.


shiru sukayi kowa da abinda yake sakawa zuwacen daddy yace amman hajiya ya kamata akaita asibiti dan atabbatar da haka.

hajiya ta kalli alhj yusuf tace toh ko kai zaka kaita?

da sauri ya mike yace wa, Allah ya kiyaye ai mijinta ya kamata ku kira bani ba, waje ya fito cikin shi cike da dariya, dan wannan mgnr ba karamin dadi tamai ba.

hajiya kuwa alhj na fita tabi bayan shi da harara sannan ta mike tace ni bari naje nakaita.

daddy ma mikewa yayi yace toh ki tasheta saina kaiku.

haka ko akayi suna zuwa bayan yan gwaje gwaje likitan ya shaida musu tana dauke da cikin sati 6.

ranar daddy ya koma gida cike da farin ciki wanda ya kasa boyewa, yana kokarin shiga gida ne suka hadu da haydar zai fita, ya dan rusuna ya gaida shi.

amsawa yayi sannan yawuce, abin kuwa yabawa haydar mamaki dan tunda abun nan ya faru daddy baya amsa gaisuwa shi, dan haka haydar ya shiga tatama kodai daddy be ganeshi bane dan yaga kamar arude yake.

******

ummi na zaune ita da taslim acikin dakin ummi, shiru sukayi kowanne cikin su da abinda yake sakawa itako ummi tunanin mijinta ne fal azuciyar ta, sabo da tun da abun nan ya faru baya mgn da kowa agidan sai taslim , acewar sa ita kadai ce take mishi biyayya.

itako taslim haydar ne ya hanata sakat agidan daya ganta neman dukanta yakeyi dan gani yake taslim munafuka ce bata son farin cikin shi , dan yaga almar harda ita ason ya rabu da fatima

suna cikin haka sukaga anturo kofar da sauri ummi ta kalli gurin dan zatonta haydar ne, baki ta saki tana kallon daddy shima ita yake kallo fuskar shi cike da murmushi , zama yayi bakin gadon, dan haka taslim ta gaidashi tamike ta fita cike da mamaki dan tunda take da wayon ta bata taba ganin daddy adakin ummi ba sai yau.

itako ummi dadi taji bakadan ba, amman saita dake ta buye farin cikin ta ahankali tace lfy kuwa?

d'an murmushi yayi sannan yace waike bakisan ina fushi dake bane , bazaki iya zuwa ki bani hakuri ba.

tace lefin me namaka kawai dai lefin haydar ne ya shafeni, kuma ni bani na turashi ba, kuma nima abin ai bemin dadi ba.

d'aga hannu daddy yayi sannan yace ni bawannan ne ya kawo ni ba, albishir nazo na miki.

ummi tace to ijinka.

daddy ya sake cewa amman fah zaki bani tukuici.

murmushi tayi sannan tace indai ya cenceci abaka ai sai nabaka .

saida ya cire hular dake kansa sannan yace fatima nadauke da ciki.

farinciki ne ya rufe ummi nan da nan tace alhj da gaske?

shima yana dariya yace zan miki da wasa ne, daga nan ya shiga labarta Mata yadda akayi.

tace kai naji dadin wanan lbrn anjima zan baka tukuiciπŸ™ˆ

da daddare ummi zama tayi tana jiran haydar ya dawo tamai albishir amma har bacci ya kwasheta be dawo ba.

sai 12:15 na dare ya dawo kai tsaye dakin sa ya nufah domin yu tun safe cikin sa ke ciyo kuma yasan bawani abu ke damun saba illa sha,awa dake damun sa, ko yau ya fita ne da niyar ya samu wacce zata biya mai bukata, amman ga yan matan yana gani ya kasa amfani dasu kusan yan mata 5 ne suka neme su kebe dashi, saiya tafi da niyar yayi saiya kasa, dan haka ya tattara ya dawo gida.

kwace yake yayi daidai akan makeken gadon sa dagashi sai garen wando, wani irin zafi yakeji amarar shi, murkusu yaitayi zuwa cen yaji numfashin shi na neman daukewa dan haka ya fara neman no alhj yusuf, yana dauka yace

" baba kazo ka kaini asibiti zan mutu"
abunda ya fada kenan ya kashe wayar, salis ne ya fado masa arai, dan da ace yana nan bazai galabaita haka ba, zai taima ke shi, koda kuwa ba gida daya suke ba, nan danan ya fara kuka.

bayan mintinan da bazasu wacce 30 ba alhj yusuf yazo ya dauke shi suka nufi asibiti, cike da bacin rai.

karfe 8:00 na safe suka baro asibitin alhj yusuf ne kejan motar yayin da haydar ke zaune agefen shi.

lokacin da suka kusa karasawa gidan daddy ne alhj yusuf ya tsaya ya kira no mahaifin su alhj

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login